MIJIN MATACCIYA

SHAFI NA SHIDA

by @ummishatu


 *6*



  ~~~*R* anar hutu Khalil da kansa yakai Aryan makaranta saboda tunda suka tashi daga bacci yaga alamar da rigima Aryan din yatashi dan sai wani tutturo baki yake yi breakfast ma saida lallami yasamu yaci amma da umma barira tayi tayi dashi ya zauna yaci yaki ci daga k'arshe ta kira Khalil awaya,yana kwance yana bacci yaji karar wayar landline ta cika masa kunne wacce ke ajiye saman drawer din gadonshi,dole tasa yatashi ya daga wayar domin yasan daga cikin gidan ake kiransa ko securities ko wani daga cikin jama'ar dake cikin gidan addu'ar shi dai bata wuce Allah yasa ba baki yayi ba da sanyin safiyar nan domin ko wanka baiyi ba,


Muryar umma barira yaji tana cewa,


"Mu'azzam zo kaji da wannan kinibabben yaron naka dan ni bazan iya ba nayi lallashi har nagaji yaki jin lallashina tunda kai kaine ubansa kila zaiji naka....."


Jin abinda umma barira tace yasashi yin murmushi mai dauke da sauti yasauka daga saman gadon yana kokarin zira silifas dinshi dake ajiye gaban gadon domin tana gama fadar abinda ta fada ta katse layin,


Gaban closet dinshi yaje ya tsaya yacire farar riga armless din dake jikinsa yasaka jallabiya kalar ruwan kasa sannan yafita,


A babban falo yasamesu suna drama umma barira nata tura masa soyayyen dankalin turawa wanda ya wadatu da kwai ga plantain shima agefe da wainar kwai sharba sharba amma yaki ci sannan ga tea dinshi nan a dan karamin cup dinshi,


Umma barira na ganin yashigo ta mike ta nufi cikin falon tabar dining room din tana fadin,


"Khalil wannan yaron naka dan jakar ubane ayita shan kansa amma yana sake botsarewa.....to nidai nayi nawa jeka kaima ka gwada taka sa'ar"


Murmushi Khalil yayi yana kallon Aryan wanda ke zaune saman dining yana ta turo baki,


"Ai ni dama tunda naga har yanzu bai shigo dakina ba nasan da walakin.... Bari naje na bashi abincin....."


Daga haka yawuce wurin Aryan ya zauna akusa dashi sannan ya dagashi ya dora kan cinyarsa,


"Baba na yau kuma abinci ake yiwa yaji? Uhmmm? Yau fa za abaku hutu amma banga kana murna ba.... Kana da kiwar zuwa school Aryan,nifa when i was young kamarka banyi gardamar zuwa makaranta ba..."


"Papa ni bazan ci wannan ba..."


"To me zaka ci? Fada min maza adafa maka kaci ka tafi school ka karbo report card dinka"


"Noodles...."


"To ai mai saukine bari adafa maka within 5 minutes...."


Tashi yayi yafita ya kira kuku nan da nan kafin wani lokaci ya dafa noodles din mai kunshe da vegetables aciki da kifin gwangwani sannan ga soyayyen kwai akai,


Zama yayi yabashi abaki yaci ya koshi sannan yaje ya kaishi da kansa daga nan ya juyo gida domin kamar koda yaushe yauma yana da inda zaije.


Tunda yafita bai samu dawowa ba sai misalin karfe 10 saura na dare yayi mamaki sosai da yaga wai idon Aryan biyu a wannan lokacin baiyi bacci ba,yana ganinshi ya ruga da gudu ya rungumeshi yana rike da report card dinshi a hannu,daukarshi Khalil yayi yana karbar report card din,fuskarshi ce ta fadada da murmushi da fara'a har yakai bakinshi kan goshin Aryan yayi masa kiss,


"Yaron kirki this time around baka yarda suhail ya kwace maka first position din ba?? Kayi kokari,zan yi maka duk abinda kake so kaji...me kake so?"


Kwantar da kanshi yayi jikin kafadar uban sannan ahankali yace,


"Mommy..."


"To Aryan din Daddy..."


Tare dashi sabe a kafadarshi yawuce bedroom dinshi ya ajiye shi saman gado shi kuma ya fara kokarin rage kayan jikinsa.


Bayan yayi wanka yayi shirin bacci yana zaune saman Rug da Aryan kan cinyarsa yana bacci umma barira ta kira waya tana tambayar ko suna tare da Aryan domin ta shiga dakinsa bata ganshi ba kuma baya wurinta,niyyar tsokanarta yayi yace,


"Umma baya wurina ni nan ni kadai ne"


"To sai ku bazama nemansa domin nima baya tare dani"


"Umma kenan kin ganshi nan yana bacci,hira ma muke yi yayi bacci ya barni..."


"Aima yayi kokari da har kadawo ka sameshi ido biyu shida kafin 8 wani lokacin yayi bacci amma yau ya dan taba baccin rana wuni yayi yana bacci inajin shiyasa baiyi na daren da wuri ba"


"Ai nima nayi mamakin ganin idonshi biyu lokacin da na shigo"


"Ina ruwan mai gida"


Katse wayar yayi yana dariya shi bama dan yayiwa Aryan alkawari ba da ya turasu umarah shida umma barira,babu abinda zaice da ita sai godiya domin tana tsananin kaunar gudan jininsa ko ita ta haifeshi sai haka abinda hajiya mahaifiyar shi zatayi masa shi umma barira take yimasa duk tsawon lokacin nan da ta dauka tare dasu shekara da shekaru bazai iya cewa ga laifinta ba kullum cikin tattalinsu shida yaronsa take. Cikin dakinshi yakai Aryan suka kwana tare,bayan kwana biyu da yiwa su Aryan hutun makaranta Khalil yasa umma barira ta shirya kayanta da na Aryan shima ya shirya nasa suka nufi gombe domin shima ya dauki hutu a office,tun da suka je gomben ma bai zauna ba kullum cikin karbar baki yake da yawon gaishe da yan uwa da abokan arziki,duk wasu dangin hajiyarsu da dangin abbansu sai da yaje ya gaidasu tare da yimusu rabon masu gidan rana,kwanansu uku a gombe ya dauki Aryan suka tafi jos wurin iyayen Ramlat,shi a hotel ya sauka bayan yakai Aryan gidansu Ramlat sai dai kullum yana zuwa gidan domin ya duba Aryan,harga Allah yana jin dadin irin yanda ummi kanwar Ramlat ke kula da Aryan sannan duk itace ke wahala da tiriniyar kaishi gidajen yan uwa,har gobe iyayen Ramlat basu daina kwadayin sake hadashi aure da itaba amma shi bazai taba iya auren ta ba da ace zai iya to da ya aureta ko dan kulawar da take yi da dansa. Kwanansu biyu a garin jos daga can suka wuce Calabar babban birnin jahar cross river domin ya fahimci Aryan yana son yaje yaga yan uwanshi wato yaran Khalid cousin dinshi,kwanansu daya da yini daya adaren ranar suka tashi suka nufi babban birnin new york.


Kamar yadda yasaba duk lokacin da suka tafi hutu shida Aryan yakan samu lokaci sosai ya zauna tare da yaron suyi ta hira yana bashi labaru na ban dariya da nishadi da tatsoniyoyi kala daban daban hakan ba karamin sake kara musu shakuwa da sakin jiki da kusanci yake yi da yaron ba, sannan yakan ware musu lokaci a kullum su fita su zaga gari su je wuraren shakatawa da wurin wasannin yara domin debewa Aryan kewa banda shagunan sayar da kayayyaki da yake kaishi ya siyo masa duk abinda yake so. Wannan karon ma hakance ta faru a k'asar new york,duk inda yadace yakai Aryan yakaishi sannan sun samu lokaci sosai wurin kasancewa da juna,sunsha hotuna har sun gaji dama Khalil yakan tafi da yar karamar camera saboda daukar hotunan tarihi,


Satinsu uku sannan suka fara haramar dawowa,saida suka je babban kantin sayar da kaya dake cikin birnin Khalil ya jibgo masa kayan sawa da takalma dan hatta school bag dinshi da combos da sauran kayan sawarshi duk acan yasiyo masa,


Baiyi wata tsaraba mai yawa ba sai yan abubuwan da ba arasa ba ya sissiya daga nan suka nufo gida Nigeria,a Abuja suka sauka dama tun da Khalil yace gobe zasu dawo umma barira ta shirya ta tafi Abuja dan haka can suka tarar da ita,


Daga Aryan tayi ta rungume suna dariya gaba dayansu yana sanye da dark blue din jeans da jar t shirt ta kamfanin polo sai jan takalmi shima na kamfanin polo,yanda yayi wannan shigar shima uban ita yayi sak jeans da t shirt duk irin na Aryan.


Bayan sun dawo sai da sukaje gombe suka gaida hajiya sannan suka juya aranar,ranar Monday Aryan suka koma school shi kuma Khalil yakoma office shikenan yazama busy kullum bashida hutu.


A bangaren Hanan itama ta shirya ta koma Abuja bayan hutu yakare nan kuma akaje aka fara koyar da dalibai babu kama hannun yaro duk sai ta zama busy itama saboda marking din script din dalibai kadai ya isheta shiyasa yanzu bata da lokaci sosai.


Shi kam Khalil Aryan ne ya bi duk ya dameshi da maganar mommy gashi baya samun lokaci sosai amma kullum yaron cikin maganarta yake daga karshe da yagaji sai yatura PA dinsa yace yaje ya binciko masa koma wacece wannan yarinyar da Aryan keta faman magana akanta kullum.


Cikin kwanaki biyu kacal nura yazowa da Khalil amsa lokacin Khalil din yadawo daga bauchi yana dan hutawa acikin falonsa,dan russunawa nura yayi sannan yace,


"Ranka yadade sunanta Sa'adatu mustapha mai jama'a taura,mahaifinta haifaffen garin taura ne,amma yanzu haka suna zaune acikin garin kano a unguwar sabon titi mandawari...."


Dan murmishi Khalil yayi yashafi sumar kanshi sannan yace,


"Ashema 'yarmu ce,to ai ta kwana gidan sauki,nura kana iya tafiya, nagode"


"Nabarka lafiya yallabai" daga haka yajuya yafita, murmushi Khalil yasake yi akaro na biyu yana jin dadi har can cikin kasan ransa zaiyi surprising Aryan,zai kawo masa Mommy har gida ya ajiye masa ita yayita kallonta hakan ita kadaice mafita. Acikin satin yaje har gombe yasamu hajiya da Abban London da maganar ai kuwa zo kaga murna wurin iyayen nasa musamman ma hajiya da dama tafi kowa matsuwa da damuwar rashin auren nan nasa,washe gari Abba da kansa ba sako ba yashirya ya tafi kanon dabo neman aure,


Da dafarko shi mahaifin Hanan ma yayi zaton ko batan kai akayi amma da Abba yayi masa bayani sai ya fahimta yagane ba batan kai aka yiba,nan yace yabada auren hanan ai ko da ace akwai wani to zai iya hanashi yabawa Khalil bare ma babu,shi ai Khalil nasa ne atakaice dai Abba bai baro kano ba sai da ranar auren Khalil sannan abbanta yace Khalil din yasamu lokaci yaje su gana.


Yan hidimar k'asa kuwa ana can Abuja ana hidimtawa k'asa yanda ya kamata,kullum suna mak'ale da mujahid awaya dawowarta kuwa zuwansa biyu kullum cikin maganar tabari yatura gidansu yake amma ta murje idonta tace sam ita ba yanzu ba. Wata ranar alhamis sukayi waya da abbanta nan yake cemata,


"Uwar masu gida ki daure ki samu kizo acikin weekend dinnan domin inada muhimmiyar magana dake sannan kuma zamu samu bakuncin manyan mutane"


"To Abba insha Allah gobe dama nake son tahowa"


Tunani tai tayi aranta bayan sun gama waya da abba,to ko suwaye manyan bakin da zasuyi kuma oho,ko menene dalilin da yasa Abba yace taje gida oho,ko wacce muhimmiyar magana zasuyi da yace mata zasuyi duk Allah masani amma gaba daya hankalinta yatafi gida kawai so take ta ganta acikin garin kano,aranar taje tayi yar siyayyar kayan marmari domin yin tsaraba dama anyi musu alawee tun ranar Monday,washe gari tun 7 tafita taje tayi signing sannan ta tafi tasha ta hau mota cikin lokaci k'ank'ani mota ta cika fam suka kama hanya.......✍️