MIJIN MATACCIYA

SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA

by @ummishatu

11*




   ***Zuwan Dr Al'amin yasashi fitowa daga cikin bedroom dinshi zuwa falo inda yake zaune yana jiransa,


Fitowarsa ta sa Dr Al'amin mikewa tsaye dan girmamawa,kan daya daga kujerun dake kawace afalon yasamu guda daya ya zauna,


"Dr ciwon ciki ke damuna tun bayan dawowata gida..."


"Ayya Allah yabada lafiya yallabai amma yau me da me kaci?"


"Da safe tea kadai nasha sai dazu da naje gombe shine naci zogale da tuwo dan kadan...."


"To ai ranka yadade ga inda matsalar take nan,dan abubuwan da kaci dinne suka dan ruda maka cikin naka gashi dama bai saba ba"


"Wallahi duk ya takura min gashi bacci nake son inyi"


"Babu damuwa Allah yakara lafiya bari yanzu inbaka magungunan da zaka sha insha Allah zaka samu bacci..."


Lumshe idanuwanshi yayi ya dan kishingida jikin kujerar yana sauraren Dr Al'amin, sai da yagama hada mishi magungunan sannan yatafi,


Cikin bedroom yakoma bayan tafiyar Dr yayi shirin bacci ta hanyar saka gajeren wando na bacci sannan ya dauko robar ruwa guda daya daga cikin bedside fridge dinshi,zama yayi yasha maganin da Dr yabashisannan ya kwanta yana lumshe idanuwanshi cike da bege da kuma tunanin Ramlat, Allah sarki Ramlat Allah dai yasa tana gidan aljannah,shi kam yasan shima har yakoma ga mahaliccinsa bazai iya mantawa da Ramlat ba kullum da tunanin ta yake kwana yake tashi.


***


 Duk da tana cikin damuwa sai dai yau bacin ranta ya ragu da damuwar ta amma fa duk da haka dai sai ahankali yanayin nata,


Karfe 8 nasafe ta kammala shirinta tsaf na komawa Abuja sai kuma satin biki sannan zata dawo,


Dakin Abba taje tayi masa sallama nan yasake dan yimata nasiha sannan yasaka mata albarka ta taso tafito, sallama tayi dasu mamaye yaya shamsu ya rakata tashiga napep zuwa tasha inda zata shiga mota,


Tun tana cikin napep din sukayi waya da mujahid kan cewa zasu hadu a tasha inda zata shiga mota,tana zuwa shima babu jimawa sai gashi ya karaso cikin motarshi,


Karasawa tayi wurinshi ta bude gaban motar ta shiga tana dan harararshi,take away din dake ajiye seat din baya ya dauko ya mika mata saboda dama yasan bata ci abinci ba,


"Good morning my love,gashi kici...."


Dan makale kafada tayi sannan ta kawar da kanta saida ya dan yimata magiya sannan ta yarda ta karba koda ta buda dankali da kwai tagani nan tafara ci mujahid na sake kwantar mata da hankali yana cemata insha Allah akwai matakin da zai dauka yana nan yana shirinsa a boye ita kanta zata sha mamaki, wadannan kalaman nasa ne suka sake sakawa zuciyarta nutsuwa har taci abincin da yakawo mata da yawa dan kadan ta rage yabata ruwa tasha,5k yabata wai tayi kudin mota amma dakyar ta karba daga nan ya rakata mota sukayi sallama dan tuni motarsu ta cika.


Agajiye lis ta isa dan karamin d'akinta dake quarters din malamai,salla kawai tayi ta dafa noodles ta kwanta domin ta huta wanda ba ita ta tashi ba sai la'asar lis wannan dinma wayarsu hajara ce ta tada ita bayan ta dauka suke cemata wai zaman wuri dayane ya ishesu yau suna son su kawo mata ziyara,


Tashi tayi tai wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atamfa sannan ta dora musu abinci kafin su karaso,


Tana shirin sauke sphagettee jalop din da ta dafa mai dauke da kifin gwangwani su hajara suka karaso,sunyi murnar ganin juna sosai saboda rabonsu da haduwa tun ranar clearance na wancan watan dan wannan watanma basu haduba saboda ba rana daya sukayi ba,


Har magriba suna tare amma sam bata sanar dasu cewa za ayi mata aureba. Sha'anin gabanta kawai takeyi dan koda anty salaha ma ta kirata akan maganar gyaran da sauran abubuwan gyara da ake yiwa amarya cewa tayi bata so,anty salaha kuwa tace to ko bata so ita zata yimata inyaso ta zubar,


"Ai kuwa wallahi zan zubar,inma anyi auren kenan" tafada cikin kunkuni,anty salaha na jinta amma dai bata yi magana ba kawai sai ta kashe wayarta,


Agefe guda kuma mujahid naci gaba da bata tabbaccin sai maganar aurenta da minister ta rushe,sai yahana wannan auren indai yana raye to baza ayishi ba sai dai afasa da minister shi ayi dashi wadannan kalaman nasa ne ke sakawa zuciyarta cikakkiyar nutsuwa da farin ciki shiyasa take abinta gaba gadi,kallon kowa take yanda gida suka dauki abin da muhimmanci gashi komai akayi sai yaya shamsu ko anty sun kira sun fada mata dan ko dazu saida anty ta kirata wai za akawo lefenta gobe gasu agida sai aikin nama suke yi amma snacks sun bada kwangila sun biya ayi musu,


Baki ta tabe aranta tace sayi sa gama aure dai ba yinsa za ayiba kamar yadda mujahid ya saba sanar da ita kuma wani sharri na Shaidan ayanzu kusan kullum sai sunyi waya da mujahid fiye da sau biyar sabanin da wanda ada idan ya kirata ma ganin nacinsa take yi amma yanzu ko bai kirata ba ita tana kiransa saboda wani sonshi ne kullum ke kara shigarta.


Kamar yadda anty salaha ke sanar da ita ankawo kaya kuma anyi bajinta anyi rawar gani kowa yaga wannan kayan yasan babu karya ankashe masu gidan rana dan har da kudin dinki dubu dari, kuma gashi biki ya matso dan haka yakamata ta dawo gida tazo ayi abinda yadace,


Kuka ta fara yi ta kira mujahid tana fada masa abinda ke faruwa nan yace mata babu komai tayi yanda suka ce din hakan bazai basu matsala ba, hutu taje ta rubuta har na tsawon sati uku domin bikin saura sati daya da kwanaki biyu,


Kamar wacce idan ta tafi ta tafi kenan haka ta harhada kan kayanta tsaf washe gari ta nufi kano.


Bayan ta koma gida aboye suke haduwa da mujahid suna yin hira yana sake kwantar mata da hankali,tun ranar da ta koma kuma anty salaha tafara kawo mata kayan gyara irin na amare amma bata sha sai dai ta faki ido ta zubar,gaba daya gidan shirin biki akeyi ganga ganga bugu da kari ansake gyare gidansu tsaf yasha fenti yasha gyara na musamman.

***

 Duk shirye shiryen da can gida gombe ke faman yi shi kuwa mai gayya mai aiki wato ango yana nan Abuja yana harkokinsa domin ayyuka sun sakoshi gaba bashi can bashi nan kullum cikin yawon ayyuka yake bashi da kwakkwaran lokacin kansa kullum da garin da zaije banda yawon taruka da bude ayyuka da yake halarta,


A gaggauce yake fitowa daga tamfatsetsen dakinshi hannunshi rike da agogon azurfa na Rolex yasha skye blue din shadda mai tsada da kyau,


Yana tafe yana kokarin daura agogon sukayi kicibus da Aryan wanda ke sanye cikin kayan shan iska kasancewar weekend ne babu school,


Rungumeshi ya ida yi sannan ya daga kai yana kallonshi,


"Papa...... Zan bika wurin mommy"


Murmushi yayi ya daga shi sama ya rikeshi yana kissing din face dinshi,


"Good morning my lovely son...., Waye yace maka wurin mommy zanje? Zanje lokoja ne fa,ba gombe zanje ba"


Makale kafada Aryan yayi ya sake rikeshi kamar zaiyi kuka,


"Zan bika Daddy,ni ka kaini wurin mommy,hajiya tace ankusa kawota nan"


Kan dining ya nufa dasu yana murmushi wallahi shi har mantawa yakeyi da wani batun auren nan saboda sam bashine agabansa ba shi sabgogin gabansa ma sun isheshi domin yawa garesu wanda idan har ba mai cikakkiyar lafiya kamarsa ba to mutum bazai iyaba shi dinma da yake da lafiyar ya aka kare stress da zama babu cin abinci kusan koda yaushe cikin kara masa drip ake shiyasa amafi yawan lokuta yafi danganta wannan mukamin nasa da wahala,


Zama yayi saman kujera ya dora Aryan akan glass table din yana kallon shi,


"Aryan kabari inje lokoja indawo zanzo indaukeka muje gombe din but yanzu ka zauna gida kaga anjima kadan lesson teacher dinka zaizo..."


Bata fuska Aryan yayi yasoma murtsuka ido,


Dakyar yasamu ya lallasheshi yakaishi wurin umma barira sannan yafita ta kofar baya.


A lissafinsa ma shi baza ayi bikin nan yana k'asar ba domin zai tafi kasar Spain shida yan wasan kwallon kwando inda za aje akara wasan kuma yana son ya halarta domin yana da muhimmin abinda zai gabatar acan,sai dai yana shakkar sanar da hajiya duk da harka ce ta aiki watakila tayi fada tace dan me zai tafi bayan gashi bikinsa za ayi, addu'ar sa dai Allah yasa kar tayi fadan.


Aranar saida yaje gombe kuma basu tafi da wuriba dan ko lokojan da yaje bai dawo ba sai karfe biyar na yamma,suna zuwa Abuja suka dauki Aryan suka wuce,


Koda sukaje gombe tuni yaga shirye shirye sunyi nisa domin ita hajiya da gaske ta dauki lamarin bada wasa ba shiyasa yayi ta fargabar sanar da ita tafiyar da zaiyi daga karshe dai yaja bakinsa yayi shiru ya zabi yasanar da ita daga baya ta waya,


Sai bayan karfe tara sannan suka baro gombe lokacin tuni Aryan yajima da yin bacci ajikinsa, PA dake gaban mota yayiwa magana,


"Gobe in Allah yakaimu zan aikeka kano,hajiya tace aje akaiwa yarinyar nan kudin menene wai ita da friends dinta...."


"To yallabai Allah yakaimu"


Shiru yayi bai kara cewa komai ba sai tunani fal da yasoma zagaye ilahirin kwanyarsa.


***


 Amarya Hanan kam tana cike da damuwa duk da mujahid kullum na sake bata kwarin gwiwar cewa aurenta ba tabbatacce bane dan haka ta kwantar da hankalinta tajira taga abinda zai faru,


Duk da idan taji yafadi haka takan ji ranta yayi sanyi amma hakan baya hanata shiga damuwa da jin faduwar gaba mai tsanani akoda yaushe,


Yau tunda sassafe taji abba na barwa mamaye sallahun wai ta fada mata zatayi bako,ranta bakikkkirin ta wuni tana jiran taga wannan bakon da zaizo tunda tasan dai bai wuce tsohon banzan nan wato angon.


Wurin misalin karfe 2 na rana nura PA yazo,ranta ahade kamar kullum taje bayan sun gaisa yazaro envelope yabata yana cewa,


"Ranki yadade gashi inji yallabai saboda yan hidindimun da zakuyi keda kawayenki, sannan yace idan kuna bukatar wani abu sai ki sanar dashi"


Karba tayi fuska ahade tace,


"Bama bukatar komai kawai dai kafada masa inada bukatar yaje asibiti yayi gwajin cutar HIV,sai yabada result din akawo min...."


Jin abinda tace yabawa nura PA mamaki amma baice komai ba kuma gaskiya bazai iya fadin wannan sakon nata ba dan yayi masa mutukar nauyi,tayaya zaije yafadawa uban gidansa haka? Dan russunawa yayi sannan yace,


"Ai ina ganin ranki yadade gara dai kawai ki fada masa da kanki ko ta waya ne saboda ni din ba lallai nasamu ganinsa ba"


"Ok to ni zan fada masa"


Daga haka tajuya takoma cikin gida tana kunkuni,kudi ne cikin envelope din da yabata har kimanin dubu dari yan dubu dubu sabbi fil ita tama yi mamakin ta yadda akayi kudin yashiga cikin envelope din,


Aranar anty salaha tasa aka fara yimata gyaran jiki wanda Hanan bawai ason ranta bane amma ko ba komai dai za agyara mata fatarta duk da auren bamai yuyuwa bane. Mujahid ke kaita gidan gyaran jikin sannan ya daukota yadawo da ita gida,tayi tayi dashi akan ya sanar da ita plan dinshi amma yaki kullum sai dai yace mata kawai ta zuba ido zata sha kallo,


K'unshi da saloon ma da kin yi tayi sai da mujahid ya lallabata shine ma yakaita kuma yajira ta har ta gama sannan yadawo da ita gida lokacin bikin yarage saura kwana biyu. 


Kamar yadda nura PA yace mata ta fada da kanta da kan nata kuwa ta fada dan sako ta turawa gogan tana rubutawa tana tsaki aranta tana cewa,


"Ance shekararsa wurin 9 babu mace wai tunda matarsa ta mutu,to waye yasan abinda yake aikatawa tunda da kudinsa gashi a Abuja yake zaune babu dangin iya bare na baba, watakila ma a hotel yake yin gaba daya weekend dinshi,kai may be ma bazai rasa karuwar da ya ajiye ba za ma ta iya yuyuwa baturiya ce"


Ita kadai taketa wadannan maganganun har ta tura masa text din sannan ta ajiye wayar ta tashi tafita tsakar gida inda take jiyo hayaniyar su anty salaha wadanda keta aiki.


***


 Kamar yadda ya shirya sai ana igobe zai tafi k'asar Spain sannan ya sanarwa da hajiya ai kuwa tafara fada tana cewa to kuma auren nasa fa? Taya zasu yarda su bashi aure adaura babu ango? 


"Hajiya "yar abokina ce fa yarinyar,kuma wallahi wannan tafiyar dole sai dani za ayita shiyasa"


Jin abinda yace yasa hajiya sakin ajiyar zuciya sannan cikin mamaki ta furta,


"Yarku mu'azzam? 'yarku fa? To ai shikenan"


"Yawwa hajjaju adai yimin addu'a da fatan alkhairin da aka saba"


Addu'a tai tayi masa sannan sukayi sallama,katse wayar yayi yana murmushi acikin ransa kuma yana cewa,


"Ga inda nasarata take, addu'ar hajiya itace take zame min jagora adukkan nasarorin da nake samu cikin rayuwata"


Yana kokarin tashi daga office kuma sakon marar kunyar nan yashigo kamar yadda yake kiranta domin tuni ya rada mata wannan sunan acewarsa bata da kunya ko kadan,dubawa yayi aransa yana cewa yau kuma dame tazo?


_Ina bukatar HIV test result dinka before adaura aure._


Tsaki yaja yamike daga kan kujerarshi yana danna kararrawar dake kan teburinshi alamar yana kiran masinjanshi sannan cikin sanyin murya yana fadin,


"Wannan yarinyar baki da hankali,you are very stupid"


Saida yabar office sannan yatura mata da reply _'Ok'_ shine kadai abinda yatura mata saboda baida lokacinta shi idanma bata saniba to da asuba zai bar k'asar baida lokacin zuwa yayi wani HIV test sai dai kar subashi auren,


Toma wai yarinyar nan me take nufine da sai yayi HIV test? Ko suna tsammanin shi mazinaci ne? Mtswwww tsaki yaja daga nan bai kara bi ta kanta ba har yabar kasar.


Ayau itace ranar da za adaura auren Ibrahim Sulaiman Ibrahim da Sa'adatu mustapha mai jama'a daurin auren da yatara manya manyan yan siyasa da masu rikeda manya manyan mukamai na k'asar Nigeria,


Amarya acike take famm sakamakon wayar mujahid da taketa kira bata samuba duk da kusan kwana sukayi suna waya daren jiya tana ta bashi labarin wulakancin da minister yayi mata wai tace yayi HIV test yaki yayi yace mata kawai ok,ita wallahi bata sonshi ita mujahid take so kuma kowa haushinta yakeji ana cewa ga arziki Allah yakawo mata har gida amma ta runtse ido,arziki na binta tana gudu.


K'arfe 11 na rana ake son adaura auren da tuni ma andaura ana jiran waliyyin ango yakaraso ne wato Alhaji Idris kanwa tsohon gwamnan jihar gombe,dama Abban London tuni yajima da karasowa shida tawagarsa,


Zuwan waliyyin ango yayi daidai da isowar mujahid wanda yacaba ado tamkar shine angon tare da zugar abokansa dake take masa baya..........✍️