WAZEER!

Power of love

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®AS-2023.






*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*





           *♡WAZEER¸.•💥*

          (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)





Bʏ.

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

https://www.arewabooks.com/u/realsmasher

 ••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*


  

   _*** Follow my whatsapp channel dearest domin samun update na book ɗin *WAZEER* da sauran wanda za su zo,har ma da tsofaffi.. Wani ƙarin abun kuma duk wanda nake da contact ɗinsa yayi following ɗina za su nuna min,idan kuna so nayi saving contact ɗinku chat me up @+234 *** ko @***. Thanks so much as u do so._


 



                16

 


#Power of love


      Ina ƙasa ta buɗe Muniba ta shige ciki ta ɓoye kanta,kunyar duniya da na su Mami gaba ɗaya ya taru yai mata yawa,Hjy Hauwa dake kallonta fuskarta cike da murmushi tace "maa sha Allah! Gaskiya ɗana bai yi zaɓen tumun dare ba.. Hjy kin ga dai ikon Allah ko?" Mom tayi murmushi also tana kallon Muniba ta gyaɗa kanta,Hjy Hauwa ta kalli Mami tace "Dr hope baza'a hanamu irin da muka gani ba,ko nace Allah yasa ba'a rigamu ba?" Mami ta sake yin murmushi,kunya irin na bafillata ya hanata cewa komai,a hankali ta ɗauke kanta kafin ta iya cewa "ai wannan magana ba nawa bane Hjy,tunda ga Mamarta nan a zaune duk abunda tace ni ba ni da ja" Mama dake saurarensu tayi murmushi itama kafin tace "baza mu hana bama in sha Allah" Hjy Hauwa tace "that means babu kowa a gabanmu kenan? Za mu iya shigowa da ƙarfinmu?" Mama tace "ehh toh! Ai kin san budurwa ba'a rasa ta da masu nema,amma dai babu maganar kowa a kanta" Hjy Hauwa tace "alhmdllh! Ai tunda babu maganar kowa,mu baza mu tsaya sanya ba,in sha Allah da ƙarfinmu za mu zo ayi komai a gama cikin lokaci" Mama tace "Allah ya amince" Hjy Hauwa tace "ameen yaa Allah.. Amma fa gaskiya mun gode da karamcinku Hjy,babu abunda za muce sai godiya,Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci" Mama ta sake yin murmushi tace "ameen yaa arhamur-rahimiiyn" underneath wani irin farin ciki ke mamayar zuciyarta,gani take a yanzu an gama zama ɗaya tunda aure ya haɗa zumunci tsakaninsu,sannan ga wani kuma yana shirin faruwa though dai yanzu aka fara maganar,amma ta tabbatar baza suyi musu zancen da wasa ba. Duk maganar da su Mama suke yi,har lokacin tana tsaye ta rasa me za tayi ko ta aikata,can ta wurga idanunta ta hango su Yaa Mubasshir su kaɗai a seat ɗinsu,ba tare da ta kalli kowa cikinsu Hammad da Sisters ɗinsa ba,sai don kawai son ta samu mafaka,muryarta na rawa tace "Mm.. Maa.. Mama ga su Yaa Mubasshir ɗin na gani" Mama data karance Muniba tsaf tai ɗan murmushi a hankali tace "gurin nasu za kije yanzu?" Kamar wanda ke tsoron za'a hanata,da sauri ta gyaɗa mata kai idanun nan nata sun yi rau² tace "ehh!" Mama ta gyaɗa mata kai also tace "toh! Kuje can ɗin sai ku gaisa,i think za ku fi sakewa kuyi magana ko?" Kafin Mama ta ƙarasa faɗan abunda ke bakinta,ai tuni kunya yasa tai saurin cewa "sai an jima" Hjy Hafsah tayi murmushi kawai tana kallon yaranta tace "Hammad! Ka kyauta,irin wannan abun na hanaka ba tun yau ba ka ƙi ji,yanzu wannan abun da kayi mata a gaban parents ɗinta da mu,idan me raguwar zuciya ce ai sai kasa ta kuka" Mama tayi murmushi tace "ai kuwa anci sa'a ma da har ta iya barin gurin nan,amma Muniba dake da idon kuka ko ɓaure haka ya ganta ya bari" Hjy Hafsah tace "u see! Sai ka wuce kaje ka bata haƙuri maza²,wannan ba wasa bane na sha faɗa maka,and this should be the last,kada ka sake yiwa wani irin wasan nan,idan ba haka ba wallahi zan saɓa maka" Hammad ya gyaɗa kansa jikinsa a sanyaye yace "ok Mom.. I'm really sorry,na biyota ne mu gaisa,ban yi tunanin gurin parents ɗinta tazo ba,da ban yi haka ba,amma kuyi haƙuri please" Hjy Hafsah tace "ok! Kuje ka sameta ka bata haƙuri" ya ɗan gyaɗa kansa fuskarsa da ɗan murmushin nadama yace "in sha Allah Mom" daga haka yaiwa su Mami sallama ya wuce tare da ƙannensa,Hjy Hafsah bata sake kallonsu ba suka ci gaba da maganar da suke ita da Hjy Hauwa,Mami da Mama suma suka ci gaba da maganar da suke Mama na yabawa Hjy Hafsah kan irin tarbiyyar da taima yaranta. Table ɗin su Mubasshir Muniba ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tace "Yaa Mubasshir tun ɗazu nake ta nemanka" Mubasshir ya kalleta yana sakin murmushin da ya ƙara masa kyau yace "bamu shigo da wuri ba,ya akai? Any news?" Muniba tai ƙasa da murya tace "kawai na kasa sakewa a gurin nan ne,don Allah ko za ka kaini gida?" Mubasshir ya sake yin murmushi yace "me yake faruwa? Wani ya takura miki ne?" Girgiza kai tayi innocently tace "a'a kawai ni dai na gaji,so nake na koma gida" Mubasshir ya ɗan haɗe fuska yace "to haka za kije gidan ki zauna ke kaɗai?" Ta gyaɗa masa kai tace "ni dai zan iya zama ka kaini pleaseee" a hankali yace "ko dai Soja ne ya takuraki?" Da sauri Muniba ta kalleshi,sai kuma ta girgiza masa kai tace "a'a ni haka kawai nake son tafiya" kallon tsaf Mubasshir yayi mata kafin yace "to gaskiya bazan iya mayar dake ba,tunda ba ki da wani dalili da zai sa ki tafi" Khalifa dake jinsu tun sanda suka fara magabar bai ce komai ba,lokaci ɗaya ya ɗago ya kallesu yace "what did she just said?" Mubasshir na danna wayarsa fuska ɗaure yace "wai gida zan kaita" Khalifa yace "sai ka kaita ai" Mubasshir yace "ba ta da dalilin komawa gidan fa,ni bazan kaita na ajiyeta ita kaɗai ba alhalin kowa yana nan" Khalifa yace "ohh! Thought ai za ka mayar da ita,yanzun nan na sanar da Mama" Muniba ta kalleshi kamar za tayi kuka tace "kai Yaa Khalifa don Allah,kai da za kasa baki ya kaini shi ne kake zugashi" Khalifa ya ɗauke kai kamar ba da shi take magana ba,Mubasshir dake ta kallonta yace "sorry lil Sis,ki yi zamanki a nan har a tashi sai mu tafi" Muniba da lokaci ɗaya hawaye ya cika mata ido tai saurin kifa kanta saman table ta kama kuka,tana wannan yanayin Baniynah ta zo gurin,a hankali ta dafata tana kiranta "Sweetheart! What's up? Me yake damunki kika zo nan kika zauna?" Muniba bata kulata ba ta ci gaba da kukanta,ɗago kanta Baniynah tayi tana faɗin "what happened to u?" Ɗauke kanta tayi hawaye na sake rolling down daga idanunta,a rikice Baniynah ta janyo kujera ta zauna tana kallonta tace "Sweetheart! Don Allah me akai miki? Kukan me kike?" Yaa Khalifa ya tsaya kallon Muniba da mamaki jin kalmar kuka a bakin Baniynah,kafin ya maimaita yace "kuka!?" Baniynah tace "wallahi kuka take,me akai mata? Ita da waye please?" Khalifa yace "a'a na shagwaɓa take yi" Baniynah ta kalleshi ta kasa cewa komai,Mubasshir da yai suman zaune saboda mamaki yace "ok! Tashi muje na kaiki" da sauri ta miƙe dai² lokacin Lieut. Abuu Turab yai musu sallama tare da bawa su Mubasshir ɗin hannu sukai musabaha,idanunsa akan Muniba da ta sunkuyar da kai ta ƙi yarda ko kallonsa tayi,ya ɗan juya yana kallon Baniynah da ta tashi tsaye also,yana son yi mata magana amma sai yaga hankalinta duka na kan Muniba,riƙe hannun Muniba Baniynah tayi muryarta ƙasa² tace "Sweetheart please,don't go back home tun yanzu,ki bari har a tashi,kin san fa babu kowa a can,mene ne amfanin ki tafi ki zauna ke kaɗai? Kin san Mami taji za tai miki faɗa" Muniba ta kalleta ta maƙe kafaɗa sai dai bata ce komai ba ta ci gaba da share hawaye,Baniynah ta dage sai roƙonta take amma ta dage,handkey dake fidda wannan sihirtaccen ƙamshin nasa Lieut. Abuu Turab da ya gama jinsu ya ciro ya miƙa mata,da huskey voice ɗinsa da yayi sanyi yace "whippe up ur face ki zauna" she can't tells me ya faru,kawai ta amshi handkey ɗin ta share hawayenta,duk yanda kake kusa da su ba lallai ka iya cewa ga abunda yace mata ba,kawai suka ga ta koma ta zauna tana sake share hawayenta,shi kuma ya ja kujerar kusa da inda take ya zauna tare da kame kansa,sakin baki Baniynah tayi tana kallon ikon Allah,Mubasshir kam da Khalifa murmushi kawai sukai,Khalifa ya kalli Baniynah yai mata alamar tazo da ido,da ƙyar ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya sannan ta ja kujerar kusa da shi ta zauna,ƙasa² yace "kina mamaki ne?" Baniynah ta ƙifta idanunta tace "i'm speechless wallahi,na gama roƙonta ta ƙi ji amma daga yi mata magana har ta koma ta zauna kamar tsafi" Khalifa yace "this is what bature yake kira Power of love.." Baniynah ta gyaɗa kai kafin tayi murmushi. Da sallama Hammad yazo gurin fuskarsa a sake ya bawa su Mubasshir hannu suka gaisa har ƴan matan,they don't need any further explanation,kamanninsu da Lieut. Abuu Turab ya wadatar da su fahimtar waye su,Hammad dake murmushi ya zauna kusa da Lieut yana faɗin "Auntynah! Good evening" Muniba ta amsa masa ta kasa kallonsa,yana sakin murmushi yace "i'm so sorry for my mistake,i never knew.." Kafin ya ƙarasa Muniba ta saki murmushi,kamar wani abu bai faru ba ta girgiza kanta tace "babu komai.. I understand" Hammad yace "really?" Ta gyaɗa masa kai tare da lumshe kyawawan almond eyes ɗinta tace "Mmmm" yace "wow! Gaskiya u are way too soft,baki da riƙo sam.." Muniba tai ɗan murmushi kawai,Hammad yace "i'm Muhammad amma za ki iya kirana Hammad,junior broh na Lieut.. Dukanmu siblings ɗinsa ne,this is Husniyah and Abrar" ƴan matan sai murmushi suke suna kallon Muniba har suka gaisa tana musu murmushi me cike da kunya,ƙasa² suke magana da juna ba'a jinsu suna kallon Muniba sai kuma su kalli Lieut,Lieut da yai shiru kamar ba ya gurin duk yana jinsu,Muniba tace "Allah sarki! Nice meeting u" Hammad yayi murmushi yace "thank u.. But ban san sunan Aunty'n nawa ba,kada mu sake haɗuwa na rasa sunan da zan faɗa,kin san Aunty suna da yawa idan na faɗa ba lallai ki juyo ba ko ki san dake nake" Muniba tayi murmushin da ya bayyana fararen haƙoranta tace "sure" Hammad yace "yawwa! Ur name please,na san dai yanda kike me kyau sunanki ma zai zama unique" duk maganar nan da suke yi bata iya kallonsa ba ta daure tace "Muniba" yace "maa sha Allah.. Kinga ban faɗi ba dai² ba ko?" Ya kalli Yayansa zai magana,Lieut yai masa wani kallo,dole tasa Hammad ya haɗiye maganarsa tare da fashewa da dariya su Khalifa suka tayashi,dole tasa Lieut. Abuu Turab yin murmushin da bai shirya ba kafin yai fuska.



*SAFWA*



   Suna tare da su Muneerah ta hango yanda su Muniba suka zauna tare da su Mubasshir da ƙarin wasu mutum 4 da bata sani ba sai hira suke,duk da dai ta san halin Muniba na rashin sakewa a guri tare da wanda bata saba ba,amma haka kawai sai bata ji daɗi ba da suka ware da brothers ɗin nasu,tana tare da su Mufeeda amma kusan fiye da rabin hankalinta na can kansu,saboda son sanin su waye wanda suke tare da su,har abinci ma ta ga an kai musu kuma bata ga alamar Muniba za ta tashi ba,lokaci ɗaya ta tashi tare da ɗaukan plate ɗinta ta tafi gurinsu,a hankali fuskarta ya ɗan sauya tai wearing murmushi,seat ne me ɗaukan mutum 10 kuma a haka ma akwai extra kujeru 2 da babu kowa akai,kujerar dake kusa da na Baniynah taja tare da zaunawa,ba nan taso ta zauna ba amma ganin kusa da inda Muniba take gefenta ɗaya Mubasshir ne ɗayan kuma sai da ta iso sannan ta gane Lieut ne zaune,mutumin da tun farkon haɗuwarsu jininsu bai zo ɗaya ba,da taga kowa hira yake da ɗan uwansa ta kalli Abrar da Husniyah,lokaci ɗaya sukaiwa juna murmushi tace "sannunku" ganin komai nata irin na su Muniba ne yasa suka amsa ta,Abrar tace "ya taro?" Safwa tace "alhmdllh!" Abrar tace "maa sha Allah,Allah ya basu zaman lafiya" Safwa tace "ameen²" a hankali ta kalli Muniba dake zaune ba ta um bare um'um,ko even plate ɗinta bata iya taɓawa ba,tace "hey Babe! What's up?" Muniba ta kalleta tare da girgiza mata kai alamar nothing,Safwa tai murmushi tace "nothing?" Muniba ta gyaɗa mata kai,Safwa tace "and why are u sitting haka ba kya cewa komai?" Hammad ya kalli Safwa yace "nima dai abun na damuna tun ɗazu na rasa waye zan tambaya Sister mu" Safwa tace "ahh! Ko dai wani ta taɓa ki ne?" Muniba ta girgiza mata kai,Baniynah dake kusa da Safwa tai ƙasa² da murya tace "kin san mutuniyar ai,an iya rayuwar kurame" Safwa ta gyaɗa kai tana sakin murmushi tace "yeah" lokaci ɗaya ta tuna yanda sukai da Aley ɗazu,buɗe ido tayi da sauri ta ɗauki wayarta ta buɗe security ɗin ta shiga contact,number ɗinsa ta shiga kira sai taji wayar nasa switch off,ta sake gwadawa amma same abunda taji shi baturiyar cikin wayar ta sake faɗa mata,lokaci ɗaya ta ajiye wayar tana ɗaga kai ta kalli Muniba tace "u know what?" Muniba dake kallonsu ita da Baniynah ta girgiza mata kai,Safwa tace "Aley fa bai zo ba" Muniba ta ɗan waro idonta waje tace "me yasa?" Safwa ta girgiza kanta tana taɓe baki tace "i don't know,wayarsa ma is off duka yau" Muniba tace "maybe wani uzurin ya hanasa" Safwa tace "dama bai niyyar zuwa ba,yesternight ma da ya ya amince yazo? Sai fa da kika sa baki" Muniba tai ɗan murmushi kawai amma bata ce komai ba,Lieut dake busy yana operating latest version of his iPhone ya ɗaga idanunsa ya ɗan kalli Safwa dake sake cewa "but maybe kuma jikin ne ya hanasa zuwa,jiya ai kinga ya tafi bai jin daɗi,and ɗazu da safe mun yi waya,still na ji kamar har sannan he's not ok" Muniba ta ɗan gyaɗa kanta tace "Allah sarki! Allah ya bashi lafiya" Safwa tace "ameen.." Lieut ya wani irin tsare gida a hankali yace "waye shi?" Muniba ta kalleshi da sauri,bai ɗago ba har lokacin hankalinsa na kan wayarsa,a hankali tace "wani ne" bai yi zaton za ta amsa ba shi yasa bai yi tunanin kallonta ba,a hankali ya ɗago idanunsa tare da kallonta fuskarsa na bayyanar da mamaki,suna haɗa ido Muniba tai saurin ɗauke kanta,yace "wani ne? Waye shi a gurinki?" A hankali tace "babu kowa" yace "really?" Ta rasa me za tace masa kawai ta ɗago kanta,kamar za tayi kuka ta kalleshi,they stared a timid at each other na few minutes kafin tai saurin ɗauke kanta,Lieut. Abuu Turab yace "uhumn!" Muniba ta ƙi yarda tace komai. Har aka tashi gurin bata iya cin komai ba duk da an kawo mata abincin,amma haka aka ɗauke bata taɓa ba,shima kuma Lieut. Abuu Turab haka,tana hango sanda su Mami suke ƙoƙarin tafiya ta tashi tana kallon Baniynah tace "Sweet think zan bi su Mami" Safwa ta tashi itama tace "kai Babe ai ba sai kin bisu ba,mu tafi mana tare kawai" Muniba tace "ok" Mubasshir ya kallesu yace "saurin me kuke yi ne?" Khalifa yace "kaima dai ai ka san halin mata da gulma,wani abun suke shiryawa shi yasa suke sauri su tafi" a shagwaɓe Muniba tace "kai don Allah Yaa Khalifa" yace "me nace? Ba halinku bane gulma?" Muniba tace "amma dai ai baka ji munce za muyi gulmarka ba" yace "wa ya sani? Ai gulmar nawa ma kuka samu dama sai kuyi,sau nawa ina kamaku kuna yi?" Safwa ta fara dariya tace "a'a Yaa Khalifa wallahi mu bama gulmarka" yace "a tsinewa me ƙarya?" Safwa ta ƙyalƙyale da dariya tace "a'a ba sai an tsine ba" yace "ashe dai ana yi ɗin" Baniynah tace "to akan me za ayi gulmarka?" Yace "oho kun fi ni sani ai" da sauri ta tashi tana ƴar dariya tace "kai dai Yaa Khalifa kawai kana da saurin tsarguwa ne" yace "auu haka ma za kice?" Safwa dake dariya tace "babu komai duk cikin so ne" Khalifa yayi murmushi ya ɗauke kansa,Mubasshir dake jinsu bai ce komai ba ya kalli Lieut yace "ran soja ya daɗe baka ce komai ba" Lieut ya ɗan waro idanunsa,kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "i think ya kamata mu tafi haka kou?" Mubasshir ya gyaɗa masa kai yace "sure" Lieut ya miƙe a nutse ya kalli Hammad yace "Malam ka tashi ka kai su gida" Hammad yayi murmushi yace "ok Sir" Lieut ya ɗan wuce ba tare da ya ce da kowa komai ba,dai² zai gifta Muniba yace "ki sameni a waje za mu sauke ku gida" ai ji Muniba tayi kamar ya watso mata ruwan zafi,kuma bai tsaya ba yana gama magana yai wucewarsa. Hammad ya kalli su Abrar yace "guys idan kun gama ku tashi mu wuce gida ai kunji me Yaya yace" Husniyah ta tashi da sauri tana ɗaukan handbag ɗinta taiwa su Baniynah sallama,Abrar ma tai musu sallama suka amsa,Husniyah ta taho kusa da Muniba tare da miƙa mata wayarta tace "Aunty kisa min digit ɗinki please,ma dunga gaisawa" Muniba ta rasa me za tace saboda kunya kawai ta karɓa tasa mata,a take Husniyah ta kirata yana shiga Muniba ta nuna mata fuskar wayarta tana mata murmushi tace "ya shigo" Husniyah tace "alright! Kiyi saving please" Muniba tai mata murmushi tace "in sha Allah" Husniyah tace "thank u Aunty" Abrar ta taho tace "kaiii³! Nima gaskiya a bani number,bazai yiwu Husny ta fini fada ba" Muniba da Husniyah sukai dariya kafin Husniyah tace "ai duk da haka na fiki,tunda ni na fara request.. Ke komai nayi sai kin yi kishi,copy² kawai" Abrar tace "ehh na ji dai babu komai" Muniba ta kalli Baniynah dake ta murmushi ta miƙa mata wayarta tace "Sweet ɗan yi mana pic please" Abrar tace "yay! Wallahi abunda nake shirin yi kenan Aunty kika rigani" wani kunya ya kama Muniba,idan suka kirata Aunty sai taji wani banbarakwai saboda rashin sabo,Baniynah ta ɗaukesu dukansu sannan tayi musu da ɗai²,Abrar ta kalli Baniynah tace "Aunty kuma kuzo ayi mana.. Yaa Hammad kayi mana please ka ji" Hammad yace "ai kuma ni ba photographer bane,sai dai in za ki biya" Abrar tace "please ka ji,ai ka iya ɗaukan photo kuma" yace "ok! Kin dai ci sa'a akwai Aunty a ciki da bazan yi ba" ya karɓa yayi musu su 5 har da Safwa hotunan duka sun yi kyau,suna cikin ɗauke²n hoton Khalidah da su Muneerah suka taho gurin,nan photographers sukai musu hotuna dukansu har mazan Lieut duk rashin don sa da hoto wannan kam bai ƙi ba,wani kuma iya su ƴan matan ne da amarya,after then sukai sallama suka fito gurin.



*WAZEER*



   Tun safe yake ta tunanin abubuwa da yawa a ransa,duk yanda yaso yai keeping kansa busy kada yai tunanin komai abun bai tafi yanda yake so ba,haka nan dai ya yini shi kaɗai sai hasko abubuwa da yawa yake suna faruwa,sanda ya fita sallar ishaa ya dawo yana shigowa parlour idanunsa suka sauka kan wall lock dake nuna 8pm sura ƴan mintuna,gaba ɗaya ya nemi nutsuwarsa ya rasa,duk wani abu nasa ya ƙarasa inda ya barsu kafin ya fita sallah ya tattara ya wuce bedroom,ba bacci yake ji ba amma haka nan ya zaɓi yai camping kansa inda babu me zuwa bare ya damesa,ba don komai ba sai saboda ya samu sassaucin abunda yake ji,jallabiyar dake jikinsa ya cire tare da shiga bathroom ya watsa ruwa,yana fitowa sanin babu inda zai kuma fita ya saka lightweight pyjamas ɗinsa ya haye gado tare da jan Macbook ɗinsa,Korean films ɗinsa da yake kallo a lokuta da dama idan yana son waniabu ya ɗauke masa hankali yayi playing,duk da films ɗinsu suna bashi takaici at the end,amma bai gajiya da sake binsu,gaba ɗaya ka kallesa za ka iya cewa kallon yake,amma zuciyarsa tana can wani waje na daban,he can't tell ga abunda yake kallo ko ake yi cikin film ɗin,lokaci² yake kai idonsa yana kallon tafiyar lokaci,ba shi ya samu releaf ba sai to 11am,jikinsa a mugun mace ya kashe MacBook ɗin tare da ajiyewa saman bedside drawer,wayarsa da tun safe ya kashe ya ɗauka ya kunna,yana gama booting ya shiga WhatsApp,abu na farko da ya fara dubawa shi ne story ɗin Safwa,nan ya ci karo da tarin hotunansu na ranar,sai wasu few da akai musu tare da su Muniba,yau dukansu babu mask ɗin a fuskarsu,babban abunda yaja yai saurin fita kenan,yana shirin kashe wayar vid call ya shigo,kallon sunan Safwa ya dunga yi ya kasa ɗauka,sai da kiran ya kusan katsewa kafin ya kashe lampshades ya ɗauka,kallonta ya ɗan yi da idanunsa da suke zafi,ko da bai kalli mudubi ba ya san a yanayin da yake ciki idanunsa sun sauya launi,fuskarta har sannan da makeup kamar yanda yake ganinta clearly saboda inda take da haske,unlike him da ba ta iya ganin komai sai duhu duɗum,Safwa tace "hey! Friend how are u doing?" Wazeer dake jinta yace "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh!" Safwa tayi ɗan murmushi tace "wa'alaikas salaam.. Ya kake?" Yace "alhmdllh" Safwa tace "na kiraka ɗazu naji wayan is off" shiru yayi bai ce komai ba,Safwa tace "hello! Are u there? I don't see anything,ban ganinka sai duhu" Wazeer ya ɗan sauke numfashi ahankali ya kunshe idanunsa yace "yeah! Bamu da wutar NEPA ne sun ɗauke" Safwa tayi ƴar dariyar shaƙiyanci tace "baku da blue line ko solar kuma?" Yace "we don't have,kin san mu talakawa ne" Safwa tace "talakawa?" Yace "uhumn!" Tace "waye zai yarda kuma?" Yace "ok! Baki yarda ba?" Tace "sure" yace "ok! Zan kwanta,sai da safe?" Safwa tace "wai jikin ne har yanzu?" Yace "Mmmm" tace "ohh! Allah ya ƙara lafiya ya yaye" yace "ameen.. Thank u" tace "good night dear.." Yace "ok! Bye" tace "bye!" Yana katse kiran ya kashe wayar duka ya ajiye,a hankali ya fara matsa forehead ɗinsa,yana jin shigowar Dad ya buɗe ido,he thought zai shigo bedroom ɗin dubashi saboda duka yinin basu ga juna ba,kuma sai yaji ya shiga bedroom ɗinsa ya kulle,a hankali ya mayar da idanunsa ya lumshe tare da sauke ajiyar zuciya. 



*MUNIBA*



   Tana sauka motar a hanzarce ko rufewa bata yi ba tace "mun gode,sai da safe.." Lieut ya sauke glass ɗin gaba na motar ya ɗan kwantar da kansa yana kallonta,ganin ko su Baniynah da suke tare ba ta da niyyar jira yace "wait please!" Baniynah da suka sauko motar ita da Safwa tana ƴar dariya tace "Yayanah sai da safe,mun gode sosai" yace "Allah ya kaimu dear,sai mun zo ɗaukan amarya" Baniynah tace "ameen,Allah ya kawo ku lafiya" ya amsa,ta ɗan yi gaba da niyyar bin Safwa da ko tsaiwa bata yi ba bare tai masa sallama tana dariya a ciki tace "Sweetheart sai kin shigo" da sauri Muniba tace "a'a ki jirani mana" Baniynah ta ɗan zaro ido tace "ok! Tou ku yi sallama tukuna,bari naje gurinsu Yaa Muneerah" Muniba ta buɗe baki ta kasa cewa komai,da sauri Baniynah ta wuce tana ci gaba da ƴar dariya,Lieut. Abuu Turab dake ta kallonta yace "sallamar ne baza ki jira muyi ba?" Muniba ta kasa cewa komai,yace "ok! Bari mu wuce,za mu yi waya?" Nan ma ta rasa me za tace,yace "ok! Zan kira idan na isa gida,hope za ki amsa?" A hankali ta gyaɗa kanta,yace "ok thanks.. Sai da safe,a gaida su Mom" Muniba ta ɗan ɗago kanta tace "za su ji" suna haɗa ido yai mata sanyayyan murmushi me tafe da saƙonni masu girma,shyly ta juya tana zaro ido gabanta na wani irin bugawa,ya sake yin murmushi kafin ya ɗaga glass driver ɗinsa yaja motar suka bar gurin. Sanda suka fara shiga gida sukaiwa su Mami sallama kafin suka wuce gidansu Safwa,yau kusan tare suka shigo dukansu,Safwa data rigasu shiga gidan tana kwance parlour bayan ta gama waya ta sauko,ta ɗago tana dariya tace "thought baza ku shigo ba yau" Muneerah tace "a'a mun shiga gida ne muka samu hira,shi ne muka zauna sai yanzun nan Mami tace mu taho" Safwa ta tashi zaune har sannan bata cire kayanta ba tace "ohh! Ai kuwa har Mama ma ta gama jiran shigowarku ta tafi ta kwanta" Muneerah tace "Allah sarki" abincin da suka shigo da shi a babban warmer Baniynah ta ajiye tana cewa "kun ga yanzu dai wanda za su ci abinci su ci mu wuce sama,kada mu dami Baba kun san yana gida" Muniba tace "ni dai bari naje na cire kayana tukuna" Muneerah tace "tou mu wuce da abincin mana kawai" Muniba tace "tou! Ai kuma baza mu iya cinyewa ba fa,sannan ba namu bane mu kaɗai" Muneerah tace "tou Safwa ta samo abu mu ɗiba sai ta karɓa ta kaiwa Umma ko?" Safwa da hankalinta ke kan waya tace "me za'a kaiwa Umma?" Muneerah tace "abinci ne na su ita da Baba,sai su Awwal kou?" Safwa tace "ok! Bari na ɗauko abunda za'a ɗebar musu" Muniba tace "ni dai in kun gama ina sama,i want go and ease myself" Muneerah tace "jeki kawai dear" da sauri Muniba ta wuce sama,Baniynah tai sauri ta bita tana cewa "Sweetheart! Muje nai mana shimfiɗa" sukai sama tare Baniynah na dariya tace "kafin su zo mun yi wanka" Muniba tai murmushi tace "ohh! Target ɗinki kenan dama?" Baniynah tai dariya,suna shiga ɗaki Muniba ta cire kayanta ta wuce toilet,sanda tai removing make-up ɗinta kafin tayi wanka tare da alwala ta fito,Baniynah data gama musu shimfiɗa tana zaune tana waya ta kalleta,Muniba tace "wai basu shigo ba har yanzu?" Baniynah tace "uhumn! Suna can kina dai jiyo su daga nan" Muniba tace "bari kiga nayi sallah kawai" Baniynah tace "ok!" Ta ci gaba da wayarta,bata jima ba ta ajiye ta tashi ta tafi tai wanka,Muniba data idar da sallah ta tashi ta wuce downstairs inda ta barsu Khalidah,ta samesu sun samu guri sun zauna suna hira,Khalidah ta kalleta ganinta sanye da hijab tace "wai har kin yi wanka?" Muniba tace "ehh har na yi sallah ma naga baku taho ba,wallahi hiranku har sama ana ji,kuma fa Baba ya kwanta" Khalidah ta miƙe da sauri tana cewa "a'a guys gaskiya ku tashi mu tafi sama to,kada mu hana masu gidan bacci" sai sannan suka tashi suka wuce sama,suna shiga ɗaki suka samu guri suka ɗora daga inda suka tsaya,Umma data fito ɗaki ta karɓi abincin bayan ta kaiwa Baba,ta shigo ɗakin da sallama tana faɗin "ƴan mata sannunku da gajiya" duka suka amsa sukai mata sannu itama,Umma tace "tou mu kwana lafiya dama cewa nayi bari na fito muyi sallama" Khalidah tayi murmushi tace "Allah yasa ba hayaniyarmu ne ya tasheku ba" Umma tace "a'a dama bamu kwanta ba,na dai shiga gurin Engr ne babu jimawa kuma naji kun shigo" Khalidah tace "Allah sarki" Umma tace "toh sai da safe dai bari na tafi" suka amsa tana fita ta rufe musu ƙofa sanda suka ci abinci,suna gamawa aka shiga hira,masu waya kuma suka fara. Washe gari da safe kamar kullum tunda aka fara bikin daga gida aka aiko musu abinci,bayan sun ci sun yi wanka kasancewar ba wani event za'ayi ba duka ma kuma an gama bikin kai amarya ne yayi saura,yini sukai a gidan sai hira suke,jikin Khalidah dai duk yai sanyi,sai bin mutane take da ido,can da yamma gabannin maghreeba motocin kai amarya suka iso,Mami ta zo da kanta tasa Khalidah a gaba suka tafi gida,bayan tasa tai wanka ta taimaka mata ta shirya,then suka fita ta kaita gurinsu Abba sukai mata nasiha,Khalidah dai ta rufe kanta a cikin mayafi tana ta share hawaye,su Abba sukai mata addu'ah sosai sannan Mami da za su kaita ta kamata suka fita,daga ita sai Yaya Talatu Yayar su Abba sai Khalidah a mota,sauran motocin kuma aka ɗebi ƴan uwa da ƙannen Mama da su Aunty Wahidah,sai ƴan matan ƙawayenta da ƴan uwanta,daga nan gidansu sanda aka fara kaita gidansu Yaa Mohan ta gaida mamarsa,bayan an gama duk al'adun da za'ayi kafin family da ƙawayenta sukai accompany ɗinta zuwa gidanta dake cikin GRA ɗin,daga gidan surukanta zuwa gidanta da ƴar tazara,haka ma daga nan zuwa gidansu da nisa,sanda suka isa lafiyayyen gidanta kana gani za ka san mijin da take aure wani ne kuma ɗan wani,ta ɓangaren iyayenta ma kuma baza'a ce komai ba don sunyi namijin ƙoƙari ba kaɗan ba sun yi mata kaya na alfarma,kowa ya cikin ƴan uwa da ƙawayenta sai faɗi suke "maa sha Allah.. Khalidah Allah yasa gidan zamanki ne,Allah yasa ki zama tsohuwar gidan" su Mami suna ta amsawa da ameen,sanda za su rabu da su Baniynah kuwa kuka suka haɗa kai suna yi su 3,kasancewar Muniba dama ta saba da gidansu kusan a can tayi wayo,tun tana yarinya take zuwa tayi kwanaki,wannan yasa suka shaƙu sosai,Aunty Wahidah da Sisters ɗin Mama sukai ta yi musu nasiha,kafin da ƙyar aka fitar da su biyun,sanda suka ƙara yiwa Khalidah nasihar zaman aure kafin suka fita aka barta da few ƙawayenta,su Muniba kan tunda aka fito da su Mami tasa suka shiga Mota,sanda za su tafi ta wuce da su gida. Daren ranar bayan sun koma gida,kayansu na gidan su Safwa duka suka shiga haɗawa,da su Muneerah suka dawo ma haka sukai jigum² babu hiran da aka saba kowa sai jin babu daɗi yake,washe gari da safe ko da suka tashi ma dai haka kowa ya fara haramar wucewa gida,wai bahaushe ke cewa abunda ya tara ya raba,haka akayi sallama cikin mutunci da alhini,su Mama sai godiya suke yiwa mutane tare da alkhairi na kayan gara,su Muneerah dai daga nan sanda suka je gidan Khalidah kafin ta can suka wuce gida,haka su Muniba ma da Mami tace baza suje gidan Khalidah ba sai an kwana biyu duk a ranar suka wuce,aka bar gidajen shiru sai mutanen cikinsa kawai,kai baza kace anyi wani taron biki ba...





     _#Alhamdulillah alaa kulli halin! I'm stepping toward shifa'a.. Anjad shukraan'kthiir³ habibaatiiy,masu kirana a waya da masu text saboda jin shirun da yayi yawa,ina godiya sosai² Allah ya saka da alkhairi,addu'o'inku kullum suna isowa gareni,Allah ya bar zaman tare da ƙauna,bahot² khushuu and i really appreciate ILYSM.._❤️😪






*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*


  _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

  _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


*Infection*

  _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_


  _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*****

*****






#Follow

#Comment 

#Vote

#Share fisabilillah!

#ASLI-SMASHER.