KULUWA

SHAFI NA BIYAR

by @zeeyabour20

KULUWA


NA ZEE YABOUR

DA SADIYA NASIR DAN


SHAFI NA BIYAR



Biyar sauran mintuna daidai lokacin ketowar alfijir, kiraye kirayen sallah ne daga masallatai daban daban na k'auyen, Sanyin asuba na ratsowa lokaci ne da yafi kowane lokaci dad'in bacci wanda sai mai rabo da k'arfin imani ke iya yak'i da zuciya da idanunsa ta hanyar kawar da baccin ya tashi ya amsa kiran ubangiji, wanda a duk sanda mumini na kirki yaji kiran sallah ya dace ya ajiye duk wani abu da yake yaje zuwa ga bautawa ubangiji, KULUWA duk irin baccin da take kiran sallar asuba a cikin kunnen ta yake sauka, bata fashin tashi sai idan tana hutun sallah, Yau ma kiran farko ta bud'e idonta dan bacci nata ba mai k'arfi ba ne haka ba mai dad'i da natsuwa ba, cike yake da tunani kala kala, fargaba da zullumi, addu'ar tashi daga bacci ta karanta, Ta tashi zaune, ta d'an yi mik'a, Ta lalubi fitilar hannun dake gefenta wacce tasha d'aurin roba alamun tsufa dan ta rabe biyu dabara ce ta mata, ta kunna haskenta na rawa, ba kasafai suke samun wutar lantarki ba a k'auyen ba sai su jera sati biyu ba tare da sun ga ko gilmawar hasken k'wan fitila ba, Zanin da ta rufa dashi ta d'auka ta yane kanta zuwa jikinta dan ba kanta kariya daga sanyi, Ta mik'e ta fito tsakar gidan yin alwala, Malam Garbati tuni yayi alwala ya fice sallah, yana cikin mutane na farko dake zuwa masallaci sallah, jam'i biyar baya fashin zuwan su kowa ya shaidar sa da ba Sallah muhimmanci, bai tab'a gazawa wurin kai wa Allah kukan sa da buk'atun sa ba, yasan yana sane dashi, shi kad'ai yasan dalilinsa na saka shi jerin talakawa, watak'ila da yayo sa mai arzik'i ya zama silar da dukiyar zata kai sa wuta, bai tab'a jin bak'in ciki na kasancewar sa talaka ba, damuwar sa d'aya yawan bashin dake kansa, wanda dole kad'ai tasa yake cin bashin, dan da ya nemi haram gara yaci bashin.



KULUWA bayan ta idar da sallar asuba ta jima zaune tana karatun qur'ani da addu'o'inta wanda suka zame mata jiki, kullum bata fashin su, Hasken ranar da ya fara hasko d'akinta yasa ta rufe al' qur'anin ta tashi ta kai sa ma'ajiyar sa ta ajiye, ta zare hijabin jikinta sosai take jin sanyi a zuciyarta, qur'ani tabbas waraka ne ga dukkan damuwa, Tsakar gidan ta fito duk da ba wani datti yai ba, sai ganyayyakin da suka sauka wanda na iska ne da akayi daren jiya, tsintsiya ta d'auka ta share tsakar gidan tas, Ta d'auki bokitin k'arfe da take d'ibar ruwa ta tsaya daga k'ofar d'akin iyayenta Cikin muryarta mai sanyi da taushi tace "Assalamu alaikum". Malam Garbati da Umman Habiba tare suka amsa sallamar tata, Ta gaishe su muryarta a ladabce suka amsa, Tace "Zanje d'ibar ruwa". Malam Garbati ya zura rigar sa dake gefe ya fito d'akin, Yana kallonta cike da yaba hak'uri irin nata yace "Yau ki bar d'ibar ruwan nan, jiya ba wani abun kirki kikaci ba, yau ma ba karin kumallo kikayi ba, taya zakiyi dibar ruwa da yunwa". A sanyaye tace "Malam zan iya ai ruwan ma baifi nayi kai uku ba". Kai ya girgiza yace "Ki bari na fita na gani me zan samo mana, idan kinci sai kije dibar ruwan". Ba dabi'arta ba ce musu da iyayen nata ko da kowa tana kan gaskiyar ta kuma duk yadda take son abun hak'ura take, Hakan yasa tace "Toh". Ta juya ta ajiye bokitin ma'ajiyar sa, ta shige d'akin ta,


Malam Garbati yabi bayanta da kallo ya sauke ajiyar zuciya mai cike da tarin damuwa da tausayin KULUWA, banda ma Allah ya basu yarinya natsattsiya a irin rayuwar talaucin da suke wanda ko abunda zasu ci gagararsu yake, yadda take da kyawun nan da tuni ta fad'a harkar banza, Hannu ya d'aga sama yace "Allah ina rok'onka ka cigaba da tsare mun ya'ta yasa ta rik'e mutuncin ta har d'akin mijinta". Ya sauke hannayen sa, ya zura sud'add'un silifas d'insa dake bak'in k'ofar, duk sun mutu ta wurin digadigi har sun soma b'ulewa, Ya lek'a kansa cikin d'akin yacewa Umma Habiba "Na tafi nema ko Allah zai sa na samu abunda zamu ci". “Allah yasa a dace”. Ta fad’a tana jin tausayin Mijin nata, ba k’aramin jarabawace ba magidanci ya samu kansa a halin da cefanen gidan sa ma zai gagare sa, sai mai k’arfin imani ke iya jurewa ba tare da ya fad’a neman haram ba, Malam Garbati haka ya fita gidan ba tare da yanke tsammanin Allah zai kawo yadda zasuyi yau ba, Yayi tawakkali da dogaro ga ubangiji, sai dai ko giyar wake yasha yau ba zaiyi gigin zuwa cin bashi ba, ko aikin k’arfi ne yau d’in zaiyi dan su samu na kaiwa baki, duk da cewar ba isasshiyar lafiya gare sa ba yana fama da ciwon baya wanda wahala ta haddasa masa amma yau zai jure.


********


Rabi daren jiya baccin nata ya zama rabi da rabi, zuciyarta dake cike da k’wadayi da burin mallakar kud’in da YARIMA HALADU ya mata alk’awari ta karkata kan tunani d’aya yadda zata shawo kan KULUWA, so kawai take gari ya waye ta samu KARIME su tattauna, Ayyukanta na yau ta riga kowa kammalawa a gidan nasu, kowa sai da yayi mamaki kasancewar kullum ita ake bari k’arshe, kafin ma ta fito daga d’aki tayi aikin sai mahaifiyarta ta sha fama da ita, gidansu gidan yawa ne matan babansu uku, yara ashirin da d’aya, Girkin gidan had’e ake yin sa hakan yasa aka rabawa duka yara matan gidan aiki, kowane da nasa, Rabi da ta kammala nata, wanka tayi ta fito ta shirya cikin zani da ragi, sai kallabi, tai kwalliyarta taja gira tayi d’igo tsakiyar goshi, RABI akwai son ado dan kawai ta rik’a jan hankalin samarin k’auyen nasu, Mahaifiyarta da ta shigo d’akin d’aukar kwanon mahaifinsu zata saka mishi d’umamen tuwo, Ta kalleta tace “Ina zakije da uwar safiyar nan Rabi?”. Dan’ kwalinta taja tana sake tamke sa ta saki jelar sa biyu kan kafad’unta ta kalli mahaifiyarta tace “Gidansu Karime”. “Ina ce dai lafiya ko?”. Tace “Zamuje dubiyar KULUWA ce bata jin dad’i”. Mahaifiyar tata da kulawa tace “Asssha Allah ya yassare mata wahala, idan kinje kice ina mata sannu”. Tace “Amin Inna, zan fad’a mata”. Ta d’auki kwanon ta fita ba tare da mata maganar kwalliyar tata ba sanin halin yar’ ta ko aikenta akai shago sai tayi kwalliya take fita, 



Rabi tana tafiya tana girgiza jiki dan taja hankalin maza, idan tazo gungun su har wani canza salon tafiya take, Shaid’anun cikinsu su dinga bin ta da kallo, wasu ma su taya, ba tare da jan aji ba take kula su,


Gidansu KARIME madaidaici ne ginin k’asa sai dai yafi nasu KULUWA wadata da tsarin gini, dan mahaifinta nada rufin asirinsa daidai gwargwado manomi ne, a tsakar gida RABI ta sameta tana wanke wanke, Ta d’aga kai tana kallon RABI tace “Kece da safiyar nan, ko kinzo kawo mun nawa kwason ne?”. Murmushi Rabi tayi tana k’arasowa cikin gidan, taja turmin dake gefen Karime ta zauna, Tace “Gidan naku ba kowa ne, ko basu tashi ba”. Karime tace “Sun tashi, bayan karin kumallo kowa ya koma d’aki kinsan garin yau da sanyi, Baba ne kad’ai ya fita gona”. Rabi ta matso gaf da Karime tayi k’asa da murya ta zayyane mata duk yadda sukayi da YARIMA HALADU, Kai ta jinjina tace “Tabb babbar magana, kinsan dai halin KULUWA ba sai na fad’a miki ba, ba zata tab’a yarda ba”. Rabi tana kallon Karime ranta ya soma b’aci tace “Ya kike magana haka, ke da nazo muyi shawara yadda zamu shawo kanta, dubu hamshin fah, muna gani zata wuce mu”. Karime tace “Ni bama kud’in ba, KULUWA nake tausayi irin rayuwar talaucin da take, ko suturar arzik’i bata da, idan ta amince da YARIMA HALADU ai zata shana”. Rabi harara ta gallawa KARIME tace “Ke ta KULUWA kike yi ba ni ba, ita kike hangowa arzik’in da zata samu”. Karime murmushi tayi tana kallon Rabi tace “Ba haka bane, dukkanmu kinsan iyayenmu sunfi nata, ki duba duk garin nan ba wanda ya kai mahaifinta cin bashi”. Rabi tace “Kinga kuwa ta samu na biyan bashin mahaifin nata”. Karime tace “Hakane, bari na gama wanke wanken muje gidan nasu”. Rabi tace “Bari na tayaki duk da bana so na b’ata kayana”. Ta saka hannu suna yin wanke wanken tare.



*****************

K’amshin designer turare na arsasi ne ya gauraye d’akin, ko ba’a fad’a maka daga yanayin k’amshin zaka shaida mai tsada ne, Shigar dake jikinsa ta kaki na sojoji masu manyan muk’ami ta masa kyau sosai, ba

kasafai yake saka kayan ba sai idan buk’atar hakan ta taso wanda ya danganci aikin su, hannun sa ya kai saitin aljihunsa inda tag na muk’amin sa ke jere, ya gyara zaman su, Ya d’auki hular sa dake kan gado ya d’aura kan askaken gashin kansa, ba’a san sojoji da barin sumar kai ba hakan yasa shima kullum cikin aske ta yake, K’afafunsa sanye suke da rufaffun takalmi masu tsada suma, sai dai duk kyaun da shigar sa tai, fuskarsa sam babu walwala, damuwa tayi kane kane a zuciyar sa, Wayoyinsa k’ira’ar sumsung da iphone 14 ya d’auka kan madubi ya zuba aljihun gaban rigar sa, Ya fito d’akin nasa zuwa b’angaren UMAIMA cike da fatan ya samu tsohuwar UMAIMAN SA ba wannan sabuwar ba da dabi’unta suka sauya,


Abunda ya fara cin karo dashi yasa shi runtse ido ya sake bud’ewa dan tabbatar da ba gizo idon sa ke masa ba, Yaran sa ne mafi soyuwa gare sa kwance k’asan carpet na falon, Aydah da uniform tun na jiya, Cikin tsananin b’acin rai da ya mamaye zuciyarsa lokaci d’aya, Ya nufin gun yara, Hannu yasa ya d’auki Ayrah, Ya tashi Aydah a hankali, ta bud’e idonta tana cewa “Mummy am hungry”. Ransa ya sake b’aci ya shafa kan yarinyar yace “Zauna anan ina zuwa”. Ya kwantar da Ayrah kan kujera duk rigimar da zasuyi da UMAIMA baya son yi gaban yaran sa, 


Da k’arfin da bai tab’a tura k’ofar d’akin ba, ya tura, UMAIMA na zaune kan dressing mirror da alama wanka ta fito tana shafa cream a jikin ta, MAJOR UMAR da rinannun idonsa da suka juye tsabar b’acin rai yace “Wane irin rashin hankali ne zaki bar yara su kwana a falo”. Cream ta d’iba ta murza a hannun ta, hankali kwance ba tare da kallesa ba tace “Rashin hankali ko kuma sanin yancin kai”. Wani irin kallo na b’acin rai yake mata yace “Har akan yaran cikin naki suma kula dasu rashin yancin kai ne”. Juyowa tai tana kallonsa har lokacin tana zaune bata fasa shafa mai a jikinta ba tace “K’warai kuwa, d’awainiyarsu ai wahala ce bayan za’a iya d’auko NANNY da zata kula dasu tunda cikinsu babu mai shan nono”. MAJOR UMAR kallonta yake yana ganin tamkar canza masa ita akayi ba UMAIMA d’insa ce da ya sani ba ko kuma mai sabuwar shafar aljanu yace “Are you okay UMAIMA?”. Tashi tayi tsaye duk da irin kwarjinin da yake mata har tana jin shakkunsa cikin ranta amma tuna matuk’ar ta saka tsoro ba zata samu abunda take so daga gare sa ba ta danne tace “Kana tantamar ko nice, to ka daina UMAIMA SALISU KABARA CE a gabanka ba wai wata aka canza maka ba, sai dai wannan mai cike da sanin ciwon kanta ne yanzu sab’anin wacce ka sani a baya mai bauta maka”. MAJOR UMAR cikin zafin rai ya d’aga hannu tamkar zai zabga mata mari yayi saurin saukewa, UMAIMA wacce har ta kid’ima tana jiran saukan yatsun hannayensa kan fuskarta, Ta d’ago tana kallonsa cike da tsiwa tace “Mari na shine kuskure mafi girma da zakayi a auren ka”. MAJOR UMAR ajiyar zuciya mai nauyi yaja, ya juya ya fita d’akin yana k’ok’arin saita zuciyar sa, UMAIMA ta fara kai k’arshen hak’urin sa, MAJOR UMAR baya son raini ko ga sa’aninsa balle wacce yake ganin tana k’ark’ashin kulawarsa da umarnin sa, sai dai girman soyayyar da yake mata tasa yake kasa d’aukar mataki a kanta, 


Falon ya dawo yana saita natsuwar sa, ya aro murmushi ya d’aura kan fuskarsa saboda yaran sa, Har lokacin Ayrah nata baccin ta, Aydah na ganinsa tace “Daddy please amun wanka jiya Mummy tace bata da lafiya, ka ga da uniform nayi bacci”. Fuskarta ya shafa yace “Yanzu za’a miki kinji My baby”. Kai ta d’aga masa tace “Okay Daddy and ina jin yunwa sosai bamu ci abinci ba mukayi bacci”. Ransa yaji ya sake harzuk’a, meke damun UMAIMA da har yaran data d’auka a cikinta tayi sanadin kawosu duniya suma take azabtar dasu haka, a zaton sa ko shi ya mata laifi zata hukunta sa ba zata yi da yaran ba, Tunanin yai k’ok’arin kawar wa ganin yin sa zai cigaba da haifar masa b’acin rai ne, Mik’ewa yayi yana nufar hanyar da zata sada shi da kitchen, tunda ya kammala ginin gidan suka tare bai tab’a takawa zuwa kitchen ba, UMAIMA mace ce mai zafin kishi sam bata yarda ya shiga kitchen dan kar yaga masu aikin duk da tasan halin sa ba mutum bane mai son mata ko doguwar mu’amala baya son ta had’a sa da mace amma tana tsananin kishin sa da taka tsantsan, Yau da ya shigo kitchen d’in ba k’aramin daburcewa ma’aikatan sukayi ba, dan tsawon zamansu gidan basu tab’a ganinsa ba, kowaccensu kallo d’aya ta masa ta mayar da kanta k’asa wani irin kwarjini ya musu, a ransu suna jinjina kyau da had’uwarsa da cewa dole uward’akin tasu ta hana a gansa, 


“Wacce tafi tsafta a cikin ku, taje ta kula dasu Aydah mamansu bata jin dad’i”. Yayi maganar cikin bada umarni ya juya ya fita kitchen d’in, bashi da wani zab’i ne kawai yasa zai bari mai’ aiki ta kular masa da yara, Kallo kallo suke ma juna, k’amshin turarensa har ya kama kitchen d’in yana mamaye na girki, Asabe tace “Hafsatu kinfi dukkanmu tsafta da wayewa ke ya kamata kije”. Babbar cikinsu tace “Eh Hafsatu kije”. Numfashi taja tace “Ina tsoro kunsan fa bama komai na yaran nan, Anty ke yi”. “Na kwana biyu ne zakiyi, baki ji yace bata jin dad’i ba”. Hafsatu ta amsa ne kawai dan ba yadda zatayi ba amma ko jin muryar MAJOR UMAR karon farko yau ya sakata fargaba kada tayi abunda bashi ba a kore ta a gidan dan daga ji bashi da sauk’in kai.



Ko KARIME DA RABI ZASU SAMU SHAWO KAN KULUWA


UMAIMA ME TAKE SO A WURIN MAJOR UMAR NE DA YASA TAKE MASA HAKA


SADIYA NASIR DAN

TARE DA ZEE YABOUR