SHAFI NA GOMA SHA BIYU
by @ummishatu
*12*
***Wata zazzakar guda ta jiyo babu k'akk'autawa wata mata wacce Allah yabaiwa baiwar hanci ta dage sai rangada ta take yi kamar anyi mata bishara da kujerar hajji ko ta umarah kafin daga bisani tafara jiyo maroka suna faman yin kirari,tsam ta dakata daga kokarin saka sarkar da take yi awuyanta,
"Ayyiriyiriyiriiiiiiiiiiiii....... Aure ya kullu,amarya Sa'adatu rai yakaiki..... Allah yasa gidan zamanki ne..... Ayyiririiiiiiiii" Matar da keta faman rangada guda agufi agufi tafada tana sake bude makogaro wurin rero wata gudar, sake saurarawa tayi dakyau har tana mika kunne domin jiyo abinda marokan nan ke fadi,
" _Sa'adatu sa'ar mata, Sa'adatu mai sa'a babu shakka kin tako sa'a da auren baya goya marayu dan mulki kuma jinin sarauta, yagaji arziki da sarauta dan na gada ba dan na koya ba, wato Alhaji Ibrahim Khalil ga kudi ga mulki... Ina amarya Sa'adatu,kifito kibani kyautar mota da kujerar hajji amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida...._"
Ai bata iya karasa jin karshen kirarin da marokan nan ke zuba mata ba jikinta yahau rawa wanda har kyakkyawar sarkar hannunta na neman sulmiyewa,anty badi'a yar gidan yayar mamaye itace tayi gaggawar riketa sannan ta rike sarkar tasoma kokarin saka mata,
Ita anty badi'a duk azatonta rudewar Hanan akan an daura auren ne bata san ita jin sunan wanda aka daura auren dashine ya rudata ba saboda taji ana ambaton wani daban sabanin mujahid. Hawaye ne suka shiga wanke mata fuska babu k'akk'autawa kamar anballe bakin fanfo,
Jin shigowar anty salaha yasata juyawa tana tambayar ta domin zuciyarta na fada mata kamar fa kunnenta karya yayi mata bai jiyo mata daidai ba,
"Anty dawa aka daura auren? Da mujahid?"
Wani kallo anty salaha ta watsa mata sannan ta fusge hannunta tana harararta,
"Waye wani mujahid? Dama ya kawo miki kayan aure ne? Mtswww" Daga haka anty salaha ta dauki abinda zata dauka tayi waje tabarsu ita da anty badi'a wacce ke faman rarrashinta amma ina hawayen dake kwaranya daga idanuwanta sun kasa tsayawa, tambayar kanta take faman yi to ina plan din da mujahid keta ikirarin ya hada? To kodai plan din baiyi aiki ba? Inama zata farka taga acikin mafarki take,inama inama....!!! Wani kukan ta sake fashewa dashi ta fada saman gado ahaka aka aiko kiranta,tashi tayi tafita tana sanye da wani dandatsetsen leshi baki mai adon pink ajiki yasha manyan stones wadanda suka kara haskashi kuma suka fito da tsadarsa fili,pink din takalmi ne akafarta wacce tasha lallen amare ja da baki,kai gaskiya ba dan wannan yanayin da take ciki ba da ita kanta sai ta yabawa kanta da kanta saboda tsabar haduwar da tayi. Su Abba tasamu zaune da kaninsa baba mahe nan suka zaunarta suka yimata nasiha akan tayiwa mijinta biyayya sannan kuma ga sadakinta nan har naira dubu dari,da wani kukan ta sake fita ai kuwa cincirindon matan dake tsakar gidan suka hau guda suna fadin,
"Ke kikace kina so da bakice kina so ba da ba abaki shi ba...."
Ko takansu bata bi ba tawuce daki tana matsar kwalla ita yanzu gaba daya tarasa me zata kira wannan abun,wai mujahid meya faru ne da har plan dinsa yarushe? Tasan inbanda mujahid din babu wanda zai iya bata amsar wannan tambayar tata gashi ita yanzu ma kwata kwata bata san inda wayarta take ba,
Zama tayi gefen gado taci gaba da kukanta,kowa yazaci kukan rabuwa da gida take yi amma ita kadai tasan dalilin kukanta,dakyar anty badi'a takawo mata maltina da madara tasata agaba tasha saboda yau bata ci abinci ba. Bayan misalin karfe 3 aka gama shirya amarya tsaff inda za atafi garin gombe da ita ta can kuma za awuce da ita gidan mijinta dake garin Abuja,
Zaid ne ke jan tsadaddiyar motar da amaryar ke ciki ita da iyaye wadanda zasu rakata sai faman sharbar kuka take ta cikin mayafin dake lullube da ita,
Daf da magriba suka shiga garin gombe ita dai bata iya gane komai amma tana jiyo hayaniyar jama'a wacce daga ji tasan suna da yawa sannan tana ta jiyo kade kade da raye raye gamida bushe bushe, fuskarta a rufe aka shiga da ita sashen uwar ango wato hajiya Zaitun wacce ke hakimce afalo ita da wasu hamshakan mata wadanda akalla zasu kai su biyar zuwa shida,biyu daga ciki matan Abban London ne daya kuma matar Alhaji Idris kanwa ce sai yakumbo da anty saudat banda wasu matan da yanmata dake biye dasu sai faman daukarsu ake yi awaya,
Gaban hajiya Zaitun aka kaita ta zauna nan hajiya Zaitun din ta kama hannayenta wadanda suka kawatu da lalle ta rike tana saka mata albarka tare da addu'ar samun zaman lafiya mai dorewa agidan aurenta, daga bisani kuma aka gudanar da addu'o'i bayan anshafa hajiya Zaitun tace akai amarya ta huta taci abinci tayi wanka bayan tayi salla domin ta sha hanya ta gaji tana bukatar hutu inyaso gobe sai atafi da ita dakinta. Hakan akayi yakumbo ta kamata zuwa wani daki marar tarukuce ciki domin iya wani kantamemen gado ne kadai aciki sai mirrior da bedside drawers shikenan sai carpet dake shimfide gaban gadon amma fa ba karya dakin ya hadu yayi kyau fiye da hasashen mai hasashe,
Sai bayan da yakumbo tafita sannan anty salaha da anty badi'a suka shigo dauke da dan madaidaicin akwatin kayanta,
Salla ta farayi sannan suka zuba mata abinci shinkafa da chicken pepe soup,ita dai dakyar ta daure ta dan ci abincin wannan dinma saboda tana gudun fadan anty salaha ne domin tasan matsawar bata ci ba to sai anyi fadan da aka saba,
Tana jinsu ita da anty badi'a sai faman yaba karamci da dattako irin na surukan nata suke yi suna cewa tayi dace tayi sa'a Allah ya zabeta yabata abinda ba kowacce mace ce zata samuba wato miji na kwarai da danginsa na arziki masu sonta da mutuntata,ita dai jinsu kawai take yi bata cewa komai amma can kasan ranta wani irin tafarfasa zuciyarta keyi alla alla take taji daga mujahid tana son jin abinda yafaru har hakan ta kasance. Sai bayan da tayi wanka ta shirya cikin jar night gown mai santsi tasha humra da turare kai kace angon yana nan wannan kuma duk aikin anty badi'a ne wai ko ango baya nan ai gara ta kasance cikin kamshi,
Saman gado ta haye zata kwanta anty badi'a ta kalleta,
"Ke Hanan bafa kwanciya zakiyi ba kinaji, lecture zamu yimiki yanzun nan dan gobe iyanzu kina dakin miji..."
"Kibarta badi'a,saura kije ki samu wuri ki yita kwasar bacci babu kula da miji,mijinki dai kinga ba yaro bane da hankalinsa kuma saboda tsabar son da yake yiwa matarsa ance tunda ta rasu baiyi aure ba anbishi anyi anyi dashi akan yayi aure amma yaki dan haka idan har kikaje kika tsaya kallon ruwa wallahi kwado ne zaiyi miki kafa tunda shikam already da kudinsa kara aure ba wuya zaiyi masa ba..."
"Kwarai kuwa maganar salaha na kan hanya,ki zauna ki nutsu ki koyi dabaru da salo na rikon miji yarinya wallahi aure babu abinda yafishi dadi mutukar akayi dace da abokin zama na gari,maza na son macen da ta iya kula dasu wacce zata rungumesu ta rarrashesu kamar baby,suna son mai kunya mai girmama su da mutuntasu amma fa bance kije kiyi masa dinkim a master bedroom ba,acan zagewa zakiyi kifito a yar bariki sak kima fishi rashin ta ido kin gane? Yanzu dama nasan baza ki iya hakanba saboda rashin sabo da kuma kunya amma ahankali ahankali kina sakin jiki dashi kina sake samun wayewa aharkar dan wasu abubuwan ma shi zai koya miki to daga nan fa kema sai kifara naki salon tunda anriga da anzama daya babu kuma sauran kunya..... Inbaki wasu sirrika akan maza? To bude kunnenki dakyau kiji yarinya"
Nanfa anty badi'a tafara farfada mata abubuwan da yadace ta rinka yimasa wadanda maza keso ita wallahi duk sunsa kunya ta kamata gashi ma ita hankalinta ba awurinsu yakeba kadan kadan dai take jinsu amma gaba daya tunaninta yatafi ga mujahid su kam babu maganar kunya bare boye boye sai fada mata abubuwan da yadace tasani suke yi musamman ma anty badi'a wacce ta takarkare tana yimata dalla dalla yadda yadace ta kula da shinfidar mijinta da yadda yadace ta sarrafashi a wannan lokacin daga karshe ta rufe da yimata bayanin irin kulawar da zata bashi a lokacin da take yin period domin mata da yawa na daukar last position a wannan yanayin,lumshe idanuwanta ita dai tayi wani bayanin tana jinsa yayinda wani kuma bata ji,
"Yar kare kike wani sissinne kai kina rufe idanuwa nan da yan wasu kwanaki zamuji ki difff da zarar kin shige gidan miji...." Inji anty badi'a wacce ta dan daki kafadarta kadan,
"Ke kyale asara,kuma irinsu sunfi zakalkalewa ba" Anty salaha tafada tana sake kishingida,ita dai bakam tayi tana jinsu sunata sake karawa maganganun nasu haske ta yadda zata fahimta sosai ahaka akayi knocking anty saudat tashigo,duk kallonsu yakoma kanta,baka ce siririya doguwa sosai tana sanye cikin material pink colour,
"Manyan yayu ataimaka abar mana amaryar mu ta huta haka tasamu dan bacci inji hajiya,ga dakinku can inda zaku kwanta"
Ai wani sanyi Hanan taji jin zasu fita su barta ita kadai,
"To ba matsala muje,amarya ga wayarki may be zaku dan taba hirar dare da ango kar mu tauye muku hakki...." Anty badi'a ce tayi wannan maganar sannan ta fito mata da wayarta ta mika mata,sake tukunkune fuska tayi saboda bata son anty saudat dake tsaye bakin kofa taganta.
Tattarawa sukayi gaba daya suka fita suka barta nan ta duba wayarta jikinta har wani tsuma yake saboda yanda take hanzarin taba wayar,miss called sama da guda 15 tagani sai massages guda biyar bata bi ta kan massages din da miss called din ba tafara kiran layin mujahid amma duka akashe,ji tayi kamar ta fashe da kuka amma babu hali sakamakon wani dunkulen abu mai kamada curin karago da yazo ya tsaya mata a kirji ya tokare mata makoshi,
Miss calls din tabi ta duba kusan fin rabi kiransa ne sai na sauran abokan arziki wanda bata tsaya bi ta kansu ba, massages takoma dubawa nan taga sakon bank guda daya anturo mata alawee sai sakon minister shima guda daya sauran kuwa duk sakon mujahid ne,
Na mujahid din tabi tafara karantawa daya bayan daya gaba daya jikinta sai yayi mata sanyi tamkar bata da sauran laka ajikinta wai ashe duk abubuwan da mujahid yajima yana fada mata gaba daya zirata yayi akwali yarufe wai dama wallahi baida niyyar yin wani abu dan yahana aurenta da minister kawai yayi hakane dan ya kwantar mata da hankali amma kamar yadda yafada mata abaya shi mai taimaka mata ne dari bisa dari tayiwa iyayenta biyayya bazai taba goyon bayanta wurin bujirewa umarnin iyayenta ba saboda soyayyar gaskiya yake yimata kuma har gobe yana sonta,ayau dashi aka daura auren ta domin ya halarta kuma yayi musu addu'a ita da mijinta Allah yabasu zaman lafiya dan Allah tayiwa mijinta biyayya fiyeda yadda taso yiwa shi mujahid din sannan ta sani ko gobe aurenta ya mutu wanda baya yimata fatan haka ashirye yake da ya aureta yakaita gidansa domin yana sonta har gaban abada,
Wadannan kalaman nasa sune suka kashe mata duk wata kafar laka dake jikinta sannan kuma suka tsayar da tunaninta cak na dan wani lokaci tabbas abunda mujahid yayi abune da yadace ta yaba masa kuma taji dadi amma kasancewar akwai Shaidan sai taji samm hakan bai burgeta ba ita wani haushi ne ma ya turnuketa dan me mujahid zai yaudare ta yamayar da ita karamar yarinya wacce bata san ciwon kanta ba? Wallahi da tun farko tasan wannan tuggun yake hada mata da tuni ta samarwa kanta mafita amma dan mugunta bai sanar da itaba sai a kurarren lokaci, lokacin da bata da matakin dauka,
Sakon minister ta bude tana jin kwalla na ciko mata ido wanda sai lokacin hawayen suka samu zarafin fitowa,
_Kamar yadda na fada miki zan kafa miki dokoki akan yarona,nafarko ba a dukan min yaro,ba a zaginsa,ba a yimasa tsawa sannan duk abinda yake so abashi,kuma ki sani ko harararshi kikayi zai sanar dani._
Ganin abinda yaturo mata yasata wurgi da wayar can karshen gado amma dai Allah yaso bata kai ga faduwa kasa ba,fashewa tayi da kuka aranta tana cewa wannan shine inuwa zafi rana kuma k'una........✍️