KULUWA

SHAFI NA BAKWAI

by @zeeyabour20

*KULUWA*


  *NA*


*ZEE YABOUR*

   *DA*

*SADIYA NASIR DAN*



*YAN TAGWAYE BIYAR*  

  *ZANGO NA BIYU*


*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*

 


SHAFI NA BAKWAI


Babban d’akin taro ne na manyan sojoji masu babban muk’ami a nigeria wanda taron ya had’a da shugaban k’asa da mataimakinsa tare da masu ruwa da tsaki cikin harkar tsaro na k’asar, Tattaunawa ke gudana kan matsalar rashin tsaro da yan’ bindiga da garkuwa da mutane sukai yawa, musabbabin taron shine garkuwa da wani babban dan’ siyasa da sukayi a hanyar sa ta zuwa k’auyen kaduna gaisuwar mutuwa, Shugaban k’asa yayi magana kan dole a saka tsaro sosai tunda matsalar har ta kai ga sun fara harin manyan mutane, MAJOR UMAR maganar tasa batai tsawo a ciki ba, dalilai biyu suka saka shirun nasa yawaita a cikin tattaunawar matsalar UMAIMA wacce ta hana zuciyar sa natsuwa, na biyu ganin tsawon shekarun nan da ake sace sacen mutane da kashe kashe ba’a tab’a taro na yadda za’a shawo kan matsalar ba sai yanzu dan ya shafi wani babba, su talakawa basu da daraja ko yan’cin da ya kamata tuntuni ace anyi k’ok’arin basu kariya, sau tari saboda matsaloli irin haka ya kan ji tamkar ya ajiye aikin sojan, sai dai abu ne da ya taso da sha’awar sa tun yana k’arami babban burinsa ya zama soja dan yaba al’umma kariya, haka yasa ya taso jajirce, MAHAIFINSA BASHAR LEMA shi ya shige masa gaba har ganin ya kawo matsayin da yake yanzu a soja wanda jajircewarsa da k’wazo sa uwa uba kuma taimakon mahaifinsa yasa ya samu matsayin MAJOR a k’ananun shekarunsa, wanda sai mutum ya jima yana hidamtuwa cikin aikin soja kafin ya samu muk’amin, Zaman kusan awanni biyu ya d’auke su suka kammala tattaunawar, Shugaban K’asa da tawagarsa suka fara ficewa daga d’akin taron, Sojojin sun sake tasu tattaunawar kafin suka watse, MAJOR UMAR a daidai lokacin nan gida ya dace ya koma, sai yake jin baya sha’awar komawarsa gidan sab’anin lokutan baya da ba inda yafi masa dad’in zama kamar gidan nasa saboda soyayya da kulawar da yake samu daga UMAIMA, Numfashi yaja tare da shafa fuskar sa, sai yanzu ya ankara kowa ya fice batare da ya sani ba yayi nisa cikin tunani, Mik’ewa yayi ya fito, Baya jin akwai inda zai samu natsuwa yanzu da ya wuce gun mahaifin sa, yasan ganinsa zai rage masa damuwa, Bayan shigar sa mota, Gidan mahaifinsa ya umarci direban su tafi, Sojan da shine escort d’insa ya kira direban motar sojojin da ako da yaushe suke tare da MAJOR UMAR dan matsayin sa da kuma basa kariya, ya sanar dashi, MAJOR UMAR jingine yake da kujerar mazaunin baya idonsa a bud’e sai dai a zahiri ba kallon abubuwan dake gabansa yake ba, ganinsa ya tafi ga tunanin k’wak’walwarsa wanda ya haddasa masa rashin walwala da natsuwa zuci, 



*******


MAMMAN umarnin YARIMA HALADU kawai yabi yazo gidansu RABI sanin ta k’ark’ashinsa yake samu, yana gudun abunda zai yanke alak’ar tasu amma yana da yak’inin zai yi wuya su shawo kan KULUWA ta amincewa buk’atar YARIMA HALADU, Dan bazai tab’a yin sanadin da za’ayi wa wata fyade ba, Allah ya saka masa ragowar imanin tunanin idan k’anwarsa ce ya zai ji, Daga gefen dakalin kofar gidan nasu ya tsaya, Ya aiki yaro ciki ya masa iso da ita, RABI na jin kiran daga MAMMAN ne, tai zumb’ur tayo waje dama tana buk’atar ganin nasa, tun dawowarta daga gidansu KULUWA take faman sak’a da warwara, hankalinta ya tafi ga abu d’aya yadda zata shawon kan KULUWA. MAMMAN cikin barkwanci yana kallonta yace “Wannan fitowa da sauri haka kamar mai jira?”. Guntun murmushi tayi tace “Dama jiranka nake, ina tunanin ina zan ganka muyi magana”. MAMMAN yace “Sai gashi Allah ya kawoni, ina fatan labari mai dad’i zanji na kin samu shawo kan KULUWA?”. Rabi kallonsa tayi yanayin fuskarta na canzawa zuwa damuwa k’arara tace “Wallahi bata amince ba, hasalima rabuwar ba dad’i mukayi”. MAMMAN ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke yace “Tirk’ashi, Ga YARIMA yasa naci akan yarinyar nan, ban tab’a ganin ya nuna kwad’ayinsa k’arara akan mace ba kamar ita”. Rabi ranta taji ya sosu tana jin b’acin rai yadda KULUWA ta rikita YARIMA HALADU ba ita ba, Danne b’acin ranta tayi ganin ba hurumin yin sa bane yanzu, kuma ko ta nuna jin haushinta kanta kad’ai zatayiwa asarar kud’in da zata samu wanda a tsawon rayuwarta bata tab’a rik’e su ba, Kallon MAMMAN tayi tace “YARIMA ya fitar da kud’i ya siya kayan abinci, ya bani na kai gidansu”. Mamman yace “Me hakan ke nufi kenan, dan naga abun duniya baya gabanta”. Rabi tace “Kai dai kayi yadda nace”. MAMMAN yace “Akwai kud’i wurina muje kawai a siya, muradi yanzu a samu biyan buk’ata, ko nawa na kashe nasan matuk’ar YARIMA ya samu abunda yake so zan samu ninkinsu”. Rabi tace “Ba zai yiyu na bi ka ba, kasan mutanen garin nan da sa ido”. Mamman kai ya jinjina cikin gamsuwa da zancenta yace “Bari naje na siyo na dawo”. MAMMAN ya wuce, RABI ta koma cikin gidansu cike da fatan shirin nata yayi aiki.


**********

“Ka tafi zuwa gobe da yamma ka dawo ka amshi kud’in aikin ka, kuma na rage d’ari biyar daga yadda mukayi ciniki”. Cewar TSALHA MAI ITACE yana kallon MALAM GARBATI a k’ask’ance, “Haba Tsalha na wuni aiki kace sai gobe da yamma kuma, sannan ice d’aya ne ban faskare ba shima sallah naje, amma ka zabge har d’ari biyar”. TSALHA a gadarance yace “Ina ce sai da na gargad’eka kar ka tafi sai ka gama”. “SALLAH ai tana gaba da komai TSALHA, kiran Allah na amsa”. Malam Garbati yai maganar a marairaice yana tsananin buk’atar kud’in ko dan KULUWA ta samu abunda ta kaiwa bakin ta, TSALHA ba alamar tausayi kan fuskarsa yace “Mu kiran shaid’an muka tsaya amsawa ai, tunda kafi kowa addini”. “Dan Allah kayi hak’uri ka bani hakk’ina yanzu”. Hula ya tura gaban goshin sa yace “Na gama magana”. Ya gyara zamansa kan kujerar robar da yake ajiyewa a gun dan zamansa yana kallon masu masa aikin faskare, Ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya, Wani magidanci dake gefensu yana sana’ar siyar da itace ganin rashin dacewar haka yacewa TSALHA “Kayi hak’uri ba na maka katsalandan ba amma babu kyau a musulunci mutum ya maka aiki kak’i biyansa a lokacin da ya dace anfi so ka biyasa kafin zufar jikinsa ta gama tsanewa”. Tsalha wani mugun kallo ya masa yace “A musulunci kai meye hukuncin naka na yin shishshigi ina ce ance mutum ya bar abunda babu ruwansa”. “Allah ya baka hak’uri”. Yai maganar yana Allah wadarai da rashin mutunci irin na TSALHA a ransa, “ MALAM GARBATI ganin da gaske ba basa zaiyi ba, ba mutum bane shi mai hayaniya ko tashin hankali hakan yasa bai tsaya rigima ko doguwar magana da TSALHA ba, sai dai zuciyarsa babu dad’i ya bar wurin, yana tafiya yana jin yadda bayansa ke kokawa alamun ciwo, zufar gajiya da ciwon jiki na tsattsafo masa haka ya taho gida, hannu biyu yadda ya fita haka ya koma, A tsakar gidan ya sami UMMA HABIBA da KULUWA tana kitse mata gashin ta mai cika sosai sai dai bashi da dogon tsayi amma bak’i ne wulik haka bashi da tauri, A tare suka masa Sannu da Zuwa, Ya amsa yana zama yace “Wash”. “Sannu”. Suka fad’a tare, Yace “Yawwa”. Yana jingina da bango ya mik’e k’afafun sa, zaman nasa sai yaji duk wata gajiya tana tattaro masa jikinsa na wani irin ciwo, Kallonsa ya kai ga KULUWA yace “Ko zan samu wurin zafi”. Tace “Toh Malam”. Tana jan d’an kwalinta ta rufe gashinta ta mik’e, Cike da tunanin me ya gajiyar da mahaifin nata dan alamun gajiya duk sun bayyana tare dashi, tsufan da ya nuna kan fuskarsa ya sake fitowa wanda bai kai shekarun saba, Tana had’a itace tan k’ok’arin hura wuta, Taji Malam Garbati nacewa “HABIBA mutane babu tausayi a ransu, tun fita ta nake aikin faskare wurin TSALHA MAI ITACE amma dan naje sallah yak’i biyawa hakk’ina wai sai gobe da yamma”. Umma Habiba cike da tausayawa take kallonsa tace “Tsalha dama kowa ya shaidesa k’auyen nan da rashin mutunci ba abun mamaki bane idan ya aikata haka sai dai faskaren da kayi banji dad’i ba, kasan fah kana da matsalar ciwon baya”. A raunane yace “Ya zanyi HABIBA dole ce ta saka, bazan iya zuba ido ina ganin KULUWA cikin yunwa ba, nayi ne saboda ita amma yak’i biyana, sau tari na kan ji na gaza a matsayina na uba da ko abincin da zata kai bakinta bana samar mata”. UMMA HABIBA shiru tayi ta kasa cewa komai dan ita kanta sau tarin hakan take ji sun gazawa KULUWA.


KULUWA duk wani kuzarinta taji ya yanke, tausayin mahaifinta na cika dukkan wata kusurwa ta zuciyarta, hawaye da suka taro idanunta take k’ok’arin tsaida su, suka rinjayeta suna sauka kan kumatun ta, hura wutar take amma zuciya ruhi da gangar jikinta babu dad’i, Ba abunda ke dagula mata lissafi ya sakata rashin walwala kamar damuwar iyayenta, Jiki sanyaye ta d’aura ruwan, Ta koma gun iyayenta, Kanta ta sunkuyar k’asa cikin sanyin murya tace “MALAM ban tab’a jin ka gaza a matsayinka na mahaifina ba, idan ma har nace haka nayiwa Allah shisshigi domin shi ya jarabceka da rashi, har kullum ina alfahari da kasancewar kai da UMMA iyayena dan kun tsaya dan ganin kun bani tarbiya wanda itace babbar gatar da zaka ma yaron ka, haka kulawa da soyayyar da kuke nuna mun kad’ai ta isheni farin ciki da jin nayi sa’ar iyaye”. Malam GARBATI da Umma Habiba basu san sanda murmushi ya sub’uce musu ba, na farin ciki da godiya ga Allah da ya basu yarinya irin KULUWA mai hankali da hangen nesa, wanda har ya zarta na shekarunta, Malam Garbati sai yake jin tamkar an cire masa wani babban dutse a k’irji da ya danne sa, jin kalaman KULUWA yasa wata natsuwa ta shige sa, UMMA HABIBA ita kanta sai take jin sanyi a zuciyarta, KULUWA sanyi ke ratsa zuciyarta na ganin damuwar dake malale kan fuskar iyayenta ta kau, zuwa ga wadatuwar murmushi kan fuskokin nasu.



********

Kayan abinci masu yawa MAMMAN ya siya, Ya kaiwa Rabi wacce taji tamkar ance duka mallakinta, sai dai tayi saurin kwab’ar zuciyarta, Ta kwashi ledojin ta samu k’aramin yaro a gidan nasu ya d’aukar mata k’aramin buhun shinkafa ba tare da mahaifiyarta ko wani d’an gidansu ya sani ba, shima yaron ta gargad’esa kar ya sake ya sanar da kowa, Ta saka shi gaba suka nufi gidansu KULUWA, Ta juyewa MALAM GARBATI ruwa kenan ta kai masa band’aki, Zata shiga d’akinta taji muryar RABI, tsintar kanta tayi da fad’uwar gaba karon farko da zuwan RABI gidan nasu, A ranta tace “Idan ma dawowa tayi ta sake jan ra’ayi har abada ba zata samu haka ba”. Tai saurin shigewa d’akinta bata so UMMA HABIBA dake tsakar gida ta fahimci wani abu,


Rabi har k’asa ta duk’a ta gaishe da UMMA HABIBA wacce ta amsa tana bin buhun shinkafar da k’anin Rabi ya ajiye da kallo, Wanda yana ajiyewa ya juya ya fita, Sauran ledojin ta ajiye tana dan’ sunkuyar da kai tamkar mai jin kunyar gaske tace “Dama YARIMA HALADU ne ya aiko dasu”, UMMA HABIBA ido ta zaro da mamaki tace “Yana rabon kayan abinci ne”. Kai RABI ta girgiza tace “Ya dai aiko ne wai KULUWA yake so”. UMMA HABIBA a zabure tace “KULUWA”. “Eh Umma Habiba, wallahi baki ga yadda ya rud’e a kanta ba, kuma aurenta ma yake son yi”. UMMA HABIBA kai ta shiga jinjinawa da mamaki ace YARIMA HALADU ya rasa wacce yake so sai KULUWA bayan kaf k’auyen nan tana jin babu wanda yayi talaucin su, Allah kenan mai iko, Umma HABIBA bata san halinsa na neman mata ba dan ba mace bace mai shige shige balle taji labari ko a mak’ota, RABI ganin zancen ya shiga Umma Habiba taji ranta yayi sanyi tana zancen zucin Allah yasa shirinta ya tafi daidai, A zahiri tace “Zan tafi”. “Ba zaki shiga ku gaisa da k’awar taki ba”. “Ina sauri ne, Mama zata aikeni”. “Toh a gaida gida”. Rabi ta fice gidan tana nufar mahad’ar da sukayi da MAMMAN, anan ta same sa yana jiranta, K’ebantaccen wuri ne da babu mutane, Tana k’asa da murya tace “Ka sanar da YARIMA HALADU ya zama cikin shiri daren yau zan kawo masa KULUWA”. “Taya hakan zata kasance?”. Mamman yayi mata tambayar yana kallon ta, “Ka jira zuwa dare”. “Ki tabbatar da hakan ta faru dan YARIMA HALADU baya son sab’a alk’awari musamman yanzu KULUWA da yasa rai akanta”. Wani shu’umin murmushi Rabi tayi tace “Ya samu KULUWA ya gama…


KO MENENE SHIRIN RABI

KU BIYO ALKALAMIN SADIYA NASIR TARE DA ZEE YABOUR DAN JIN ME ZAI FARU?


SADIYA NASIR DAN CE TARE DA

ZEE YOBOUR