KULUWA

SHAFI NA SHIDA

by @zeeyabour20

*KULUWA*


  *NA*


*ZEE YABOUR*

   *DA*

*SADIYA NASIR DAN*



*YAN TAGWAYE BIYAR*  

  *ZANGO NA BIYU*


*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*


SHAFI NA SHIDA


Kishingid'e take kan tabarmar d'akinta, idonta lumshe a kallon farkon idan ka mata zaka ce bacci take, sai dai a zahirin gaskiya ba baccin take ba, nisan tunani ta tafi mai had'e da damuwa wanda ya haddasa sauyawar yanayin ta, Muryarsu Karime da tajiyo daga tsakar gida, Ta bud'e lumsassun idon ta da ake cewa sexy eyes, cike da mamakin me ya kawo su gidan nasu da safiyar nan, tana fatan lafiya, Bata musu shamaki da shiga d'akin nata ba hakan yasa a duk sanda suka zo, suke shiga kai tsaye, Karime ta fara kutsa kai cikin tsakurrurin d'akin wanda ba zai ci mutum biyar ba, Rabi ta rufa mata baya, "Sarkin zaman d'aka wai ke ko fitowa bakiyi kuyi hira da UMMA". Karime ta fad'a tana zama kusa da KULUWA wacce tayi murmushin da iyakacinsa fatar baki zuciyarta babu wata natsuwa, Rabi tana kallon KULUWA zuciyarta na k'ara shaida mata dole ta rikita YARIMA HALADU dan Allah ya mata wani irin sihirtaccen kyau ga k'irar jiki mai kyau, KULUWA tana kallonsu tace "Ina fatan lafiya naga baku tab'a zuwan safiya irin haka ba". Rabi tace "Babban kamu kikayi". Karime ta k'ara da cewa "Gaskiya KULUWA ke mai sa'a ce". Kallo take musu na nuni da cewa bata fahimci inda zantukansu suka dosa ba, Karime ta kamo hannun KULUWA tana kallon ta tace "Abunda zan sanar dake Dan Allah kada ki watsa mana k'asa a ido, ko ba dan kanki ba ki duba rayuwar da mahaifinki yake ciki". Rabi tace "Dama ce kika samu na yanke hannun riga da talauci". "Ku sanar dani kai tsaye abunda kuke son fad'a ban gane wannan karatun naku ba". Karime tayi murmushi tace "YARIMA HALADU ne ya gani yana so kuma matuk'ar kika amince dashi ba k'aramin arziki zaki samu ba". Wani irin kallo take ma Karime ta fisge hannunta daga rik'on da ta mata tace "Ta wurinku ya biyo kenan, ina so ku koma ku sanar dashi ni KULUWA ba zan tab'a bada kaina ba akan k'azantar duniya". Kallon juna sukai Karime da Rabi, Kafin Rabi tace "Wannan tsaurin ra'ayin naki ki sani ba inda zai kai ki KULUWA, a irin rayuwar nan da muke ciki da babu tausayi ko imani a zuciyar masu hali na taimakon talaka, masu taimakon k'alilan ne, ke kin samu damar da zaki huta, iyayenki har mu k'awayenki mu yanke hannu riga talauci amma kina k'ok'arin sa k'afa ki shure". KULUWA dukkan sauran far'ar dake kan fuskarta ta d'auke mamakin RABI na kamata cikin muryar dake nuni da b'acin rai tace "Ban tab'a damuwa da talaucin da nake ciki ba, balle ya kaini ga ba da mutuncina dan tsira daga gare sa, nayi mamakin yadda idonku ya rufe akan duniya kuke ganin dacewar haka". "Dama nasan zaiyi wuya ki fahimcemu amma ki sani amfanin kanki ne, Rabi tashi mu tafi". Karime tayi maganar a k'ufule tana duban Rabi wacce jikinta yayi sanyi tana jin ba zata iya hak'ura da dubu hamsin d'in da YARIMA HALADU ya mata alk'awari ba dole su shawo kan KULUWA, Cikin taushin murya tace "Kada muyi fushi KARIME indai taimakonta muke son yi, dole sai mun bi a hankali". KULUWA kallon mai cike da takaici ta ma RABI ta kasa furta komai, ba da kanta ga wani d'a namiji da sunan zina abunda Allah ya hane mu da ko kusantar ta suke kira taimako, Idonta ta runtse tana jin bata son ganin su ya zama dole ta nisanta kansu dasu, ba k'awayen kirki bane, dan duk k'awa tagari ba zata ja ka ga hanyar banza ba, Karime ranta taji ya sake harzuk'a ganin KULUWA ta rufe ido tace "Kalli ki ga, bata son ganin mu, kawai ki tashi mu tafi". "Tafiyar taku itace alkhairi gareni". KULUWA ta fad'a har lokacin idonta a rufe, Rabi jin haka tasan ko ta zauna ba zatayi nasarar shawo kanta ba, yasa dole tabi KARIME suka tafi, a ranta tana sak'e sak'e yadda zata shawo kan KULUWA, taci d'amarar cikar burinta dan mallakar dubu hamsin, KARIME a hanya tana ta masifa KULUWA bata tab'a mata rai irin yau ba, RABI ta numfasa tace "Haba Karime kina magana kamar dai baki san wacece KULUWA ba". Karime rai b'ace tace "Kina gani fah daga taimako tana neman gaya mana magana, ni wallahi tausayin halin da take ciki yasa na amince zan mata magana". Rabi cikin sigar lallashi da son sake shawo kan KARIME tace "Hak'uri zakiyi anjima mu dawo watak'ila ta amince". Wani kallo Karime ta mata tace "Tab ba dai ni KARIME ba, kinga na zame hannuna ke dai kije kiyi tayi". Dole Rabi taja bakinta tai shiru, a ranta tana jin ko babu taimakon KARIME ita zata cigaba da gwada sa'ar ta.



*******************


Karo na uku da ta kalli kanta a madubi dan son tabbatar da komai ya tafi kan tsari da shigarta, glasses da ya mamaye fuskarta ta sake gyara zaman sa ya saitu tsakanin idanunta zuwa karen hancin ta, ba k'aramin kyau ya mata ba, ta kai hannunta kan kwalbar turaren dake kan teburin gabanta ta fesa tana bin dukkan kayan jikinta zuwa mayafinta ta bad'e da turaren, wanda a take d'akin ya d'auki k'amshinta, Ba tare da ta damu da kasancewarta matar aure ba, K'aramar jakarta mai tsada ta d'auka, ta rik'e a hannu, d'ayan hannun kuma wayarta k'irar 15pro max, wacce ta siya kwanaki kad'an da suka shud'e a cewarta ta girmi 14 yanzu, wacce tare MAJOR UMAR ya siyan musu, tsawon shekaru waya iri d'aya yake siyan musu, kala kad'ai ke bambamta, Cikin taku na k'asaitattun mata masu ji da kansu had'i da naira ta fito d'akin nata, Ba tare da ta damu ta duba lafiyar yaranta ba, Tayi k'ofar da zata fitar da ita zuwa farfajiyar gidan, 


Motarta ta fara k'irar mercedez wacce take fes da alamu safiyar yau an wanketa ya sake bayyana sabuntar ta dake nuni da ba'a da siyan ta ba, Ta bud'e mazaunin direba ta shiga, ta zauna tayiwa jakarta da waya ma'ajiya kan kujerar gefen mai zaman banza, ta tada motar tana saita sanyin ac, ta kunna wak'a cikin album na wak'ok'in UMAR M SHAREEF, Taja motar ta fita gidan, a kallo d'aya idan ka mata a motar zaka sakata cikin jerin rik'akk'un matan bariki dan sam shigarta da yanayinta baiyi kalar mace mai d'auke da igiyiyon auren wani a kanta ba,


Babbar ma'aikatar MINISTRY OF FOREIGN AFFAIRS tayi parking motar ta, daga waje ta soma amsa gaisuwar k'ananun ma'aikata wanda basu kai matsayinta a gun ba, har zuwa ciki tana gaisawa da sauran abokan aikinta, lift ta shiga ya kaita 2nd floor wanda anan office d'inta yake, Ta wuce kai tsaye ciki madaidaicin office ne a tsaftace da alama kullum yana samun gyara ga k'amshin air freshner da ya gauraye sa, zamanta ba jimawa ta soma jin knocking, "Come in". Ta bada umarnin shigowa, tana kai kallonta ga k'ofar, Murmushi ya wadatu kan fuskarta ganin wacce ta shigo ZULAI MAIKUSA kallo d'aya zaka mata kasan ta gogu da naira kuma macece mai ji da gayu, suturarta da shigarta zata shaida maka haka, "Wankan naki na yau fah ya d'auko hajiyata". UMAIMA ta fad'a tana kallonta cikin matuk'ar burgewa da yabawa, Murmushi ZULAI tayi tana jan kujera mai fuskantar UMAIMA ta zauna, Tace "Macen da tasan kanta kenan". Umaima manyan zobunan dake sanye hannun ZULAI take kallo wanda ko ba'a fad'a maka kud'insu ba kasan ko a cikin gwal manya ne, ZULAI tana sake gyara zamanta tace "Ya kukayi da sarkin mulkin mulkar naki wanda ko a zamanin sarki da baiwa sai haka". Umaima baya ta d'an yi tana jingina da bayan kujera taja numfashi tace "Da alama bada jimawa ba zan samu biyan buk'atata, dan jiya har hannu ya d'aga tamkar zai mareni". ZULAI wata irin dariya tayi mai ma'anoni daban daban tace "Ki cigaba kada ki sassauta masa ko na second d'aya matuk'ar kina so kiyi rayuwar yan' ci kema a dama dake kamar sauran matan". Kafin UMAIMA ta bata amsa, Muryar SARATU HASSAN ta katse ta "Me kuke tattaunawa yau babu ni". ZULAI DA UMAIMA kallonsu ya koma kanta itama shiga ce ta kece raini a jikinta, ga zobunan zinare zagaye da hannyenta kallo d’aya zaka mata kasan bata cikin jerin mata masu amsa sunan MATAN AURE, Umaima ganin shigar SARATU sai take jin duk ta muzanta a cikinsu sun fita shiga mai kyau da tsada, zoben zinari biyu kacal ne a hannunta amma kowacce cikinsu tana da ya kai biyar a yatsun hannayen ta masu tsada, SARATU ta k’araso ciki tana jan kujerar kusa da ZULAI ta zauna tace “Ku fad’a mun wacce miyar kuka sha babu ni”. ZULAI tace “Zancen ita da gogan nata ne”. SARATU tace “Ina fatan ya fara d’aukar karatun”. UMAIMA ta jinjina kai tace “K’warai”. “Kada ki kuskura ki karaya ko son sa ya saka ki kasa cigaba idan ba haka ba ke da rayuwar yanci har abada”. Murmushin gefen baki tayi tace “Ku zubo ido kawai ku jira lokaci”. Shewa sukayi tare suka tab’a hannu, Sun jima suna tattaunawa kafin kowacce ta nufi office d’in ta, dukkansu ma’aikata ne a ministry d’in wanda suka zama aminan juna,



*******


YARIMA HALADU tsakanin jiya da yau sam ya rasa natsuwar sa akan KULUWA, bai tab’a had’uwa da macen da ta hargitsa masa tunani da hana zuciyarsa sukuni irin KULUWA ba, da ya rufe idonsa suffofin jikinta ke masa yawo yana jin tamkar ya ganta a gabansa ya kauda kwad’ayin sa, Zaune suke da MAMMAN k’arkashin wata babbar bishiya wacce mafi yawa lokuta idan yana k’auyen nan ne majalisar sa wurin zaman sa, Kallonsa ya kai ga MAMMAN yace “Matuk’ar ban samu yarinyar nan ba, bana jin ko makaranta zan iya komawa”. Mamman a ransa ya jinjina irin k’wadayin da YARIMA ya saka kanta lallai ba k’arami ba ne, A zahiri yace “Zaka sameta ma YARIMA, da kanta zata zo”. “Kaje ka samu k’awarta RABI kusan yadda zaku kawo mun ita yau”. Yayi maganar cikin bada umarni, yana runtse idonsa cikin wani irin yanayi, MAMMAN kallon YARIMA HALADU yayi yana nazarin yanayin sa kafin yace “Kawota yau zaiyi wuya yau YARIMA, kasan taurin kan yarinyar”. “Ba dole sai da amincewarta ba, kawota kawai nake buk’ata kuyi”. Yayi maganar a fusace, MAMMAN dole ya amsa da to yana mik’ewa ya bar wurin, YARIMA HALADU yana jin a yau zai karya alk’awarin da yayi ma kansa na bazai tab’a yiwa wata ya’ mace fyade ba, duk macen da zai tara da ita sai da amincewarta, a yadda ya zak’u da KULUWA yana ganin zata masa wahalar samu, ta hanyar fyade kadai yake jin zai iya kawar da sha’awar sa kanta.


*******

MALAM GARBATI aikin sarar ice yau ya wuni yi duk da yadda bayansa ke kwank’watsa yana jin k’ashin tsakiyar bayansa tamkar zai tsage biyu haka ya daure, dan ganin yau ya samu kud’in abunda zasu kai bakin su, Ana kiran sallar la’asar ya ajiye gatarin yana goge zufar da ta mamaye goshin sa tamkar ruwa yadda har wuyansa gumi ne, “A’ah Malam GARBATI ya ka ajiye kuma”. Cewar Mai itachen, Malam Garbati dake sauke numfashin gajiya yace “Zanje sallah ne”. TSALHA MAI ITACE yace “Ka k’arasaa sare icen nan guda d’aya sai na sallameka ka tafi gaba d’aya”. Malam Garbati kai ya girgiza yace “Bana son rasa jam’i ka bari na dawo”. TSALHA fuska ya tamke sosai yace “Idan ka b’ata mun lokaci nima sai na b’ata maka naka wurin biya”. Malam Garbati jin ana neman tada iqama yayi saurin wucewa ba tare da ya tsaya ba TSALHA amsa ba, Kwafa yayi yace “Zaka gane”. 



SADIYA NASIR CE

TARE DA ZEE YABOUR