MIJIN MATACCIYA

SHAFI NA BAKWAI

by @ummishatu



*7*



   ***Har motarsu ta isa kano tunani daban daban bai daina kai kawo acikin ranta ba,duk ta kasa samun nutsuwa sai tufkawa da warwarewa take ta faman yi tana son gano dalilin wannan kiran gaggawar da Abba keyi mata wanda abisa dukkan alamu akwai abinda ke faruwa ko kuma yake shirin faruwa.


Ita dai har motarsu tashiga kano ta sauka ta tare mai napep ta shiga zuwa gida zuciyarta bata daina yimata wasi wasi ba,alla alla takeyi taganta agida dan taga abinda ke faruwa shiyasa jiki a sanyaye ta shiga gidan bayan ta sallami mai napep din da ya sauketa,


Mamaye ce kadai tana kwaba fulawar da zatayi dan wanke a kofar kitchen abisa dukkan alamu shima yaya shamsu baya nan,ganin fuskar mamaye awashe sannan kuma asake alamun babu matsalar komai yasata ta danji sanyi acikin ranta,


Kayanta ta shigar cikin daki sannan ta dawo wurin mamaye suka fara gaisawa,


"Mutanen Abuja kinsha hanya kuma kun fito da wuri..."


"Ehh wallahi mamaye tun wurin 7 fa muka fito dan ni ko karyawa ma banyi ba"


"To ai akwai ruwan zafi a flask sai kije kihada shayi kisha"


"To bari insha abisa lalura amma shan shayi da rana ai sai ahankali"


Daga haka ta tashi tawuce falo ta hado tea ta dauko bread ta sake dawowa wurin mamaye. Sai la'asar sannan abbba yadawo lokacin suna zaune da mamaye da yaya shamsu suna hira,


Wurin Abba taje suka gaisa sannan suka dan taba hira kadan har zata tashi abba ya dakatar da ita,


"Uwar masu gida sai kuma kikaji kira ko?"


"Ehh Abba dama nima ina son inzo gidan inganku ai"


"To wani abokina ne kuma aminina ya nemi wata alfarma awurina wadda nikuma bazan iya kin yimasa itaba,ya bukaci inbashi aurenki nikuma bazan iya hanashi ba...."


Jin abinda Abba yace yasata zaro ido tare da jin firgici gamida gagarumar faduwar gaba,bata san lokacin da tace,


"Abba abokin ka?"


"Ehh uwar masu gida... abokina amma nasan insha Allah zaki sameshi kamar yadda kike so,zaki ji dadin kasancewar shi mijinki, matarsa ce ta mutu a lokacin haihuwa,dansu daya kacal wanda ta mutu ta bari...."


Kamar wacce aka zarewa laka ajikinta haka taji bata san lokacin da hawaye ya ziraro ta idanuwanta ba,


"Abba kuma shine da kansa yaganni yace yana sona?"


"Shine Hanan,shi yaganki anan Abuja,acan yake da zama minister ne,shine ministern yada labarai,matasa,raya al'adu da wasanni,yanemi da inbashi aurenki kuma na bashi nan da sati uku za adaura muku aure,sai kije kifara shirye shiryen da duk ya kamata.... Allah yayi miki albarka"


Bata iya cewa komai ba ta tashi tafita idanuwanta cike da hawaye tausayin kanta da kuma mujahid take yi,yanzu me zata cewa mujahid? Da wacce kalma zata dosheshi har tayi masa bayani? Da wacce kalma yadace tayi amfani wurin sanar dashi wannan bakin labari?


Daga mamaye har yaya shamsu babu wanda tayiwa magana tawuce daki taje ta kwanta tasoma shakar kuka,duk tsawon shekarun da suka dauka tare da mujahid bata taba jin sonshi ba sai yau da taji zata rasashi,wata zazzafar soyayyar shi take jin tana shigarta babu k'akk'autawa,


Tajima tana kuka kafin mamaye tashigo ta zauna gefenta tasoma bata baki,


"Hanan kiyi shiru wannan kukan baida wani amfani,kiyi shiru ki mika al'amuranki ga Allah ki nemi alkhairinsa da kuma albarka acikin aurenki...."


Kamar jira take tasake fashewa da wani hargitsattsen kuka mai tsayawa arai,


"Mamaye abokin Abba ne fa wai,wai abokin Abba,mamaye yanzu ni anyi min adalci kenan idan aka aura min wannan mutumin? Mutumin da ya haifi yani? Mutumin da yafara ban kwana da duniya yana kusantar kabari,inama laifin abani zabi idan ina sonshi a aura min idan bana so abarni amma sai kawai ayi min dole ayanke hukunci batare da anji ra'ayina ba...."


"Ki daina fadin haka Hanan,iyaye sunada damar zabawa yaransu mazaje hakan bai saba ka'idar musulunci ba,kiyiwa mahaifinki biyayya sannan kiyi addu'a insha Allah bazaki tabe ba"


"Mamaye nidai har ga Allah bana sonshi, tayaya zan auri sa'an babana? Abokin Abba fa,sa'an abba ne fa mamaye, yanzu Abba yarasa wanda zai aura min sai abokin sa?"


"To ni me kikeso inyi akai Hanan? Yariga da ya yanke hukunci,aikin gama yagama, k'addara tariga fata sai dai kawai kidau hakuri kiyita addu'a, Allah ya zaba miki abinda yafi alkhairi a rayuwarki"


Daga haka mamaye ta tashi tafita tabarta tana ta faman gursheken kuka kamar ranta zai fita,


Wannan wacce irin k'addara ce? Ita mema yakaita Abuja yin service gashi nan mutum yaganta yazama silar rushewar farin cikinta, duk yanmatan Abuja yarasa wacce yagani yake so sai ita? Dan dai kawai yana da kudi sai yarinka amfani da damarsa yana taka duk wanda yaso? Insha Allah sai Allah yasaka mata,ita dai tasan Abba bawai kudi yabi ba wurin aurar da ita ga wannan bawan Allah,koda yake yace abokinsa ne watakila wannan shine dalilin da yasa ya bayar da ita batare da yajira yaji ra'ayinta ba.


Wayarta ta dauka tana share hawayen dake zuba daga idanuwanta tana face hancinta da tissue,text massage ta turawa mujahid kamar haka,


_Ban taba sanin cewa bakaine abokin rayuwa ta ba sai yanzu da k'addara ta gifta,ashe ba Kaine mijina ba shiyasa kayita bina akan zaka turo gidanmu amma naki gashi yanzu Abba ya bayar dani ga abokinsa,ya zanyi mujahid? Wallahi ina tsananin sonka musamman ma yanzu da ake neman rabamu._


Ai tunda mujahid yaga massage dinta hankalinsa shima yabar jikinsa,jiki yana rawa yakirata,shiru yayi yana sauraren sautin kukanta da yacika kunnuwanshi,


Daga shi har ita sun kasa cewa komai ita sai kuka takeyi murya adashe,


Cikin sanyin murya mai kunshe da damuwa yace,


"Hanan kiyi shiru....kiyi hakuri ki daina kuka kinji,ni nafi cancanta da inyi kuka bake ba domin wallahi ko tantama banayi soyayyar da nake yimiki ta ninka wacce kike yimin.... Ina sonki fiyeda tunaninki,kullum da sonki nake kwana nake tashi...."


"Mujahid tsohone fa,wai minister ne a Abuja, Abba baiyi min adalci ba,abokinsa fa zai aura min"


"Hanan ina son ganinki,yaushe zan ganki?"


"Mujahid sai dai mu hadu agidan anty salaha kaga bazai yuyu kazo nanba Abba yaganka,idan nafita zan kiraka"


"Shikenan babu matsala amma ki daina kuka kinji"


Shiru tayi ta katse wayar amma maganar ta daina kuka kam tasan abune wanda bama zai taba yuyuwa ba, ai dole tayi kuka rabuwa da masoyi sai dole bawai dan ana so ba, mujahid ako ina zata kirashi masoyinta domin yana tsananin kaunarta kamar ita kadaice macen da tayi saura a duniya,


Kuka kam tayi shi ta kara har tagaji, zuciyarta koda yaushe cikin kunci take da radadi Allah ya isa kuwa tayiwa abokin Abba tafi sau dubu domin shine mutum na farko da yafara yunkurin rabata da farin cikinta,


Washe gari ta tashi da niyyar zuwa gidan anty salaha amma Abba yace babu inda zataje tajira saboda zatayi bako domin yau angon yace zaizo su gana,tamkar zata fashe haka tazama saboda tsabar cikar da tayi.


***


 Tunda ya fadawa Aryan cewa nanda 3 weeks zai kawo masa Mommyn shi yaron ke cikin farin ciki marar misaltuwa,


Dadi ne ya lullube zuciyar Khalil sosai saboda ganin Aryan cikin farin ciki,aranar ya shirya yatafi gombe yaje yaga Abba suka tattauna akan yanda abubuwan zasu kasance anan Abba kece masa sai yasamu lokaci yashirya yaje su gana da yarinyar,yadai ansawa Abba da toh amma harga Allah ba zuwa zaiyi ba shi ina yaga wani lokacin zuwa zance wurin budurwa yanzu? Acikin ayyukan sa wanne zai tsallake yatafi hira? Duk ma ba wannan ba shifa auren nan kawai zaiyi shine saboda Aryan bawai saboda kansa ba shi idan dan ta shine shida aure sai dai yaga anayi amma ayanzu kam babu macen da ta isa,


Maimakon yaje sai kawai yatura PA dinsa yaje yaga Hanan sannan yakai mata sako,


Lokacin da nura PA yaje Hanan a murtuke taje ta sameshi a dakin saukar baki dake kofar gida,motar ma da yazo da ita kawai abar kallo ce saboda kyanta da tsaruwarta,duk azotanta akwai ubban gayyar sai taga sai iya mutum daya,


Dan russunawa nura yayi sannan yace,


"Ranki yadade barka da fitowa,ayi mana afuwa yallabai bai samu damar zuwa ba da tare zamu zo dashi to sai kuma meeting na gaggawa ya sameshi,amma duk da haka ga sako yabayar inkawo miki...."


Envelope ya ajiye mata da wata babbar leda,


"Babu komai.." shine kadai abinda tace bayan yagama rattabo mata bayanin. Daga haka yamike da niyyar tafiya domin tuni dama tun kafin fitowarta yaci snacks da drinks din da aka tanadar masa,


"Amm yawwa sannan yace idan kina bukatar ganin hotonshi sai in......"


Tun kafin ya karasa ta dakatar dashi,


"Bana bukata...."


Mamaki ne ya addabi ruhin nura PA ita kuwa wannan yarinyar ya take kokarin yin sakarkaba? Ya take kokarin yiwa kanta asara? Ita da Allah yayi mata gam da katar da kabakin arziki ya zabota cikin dubban mata amma shine take nema ta butulce?


Saka takalmansa yayi sannan yasake dan russunawa,


"Na barki lafiya ranki yadade"


"Nagode,ka gaida gida"


Fita nura yayi babu jimawa itama ta tashi tafita batare da ta dauki kayan da nura ya ajiye mata ba sai yaya shamsu ne lokacin da yashiga ya fito mata dasu yabita cikin gida ya kai mata,


Tana daga kwance cikin daki tajiyo muryar abba yana cewa,


"Uwar masu gida kina ina? Inbanda shirmenki uwata kuma akawo miki kaya ki taho ki baraso acan? Ai sai ki dauka ki duba haka akeyi"


Fita tayi ta saka hannu biyu ta karbi kayan awurin Abba sannan tajuya takoma daki zuciyarta nayi mata wani irin tukuki........................✍️