MIJIN MATACCIYA

SHAFI NA GOMA SHA UKU

by @ummishatu



*13*



   ***Kwana tayi tana kuka sam bacci baiga idonta ba, abubuwa biyu ke sakata kuka abinda mujahid yayi mata da kuma abinda minister yafada mata dagaske dai raino zataje tayi masa na yaro,kaico,kaiconta inama iyayenta sun san manufar wannan auren nata,inama sun san abinda ke lullube da wallahi tasan ko za ayi kuli kulin kubra dasu bazasu yarda ayi wannan aurenba amma da yake wasu mutanen Allah yahore musu baiwar iya tsara mugunta da cuta shine aka rufi kura da fatar akuya aka yiwa iyayenta ungulu da kan zabo su sunata murna yarsu ta auri babban mutum basu san nan kuwa a matsayin yar raino ta fito ba,ai kuwa minister zaisha mamaki domin zata saka kafafunta duka biyu tayi kolin kolin fatali da wadannan sharrud'an nasa inyaso idan yaji haushi ya korata gida.


Da bacin rai da bakin ciki ta wayi gari wanda ko diss bata samu bacci ba,wanka tayi bayan tayi salla wanda su anty salaha ne suka tilastata bayan sun shigo cikin dakin,humrah masu sanyin kamshi da jan hankali suka shasshafa mata sannan tasaka kaya wadanda suma suka sha turare na daukar hankali,


Doguwar riga zuwa gwiwa tasaka da zaninta duka na atamfa orange and blue colour bayan sun gama shiryata tasaka su sarka da dan kunne akayi knocking a kofa aka shigo yanmata ne guda uku wato mufida da Sarah da Zarah kowaccensu dauke da madaidaitan warmers masu kyau iri daya,kasa kasa take kallon yanmatan wadanda daga gani kasan jin dadi da hutu sun jima da samun muhallin zama a jukkunansu,


Kayan breakfast ne suka kawo musu sannan suka gaggaishesu sai kallonta suke suna dan magana kasa kasa shiyasa taji duk sun isheta domin ta tsani kallo,kamar sun san abinda ke cikin ranta suka tashi suka fita.


Abincin karyawa ne na gani a na fada domin farfesun koda ne da soyayyar agada sai wainar kwai fal sannan ga wainar shinkafa itama da zuma ga kuma kayan tea da ruwan zafi agefe abinci dai kaca kaca gashi nan sai wanda ka zaba ita kam ruwan tea din kadai ta iya sha sai da anty salaha suka bude mata wuta sannan tasamu ta danci farfesun kuma suka tilasta mata saida tasha romon tass,sake gyara mata jikinta sukayi suka nada mata lafaya suka fita zuwa dakin hajiya Zaitun,


Ita ma taci ado Sosai cikin wani leshi, kama Hanan tayi ta rungume tana dan shafa bayanta ahankali take yimata magana,


"Barka da zuwa cikinmu Sa'adatu,lale marhabun dake,kinyi dace da miji mai biyayya ga iyayensa bawai dan nina haifeshi ba a'a sai dan kawai halinsa ne,ko kai ka haifi mutum halinsa shi zaka fada,ki zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya duk abinda yayi miki wanda ba daidai ba ki sanar dani,tsawon shekaru kusan bakwai kenan rabonshi da mace tunda matarsa ta mutu wurin haihuwar yaronsa shikenan bai kara aure ba nayi nayi amma baiyi ba sai yanzu bagatatan yazo min da maganar ki kuma gashi da yake Allah ya kulla anyi, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka....." Wadannan sune kalaman mahaifiyar sa wanda harda kwalla take yi lokacin da take fada mata domin duk da fuskarta arufe take amma tana fuskantar komai kuma tana jin lokacin da matar Yakumbo ke cewa,


"Haba hajiya kema kukan zakiyi Khalil din da ba shine auta ba......."


Sun dan jima awurin hajiya sannan akace sufita domin tafiya Abuja,kamar jiya yauma zaid ke jan motar da take ciki tun daga garin gombe har Abuja wanda tafiyar awanni kadance ta kaisu,tana jin anyi parking gabanta ya tsinke ya fadi,


Da addu'a abakinta ta taka tashiga da k'afar dama wadda iyaye keta nanata mata wadanda ke tare da ita, Masha Allah, Masha Allah,shine abinda kunnuwanta keta jiye mata lokacin da suka shiga gidan gashi babu laifi tafiya taki karewa abisa dukkan alamu gidan da zurfi dan harda su hawa bene taji anyi daga bisani aka danyi yar tafiya taji anbude wani daki sun shiga wanda sanyi da kamshi ya cikashi kai gaba daya cikin gidanma sanyi da kamshi ne acikinsa dan tunda suka shigo taji yana shigarta,abakin wani luntsumemen gado taji an zaunar da ita kan wata hadaddiyar katifa mai sifrin tamkar kahau irin gadon nan na da irin na karfen nan wanda zakaji yana tsalle dakai,


Har lokacin bata bude fuskarta ba tana jin lokacin da su anty badi'a suka shigo anty badi'a tazo kusa da ita ta zauna cikin rada take cemata,


"Wallahi yarinya kin more da gida, aljannar duniya,kinga gidanki kuwa Hanan? Wallahi girman wajen nan ya isa mata hudu su zauna basu takura ba, Allah yasa rabonki ne yasa gidan zamanki ne har abada, Allah yasa mutuwa ce kadai zata raba..... Ai tun dazu muna kasa muna ta santin wannan aljannar duniyar, Masha Allah wallahi gidanki ko a London iyakaci kenan sannan gaki ga Villa...."


Ai Hanan ji tayi kamar ta dora hannu aka saboda takaicin wadannan addu'o'in na anty badi'a danme zata rinka yimata addu'ar kare rayuwarta a wannan gidan da yafi kurkuku tsanani agareta babu kunya bare tsoron Allah aranta ta rinka cewa, "Ba amin ba"


Tana tukunkune atakure har saida dakin yarage daga ita sai su anty salaha sannan ta bude fuskarta,tamkar amafarki tajita lokacin da tayi ido hudu da dakin da ake kira da mallakinta bata san lokacin da ta furta,


"Masha Allah" 


Ba kadan ba taga dakin yayi bala'in haduwa gashi tangamemen gaske duk kayan ciki dark purple ne masu dan sirki sirkin haske ko ina sai sheki yake magana ta gaskiya bata taba cin karo da furnitures makamantan wadannan ba wurin kyau da haduwa, sunkuyar da kanta tayi saboda bata son su gane dakin take kallo tabari har sai sun tafi sai ta bude idonta ta kashe kwarkwatar idonta dakyau gida kamar akasar turai?.


Saida suka ci abinci sukayi sallar azahar sannan yan kawo amarya aka fara haramar tafiya nanfa Hanan tace bata san zance ba domin zama tayi ta rinka rusar kuka ahaka suka tafi suka barta, kwanciya tayi saman gadonta tana cigaba da kukanta cike da kunar rai har tayi tagaji tunda babu mai rarrashinta dan abisa dukkan alamu ma ita kadai ce agidan sai ko ma'aikata domin bata ji motsin ko kare ba duk da cewa ma gidan yana da girma da fadi ko da ace akwai wani ciki ba lallai kasani ba indai bawai yashigo side din da kake bane,ita kam ko tantama batayi tasan ita kadaice cikin wannan katon gidan domin dazu lokacin da suna kan hanya tana ji zaid yana waya da wani wanda bata san ko wanene ba yana cewa wai su umma barira da Aryan na tsohon gida ita amarya yanzu sabon gida za akaita amma suma su umma barira din nanda anjima ko gobe za akawo su sabon gida basu karasa parking din kayan su bane. Saida tayi kukanta ta gaji dan kanta sannan ta tashi da niyyar yin alwala domin la'asar ta kusa zaman dirshan tayi tana bin d'akinta da kallo wanda ya amsa sunan aljannar duniya, mai karatu Hanan bata san ta inda yadace tafara kwatanta muku haduwar da d'akin baccinta yayi ba domin komai yajine ba karya komai yadace da muhallin da aka ajiyeshi tun daga kan labulayenta gadonta wardrobe dinta,da komai dake cikin dakin sannan daga can dan gaba kadan da gadonta wasu hadaddun kujeru ne guda uku suma dark purple an dan yi circle dasu an ajiye glass table a center sai wurin yabada ma'ana tamkar dai aturai sannan ga wurin sallarta nan an tanada ga katuwar tv ta bango da dan karamin fridge kawai dai komai yaji ne fa,sauka tayi ahankali da niyyar zuwa toilet nan ta tsaya yin wani kallon domin shi kansa bathroom din nata da glasses aka zagaye shi marassa duhu sai dai ba lallai ne ka iya hango mutum ba idan yana ciki amma ta yuyu zaka iya ganoshi tsaff,kamar mai shirin daukar kwai haka takama kofar bathroom din ta tura ahankali tashiga,bandaki kamar wani filin shakatawa? Ta fadi hakan aranta domin shima an kawatashi an shiryashi sannan anzuba daula acikinsa kamar ba wurin wanka da fitsari ba,irin haduwar da bathroom dinnan yayi fadarshi bata bakine yahadu fiye da duk yanda zaka kissimashi cikin ranka,ita dai gidansu ba hamshakan masu kudi bane shiyasa sai da tabi komai asannu gudun kada tayi barna domin wasu abubuwan ma yaune tafara ganinsu haka dai ta lallaba tayi alwalar tafito tazo ta bude wardrobe ta ciro hijabi daga cikin jakunkunanta wanda su anty salaha suka saka mata cikin wardrobe dinta dazu.


Rasa wacce irin addu'ar da zatayi tayi saboda ita dai bata son zaman gidan nan ko kadan bare tayi addu'ar Allah ya tabbatar da ita agidan,daga karshe dai sai kawai ta roki Allah da ya zaba mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta,


Saman gado taje ta hau ta kwanta domin bata san abinda zatayi ba ayanzu juyi kawai tashiga yi tana ta tunanin rayuwa wai yau itace acikin wannan gidan wanda ko acikin mafarkin ta bata taba mafarko gida makamancinsa ba a tarihin rayuwarta,duk da gidan ya cancanci akirashi da aljannar duniya ita kam bata yiwa kanta fatan tabbata acikinsa, nasihar Abban ta ce ta fado mata inda yake cewa,


"Hanan ki yiwa mijinki biyayya kibishi sau da k'afa ban yadda kiyi ko musu dashi ba sannan ban amince miki kiyi koda yaji ba bare ki nemi saki a hannunshi,kada naji kuma kada nagani,duk ranar da kika zo gidan nan da sunan yaji to ba zamu kwashe dakyau ba,mijinki shine aljannarki domin tana karkashin kafarsa ne dan haka kiyi masa biyayya iya iyawarki daidai gwargwadon yanda zaki iya..... Allah yayi miki albarka"


Wasu tagwayen hawaye ne suka zubo mata sakamakon tuno wannan nasihar ta abbanta da tayi,to wai ita yanzu ta ina yadace tafara ne? Wanne irin zama zatayi a wannan gida? Wanne irin zama zatayi da abokin mahaifinta? Wacce irin rayuwa zatayi da dansa da sauran jama'ar da ke rayuwa cikin wannan gida? Menene makomar rayuwarta? Wadanne irin kalubale ke jiran rayuwarta saboda auren babban mutum da tayi shin zai dauke mata dukkanin bukatunta ko kuwa zai yi watsi da lammuranta? Wadannan tambayoyin sune keta circulating acikin kwakwalwarta wanda ta gagara bawa kanta amsa............✍️