Envious
by @realsmasher
💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*
*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*
*♡WAZEER¸.•💥*
(A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)
Bʏ.
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*
_Join our group domin samun update *** And then follow my new channel *** Ba sai na yi ƴar murya ba,please show the real love ɗin nan da kuke min ta hanyar following kunji mutanen kirki._ 😪
15
#Envious
*MUNIBA*
Ana tashi Muniba ta hango su Mami za su tafi,da sauri ta wuce ta fita ta bi su,ta tabbatar idan ta tsaya har sai lokacin da dukansu bride maids suka haɗu sannan za su wuce gida,abunda ya faru ɗazu ne zai sake maimaita kansa,ita kuma bata shiryawa faruwar komai ba,baza ta so a dalilinta ace wani abu mara daɗi ya faru ba,ana taro cikin farin ciki da dariya,ace dalilinta kuma an samu misunderstanding da wani,sai a tafi da ita a baki ana cewa ai saboda ita ne haka ta faru,duk kusancinta da su Khalidah ba lallai ne wasu suyi mata uzuri ba,da haka ta faru kuma gara ma ace tun farko bata zo gurin bikin ba,tana da bala'in gudun zuciya ga saka abu a rai,yanzun nan maganganun da za suyi ta going round,sai su sa kaga ta sauya kamanni ta koma kamar me jinya,dai² lokacin motar Mami da driver yazo ɗaukansu yana shirin tafiya tai maza tai knocking,Mami da suke back seat ita da Mama ta sauke glass tana kallonta tace "ya akayi Sweetheart?" Muniba ta rausayar da kai tace "Mami don Allah zan biku gidan" Mama dake cikin motar also ta karkato kanta tana kallonta tace "daughter ki bari ku taho tare da ƴan uwanki mana" Muniba tace "Mama don Allah,ni gida nake son tafiya,i'm tired da zaman gurin nan" Mami dake ta kallonta tace "da tare muka zo da za ki ce yanzu za ki bimu?" Muniba tayi kalar kuka tace "Mami please ƙafata na ciwo" Mama tayi murmushi tace "Dr ayi haƙuri a barta tazo mu tafi,tunda tana son bin namu" Mami ta ɗauke kanta daga kan Muniba tayi shiru,Mama ta sake yin murmushi tace "Muniba shiga mu tafi" Muniba ta sauke ajiyar zuciya tace "thank u Mama" da sauri bata tsaya ɓata lokaci ba ta buɗe gaba ta shiga,tana rufewa driver yaja mota suka bar gurin. Suna isa line gidan Uncle ɗin nata tace "Mami a sauke ni a nan ba sai an shiga ciki ba" Mami tace "um'um! Ki bari dai har sauran ƴan uwan naki su dawo sai ku tafi,ai kin san masu gidan ma basu taso ba,mene ne amfanin kije kiyi ta zama ke kaɗai?" Muniba tayi shiru bata sake cewa komai ba har suka shiga compound ɗin gidan,driver na yin parking ta sauka motar,a kan idonta su Mami suka shiga cikin gida,tana zaune balcony motoci suka dunga yin parking,ganin sai dawo da mutane ake yi,ta yi zaton zuwa lokacin ya ci su Umma duk sun taho,a hankali ta tashi ta fita ta tafi gidan su Safwa,ta daɗe tsaye a gaban get ɗinsu tana knocking ba'a zo an buɗe mata ba,da alama har sannan a kulle gidan yake,dole tasa ta juyo da nufin ta koma gida ta jira har sanda su Baniynah za su iso,a mugun gajiye take ga baccin da taci bashinsa kuma,data dawo cikin gida ta sake zaunawa a balcony saboda ciki tana jiyo hayaniyar wanda suka dawo,tana gurin motoci suka dunga horn,sai daga baya sannan mutane suke ta shigowa,ana haka Umma suka iso tare da su Bilal dan dukansu suka tafi gurin dinner ɗin,a bakin get ta basu makullin gidan tace suje gida za ta shiga gurinsu Mama,Umma na ganin Muniba ta saki murmushi tace "a'a Muniba! Har kin rigamu dawowa ashe.. Ke kaɗai kika taho?" Muniba ta girgiza kanta tace "a'a! Su Mami na biyo" Umma tace "ni dai fa nace,su Safwa ai can gurin muka baro su,babu alamar nan kusa za su taho" Muniba tace "nima bacci nake ji kuma kaina yana min ciwo shi yasa na gudo,na yi zaton gida a buɗe yake ko da wani da ya dawo,naje naita knocking naji shiru,ciki kuma akwai hayaniya shi yasa na zauna a nan" Umma tace "Allah sarki! Ai kuwa yanzun nan na bawa su Awwal mukulli nace su tafi gida gani nan zuwa.. Bari nai sauri naje naiwa su Hjy Batoolu sallama na fito,sai muje ki samu ki kwanta kafin ƴan uwan naki su dawo" Muniba tace "tou!" Umma na shiga parlour da sallama,su Mami suka amsa mata,ta ɗan tsaya daga tsaye tana murmushi tace "dukanmu ina yini? Ya gajiya? Mun dawo lafiya?" Fuskar Mami da murmushi akai tace "alhmdllh! Sannu Hjy Murjanatu.. Allah ya saka da alkhairi ya bar zaman tare" Umma tayi murmushi tace "ameen² Dr.. Toh! Mu kwana lafiya,zanje gida kafin ƴan matan su dawo,ga Muniba ma zaune a waje tana ta jira,sai gobe kuma in Allah ya kaimu" Mami tace "toh Hjy,Allah ya tashemu lafiya,a huta gajiya,mun gode³ sosai Allah ya ƙara rufa asiri,ya bar zaman tare" Umma ta amsa sannan ta fito Mami da Mama suka rakota suna mata sannu da godiya,Muniba na ganin fitowar Umma ta ɗan juya,Umma ta sauka balcony tana cewa "toh! Muniba taso muje gidan" Muniba tai saurin miƙewa,tsaiwa tayi a guri ɗaya tare da riƙe kanta saboda wani irin sara matan da yayi,dama idan ta shiga hayaniya yana mata haka,tana kallon Mama tace "Mama kaina na ciwo,don Allah akwai drugs ki bani?" Mama tace "ehh akwai bari na shiga na duba miki" Umma na kallonta tace "assha! Daure kizo muje gidan ki huta,zan turo kou Awwal ne yazo ya karɓar miki" Muniba tace "tou! Na gode.. Mami sai da safenku" Mami na kallon ƴarta tace "Allah ya ƙara sauƙi ya tashemu lafiya" Muniba suka amsa ita da Umma. Suna fitowa gidan motar da ya ɗauko amarya da convoy ɗinsu suka yi parking dai² get,Muniba za su wuce ita da Umma taji muryar Baniynah na ƙwalo mata kira,tsaiwa dukansu suka yi,Umma na cewa "madallah! Ga nan ƴan uwan naki suma duka sun dawo,sai mu tattara mu tafi gaba ɗaya" Baniynah na isowa ta riƙe hannunta tana dariya tace "guess what?" Muniba tayi shiru tana kallonta,Baniynah da bata ga alamar wani abu a fuskarta ba tace "zo muje kiga" Muniba ta zame hannunta daga cikin na Baniynah,a hankali maganarta can ƙasa² tace "leave me please kaina na ciwo,ina so naje na kwanta" Umma dake tsaye tace "uhumn! Mu tafi Muniba,sa zo su same mu a gida" Baniynah tayi fuskar damuwa tana kallon Muniba tace "subhanallah! Sannu Sweetheart,bari na sanar masa baki da lafiya kawai" kallo me cike da tuhuma Muniba ta bita da shi,Baniynah tayi murmushi tace "Lieut. Abuu Turab ne fa yace min dama nai miki magana kafin su wuce kuyi sallama" Muniba ta dunga kallonta ta kasa magana,Umma tayi wani dariya tace "iyyeehhh! Suruki akai mana ne?" Baniynah tai murmushi tace "ehh Umma sallama ne bata tsaya sun yi ba ta biyo su Mami,shi ne yanzu suka dawo da mu yace na kira masa ita" Umma tace "a'ahh! Tou kuje mana.. Muniba lallaɓa kije kuyi sallama,ni bari na shiga cikin gida,kafin ku shigo sai nasa aje a karɓo miki maganin" Muniba dai kamar tace baza taje ba take ji,haka nan ta daure ganin Umma ta ce suje tabi Baniynah tana tafiya a hankali,dai² motar da yake ciki suka tsaya Baniynah tayi knocking,a hankali aka sauke glass ɗin motar,Lieut. Abuu Turab daya hakimce a back seat yana kallonsu yayi ɗan murmushin da ba lallai ka gane ba,Baniynah na ƴar dariya tace "Yayana gata nan na samota.. Amma ba ta jin daɗi kuma" hankalinsa akan Muniba da kanta ke ƙasa,yace "what's happening?" Baniynah tace "she said kanta na ciwo,yanzunma zuwa za tayi ta kwanta na gansu" fuskarsa na bayyanar da damuwa yace "so sorry dear.. Amma baza muje hospital ba?" Baniynah na dariya tace "um'um! Idan akwai buƙatar haka,Yaa Khalifa and Yaa Mubasshir are there,someone cikinsu will take care of her" Lieut. Abuu Turab ya ɗan gyaɗa kansa yace "oops! Na manta family ɗinmu akwai yawaitar likitoci" Baniynah ta gyaɗa masa kai tana ƴar dariya,Muniba dai bata ce komai ba kawai tana nan tsaye kamar an sassaƙata,yana kallonta ya ɗan kwantar da kansa yace "bari mu wuce,Allah ya ƙara sauƙi dear.." Muniba ta buɗe bakinta da ƙyar tace "ameen.. Thank u" ya ɗan gyaɗa kansa a hankali yace "ƙanwata a shiga da ita gida ta kwanta ta huta.. And please ba na so wani abu ya dameta,a kula min da ita sosai" Baniynah na dariya tace "done Ƴaƴana" ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe yace "thank u dear.." Hannun Muniba ta riƙo tana kallonta da kyau tace "muje Sweetheart" babu musu ta gyaɗawa Baniynah kai maganarta can ciki kamar ba ta so aji tace "sai da safe" ya amsa yana zubo mata idanunsa,ji yake inama yana da iko da ya cire ciwon daga jikinta ya mayar nasa,sai da sukai nisa kafin ya ɗaga glass ɗin motar driver ɗinsa yaja suka bar line. Suna shiga gidansu Safwa Umma ta amsa sallamar da suka yi,Muniba ta zauna saman kujera,a hankali Baniynah tace "bari naje gida na nemo miki drugs" Umma dake kallonsu tace "na aika Awwal yanzun nan ya karɓo mata" Baniynah tace "ohh! Tou bari na zauna" ba'a jima ba Awwal ya shigo da sallama Umma suka amsa,ya shigo tare da cewa "Umma ga maganin" Umma tace "yawwa! Muniba za ka bawa,itace kanta yake ciwo" yace "ayyah! Allah ya sawaƙe" Muniba da ko magana ba ta son yi ta karɓa tace "thank u" Umma na kallon Baniynah tace "Baniynah samo mata ruwa a kitchen" Baniynah ta tashi ta tafi kitchen ta samo mata ruwa mara sanyi ta bata,Umma na kallonta tace "sannu Muniba" Muniba tayi ɗan murmushi tace "yawwa" Umma tace "za ki iya zuwa kiyi wanka kou? Sai kiyi kwanciyarki ki huta" Muniba tace "ehh" Umma tace "toh! Lallaɓa ki tashi,Allah ya ƙara sauƙi" ta amsa tare da tashi tace "sai da safe Umma" Umma tace "Allah ya tashe mu lafiya" ta amsa,Baniynah ta tashi tace "sai da safe Umma" Umma tace "Allah ya tashe mu da alkhairi" Baniynah ta amsa tabi Muniba suka wuce sama,suna shiga ɗaki ta taimaka mata tai removing make-up ɗin fuskarta then ta cire kayanta,Baniynah na kallon Muniba dake ƙoƙarin shiga banɗaki tace "Sweetheart bari na haɗa miki ruwan" Muniba tace "no! Zan iya" Baniynah tace "ok" wardrobe ta buɗe ta kwaso manyan duvet da suka taho da su daga gida tai musu shimfiɗa ta ajiye pillows,sanda ta cire kayanta kafin ta koma bakin gado ta zauna tana duba texts da akai mata na fatan alkhairi,ba'a jima ba sosai Muniba data shiga wanka ta fito ɗaure da towel,Baniynah ta ajiye wayar hannunta ta tashi ta wuce bathroom tana cewa "gara mutum yai wankansa kafin azo ana haɗa traffic" Muniba dai bata ce komai ba,kayan baccinta ta duba tasa tai sallar ishaa,bayan ta idar ta tashi ta koma kan shimfiɗar da Baniynah tayi musu ta kwanta,bed time prayers ta gama karantowa ta shafa jikinta,a hankali ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya,tana kwancen ta dunga jiyo hayaniyar shigowar su Khalidah,dai² lokacin wasu cikinsu suna shigowa ɗakin da sallama,Safwa ta waro idanunta tace "wace ce ta kwanta tun yanzu?" Baniynah ta buɗe ƙofa ta fito daga banɗaki tace "Sweetheart ce" Safwa tace "taɓɓɓ ɗin ai hayaniya bazai barta ta iya kwanciya yanzu ba,duka fa mun dawo kuma tare muka shigo da su Yaa Khalidah. A'ahh! Wallahi gara ma ta tashi" ta tafi za ta tasheta,Baniynah tace "don Allah ki barta tai baccin,yanzun nan ta sha magani" Safwa ta tsaya tana kallon Baniynah tace "ba ta da lafiya ne?" Baniynah data wuce tana duba kayanta tace "ehh nima na dawo nake ji a bakin Umma,ina jin tare suka dawo da su Mami" Khalidah data sawo kai cikin ɗakin ita da su Muneerah suka fara tambayar "waye babu lafiya?" Safwa tace "Muniba ce" Khalidah ta shigo da sauri tana tuje head dake kanta tace "subhanallah! Me ke damunta?" Baniynah tace "kanta ke ciwo" Muneerah suka nemi guri duk suka zauna suna faɗin "Allah sarki! Ashe shi yasa bamu ganta ba da zamu taho,duk sai nemanta muke ta yi" Baniynah tace "ai sun rigamu dawowa" duka suka shiga jimami da jera mata sannu,Muniba ta ɗan buɗe ido tare da adjusting kwanciyarta,Khalidah tace "ta sha magani kafin ta kwanta?" Baniynah dake shirin tada sallah tace "ehh ta sha" Khalidah tace "Allah sarki Sweetheart.. Allah ya baki lafiya.."
*SAFWA*
Fita daga ɗakin tayi tunawa da yanda suka rabu da Wazeer,ɗakinta ta shiga ta zauna gefen gadonta,ko kayanta bata iya cirewa ba ta fara ƙoƙarin kiransa a waya,kiran yana ta tafiya sai dai ba'a ɗauka,sai da tayi masa 5 missed calls kafin ta haƙura ta ajiye wayar ta tashi ta cire kayanta,bathroom ta shiga tayi wanka ta fito,sansa ta gama abunda take tas kafin ta ɗauki wayarta ta buɗe data,hotunan da akai musu da wanda aka turo na ɗaurin aure tai story da su,mafi yawanci wanda suke tare da mutane ne sosai,sai wanda take ita kaɗai,after then ta shiga contact ɗin Aley ta rubuta masa good night text me tsuma zuciya tare da fatan samun lafiya,tana tura masa ta sauka online ta kashe data tana sakin murmushi,nan tayi kwanciyarta ita kaɗai,kasancewar a gajiye take saboda zirga² da hidima yasa babu jimawa bacci me ƙarfi ya ɗauketa.
*WAZEER*
Da safe ko da ya farka lafiya lau ya tashi,sai dai abunda idanunsa suka gani jiya ya ƙi barin ƙwaƙwalwarsa,har ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya da suka amsheshi fuskarsa babu walwala,ko wayarsa bai tsaya dubawa ba ya fita gidan,ɓangaren Daada ya shiga ya sameta zaune a parlour sai hadimanta suna hira,ya nemi guri ya zauna suka gaisa da Daada,Daada na kallonsa tace "me gidan ka yi karin safe ne?" Fuska ɗaure babu walwala yace "um'um!" Daada tace "tou a kawo maka yanzu? Ko can gidanku za ka tafi da shi?" Ya sake cewa "um'um!" Daada ta tsaya kallonsa tana jiran yayi magana,amma sai yai mata shiru,tayi ƙwafa kawai ta ɗauke kanta,bai wani jima sosai ba ya tashi,ciki² yace "sai an jima" Daada ta bisa da kallo tace "Allah ya kaimu" har ya fice bata bar kallonsa ba,dama ta san ba lallai ya kulata ba. Sanda ya shigo ɓangarensu a parlour ya zauna,kamar me tunani kuma sai ya tashi ya wuce bedroom ɗinsa,wayarsa da ya bari da Macbook ya ɗauko ya fito,inda ya tashi ya koma ya ajiye notebook kusa da shi,a nutse yake kallon notification da suke saman screen ɗin wayar tasa,text ɗin ya fara buɗewa ya dunga bin content ɗin da kallo kafin a taƙaice ya tura mata kalmomin godiya,yana ƙoƙarin ya kirata saboda rututun missed calls da ya tarar,wani kiran nata ya shigo,kamar bazai ɗauka ba ya dunga kallon sunanta dake yawo saman fuskar wayar,sai da kiran ya kusa katsewa kafin ya yi answering yasa a speaker,cikin karaɗi Safwa tace "hello friend!" Idanunsa ya lumshe yace "assalam alaikum warahmatullah wabarkatuh!" Safwa tayi ƴar dariya tace "wa'alaikumus salaam.. How are u doing? Ya jikin? Ka isa gida lafiya?" A hankali yace "lafiya alhmdllh" Safwa tace "jiya nayi ta kiranka ba na samu,hope everything is fine?" Yace "Mmmm" tace "thank God.. Allah ya ƙara lafiya" yace "ameen" shiru suka ɗan yi kafin Safwa tace "hope za ka zo dinner ɗin yau ai ko? Na manta ba muyi maganar ba.." Bata ƙarasa ba ya buɗe idonsa da suka fara sauyawa nan take,yace "um'um" Safwa tace "ohh! C'mon friend kace za ka zo,pleaseee" yace "sorry! I have a lot of work da nake son kammalawa da su.." Kafin ya ƙarasa faɗan abunda ke bakinsa Safwa tace "pleaseee! Ko sai na bawa Muniba yanzuma ta yi magana sannan za ka yarda?" Kamar bazai ce komai ba a hankali ya sake lumshe idanunsa,Safwa tayi murmushi me sauti tace "ok! Hold on.. Bari naje upstairs na bata wayar.. Oops! Na manta itama jiya haka muka dawo gida muka iske ba ta da lafiya" maganarsa cike da izza yace "what happened?" Safwa tace "headache" a hankali yace "ok! Give her the phone" Safwa ta waro idanunta tace "me za kace mata?" Yai shiru bai ce komai ba,sai can a hankali yace "will u.." Sai kuma yayi shiru,Safwa dake saurarensa tace "uhumn! Mene ne? Speak up" yace "nothing.." Safwa tace "kuma kana so na yarda?" Yace "ok! Help me with her digits,then i will call and greet her.." Sauyawa fuskar Safwa yayi nan take,gabanta na faɗuwa ta daure tace "ok! I will talk to her,idan ta bani permission then i will send it to u" yai shiru yana sauraren yanda take magana,a hankali ta lumshe idanunta tana calming kanta tace "ok! Muyi magana yanzu,za ka zo ɗin?" Strictly yace "um'um! I don't think so,but let's see idan zan iya zuwa" bai son hayaniya sam,underneath kuma ya gama yanke hukuncinsa,amma ya san ko ya faɗa ba tsaiwa za tayi ta saurareshi ba,za su sake maimaita irin ta jiya ne,Safwa tace "ok! Will send u the address,saboda ba gurin jiya bane" a hankali yace "did i said that zan zo?" Safwa tace "ohh! Please friend,kai kaɗai fa nai inviting,shi ne za ka watsa min ƙasa a ido? Ok,thanks.. Bye" yana ji ta katse wayar bai hanata ba,sai ma switching phone ɗinsa da yayi off ya ajiyeta saman centre table,not minded yaja MacBook ɗinsa ya buɗe tare da sa airpod a kunnensa ɗaya,sam yau bai tsarawa kansa fita ko ina ba bayan masallaci,shima ana idar da sallah ya fito zai dawo gida.
*MUNIBA*
Da asubah ko da suka tashi tunda suka yi sallah babu wanda ya sake kwanciya,hirar da basu samu damar yi da dare ba na gurin dinner shi suka shiga maimaitawa har gari ya waye sosai,Muniba na shirin tashi za ta fita sai ga Umma ta yi sallama ɗakin suka amsa,Umma tace "ashe duk kun tashi" Muneerah tace "ai tun asubah bamu koma ba" Umma tace "Allah sarki.." Nan suka gaisa,tana kallon Muniba tace "Muniba ya ciwon kan?" Muniba tayi murmushi tace "alhmdllh ya yi sauƙi Umma" Umma tace "maa sha Allah.. Allah ya ƙara afuwa" Muniba ta amsa da ameen,Umma tace "tou bari na shiga gidan bikin kada aga har gari ya waye ban leƙa ba" sukai mata fatan dawowa lafiya ta juya ta fita. Muniba dake ta son tashi ta miƙe,Khalidah ta kalleta tace "ina za kije?" Muniba tace "wai da ɗan tattare ɗakin zan yi kafin a kawo mana breakfast" Mufeeda tace "a'a kiyi zamanki bari na gyara,ke da ba lafiya gareki ba,ina za mu bari kiyi aiki?" Muneerah tace "ai kuwa.. Yi zamanki ƙanwata,idan mukai breakfast sai a gyara" Muniba tace "ok! Thank u" tana zaunawa wayarta ya fara beeping,Layla da ta fita kusa da wayar ta miƙo mata,kallon wayar ta dunga yi tana mamakin sabon special digits da ake kiranta da shi,haka kawai gabanta ya shiga faɗuwa,ta dunga kallo fuskar wayar ta kasa amsawa,sai da Khalidah tace "pick up Sweetheart kin tsaya kallon wayar kada kiran ya katse" cike da shahada ta ɗauka lokacin kiran yana daf da tsinkewa tasa a kunnenta tace "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh!" Daga can gefen akai murmushi me tafe da ajiyar zuciya kafin a amsa "wa'alaikis salaam warahmatullah wabarkatuh! Good morning Angel" gabanta na faɗuwa sosai ta buɗe ido tace "ina kwana?" Yace "lafiya lau dear.." Tunani ne iri² ya dameta,muryar yana shiga cikin kanta tana ji kamar ta san me maganar,tana ƙoƙarin tambayar waye,calmly da wannan huskey voice ɗin nasa yace "i am Abuu Turab.. So how are u feeling now?" Waro idanunta waje tayi cike da mamaki tace "alhmdllh.. I'm feeling better" yace "maa sha Allah" sukai shiru na wani lokaci kafin yace "hey! Are u there?" A hankali tace "Mmmm!" Yace "ok! Hold on ga Mom za ta gaisheki da jiki" Muniba ta sake waro idanunta waje,ƙirjinta sai bugawa yake bim²,da sauri a daburce tace "wait please.." Fuskarsa na bayyanar da murmushi yace "uhumn! What's up?" Muryarta na rawa tace "a ina ka samu number na please?" Yace "kina mamakin inda zan samu ne?" Tace "Mmmm" yace "ok! We will talk about this later.. Ga Mom ku gaisa" batai musu ba tace "ok!" Taji shiru na few seconds kafin muryar mace dake cike da nutsuwa tai mata sallama,gaba ɗaya Muniba ta rikice tace "wa'alaikis salaam.. Good morning Mom.. Ina kwana?" Mom ɗin Abuu Turab dake murmushi tace "lafiya lau daughter,ya jikin naki?" Muniba da kanta ke ƙasa za ka rantse tana gaban Mom ɗin tace "lafiya lau alhmdllh" Hjy Hafsah tace "maa sha Allah.. Allah ya ƙara lafiya,ya tashi kafaɗa" Muniba tace "ameen Mom.. Na gode sosai,Allah ya saka da alkhairi" Mom tace "mene ne abun godiya a nan? Ai ke ƴata ce babu godiya tsakaninmu,yanda Abuu Turab yake a gurina haka nake kallonki.. Alhmdllh! Na ji komai daga bakinsa,bayan wanda na gani da idona,bai ɓoye min komai ba ya sanar min,Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa.. Ubangiji yasa albarka cikin tarayyarku" kan Muniba ya ɗaure ta shiga tunanin me yace mata? Mom tace "ga Abuu Turab ɗin daughter,Allah ya ƙara afuwa" Muniba ta amsa tare da yi mata sallama. Lieut. Abuu Turab na karɓar wayar yace "hey!" Kamar za tayi kuka,ita kanta bata san daga ina tambayar yazo mata ba tace "me ka sanarwa Mom?" Fuskarsa da murmushi akai yace "kina son sanin me na faɗa mata?" Da sauri ta gyaɗa masa kai kamar tana gabansa,sai kuma tace "Mmmm!" Yace "ok! Anjima idan mun haɗu zan sanar miki,yanzu ina tare da Mom muna magana,hope baza ki gudu ba irin na jiya" a hankali kamar baza tace komai ba tace "ok!" Yace "take care of urself for me please" ta turo baki a hankali kamar za tai masa rashin kunya,da yake kuma bata iya ba sai kawai tace "uhumn!" Yace "ok bye" tana amsawa ya katse kiran daga can ɓangarensa. Baniynah ce ta shigo ita da Safwa da suka tafi karɓo breakfast gida,Muniba ta dunga kallonta fuska ɗaure tace "Sweet wa kika bama number na?" Baniynah tai saurin kallonta,Muniba ta tsareta da ido tace "i'm asking" lokaci ɗaya Baniynah ta tsuke fuska tace "wa kuwa na bama? Did someone call u yace nice na basa?" Muniba tace "in bake ba to waye ya basa number na?" Baniynah tai kicin² tace "to kije ki tambayesa mana,ni me yasa zan basa? Na ma san wa kike magana akai?" Ba Safwa kawai ba har su Khalidah kallonsu suka tsaya yi,Muniba ta haɗe rai tana kallon Baniynah da tayi kamar bata san me take nufi ba,lokaci ɗaya Khalidah tace "guys please what's happening? Akan me kuke magana ne?" Muniba da kamar za ta fashe da kuka tace "Yaa Khalidah number na fa taje ta basa" Khalidah tace "waye aka bawa?" Muniba tace "shi mana.. Ai ita ta san wa ta bawa" Khalidah ta kalli Baniynah tace "Baniynah wa kika bama number ɗinta?" Baniynah tace "a'a ni fa babu wanda na bama,in kuma ba tsoro ba ta fito ta faɗi wanda na bawa" Muniba tace "shi wannan abokin Yaa Mohan ɗin da na ganku kuna magana" Khalidah ta waro idanunta tace "ohh! Wai Lieut. Abuu Turab?" Muniba ta gyaɗa kai kamar sakarai,ba Khalidah kawai ba duka har su Muneerah suka haɗa baki gurin faɗin "awwnnn!" Muniba ta dunga kallonsu da idanunta,lokaci ɗaya kunya ya kamata ta ɓoye kanta tana cewa "ni dai Allah ba na so ku bari" gaba ɗaya suka sa shewa kafin suka fara zolayarta,Safwa dai bata ce komai ba har sannan sai kallon da take bin Muniba da shi,she can't even tell me take ji a ranta tunda aka ambaci sunansa,wani irin haushinsu duka da suke maganar ya kamata,lokaci ɗaya ta juya ta fita ɗakin. Da yake yau babu inda za suje yini ne za'ayi a gida,sai da dare dinner na can ɓangaren gidan ango,suna yin breakfast duka sukai wanka suka canja kaya,then suka fito suka shiga gida aka gaisa da iyaye,sai guraren asr sannan sukai shirin tafiya gurin make-up,Muniba na kallon Khalidah tace "Yaa Khalidah a yaya za mu tafi?" Khalidah tace "don't worry Sweetheart,akwai motocin da za suzo su kaimu" Muniba tace "ok!" Not too long drivers suka zo tafiya da su,suna ajiyesu gurin kuma suka juya,nan sukai maghreeb kafin aka fara yi musu kwalliya,it tooks them good 3 hours kafin aka gama,sun fito sun yi kyau kamar me,amarya and her maids banda walwali babu abunda suke,sai dai yau dukansu babu mask a fuskokinsu,sak suke ɗinkinsu free vail wannan na cewa wane wannan,yauma kayansu su 3 iri ɗaya,while su Muneerah manyan ƙawaye suma haka,angwaye na zuwa aka ɗaukesu zuwa gurin,kamar yesternight bikin ya tsaru,komai cikin mutunci da daraja,family sun fitar da ƴaƴansu kunya. Muniba suna tare da Khalidah a fili suna rawa,Lieut. Abuu Turab ya fito tare da siblings ɗinsa,cike da zolaya Mohan yace "ran soja ya daɗe,anga dama an fito? Ko Madam ce ta janyoka?" Lieut yayi kyakkyawan murmushin da ya bayyana dimples ɗinsa,brother ɗinsa da suke tsananin kama da shi yana kallon su Muneerah dukansu yace "Yaya wace ce Aunty'n namu please?" Lieut yai masa wani kallo yana ɗaure fuska,Mohan yace "Hammad zo zan nuna maka ita" Lieut yace "ai kai dama magulmaci ne" Mohan yace "ya muke da kai? Duk wasu hali ai gurinka na koyosu" ƴan mata biyun da suke tare da shi suka ce "Yaya don Allah ka faɗa mana,we are eager to know who.." Ai Muniba bata tsaya jin maganarsu ba tai sauri ta fita daga gurin,Baniynah me za tayi ita da su Muneerah ba dariya ba,Hammad ya kallesu yace "wait guy's.. Idan na fahimci abunda ke faruwa,wanda ta bar gurin nan ne budurwar Yayanmu,right?" Baniynah tace "absolutely!" Ya buɗe ido da kyau yana cewa "taɓɓɓ ɗin! Ai ta fi Yayanmu haɗuwa" Lieut yace "Hammad!" Hammad ya kwashe da dariya yace "ok! Bari naje mu gaisa,ai har Mom yau sai na kai mata surukarta" da sauri ya tafi ƴan matan suka bisa. Muniba na barin gurin ta tafi table ɗin su Mami,bala'in tsoron su rutsata take,ita ba me yawan magana ba,tsaf za susa ta kuka idan ta rasa abun faɗa,Mami ta ɗaga kai tana kallon ƴarta tace "ya akayi Sweetheart?" Muniba ta kalli wanda suke zaune gurin ganin bata sansu ba amma dai it seems kamar dangin Yaa Mohan ne,tace "ina yininku?" Da fara'a duka suka amsa mata,a hankali Muniba ta sunkuya jikin Mami tace "Mami kunyi waya da su Yaa Khalifa sun sanar miki sun zo?" Mami ta ɗan girgiza kanta tace "bamu yi waya ba,amma na dai ga kamar sun zo" Muniba tace "bari naje gurin Yaa Mubasshir tou" Mami tace "ok!" Dai² nan Hammad ya iso gurin fuskarsa da murmushi akai ya gaida Mami ta amsa,yana kallon Muniba yace "Auntyn'mu baki tsaya mun gaisa ba" Muniba ta wani irin waro idanunta waje,kamar za ta fashe da kuka ta kalli Mami,Mami dai kallonsu kawai take bata ce komai ba,lokaci ɗaya Hammad ya kalli wata kyakkyawar mata da kana kallonta za ka iya gano kamar da suke ɗan yi da ƴan matan,yace "Mom ga surukarki fa" Hjy Hafsah da tun zuwan ƴaƴan nata ta ɗan tsaya taji ko wani abu za suce mata,ta saki murmushi sosai tace "Hammad gidanku" ya kwashe da dariya yace "wallahi Mom itace budurwar Yayanmu" Hjy Hafsah da Hjy Hauwa Mahaifiyar Yaa Mohan duka suka tsaya kallon Muniba da kunya ya kusan sawa ta nutse a gurin,Hjy Hauwa na kallon Mami tace "a'ahh! Shi ke nan sai muyi tuwona maina.." Mami ta saki murmushi bata dai ce komai ba,Mama ma fuskarta a sake take kallon Muniba,abunda Muniba bata sani ba,waɗanda ta gaisar iyayen ango ne suke tare da nata,su kuma tsarin gurin haka suke yi su haɗa iyayen amarya da na ango seat ɗaya...
#Afwaan habibaatiiy! Kwana biyun nan jikin dai sai hamdala,amma ba wani cikakken lafiya ne ya wadaceni ba,ayi haƙuri da ni da jin shiru kuma.. Wanda suka nemeni saboda jin shiru,ina godiya sosai² Allah ya saka da alkhairi,addu'o'inku sun iso gareni,Allah ya bar zaman tare.
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
*Infection*
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*****
*****
#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.