SHAFI NA UKU
by @zeeyabour20
KULUWA
NA ZEE YABOUR
DA SADIYA NASIR DAN
SHAFI NA UKU
03
Da yawa daga cikin yan' matan da suka so ace Yarima Haladu ya kula su basu so tafiyar sa ba, musamman Rabi wacce taci buri, amma sun k'udurta a ransu gobe zasu dawo ko dan Yariman, Karime ta kalli saitin da KULUWA take tace "Mutuniyar har ta tafi kenan". Rabi ta yatsina baki tace "Idan kina wata maganar kamar baki san wacece ita ba, kinfi kowa sanin dama ba wani daɗewa take ba ko tazo". Karime ta jinjina kai tace "Hakane, ni ina mamakin rayuwa irinta Kuluwa, da nice mai kyau da farin jininta ai da babu macen da zata kaini saka suturu da ado a k'auyen nan". Rabi tace "Ai bata da wayo ne ita, muje mu siyo rake". Rabi ta nunawa Karime gun masu rake dan bata so Karime na yawan yaba KULUWA da fad'in irin baiwar kyau da Allah ya mata da farin jini, sai taji bak'in ciki ya cika mata zuciya.
Cikin natsuwa take tafiyar ta, tana tunanin Mahaifinta tausayin sa na cika mata zuciya, ta d'auka zuwanta dandalin zai kawar mata da damuwa, sai dai damuwar tana mak'ale a zuciyarta tayi kane kane ta hanata walwala, Yarima Haladu ya umarci hadiman sa su wuce gida zai taho, suka bi umarninsa suka tafi ba ja, Tare da Mamman suka biyo bayan KULUWA, ganin tana neman b'ace musu suka k'ara saurin tafiya, Mamman har mamaki YARIMA ya basa, irin isa da tak'amar sa yana tafiya dai' dai' yau shine da tafiyar sauri, tabbas ba k'aramin jan hankalin sa KULUWA tayi ba,
"KULUWA tsaya Dan Allah". Mamman ya fad'a cikin hanzari yana k'ok'arin shan gabanta, Banza tai kamar bata ji ba tasan wani ne zai tsayar da ita ya cikata da surutun da basu da amfani a gun ta, Ganin bata tsaya ba MAMMAN yai saurin shan gabanta, Ba tare da ta d'aga kai ta kalle sa ba balle tasan waye dan bata ra'ayin sanin sa, ta rab'a gefe da zummar wucewa, Ya sake tare gefe yace "YARIMA ke son magana dake". Cak ta tsaya kamar tsayuwar battery idan ya daina aiki, taji wata irin fad'uwar gaba, Tsayuwar Yarima a gabanta ya sake katse duk wani kuzari nata tana jin k'afafunta sun mata nauyi kamar bazasu iya d'aukarta ba suna shirin kai ta k'asa, Mayatattun idonsa ya zuba mata yana bin surar jikinta da kallo, zai iya rantsewa duk bin matan sa bai tab'a cin karo da wacce ta tafi da imanin sa irin KULUWA ba, ya yarda da maganar Mamman da yace masa zai ga yan' matan da bai tab’a zata akwai su a k'auyen ba, gashi yaci karo da d'aya, Tsukakken k'aramin bakinta mai zagaye da leb'e pink yake kallo yana jin tamkar ya had'e bakinsa da nata, wani irin shock ke jan sa zuwa jikinta tamkar an saka mayen k'arfe yana jan sa zuwa gare ta, Babu haske a wurin kasancewar duhun gari sai hasken taurari da wata shi ya hana masa k'arewar kyakkyawar fuskarta kallo amma ko a haka yasan kyakkyawa ce mai irin sihirtaccen kyaun nan, Da k'yar ya iya danne kansa ya saita bakinsa yace "Hak'ik'a ke d'in kyakkyawa ce, wacce zan iya cewa ban tab'a cin karo da mace mai kyawun surarki ba". KULUWA ja baya tayi gabanta na tsananta faɗuwa, ga kalamansa na jefata cikin wani irin tsoro, Wani murmushi yayi yana sake binta da kallo tun daga sama har k'asa idonsa na k'ank'ancewa na jaraba yace "Ina fatan zan samu karb'uwa, ni kuma na miki alk'awarin kud'i naira dubu d'ari". A razane ta kalle sa wanda a zaton sa yawan kud'in da ya fad'a yasa take kallon sa, Ya matso kusa da ita tare da kai hannunsa kan fuskarta ya shafa yace "Idan na sameki yadda nake so ma zan ninka miki kud'in". KULUWA wani mugun tsoro da firgici ya shigeta taja baya da sauri, hannunsa na sauka daga kan fuskarta, jikinta ya hau b'ari yau ce rana ta farko da hannun da' namiji ya kai kan fuskarta, "Relax baby kada kiji tsoro ba wanda zai san me zai faru tsakanina dake zai zama sirri idan tsoro kike ji". Ya fad'a yana sake nufo ta, KULUWA a razane taja baya tana fad'in "Kada ka sake tab'ani idan kai baka tsoron Allah ni ina tsoron sa, kuma ni ba kwad'addaya ba ce, me zanyi da kud'in k'azanta, kaje ka nemi irin ka, ni mutuncina yafi mun komai". Maimakon taga b'acin rai kan fuskar Yarima sai murmushi da yayi yana kallonta idonsa cike da tsananin sha'awarta yace "Ban tab'a d'aura k'wadayina kan wata mace ba tare da na kawar dashi ba, balle ke da gani d'aya kika birkita mun tunani, kalli nan". Ya nuna mata gabansa abarsa ta mik'e sosai tamkar zata fasa wandon sa ta fito, Runtse ido tayi cikin tsananin tashin hankali da mamakin rashin kunya irin ta Yarima, "Ban tab'a jin sha'awa irin yadda naji a kanki ba, dan haka sai na sameki". "Allah yafi ka kuma bazai tab'a baka nasara ba". Ta fad'a cikin tsananin tashin hankali tana fashewa da wani irin kuka, Mamman jikinsa yai sanyi sosai, yana jin tausayin KULUWA yana tunanin idan k’anwarsa ce ya zai je, ba zai yarda a keta mata haddi ba, yana yi wa YARIMA jagora ne inda yasan da amincewar yarinya, Kusa da Yarima Haladu ya matso murya k’asan mak’oshi ta yadda KULUWA ba zataji ba yace “Na fad’a maka tana da girman kai, ba zaka sameta ta lallami ba, ina ganin ka samu wata yau kawai ka kauda sha’awar ka, ita daga baya sai a shawo kanta”. Yarima Haladu idonsa ya runtse ya bud’e tabbas bazai iya bacci ba yau matuk’ar bai tara da mace ba, yana buk’atar wata dan yaga alamar KULUWA ba zatai saurin shigowa hannu ba, Kai ya d’agawa Mamman alamar gamsuwa da zancen sa, Mamman ya juya kan KULUWA, wacce gaba d’aya jikinta ke rawa tana wani irin kuka, “Ki sake tunani wannan wata dama ce da zaki fitar da kanki daga talaucin da kike ciki har ki taimaki iyayenki, zaki iya tafiya idan kin canza shawara ki nemeni ni zan had’aki da YARIMA HALADU, kada ki bari arzik’in dake kiran ki ya wuce ki”. KULUWA yadda maganganun sa ke shiga kunnuwanta haka suke fita sam bata basu muhalli a zuciyarta ko na second d’aya ba, Mutuncin ta da na iyayenta yafi mata k’azantar duniya, bata kalli MAMMAN ba balle Yarima da take jin tsana da duk wata k’imar sa ta zube a idon ta, Ta rab’a gefen su tana fallawa da gudu, YARIMA HALADU yabi bayanta da kallo yana jan wani irin numfashi, Har wandon sa yake jin ya b’aci saboda tsananin sha’awa, Muryarsa k’asa ya misaltawa MAMMAN yarinyar da ya gani d’azu taso jam hankalin sa yace yana son ya taho masa da ita, Mamman ya jinjina kai yace “RABI ce ka gani, ita wannan bata zai wahalar shigowa hannu ba, bari na koma dandalin Allah yasa bata wuce gida ba”. “Ko ta tafi kasan yadda ka kawo mun ita”. Yarima Haladu ya fad’a yana matse k’afafun sa saboda abarsa da ta mik’e ta kwanta.
***************
ASOKORO, ABUJA
Mota ce mai azabar kyau da had’uwa kana gani kasan an cire miliyoyi kud’i wurin mallakar ta, bak’a ce wulik mai tented glass baka ganin na ciki, gaba da bayanta motocin sojoji guda biyu ne, wanda hakan zai shaida maka mamallakin motar yana da wani babban matsayi, A jere motocin suka shigo layin mai shimfid’e da kwalta tun daga farkonsa har k’arshen sa, gidajen dake kewaye da layin zai shaida maka unguwa ce ta masu hannu da shuni dan babu gidan da bai k’eru ya tsaru a layin ba, Ga yanayin unguwar tsit babu hayaniya ko tarkacen masu siye da sayarwa da zai nuna maka unguwar masu k’arancin hali ce, Bakin wani tafkeken gida motar dake gaba ta tsaya tana horn, gate d’in gidan kansa abun kallo ne saboda girmansa da tsaruwa irin na zamani, ko karfe da akai amfani wurin yin sa kasan bana banza ba ne, gashi da wasu designs a jikin sa, gaban gidan fulawowi ne shuke cikin k’arfe dake zagaye gaban gidan ya sake k’awata ga fitilu kunne da hasken su ya haskaka gaban gidan yai kyau sosai, fitilun kansu idan ka kalla kasan sai gidan wane da wane, Wani K’ato ne mai murdadden jiki, sanye da kayan sojoji ya lek’o ganin motar dake wajen, Ya koma ciki ya wangale gate na makeken gidan, suka saka kan motocin ciki, suna parking wurin makeken filin ajiye motoci wanda shi kansa abun kallo ne, gida ne na hamshakin mai kud’i wanda ya tara da yawa, Cikin hanzari d’aya daga cikin sojojin ya fito daga gaban mota, Yai saurin bud’e k’ofar baya yana sarewa, K’afar sa d’aya ya fara zurowa daga cikin motar ta sauka kan interlocks na zamani dake malele da tsakar gida, sanye take da half covered shoe na kamfanin prada, d’ayar k’afar ya zura waje, ya fito,
Matashi ne wanda a kallo d’aya zaka yi masa ka d’auka bai haura shekaru ashirin da biyar a duniya ba, sai dai a zahirin gaskiya watanni biyu da suka wuce ya cika shekarun sa na talatin, tsabar hutu da kyawun k’irar jikinsa ke b’oye shekarunsa tana sake maida shi yaro, Designer suit ne a jikinsa da suka amshi jikinsa suka masa kyau sosai, Kyakkyawar fuskarsa dake zagaye da saje da ya k’ara masa wani irin kyau sam babu walwala ko far’a akanta tamkar baya farin ciki da dawowar sa gidan, Haka ya taka zuwa k’ofar da sada shi cikin gidan, Card ya zaro daga aljihun sa yai amfani dashi k’ofar ta bud’e, Ya saka kai ciki, Yana kai hannunsa ya sak’a card d’in gefe falon ya wadatu da haske k’ananun fitilu dake jikin pop, Kallo yabi falon dashi yana hango k’ura saman centre table da tv stand hakan na tabbatar masa yau ma falon bai samu gyara ba, Iska ya fusgar mai zafi daga bakin sa cikin takaici, Takawa ya fara yi zuwa wata k’ofa ya bud’e ya wuce wani dogon corridor ya sake bud’e k’ofa ta kai sa wani falo wadataccen falo mai fentin cream, kujeru da labulen falon suma cream, komai na falon dai an shiryasa ta yadda ya tafi kan tsari ya kuma had’u, Yara mata biyu ne zaune suna kallon cartoon, babbar ba zata wuce shekaru biyar ba k’aramar kuma biyu, Da gudu suka taso ganin mahaifinsu suka rungume sa, K’aramar ya d’aga sama yana mata wasa, b’acin ran dake kan fuskarsa yana sauka ya tsaya iya zuciyar sa, Ya mata wasa na kusan minti biyu kana ya sauketa yana duban babbar yace “Ina Mummyn ku?”. “Tana d’aki”. Ta fad’a tana jan dogon gashinta da kitson kansa ya tsufa sosai, yarinyar yabi da kallo yana ganin uniform ne jikin ta, ya kalli agogo takwas da mintuna tun biyar da rabi tashin su dan bokon da take had’e take da islamiyya amma har yanzu ba’a cire mata uniform ba, wani b’acin rai yaji ya sake cika sa, Ya nufi hanyar bene, Yana takawa yana jin yadda zuciyarsa ke sake harzuk’a.
MAJOR UMAR BASHAR LEMA mutum ne mai zuciya sosai, ga saurin fushi abu kad’an ke harzuk’a shi, uwa uba dama ga sojoji da zafin rai, baya son raini ko kad’an hakan yasa bai cika doguwar mu’amala da mutane ba, a cewar sa yawan sakewa da mutum shi ke kawo raini.
K’ofar d’akin ya tura da k’arfi, Kyakkyawar macece wanda ake musu kira da black beauty kwance kan royal bed ta lullub’e iya k’afafunta, tana danna waya tana dariya da alama chatting take, Bakin gadon ya k’araso cikin zafin rai ya fisge wayar dake hannun ta yana kallon ta cikin tsananin b’acin rai, Umaima tashi tayi zaune ba alamar tsoro ko shakkar sa take kallon farar kyakkyawar fuskar sa da babu far’a a kai, ta mik’a masa hannu tace “Bani wayata tunda dai ba kai ka siya ba”. Wani irin kallo yake mata yace “Meyasa kike son canza dabi’unki da na sani a baya zuwa ga wanda basu kamace ki ba?”. Umaima ta had’e rai sosai tana son nuna masa itama ta isa tace “Kana magana ne a lokacin da duhun jahilci da rashin wayewar kai suka mun kwanya, yanzu kuwa idona sun bud’e daga yanar da ada tai musu kwanya….”
To fah…..
Ku dai biyo mu a cikin tafiyar YAN TAGWAYE
SADIYA NASIR
TARE DA ZEE YABOUR