SHAFI NA BIYU
by @zeeyabour20
KULUWA
NA ZEE YABOUR
DA SADIYA NASIR DAN
SHAFI NA BIYU
02
Umma Habiba da Malam Garbati kallon juna sukayi ko basu furta ba, kowannensu yasan d’aya Kuluwa yake ji sun san tana cikin damuwa na mahaifin nata duk da tana k’ok’arin b’oyewa amma yanayinta na yau ya bayyana hakan, Malam Garbati cikin wata irin murya mai rauni yace “Ba kowa nake ji ba sai KULUWA nasan ba zata iya jure ganin hukuncin da za’a d’auka kaina ba, shin idan ma suka shigar dani k’ara wane hali zata shiga, ta taso ba tare da mahaifi ba, dan nasan sai dai na k’are rayuwata can babu mai fiddo ni, kaf danginmu babu mai hali kowa yana fama da kansa”. Umma Habiba sosai zantukan Malam suka sosa ranta tana jin itama ya zatai rayuwa babu mijinta amma tafi jin KULUWA yarinya mai k’arancin shekaru ta kuma san irin yadda ta damu da duk wani al’amura na iyayen nata. Cikin sanyin jiki tace “Akwai Allah, shi zamu mik’awa al’amuranmu, In Shaa Allahu zai kawo mana mafita”. Malam Garbati kai ya jinjina alamar gamsuwa da zancen nata yace “Allah ya warware mana matsalolin mu”. Umma Habiba tace “Amin, mu shiga ciki nan waje sanyi yanzu sai kaga mura ta kama mutum”.
Sun juya da zummar shiga Sallama ta karad’e gidan, Umma Habiba ce ta waigo jin muryar yan’ mata, Malam Garbati ya shige d’akin,
“Umma Barka da dare”. Suka gaisheta a tare, Umma ta amsa tana kallon su, Sun chab’a ado irin na matan k’auye, Sun sha d’aurin zani da riga sai kallabi daban irin mai santsi d’in nan, kowacce ta lafta janbaki ga d’igo a goshi, Dukkansu bazasu gasa shekaru sha biyar ba sa’annin KULUWA, haka girma da yanayin jikinsu d’aya da KULUWA sai dai sun d’an fita jiki kasancewar jikin nata sak na fulani ba wani k’iba gareta ba, D’aya daga cikinsu tace “Umma dama KULUWA muka biyowa za muje dandalin”. Umma HABIBA ta numfasa tace “Ku shiga d’aki kuji ko zata je”. A ranta tana ayyana da wuya yau d’in ta fita dan ganin yanayin ta, kuma dama KULUWA ba mai son fita ba ce, sai tayi wata ma bata lek’a dandalin ba, mafi yawa lokuta k’awayen nata Rabi da Karime ke matsa mata ta fita, Yau d’in ma sune suka biyo mata,
KULUWA na daga kwance tana jiyo su ta tashi zaune, daidai nan suka sa kai cikin d’akin nata, Karime tana kallonta tace “Hala ma bacci kike?”. Kuluwa ta girgiza kai tace “Ina kwance ne kawai”. Rabi tace “To tashi mu tafi dandali kuma kar kice ba zaki ba wallahi, dan yau wasannin zasu k’ayatar yaron mai gari zai zo tare da tawagar sa”. Kuluwa gyara zama tayi tace “Dama ina da ra’ayin zuwan amma fa ba dan wani yaron mai gari ba kawai zaman ce naji ta ishe ni”. (Tana son fita ko zata rage damuwar da take ji), Karime ta tab’e baki tace “Na rasa irin ki KULUWA, ke ba shi ne daku ba, mahaifinki bashi da k’arfi amma kinsa d’an banzan girman kai, ace ko saurayi baki da a k’auyen nan duk tarin samarin dake nuna suna son ki”. Rabi tana tab’e baki wacce itama mugun k’yashin KULUWA take ji na ganin yadda samarin k’auyen ke son ta tace “Girman kai rawanin tsiya ba, dan taga tana da kyan ne take ja musu aji, su kuma maza ba’a musu haka musamman idan kasan zaka k’aru dasu”. KULUWA wacce sam babu saurayi ko tunanin soyayya a tsarinta yanzu tafi maida hankali wurin ganin ta samu ilimi wanda take tunanin dashi zata taimakawa iyayenta taja numfashi tace “Nayi girman kai a matsayina ta wa? ko da mahaifina yafi kowa kud’i a k’auyen nan ba zan kasance mai girman kai ba, dan dabi’a ce da Allah ya hane mu da ita, kawai bana ra’ayin soyayyar ce yanzu karatu shine burina”. Karime tace “Yanzu ke duk girmanki kice ba soyayya a tsarin ki? wallahi ki canza tunani ma tun wuri, dubi ki ga d’akin da kike kwanciya fah KULUWA ko katifa babu baki cancanci rayuwa irin wannan ba”. Mik’ewa tayi tace “Ku tashi mu tafi ina so na dawo da wuri”. Tayi hanyar k’ofa tana son kawar da zancen da basa rabuwa da mata, ko bitar karatu ne yaci ace zuwa yanzu ta haddace saboda kullum zance d’aya kenan sai dai har yau basu tasirin karkata hankalinta ga zuwa irin tunanin su ba, Karime tace “Wai budurwa kamar ki ko ado bakya yi idan za kije dandali?”. Rabi tace “Kema kina son b’ata yawun bakin ki ne kawai, bayan kinfi kowa sanin halinta”. Ta katse Karime dan bata son KULUWA tai kwalliyar da zata ja hankalin samarin wurin duk da ko batai ba bata rasa masu kula ta, KULUWA ba tare da sake cewa komai ba ta fito daga d’akin nata, Ta lek’a na iyayenta ta sanar dasu fitar tata, Malam Garbati yace “Ki kula da kanki kinji KULUWA?”. Tace “In Shaa Allahu Malam”. Umma Habiba ta k’ara da cewa “Kada kiyi dare duk da nasan bakya jimawa cam d’in”. Cikin muryarta mai ladabi tace “To Umma”.
Sai da ta ware d’an kwalinta ya sauka kan kafad’un ta, Suka fito gidan zuwa dandali, Suna tafe a hanya suna hira wacce fin rabi Karime da Rabi ke yi jefi jefi take saka baki,
Tun daga nesa suka jiyo kad’e kad’e yana tashi, da alama yau hadda sifiku aka d’auko dan sautin kid’an dake tashi na daban ne, Karime tana washe baki tace “Kai wallahi yau ranar ta musamman ce, kuji irin kid’an dake tashi”. Rabi tace “Dole ranar yau ta bambamta da saura, Haladu yaron mai gari ne fah zai zo dandalin bayan bai tab’a zuwa ba”. Karime na washe baki tace “Hakane”. Rabi cikin zuciyarta addu’a take Allah yasa yace yana son ta, Duk da kaf k’auyen anyi shaidarsa da son mata da lalata su, idan ya k’afa kwad’ayinsa akan yarinya sai ya kawar, sai dai bai tab’a yiwa ko wacce yarinya fyade ba duk wacce ya tara da ita to da amincewarta, Rabi ta sawa ranta zata basa kanta matuk’ar zai kula ta tasan kud’i zai jik’ata dasu ita kuma muradinta kenan,
Yan’ mata da Samari ake ta raye raye, masu ciye ciye na yi, KULUWA gefe d’aya can wajen wani dankali wanda yasha sementi taje ta zauna, tana bin su da kallo, Tana ganin yadda suke raye raye, Samari na shigowa suna ma yan’ matan lik’i, tunda take zuwa dandali bata tab’a shiga filin rawar ba, kallo kad’ai ke kawota ba, amma duk wasu wasanni bata shiga, haka duk tazo sai ta samu saurayin da zai nuna yana sonta bata kula sa hadda hakan ke sa bata cika son zuwa dandalin ba.
******
“Yarima yau na tabbatar sai ka bani lada, dan zaka ga tsala tsalan mata wanda baka tab’a zata akwai su k’auyen nan ba”. Mamman wanda yaron Haladu ne kuma abokinsa ke sanar dashi, suna tafiya a k’asa zuwa dandalin hadimai na take musu baya, Haladu ya gyara zaman hular sa sabuwa dal yau ya saka tare da shaddar sa itama sabuwa kalar ruwan k’asa tana k’yalli na sabunta, k’afafunsa sanye da takalmi kuffta bak’ak’e, yayi kyau matuk’a dan fari ne kuma kyakkyawa ga uwa uba suturar da yake sawa wacce kaf k’auyen babu mai saka ta, Yayi murmushi yace “Idan kuwa na samu tsala tsala guda uku da zan rage zafi dasu na kwanakin da zanyi kafin na koma makaranta dole na maka babbar kyauta”. Mamman ya washe hak’ora yasan ba tantama Yarima zai same su, Haladu shine babban yaron mai garin wanda ya sangarta sa yake nuna masa tsantsar so, bai cika zama k’auyen ba ya taru sa karatu birni yana jami’ar bayero ajin sa na biyu, inda yake karantar mass com, wato aikin jarida. a makarantar ma sharholiyar sa yake yana kula mata son ransa, maitar sa a fili take kan mace, Shiyasa ko k’auyen yazo sai ya samu wacce ya rage zafi da ita, Yan’ matan k’auye da kwad’ayi kuma suna ganinsa dan’ gayu yana zuwa birni gashi da yan’ chanjin sa yasa suke amince masa har so suke ya kula su.
Mai shirya taron dandalin ne ya soma sanarwa ga YARIMA nan zai shigo, Yan’ matan kowacce ta shiga gyarawa tana yanga tana duba jikinta ko Allah zai sa ya kula ta, Rabi ma sai matsowa take gaba gaba tana turo k’irji, KULUWA na kallon ta kai kawai ta girgiza bata ga abun so! Ko burgewa ga yaron da kowa yayi masa shaidar lalata da yan’ mata, Fatan ta ko da yaushe ta tsare mutuncin kanta kada tayi abunda zai jawowa iyayenta zubewar mutunci ko k’ima duk da kasancewarsu talakawa akwai k’ima da darajar da ba kud’i ke kawo su ba sai dabi’a, Tunaninta ya katse ganin shigowar HALADU filin wurin yana taku tamkar baya son taka k’asa bayan a cikinta za’a binne sa ya zama abincin ta.
Wasanni aka soma gabatarwa iri iri, Haladu na hakimce kan wata kujera da aka ware masa, Mamman ya rad’awa saurayin mai magana kan cewar Yarima yana son ya samu budurwa yau a cikin yan’ matan nan, Saurayin ya jinjina kai yai sanarwa kan duk yan’ matan dake gun kowa ya fito, a taka rawa, Kowacce ta taso tana gyarawa dan son burge YARIMA sanin halinsa na kula mata, KULUWA na daga gefe tak’i tasowa tana kallon sa, suna rawa, Yarima na bin kowaccensu da ido yana kallon yanayin k’irjinta da mazaunanta sune abunda suka fi jan hankalin sa ga mace, HALADU idonsa ya karkata kan Rabi ya taso da zumar ya mata lik’i yaji ya taka abu, d’an baya yai daidai nan idon sa ya sauka kan KULUWA, wacce gajiya da zaman yasa ta yin mik’a tana hamma alamun ta fara jin bacci, Idonsa ya sauka kan k’irjinta da ya b’ankaro, Wani abu yaji ya tsirgar masa gaba d’aya hankalinsa ya karkata kanta, Sam KULUWA bata lura dashi ba, hannayenta ta sauke ta tashi tsaye, tana sake gyara zaman d’an kwalinta, Gida zata tafi ta gaji da zaman ga bacci, Mik’ewar da tayi ya sake hango mazaunanta da k’irarta wanda take da baiwar hips, Idonsa ya lumshe wata masifaffiyar sha’awarta na fisgar sa, yana jin matuk’ar bai tara da ita ba, ba zai samu natsuwa ba, Baya yayi saitin Mamman da ido ya nuna masa KULUWA yace “Waccan yarinyar nake so, yau d’in nan kuma nake buk’atar ta”. Mamman saitin KULUWA ya kalla yace “Yarima da k’yar idan zaka sameta yau, dan yarinyar akwai masifar girman kai zaiyi wuya a iya shawo kanta”. Murmushin gefen baki Haladu yai yana shafa kansa irin na mazan duniya yan’ bariki yace “Mu bi ta naga zata wuce”. Mamman yace “Toh bari na sanar dasu wucewar mu”. Yai saurin k’arasawa ya rad’awa saurayin a kunne kan wani uzuri na gaggawa ya taso zasu tafi amma gobe zasu dawo, Yasan Yarima yana buk’atar wasu yan’ matan biyun bayan KULUWA dole gobe zasu dawo dandalin ya lura gaba d’aya hankalin Yariman yanzu ya karkata kan KULUWA wanda idan ba samunta yayi ba hankalinsa ba zai tab’a kwanciya ba
Hmmm kuna ganin KULUWA zata amincewa YARIMA HALADU kuwa
Zaiyi nasarar shawo kanta
Ko fyade zai mata duk da ba dabi’ar sa bace?
KU DAI BIYO MU CIKIN TAFIYAR YAN TAGWAYE
SADIYA NASIR DAN CE
TARE DA
ZEE YABOUR