KULUWA SHAFI NA FARKO
by @zeeyabour20
KULUWA
NA ZEE YABOUR
DA SADIYA NASIR DAN
SHAFI NA FARKO
Garin yayi sanyi da ni'imtaccen iska kasancewar lokaci ne na damina, shukoki koraye da bishiyoyi ne zagaye da wurin wanda suke kada iska mai daɗi. Zaune take kan ɗaya daga cikin duwatsun dake bakin tekun ƙafafunta cikin ruwa, hannayenta ta ware su tana ɗibar ruwan tana ɗan watsawa tana wakokinta na dandali. wuri ne da take samun natsuwa da nishadi da son keɓewa don babu hayaniyar mutane, mafi akasarin lokuta nan take zuwa ta zauna musamman lokutan damuna tana shak'ar iska mai daɗi da sanyaya zuciya.
Hadarin da ya soma gauraye sararin samaniya garin ya fara duhu ya sata zame ƙafafunta daga cikin ruwan, Tana gyara babban ɗan kwalinta ta ware sa ya sauka saman kafadarta, Ta tashi tsaye tana ɗaga manyan idanunta tana kallon sararin samaniya, ganin hadari ya haɗu sosai ruwa na gaf da sauka yasa tayi murmushi ta furta "Allah ka bamu damina mai albarka". Tayi addu'ar a zuciyarta, tana sauke idonta ƙasa.
a hankali take tafiya cikin natsuwa kanta sunkuye ƙasa bata son cin karo da samarin ƙauyen nasu masu kallon fitina, idan suka zuba maka ido tamkar zaka faɗi ƙasa, Kaf yan' matan kauyen babu wacce tayi farin jini irin nata saboda baiwar kyau da surar jiki da Allah ya bata, Yan' mata da yawa k'auyen nasu haushinta suke ji suna ganin tamkar ta hana tauraronsu haskawa, Kuluwa yarinya ce natsattsiya waccce magana mai tsayi ma gagararta take, ba zaka taɓa jin abokin fadan ta ba, yana da matukar wahala kaga ta zauna tana hira, gata da zurfin ciki duk kusancin ku ba zaka ji sirrin ta ba.
Gungun samarin da ta ci karo dasu gaf da shiga gidan su yasata k'ara saurin tafiyarta har kafafunta na hardewa kiris ta faɗi. "Tafi a hankali Kuluwa kada ki mana asarar kyakkyawar surar ki". Ko daga bacci ta tashi tasan me muryar yadda ta haddace amon maganar sa tamkar yadda sunanta ya zauna rad'au a kwakwalwarta, har ta shige Iro yana bin ta da kallo abokinsa ya tab'o sa yace "Haba Iro wannan kallo ai ya wuce na musulunci". Bakinsa ya d'an lasa kadan yace "Wato kuluwa wallahi ta haɗu ne ba zaka fahimta ba, yarinya kamar ba tashin kauye ba, ka duba yadda komai nata yake zaune cif-cif, ga haskenta kamar na larabawa". Tasi'u tsaki yayi yace "Ka dai rage zalamar ka wallahi, kaga kowa ya watse muma mu tafi kafin saukar ruwan nan". Iro ya mike zuciyarsa na sake kwadaita masa KULUWA.
Gida ne ginin kasa wanda kofar sa sak'a ce take da asabari, ko ba'a fad'a maka ba kasan mamallakin gidan talaka ne, don idan ba talaka ba ko kofa ce ta langa langa zai sakawa kofar sa don rufin asirinsu. Kuluwa ta d'aga asabarin ta shiga gidan nasu a nutse, A tsakar gida ta tarar da iyayen nata suna zaune kan tabarmar kara, daga yanayin fuskokin su zaka fahimci akwai damuwa tattare dasu, Damuwar d'aya ce ko ba'a fada ba ta babun da suke ciki ne, Tana fatan Allah ya warwarewa mahaifin nata ya biya bashin da suke kansa, dan babun sa tasa yasa ya zama mai masifar cin bashi, ɗaidaikun ranaku ne ba za'a zo gidan nasu da zancen ya biya bashi ba, wasu daga waje suke tsayawa wasu kuwa kai tsaye zasu faɗo ciki kan ya basu hakk'in su, haka zai ta rok'on su kan su k'ara basa lokaci wanda mafi akasari sai sun juye masa rashin mutunci suke tafiya, Ko ba'a faɗa ba tasan yau ma cikin masu bin mahaifin nata bashi ne wani yazo, Cikin sanyi jiki ta gaishe su, Suka amsa tare, Malam Garbati yace "Kuluwa bakya jin tsoron jejin nan da kike zuwa?". Murmushi tayi tace "Babu tsoro Malam". Dan haka suke kiran sa, Yana kallonta yace "Toh shikenan, Allah yai albarka ya tsare mana ke". Cikin ladabi kamar yadda ta saba tace "Amin Malam". Ta shige k'aramin ɗakinta wanda babu komai cikin sa sai k'ullin kayanta da tabarma, tun tashinta bata taɓa ganin katifa a gidan nasu ba, wani lokaci har mamakin talauci take irin na mahaifinta sai dai takan danganta hakan da tsari ne na ubangiji, shi ke azurta wanda yaso a lokacin da yaso, ita kadai iyayenta suka haifa, sun jima kafin su samu haihuwa, daga kanta kuma basu kara haihuwa ba, hakan yasa iyayen nata ke kaunar ta sosai duk da basu da arzikin da zasu wadatar da ita na abubuwan more rayuwa, amma kauna da kulawar da suke nuna mata yana sakata farin ciki sosai da jin cewar tayi sa'ar iyaye, ko gefen tarbiyarta sun tsaya tsayin daka wurin ganin sun bata tarbiya mai kyau. KULUWA yarinya ce mai son karatu da ilimi hakan yasa bata wasa da zuwa makaranta islamiyya suna samu karatu sab'anin boko da makarantun gwamnati ba ilimin kirki ake koyar da yara ba, hakanan take zuwa tana fahimtar iya abunda ake koya musu, yanzu har ta kai Js3.
Kishingid'a tai kan tabarmarta, ruwa ne ya tsuge tamkar da bakin k'warya ta lumshe idonta tana jin sautin saukar ruwan ta fara karanta addu'ar "Allahumma sayyiban nafi'an".
Umma Habiba ce ta kalli mijinta cike da damuwar halin da suke ciki tace "Mutumin nan da yazo yau ina tsoron ya ɗauki hukuncin da yace zai ɗauka akan ka matuk'ar baka basa kud'in sa nan da kwana biyu ba". Malam Garbati damuwa k'arara kan fuskarsa wacce tsufa ta bayyana a kanta har ta zarta na shekarunsa, tsabar wahala ce, babu da rashin kwanciyar hankali yasa tsufan da ba kai ba ya taso masa, Yace "Ban taɓa shiga damuwar bashi irin ta yau ba, dan na tabbatar ba zai ɗaga mun k'afa ba kamar yadda ya shaidamin dole na nemo kud'insa na basa". Umma Habiba ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa tace "A ina zaka samu kai da ba wata sana'a ba balle kace zaka iya had'a masa kud'in sa a kwana biyu? ba kuma wani abu ne da kai ba da zaka iya siyarwa". Shiru Malam Garbati yayi damuwarsa na k'aruwa yasan bashi da wata mafita, baisan inda zai nemo kud'in dubu goma ya biya ba, shi bashin da suke kansa sun fi k'arfin sa, Allah kad'ai ne zai warware masa, Gashi yau ko tukunya basu d'aura gidan ba saboda babu, garin rogo da gyad'a suka sha da safe. Shiru ya ratsa tsakurkuren d'akin nasu da babu komai ciki sai tabarmar saƙa da shirgin kayansu, ba mai cewa komai, sai addu'a da kowannensu ke yi a zuci.
KULUWA cikinta taji ya d'an murd'a alamun yunwa, garin rogon kad'an tasha d'azu, dama ita ba gwanar cin abinci ba ce, shiyasa rashin nasu bai taɓa ta sosai ba ko ya nuna a jikin ta, sai dai tana zuwa taya wata mata dake abincin siyarwa bakin tasha aiki, ta bata abinci wanda shi take kawowa lokuta da dama suci a gida, ko iyayen nata sunce taci ita kad'ai bata yarda sai dai suci tare, Yau jejin da taje ya hana mata zuwa,
Ana gaf da magrib ruwan ya tsagaita, Ta mik'e ta fito tsakar gida ta d’auki butar k’arfe ta d’ibi ruwa a cikin dorum da suke tara ruwa wanda tsufan sa yasa har ya fara tsatsa ta k’asa, Ta duk’a tana alwala, Malam Garbati shima ya fito yai alwala ya fita masallacin bakin gidan nasu.
Umma Habiba ta kalli yarinyar tata cike da tausayin yadda ta taso cikin rashin gata da babu tace "KULUWA kiyi hak'uri da irin rayuwar da kika taso cikinta, nasan dole kina jin yunwa tunda bakije gun Lantana mai abinci ba". Duk da k'ananun shekarunta dan a yanzu ne take cikin shekaru sha biyar amma tana da hankali da zurfin tunani murmushi tayi tace "Umma meyasa zan damu akan tsarin Ubangiji shine yaso ganinmu a haka, ba wayo ko dabararku ba ce, na tabbatar da kuna da hali ba zaku tab'a bari na cikin yunwa ba, kuma ni bana ma jin yunwa". Umma Habiba tana kallon Kuluwa tace "Nagode ma Allah da ya bani ke Kuluwa yarinya mai hankali da hangen nesa Allah ya miki albarka ya baki miji nagari". Kuluwa maganar Umma ta k'arshe yasa ta kasa cewa "Amin".
Sai alwala da ta cigaba, ta kammala ta shige d'akin ta.
Malam Garbati bayan ya idar da sallah a masallaci ya zauna sai anyi isha'i kamar yadda ya saba, in dai ya fita sallar magrib sai anyi ishai yake dawowa gida, Yana zaune gefe d'aya hannun sa rik'e da charbi yana lazimi gaba d'aya tunanin sa inda zai samu kud'in da zai biya bashi, rayuwar ta masa d'aurin goro masifar bashi tasa ya sake rasa natsuwar sa baki d'aya.
****************
Hayaniyar da take jiyowa daga waje ya saka tai zumb'ur ta tashi, Tare da jan wani numfashi tana fatan Allah yasa lafiya, Hijabin da tayi sallah yana jikinta ta fito k'aramin tsakar gidan nasu wanda yake fes, kullum Kuluwa sai ta share sa, duk da rashin da suke ciki hakan bai hana musu tsaftace muhallinsu ba, Umma Habiba ta gani itama ta fito da alamar damuwa kan fuskarta,
"Malam Garbati iya hak'uri na maka, bashi tsawon wata bakwai amma shiru ko tashin zance to gaskiya hak'urina ya k'are". KULUWA baya ta d'an yi tana jingina da garu, damuwa ta mamaye zuciya da fuskarta, na jin yanzu ma kan bashi aka zo gun mahaifin nata, Malam Garbati cikin sanyin murya da kwantar da kai yace "Dan girman Allah DanLadi ka k'ara bani lokaci wallahi ko ficika bani da ita, yau gidana ko tukunya ba'a d'aura ba". Tsaki DanLadi yaja yana masa mugun kallo yace "Kai Garbati na gaji da jin zantukan ka, talauci dai ba kanka aka fara ba da zaka dinga cin bashin mutane baka biya, kaf fad'in garin nan kowa ya maka shaidar cin bashi, dan haka kwana uku na baka wallahi idan baka biyani ba zaka ga me zai biyo baya". Malam Garbati yana k'ok'arin basa baki bai tsaya sauraren sa ba Ya wuce yana masifa,
Hannu yasa ya dafa goshin sa, Yau sai yake ganin abun ma tamkar had'in baki yadda DanLadi da Habu suka zo kan cewar dole ya basu kud'insu a kwanaki kad'an ko su d'auki hukunci, K'odadd'iyar rigar shadda dake jikinsa wacce duk taji jiki ya jawo ya goge gumin da ya karyo masa kan goshi duk da sanyi na garin amma tashin hankali ya saka shi yin gumi, Yasa kai ya shiga cikin gidan sa mai rashin wadataccen fili mai d'auke da k'ananun d'akuna biyu sai band'aki k'arami shima, gidan ya siye sa tun auren sa da Umma Habiba lokacin yana da d'an rufin asirin sa, kafin daga baya al'amura suka cakud'e masa, sana'ar gyaran takalmi yake goma ashirin hamsin ce ake biyan sa, basa isar sa hidimar gida har ya fara cin bashi, wanda bashin mutanen dake kansa ba zasu lissafu ba,
KULUWA kasa kallon mahaifinta tai tsabar tausayin sa, zuciyarta na wani irin rauni, ta lumshe idon ta, tana jin rad'ad'i na irin cin zarafin da ake ma mahaifin nata, Juyowa kawai tai ta shige d'akin ta, Ta zauna k'asa kan tabarma tana had'a hannayenta ta tallabi kumatun ta, yaushe ne al'amura zasu daidaita yaushe ne zata daina fuskantar cin zarafin da ake wa mahaifinta, babban tashin hankalinta yau shine jin furucin mutumin na cewar zai d'auki hukunci, tasan mahaifinta bashi da wata hanya da zai biya kud'in a kwana uku, sai dai su shirya rungumar k'addarar hukuncin da Danladi zai d'auka kan mahaifinta, babbar damuwarta kada yace zai sa a kulle sa, basu da wani mai tsaya musu da zai fitar dashi matuk'ar aka kai sa, Allah ne kad'ai zai tsaya musu, Kanta ta saka cikin cinyoyinta ta saki wani irin kuka na tausayin rayuwar su da tsoron abunda zai biyo baya.....
Ya kuke ganin tafiyar labarin nan zata kasance?
Malam Garbati zai samu kudaden da zai biya bashin kansa cikin kwanakin?
Ku biyo mu cikin tafiyar yan tagwaye
SADIYA NASIR DAN CE
DA
ZEE YABOUR