KULUWA

SHAFI NA HUDU

by @zeeyabour20

KULUWA


NA ZEE YABOUR

DA SADIYA NASIR DAN


SHAFI NA HUDU


MAJOR UMAR cikin tsananin b’acin rai yake kallon ta da idanunsa da suka canza launi sukai ja, da muryarsa dake fitar da zallar b’acin rai yace “Bijirewa umarnin miji da rashin kula da gida shi kike kira wayewar kai UMAIMA?”. Ya k’arasa maganar da fad’in sunanta da wani irin amon da yasata razana, amma ta dake zuciyarta ta riga ta bushe abu d’aya take buk’ata daga gare sa hakan yasa ba zata bari kwarjininsa yai tasiri a kanta ba, Manyan idanunta ta zuba kansa ta tattare duk wani tsoro ta masa ma’ajiya can k’asan ranta cike da tsiwa tace “Ni ba baiwa ba ce da kake tunanin zan cigaba da bauta maka kana juyani tamkar waina a tanda, Allah yayi maka arzikin da zaka iya d’aukar ma’aikata daga d’aya har zuwa ashirin ko fi idan ka so, bansan dalilin da yasa sai ni kake so na wahala ba, idan a da nayi bisa rashin sanin ciwon kai na yanzu nayi hankali nasan yancin kaina”. MAJOR UMAR a fusace ya wurga mata wayar ta, ta sauka kan cinyarta ya juya ya nufi hanyar fita d’akin, a yadda zuciyarsa ta kawo wuya tsaf zai iya kifa mata mari, baya son yayi abunda ba halin sa ba, wanda yake ganin rashin hankali ne namiji ya d’aga hannunsa ya kai ga jikin mace da sunan duka, Cikin wani irin taku ya fita daga b’angaren nata gaba d’aya ya shiga na sa, 


Huci yake tamkar zuciyarsa zata tsaga k’irjinsa ta fito saboda tsananin b’acin rai, jijiyoyin kansa na fitowa rad’au kan goshin sa. MAJOR UMAR mutum ne mai tsananin zafi da d’aukar fushi, shi kansa wataran tsoron zuciyar sa yake shiyasa yake kaucewa abunda zai b’ata masa rai sanin yanayin sa, gefen makeken gadon dake d’akinsa wanda kaf gidan yafi kowane d’aki girma da tsaruwa komai an masa adon blue da white kalar da yafi so, Ya zauna yana bin kowacce kusurwa ta d’akin da kallo ba zai iya tuna rana ta k’arshe da UMAIMA ta shigo ta gyara masa d’akin ba, Idonsa ya runtse yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta harbawa, “Meke damun UMAIMA? me ya canzata haka? Ko na mata wani laifi ne ban sani ba?”. Ya jerowa kansa tambayoyin da bashi da amsar su sai ma damuwar dake k’ara sark’afe sa, Zuciyarsa ke ingiza sa yaje ya tambayeta yaji laifin me ya mata ta zab’i hukunta shi ta wannan hanyar take neman ruguza dukkan sauran farin cikin da ya rage masa, bayan tasan itace babban jigon farin cikin sa, ya mata sadaukarw da babu wani mahaluki a doron k’asa da ya mata, gaba d’aya rayuwarsa ta ta’allaka ne a kanta, itace mutum ta biyu da yake jin sun zame masa wani b’igiri na rayuwar sa, sai yaransa da ya samu ta dalilin ta wanda hakan ya k’ara mata wani matsayi mai girma a zuciyar sa, ya bata wani muhalli na musamman a cikin ransa, “Me ya canza ki UMAIMA, wane laifi na miki da bazaki iya sanar dani mu fahimci juna ba, nasan ba halinki ba ne hakan, dole akwai abunda ya canza”. Yayi maganar cikin zafin zuciya ya mik’e zuciyarsa na ingiza yaje ya tambayeta, Saurin komawa yai ya zauna, Yana jin kowane laifi ya aikata baiyi deserving ta masa haka ba, sannan zuwa wurin nata zai sake bata damar raina sa, Baya yai ya kwanta yana kallon had’adden chandelier dake jikin POP, Zuciyarsa na masa bak’i k’irin ba natsuwa tare dashi.



************

Mamman baiyi nisa a tafiya ba yaci karo da Karime da Rabi a hanya, Sallama ya musu suka amsa da sakewa musamman Rabi har da washe hak’ora, Yana kallonta yace “Yarima ya aikoni wurin ki”. Ido ta ware sosai dan son tabbatar da kunnenta daidai suka jiye mata ko tsabar saka abun a ranta ne taji kamar yace haka, Tana kallon Mamman tace “Ni RABI kake nufi YARIMA yana kira”. Kai ya d’aga yace “Eh mana, har mun tafi yasa na dawo na kira masa ke”. Baki ta washe cikin tsananin farin ciki tace “To Muje”. Karime na dariya tace “Yau dai kice kin fito dandalin a sa’a”. Ta kalli Karime tana fari da ido tace “K’warai kuwa, banyi kwalliyar banza ba”. Karime tace “To nidai kada a manta dani”. Yarinya ce da sam bata da k’yashi ko hassada, Rabi tace “Kema kinsan bazan manta dake ba”. Anan sukai sallama Karime ta wuce gida, Rabi tabi Mamman zuwa inda YARIMA HALADU ke tsaye yana jiran sa, Tunda ya hango su yake kallon Rabi sai yaji sam bata burge sa ba, har ta k’araso kusa dashi tana wani yanga tana bank’aro k’irji, YARIMA HALADU maimakon yaji sha’awa sai yaji haushinta na cika sa, suffofin surar KULUWA kad’ai ke masa yawo tsakanin idanunsa da k’wak’walwarsa, Rabi na satar kallonsa ta gefen ido zuciyarta kamar an zuba mata k’ank’ara wai ita YARIMA ke so har yasa aka kira masa ita, Alama yayi ma Mamman kan yazo kusa dashi, Ya taho cikin hanzari yana saita kunnensa bakin Yarima wanda murya k’asa yace “Ni fa sam naji bana sha’awar wata mace sai KULUWA”. Mamman a ransa yace “Tirk’ashi”. A zahiri yace “Wannan k’awarta ko zaka mata magana kace ta shawo maka kan KULUWA”. Yarima ya d’aga kai shawarar MAMMAN na zama a kansa, Ya d’an matsa gefe yana kallon Rabi yace “Na aika a kira mun ke ina son kiyi mun wani aiki ne da zan biya ki”. Rabi a take ranta ya bata kwanciya yake son yi da ita, Ta d’ago idonta tana wani lumshe su tamkar matan bariki tace “Baka da matsala da hakan”. Yayi gyaran murya yana sake kallonta tabbas da a baya ne ba abunda zai hana ya kusancenta da ga dukkan alamu yar’ hannu ce sai dai yanzu gaba d’aya hankalinsa na kan KULUWA, Yace “K’awarki KULUWA nake son ki shawo mun kanta, na kasance da ita ko da na yini d’aya ne”. Wani irin kallo ta masa zuciyarta na harzuk’a, hassadar KULUWA na sake mamaye zuciyarta “Wai meyasa kowane namiji ita yake gani”. Tai zancen a zuci wanda bata san ya fito fili ba sai amsar Yarima da taji yace “Saboda tana da baiwar kyawun halitta ba kowacce mace ke da shi ba”. Cikin k’ufula tace “Sai dai kuma duk nacin namiji bai isa yasa ta mallaka masa kanta ba”. YARIMA tuni ya harbota har da hassada ke d’awainiya da ita yana kallonta yace “Matuk’ar kika shawo mun kanta na miki alk’awarin naira dubu hamsin”. A razane ta kallesa tace “Dubu hamsin”. Ya d’aga mata kai yace “Indai kika shawo kanta, ta bani had’in kai na miki alk’awarin sa”. A take Rabi tace “Zan yi k’ok’arin ganin hakan duk da tana da girman kai”.

 “Kiyi amfani da dabarunku ta mata”. Yarima ya fad’a yana saka hannu a aljihu ya fiddo mik’ak’un d’ari biyar guda hud’u ya mik’a mata yace “Ki fara da wannan”. Hannu biyu ta saka tana masa godiya, Yace zata iya tafiya,


Rabi ta juya tabi hanya, tana jin duk wani b’acin rai da take ciki ya kau, dama saboda kud’i take son alak’a ta shiga tsakaninta da YARIMA HALADU wanda dubu ashirin take kiyastuwa ya bata, gashi yanzu ya mata alk’awarin dubu hamsin ya zama dole tai k’ok’arin shawo kan KULUWA ta amshi yan’ chajinta, amma tana buk’atar taimakon Karime, dole gobe taje gidansu su tattauna.



******

KULUWA cikin wani irin yanayi na rashin natsuwa ta shigo gidan su, fuskarta tai jajir tsabar kuka, muryarta ta dishe, gudun iyayenta su fuskanci yanayin da take ciki hankalinsu ya tashi yasa ta wuce d’akinta ba tare da ta sanar dasu dawowarta ba, Kan tabarmata ta fad’a har tana bige hannu, Kuka take sosai tamkar an aiko mata sak’on mutuwa, wani bak’in ciki da tashin hankali take ji tare da ita, yayin da nadamar fitar ta yau dandali na lullub’eta, da tasan abunda zai faru kenan ko k’ofar d’akinta ba zatai yunk’urin takawa ba, balle taje dandali wanda zuwan sa ya zame mata masifa, babu abunda ke d’aga mata hankali sai furucin YARIMA na cewar sai ya sameta, tasan k’arfin ikon sa a k’auye, ita iyayenta ba kowa ba da zasu tsaya wurin k’watar mata yancin ta, amma tasan Allah yana tare da ita shi zai kare ta daga sharrin YARIMA, tana jin da ta rasa mutuncin ta gara Allah ya d’auki rayuwarta akan taga wannan bak’ar rana da zata zame ma daga ita har iyayenta sanadin toshewar farin cikin su, Kanta ta cusa cikin cinyoyinta tana sakin wani kukan, ta shiga karanta dukkan addu’o’in da ta iya.


“KULUWA bata dawo bane har yanzu”. Ta tsinkayo muryar UMMA HABIBA daga tsakar gida, Lafewa tai tamkar mai bacci taja zani tana rufe har fuskar ta, K’odadden zanin da yaji jiki wanda dashi akai ma bakin d’akin kariya UMMA HABIBA ta d’aga tana lek’awa da mamaki tace “Kin dawo har kin kwanta ba sanarwa KULUWA, Allah yasa dai lafiya”. Tai maganar tana sauke zanin ta juya da mamakin sanin ba dabi’ar KULUWA bace yin hakan, idan zata fita zata sanar dasu haka idan ta dawo, KULUWA numfashi taja wasu hawayen na zirya kan kumatun ta.


*******

YARIMA HALADU kwance yake kan gadon madaidaicin d’akinsa wanda ke wajen gidan nasu ta can gefe d’aya, baka sanin akwai d’aki idan ba an sanar da kai ba, hakan ya sake basa damar kawo mata d’akin ba tare da anga shigar su ba, musamman masu tsoron iyayensu su sani, Juyi yake bacci yak’i d’aukar sa gaba d’aya suffar jikin KULUWA ke masa yawo, yana faman rik’e mararsa dake murd’awa tabbas idan bai kusancenta ba akwai matsala, kwata kwata baya jin sha’awar kowa sai ita, sai wuraren asuba ya samu bacci ya d’auke sa wanda yake cike da mafarkinta suna tarawa.



*********

MAJOR UMAR ya dad’e kwance cikin yanayi na b’acin rai da zafin zuciya, K’ok’arin yak’i yake da zuciyarsa yana ture damuwar waje d’aya, yana nunawa kansa shi namiji ne bai kamata mace ta saka shi shiga damuwa haka ba, yana son nunawa zuciyar tasa wacece UMAIMA a gun sa da yadda ya d’auketa da muhimmanci a rayuwar sa, Idonsa ya runtse ya sake bud’e sa ya tashi ya shiga band’akin sa, komai tsaf kamar bayin mace, duk da shima ya d’auki kwanaki bai samu wanki ba, kasancewar MAJOR UMAR mai tsananin tsafta yasa bai yi datti ba, kayan jikin sa ya rage yana sakawa cikin laundary basket dake gefe d’aya na makeken band’akin, Ya shiga cikin jacuzzi bath d’in, ya fara wanka yana yi yana fusgar da ruwan bakin sa, hannun sa ya kai kan kwantaccen gashin dake kan k’irjinsa ya shafa yana sauraren bugun zuciyar sa, “YOU ARE SOLDIER ba’a san ku da raunin zuciya ba”. Ya cewa kansa, Yai saurin girgiza kai yana fusgar da ruwa, Wata dakiya na zuwan masa, Har ya kammala wankan ya fito yai shirin baccin sa, Ya kwanta yaja bargo ya rufe ya kai hannunsa kan switch dake manne gefen gado ya kashe, Ya rufe idonsa yana fatan bacci ya d’auke sa ba tare da dogon tunani ba.


*****

UMAIMA tun fitar UMAR a d’akin ta d’auki wayarta tana banzarta da lamarin sa, ta cigaba da chatting da k’awayenta wayayyu kuma gogaggu wanda idonsu ya bud’e sosai da duniya, sam bata jin mijin nata a ranta yanzu bata damu da damuwar sa ba, wanda a lokutan baya bata da wani abun so, bege, tarairaiya, kulawa sama dashi, Ko yaran ta sam batai tunanin lek’awa falon taga me suke ba, wanda tuni bacci ya kwashe su a k’asan carpet na falon, Babbar Aydah tana rungume da k’aramar Ayrah, UMAIMA shirin baccin tai ta kwanta, a ranta tana ayyana mahaifinsu yazo ya d’auke su ya musu shiri bacci da kansan sanin halinsa da masifar son yara, ko masu aiki baya so suna masa hidimar yaran sa, Akwai masu aiki har uku a gidan, sai dai ba komai MAJOR UMAR ya amince suyi a gidan ba, cike hadda girki da kula masa da yara, ko shiga b’angarensa gyarawa wanda itama UMAIMA ta yarda da tsarin sa, amma yanzu tasa k’afa duka ta shure take tsiru da wasu halayya da a baya bata dasu.




Ko meke faruwa tsakanin MAJOR UMAR DA MATARSA UMAIMA MEYA CANZATA?

RABI ZATAI NASARAR SHAWO KAN KULUWA KUWA


KU cigaba da bin YAN TAGWAYEN NAKU


SADIYA NASIR DAN

DA ZEE YABOUR CE