Affinity
by @realsmasher
đź’ đź’ đź’ đź’ đź’
©®AS-2023.
*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*
*♡WAZEER¸.•💥*
(A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)
BĘŹ.
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*
_Sorry for the inconveniences dearest! Al'amarin Allah kana naka tsarin ne yana nasa,na san kuma a kullum shi ne dai²,ba don na riga na fara book ɗin nan ba,and bawa ba ya taɓa sanin me zai faru da shi before,tabbas da ba zan sakesa ba,abubuwa ne suke ta faruwa da ni cikin lokacin nan,and i believe that duk cikin ƙaddarata ne,na yi rashin lafiya wanda mukai kwanaki bamu yi update ba,and yanzun haka rasuwa akai min Yayar mahaifiyata,sannan Sister na ta haihu,kuyi haƙuri³ da ni don Allah,komai nake kuma a ko'ina nake kuna raina ban manta da ku ba,but in sha Allah everything will be back to normal soon.. Thanks so much for your patience and warmth prayers,both condolence and for my new born baby,Allah ya bada lada ya ƙara zumunci da ƙauna,i really² appreciate.._
19
#Affinity
Kasa cire wayar tayi daga kunnenta duk da ta ji ya katse kiran,zuciyarta banda wani irin bugawa da sauri² babu abunda yake,a fili ta dunga tuhumar kanta "me nace masa ne wai?" Lokaci ɗaya ta nemi nutsuwarta ta rasa,bata san me ya faru ba amma haka kawai zuciyarta ta bata umarni kuma tabi,da sauri ta ɗaga wayar daga kunnenta tare da aika masa kira,sai dai har wayar ya gama ring ya katse bai ɗauka ba,al'amarin sosai yasa taji damuwa ya rufeta,bata taɓa yin abunda taji tana regretting irin wannan ba,tuna irin maganganun da ta faɗa masa sosai suka dagula mata lissafi,ba komai take nadama ba irin yanda ta gaggaya masa magana kuma bai iya hanata ba,ta san duk wanda yaji zai ce ta masa rashin kunya,ita kuma abunda a rayuwarta bata taɓa yiwa wani mutum ba kenan,yau gashi rana ɗaya ta biye zuciya ta aikata abunda zai ta ganin baƙinta,kuma ta san mistakenly in har maganar nan yaje kunnen Mami sai ta mata faɗa,ba ita kaɗai ba har Abba ma da Yaa Khalifa,duk za suce ta yiwa wanda ke gaba da ita rashin kunya,a hankali tayi shiru tare da runtse idanunta tana faɗin "ohh! Yaa Allah,help me out please.. Ni dai da na san ban tanka masa ba kamar da bikin Yaa Khalidah wallahi.. What he said really hurt my feelings,but his apology sounded so sincere that i couldn't help but forgive him.." Baniynah data shigo lokacin ta kalleta tace "ke kuma maganar me kike ke kaɗai?" Muniba ta kalleta da sauri,har ta buɗe baki za ta sanar mata kuma sai ta fasa tare da tsuke fuska,Baniynah dake kallonta tayi murmushi kawai,daga haka tai wucewarta ta cire kaya ta shiga bathroom. Tunanin tura masa text ne yazo kanta tunda bai ɗauki kiran ba,nan ma ta jima tana saƙa abunda za ta faɗa kafin ta rubuta,tana tura masa ko cikakken minti biyu ba'a yi ba kiransa ya shigo,ita tai masa text kuma ita ɗin dai ta tsaya tunani da tambayar kanta me za tace? Sai da kiran ya kusan katsewa kafin ta ɗauka tare da runtse idanunta gabanta sai dukan 3-3 yake,cikin tattausan muryarsa kafin ma tayi magana ya rigata da faɗin "i'm sorry! Kin kira lokacin na ɗan fita" gyaɗa kanta tayi kamar tana gabansa,a hankali maganarta kamar ba ta so aji tace "i'm very sorry.." Kafin tace komai yace "u don't have to apologize,laifin me kikai?" Cikin sanyin murya tace "aii.. Mmm.. Na.. Maka" sai kuma tayi shiru,sun ɗauki kamar minti biyu duka sukai shiru kafin can ciki² muryarta na rawa kamar za ta kece da kuka tace "na maka rashin kunya.. But believe me ba halina bane yiwa na gaba da ni rashin kunya" ɗan murmushi yayi yace "yeah! I know and na ce it's not u,if halinki kenan tun a haɗuwarmu na farko zan tabbatar,so don't mind" tace "to ka haƙura?" Yace "i said baki min komai ba,ni nayi laifi and ina sake ba da haƙuri" da sauri tace "ai na haƙura.. Mmm! Amma.. Ai baka ce ka haƙura ba har yanzu" yanda take magana baza kace ƴar 20+ yrs bace,yayi ɗan murmushi yace "ok! I accept ur apology too" a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace "thank u" yace "u are welcome dear.. I think lokaci ya tafi yanzu,ya kamata na barki haka ki huta,ki yi bacci da safe za muyi waya" ta gyaɗa kanta a hankali cike da kunyarsa tace "ok! Good night" yace "have a peaceful night.. And" sai kuma yayi shiru,ba ya so ya faɗi abunda zai sake ɓata mata rai,because ya karanci tana da tsananin haƙuri,Muniba dake saurarensa jin ya yi shiru ta daure kamar a shagwaɓe tace "and.. What?" Ganin ta fahimci magana zai yi ya fasa,yace "do u want to hear abunda zance?" A hankali ta gyaɗa kai tace "Mmm" yace "hope ba zai ɓata miki rai ba?" Ta gyaɗa kai tace "in sha Allah!" Yace "ok! Kiyi mafarki me daɗi" zazzaro idanunta tayi a kunyace tace "mafarki kuma?" Yace "yessss!" Tace "dama ana yin me daɗi?" Yace "sosai² akwai masu daɗi" tace "like?" Yace "na aurenmu" da sauri ta rufe baki da idonta,wani iri kunyarsa ne ya sake rufeta ta gyaɗa kai kamar yana kallonta tace "ok thank u!" Yace "will u?" Ta gyaɗa kai tace "Mmm" yayi murmushi me ɗan sauti yace "ok! Bye.. Tasbahii alaa khaiir" tace "wa'anta kamaan" ya sake yin murmushi yace "ohh! Ashe duk inda aka taɓa u are in? Wow!" Tace "um'um! Koya fa nake" yace "alright! Yana da kyau hakan,but idan kin koya sai ki ɗauke ni as ur student ko? Will u teach me?" Tace "a'a ai ka iya" yace "a'a sai dai idan baza ki koya min ba" tace "ok!" Yace "promise?" Tace "a'a ni ba na yin alƙawari" yace "me yasa?" Tace "haka nan saboda kada na manta ban cika ba" yace "har ni baza ayi min ba?" Ta girgiza kai tace "Allah ya bani iko" yace "ameen.. But son samu ayi min alƙawarin,na san baza ki manta ba,and baza ki kasa cikawa ba" tace "um'um ni dai" yace "ok! Thank u.. Sai da safen?" Tace "Mmm! Allah ya tashemu lafiya" ya amsa suna yin sallama ta jira har ya katse wayar,da ƙarfi ta sauke wawan ajiyar zuciya mai nauyin gaske,a hankali ta dafe ƙirji tana faɗin "thank God! Daga yau bazan sake tanka duk abunda za'a cemin ba,kada naje ana min kallon mara kunya,and Mami ko Abba suka ji na san sai sun min faɗa.."
*SAFWA*
Kamar wasa sukai maganar nan da Umma da Aunty Hilda,washe gari taita zuba ido taga kiran Aunty'n nata taji inda aka kwana,amma har dare basu ji wani feedback daga gareta ba,sai ranar Wednesday da yamma sannan ta kira Umma,Umma na ɗauka bayan sun gaisa,Hilda tace "kiyi haƙuri don Allah Sister! Jiya ban samu fita ba wallahi saboda in-law ɗinki yana gida sai yau,amma yanzu haka ma gashi na karɓi kayan zan wuce gida,banda yamma ya yi da yanzu sai naje na nemi driver na bayar a park a kawo miki,amma ya kike gani za ayi? Na bari har zuwa gobe babu matsala sai na basu da wuri,ko yanzun naje idan zan samu masu zuwa ko kuma masu tashin asubah?" Umma tace "idan za'a samesu yanzu ina ga ki samu ki bayar ɗin tunda baki riga kin koma gida ba,amma yau kin fito gobe ma ki fita ai bai yi tsari ba al'amarin,da aurenki asa kiyi ta yawo daga nan zuwa can,kuma kina da ƙananan yara idan ba Meenah na nan ba,gurin wa za ki barsu?" Hilda tace "to shi kenan Aunty,nima na yi tunanin haka sai nace ko na bari har zuwa goben,amma tunda kin kawo shawarar nan bari kawai naje na kai,ko babu driver ma zan bayar office na ƴan union,su za su bama driver yayi delivery" Umma tace "to babu laifi,na gode sosai,Allah yasa afi haka,ya ƙara mana zumunci" Hilda tace "ameen².. Sai mun yi waya idan kayan sun iso" Umma tace "toh shi kenan idan kin samu bayar da kayan yanzun ki min ko flashing ne yanda zan gane,na gode sosai" Hilda ta amsa,suna yin sallama Umma tayi murmushi bayan ta katse wayar tace "bari Safwar ta dawo taji labarin nan,ko kuma ma dai ƙyaleta zanyi kawai ina jin har sai sun iso nai surprising ɗinta.." Gabannin maghreeb Safwa ta yi sallama,Umma dake zaune ita kaɗai ta amsa tana kallonta tace "wai ina kika je kikai zamanki haka Safwa? Na san dai Baniynah ba ta gida bare kice min gurinta kika je" Safwa ta ajiye mayafinta tana zaunawa tace "wallahi gurin Radhiya naje" Umma tace "amma kika je kika daɗe haka? Tun yaushe kika fita gidan nan? Kina dawowa school kika ce min kin fita,sai yanzu ana kiran sallar maghreeba.. Ya maki kyau,Allah ya haɗaki da Babanku wata rana,ni bazan iya da lamarinki ba gaskiya" Safwa tace "kai Umma,ba fa wani daɗewa nayi ba sosai" Umma tace "don ubanki ki faɗa min yaushe rabon ita Radhiyar da gidan nan? Ko shigowa tayi a tsaitsaye ake gaisawa da ita,idan ta yi cikakken minti 5 a godewa Allah" Safwa tace "to ni ma fa ɗin ba zuwa gidansu nake ba,yanzuma dalili ne ya kaini" a fusace Umma tace "dalilin ubanki?" Da sauri Safwa ta tashi tana turo baki ta ɗauki mayafinta ta wuce sama tana ƙunƙuni,tana shiga ɗakinta tace "fire! Ni dai ai na riga na fita,kuma tunda gashi na dawo faɗan me za'ayi min? Shi kenan mutum bazai je waje ya sha iska ba sai a kama yi masa faɗa.. Daga ace ka yi kaza sai ace ka yi wancan,kullum sai ance ka yi laifi sai ɗari.. Allah ya kawo min miji dai nayi aure na huta,sai inga kuma abunda za'a ce mutum ya yi.. Wallahi a gidana kare na zan ci babu babbaka babu me sa min ido,ehheee!" Ita kaɗai tai ta ƴan ƙananan mita da surutai. At that same night Hilda ta kira Umma ta labarta mata ta samu bada kayan,motar asubah ne da zai taso daga Minna,so ta bada number ɗinta gudun matsala yasa bata ba da na Safwa ba,kada a kirata ta nemi tai musu rashin kunya,Umma tace "ehh kin kyauta wallahi,kin san halin ƴar taki kam,yanzu sai ta ƙi tsayawa ta fahimci me za'a ce mata tai musu hauka,su kuma tunda ba ƴan gidansu bane ai mayar da saƙon za suyi" Hilda tace "ai fa Safwa dai halin nan nata yana nan" Umma tace "wannan ƴar taki lamarinta ai sai Allah" Hilda tace "in sun kawo dai za muyi magana sai in faɗa miki duk yanda za tayi" Umma tace "toh babu laifi,na gode sosai,a gaida yaran da megidan" Hilda ta amsa sukai sallama. Washe gari around 3pm aka kira Umma daga Kano line,tana ɗauka tace "hello!" Wanda ya kira yace "suna na Rabi'u ni driver ne daga garin Minna,yanzu haka ina magana ne daga tashar Kano line,shin ina magana da Murjanatu Abba Isah? An bani saƙo daga can Minna tare da number ki" Umma dake gyaɗa kai tace "ehh itace,saƙon da Hilda ta bayar ko?" Yace "ehh shi ne" tace "toh! Yanzu za'a sameka a Kano line ɗin?" Yace "ehh ina nan a cikin tasha" Umma tace "toh shi kenan zan aiko yarona ya amsar min yanzu,na gode sosai" suna yin sallama ta kira Awwal,yana ɗauka tace "Awwal idan kana kusa zo don Allah kaje Kano line ka amso min saƙon da Aunty'nku ta aiko min" Awwal yace "ga ni nan" ta katse wayar. Ba'ayi minti uku ba Awwal ya shigo,Umma tace "yawwa! Kano line ɗin za kaje,ga number sai ka ɗauka,idan ka je sai ka kira direban kace nice na aiko ka" Awwal yace "toh! Amma fa Umma kin san bani da kuɗi.." Umma tace "haka dai! Kullum kai baza'a aikeka ba sai mutum ya baka kuɗin mota,daɗin Safwa kenan idan itace baza ta tsaya tambayata ba wallahi za ta tafi,amma kai kullum babu ka iya faɗa.. Sai kaje ka ɗauko ₦200 a drawer ɗin ɗakina kazo kaje ka karɓo min" ya tashi ya wuce sama,yana saukowa yace "na tafi" Umma tace "zo nan Awwal nawa ka ɗauko min?" Ya tsaya a bakin ƙofa yace "yanda kika ce fa na ɗauko" tace "ban yarda da kai ba wallahi zo nan na gani" yace "haba Umma ban fa ɗauka miki kuɗi ba,sai na dawo" Umma tace "kazo nace maka,kada ka fita gidan nan baka gayan gaskiya ba" Safwa ta shigo da sallama a gajiye tace "Umma sannu da gida" Umma tace "yawwa" ta ci gaba da maganarta,Awwal yace "don Allah Umma ki bari naje,sauri nake na dawo ana jirana" Umma tace "wallahi² kada ka fita baka gayan nawa ka ɗauko ba" yace "na ɗauki ɗari ne fa kawai,kuma zan baki aro na ɗauka" Umma tace "kuma shi ne ban isa ka faɗan ba,sai kai gaban kanka?" Yace "yi haƙuri bari naje na karɓo miki" ta girgiza kai tace "Allah ya tsare" Safwa tace "ina ze je?" Umma tace "aikensa nayi" Safwa ta taɓe baki ta ɗauki jakarta tai sama. Awwal na karɓo saƙon ya juyo gida,yayi sallama Umma dake zaune parlour ta amsa,ya ƙarasa gabanta yace "ga saƙon.. Dama kayan kenan?" Umma tace "toh! In ma ba su kenan ba ai ka gani ko?" Yace "Allah ya baki haƙuri.. Na fita za mu kallon ball" Umma tace "auu! Ɗarin nawa daka ɗauka kallon ball za ka?" Yace "wallahi Umma ba ni da kuɗi ne,kuma yau match ɗinmu ne bai kamata ace ban je ba" Umma tace "ni wannan kallon ball sai kace jaraba,mutum yaita adashin da babu ranar ɗauka,in ba jaraba ba kuna da channel ɗin da ake yi a gidajenku amma baza ku zauna ba,kun fi son na cikin hayaniya ai ta musu da ihu har ta kai ga rigima,to dama ka nemo min ɗari na ka dawon da shi ko wallahi na cire a kuɗin makarantarka,ban ci nanin ba nanin baza ta ci ni ba" Safwa ta sauko sanye da dogon shimi da ya kai mata guiwa,Umma ta kalleta tace "Safwa kawo ɗari biyar ki fanshi saƙonki" Safwa tace "saƙona inji wa?" Umma tace "wanda Aunty'nki Hilda ta turo" da sauri Safwa ta taso tace "yana ina?" Umma tasa ƙafarta akan ledar tace "fara bani tukuna kafin ki ɗauka,yanzun nan nasa Awwal yaje ya amso a tasha,shi kuma kin san halinsa ai,ba'a aikensa sai ka bashi kuɗin napep" Safwa ta washe fararen haƙoranta tace "don Allah Umma ki bani,zan baki wallahi" Umma tace "je ki ɗauko min dai kuɗina tukuna,akan aiken naki har ɗari ya ɗaukar min zai je kallon ball" Safwa ta tashi da sauri tai sama,bata jima ba ta sauko tare da miƙawa Umma 1K tace "ga shi" Umma ta karɓa tace "banda canji kuma,kya karɓa idan na samu ko?" Safwa tace "a'a ki riƙe kawai ki bani ni dai na gani" Umma ta ɗaga ƙafarta tare da tura mata ledar,Safwa ta ɗauka ta shiga fito da kayan da suke ciki,turare ne a wata ƴar siririyar kwalba kamar roll-on,ka kalli cikinsa za kaga wasu ƴan ganyaye kamar tsiron shuka,sai wani kuma shima daban na fesawa,da wanda za'ayi hayaƙi zuwa rubutu na sha,da garin magani da za'a iya ci ko wanka ne dai oho,ta gama dubawa ta ɗaga turaren tana kallo tace "Umma ya tace miki za'a yi amfani da shi?" Umma tace "a'a sai dai ki kirata kiji,dama ai cewa tayi sauran bayani sai ta kira tukuna" Safwa tace "to bari ni dai na kirata naji" Umma tace "ki fara yi mata godiya dai tukuna sai ki tambayeta kuma" Safwa tace "toh!" Number Aunty'n nata ta kira,tana ɗauka suka gaisa tace "Aunty na ga saƙonki na gode Allah ya saka yasa afi haka" Hilda tace "ameen² daughter! Yawwa yanda za kiyi amfani da shi duk na turo miki ta whatsapp yanzun nan,ki duba ki saurara da kyau" Safwa tace "to Aunty,na gode.. Ga Umma" ta miƙawa Umma wayar suka gaisa tare da ƴan magungunsu kafin suka yi sallama,Umma na miƙawa Safwa wayarta ta shiga whatsapp ta buɗe duka voice note da hotunan da tai attaching ta saurara,Umma duk tana ji itama,bayan sun gama saurare ita ta taimaka mata gurin ware turaren,rubutun kam take ta shanye ta kwashe sauran ta kai ɗakinta ta adana cikin wardrobe,kaga yanda take ta farin ciki al'amarin zai baka mamaki,ta dunga kallon ɗan turaren me haɗe² a ciki tana tuna yanda Aunty Hilda tace sai za ta fita sannan za ta goga a saman goshinta,banda yamma ya yi yanzu kuma ta san Umma baza ta lamunci ta fita ba,da tun a yau za ta jarraba taga ƙarfin aikinsa da Aunty Hilda ke jaddada mata kada tayi wasa da su,amma ta barwa gobe tunda za taje school. Da safe ko da ta tashi tana gama shiryawa,ta tsaya gaban wardrobe ɗinta,turaren data adana ta ɗauko ta kalli na fesawar da Aunty Hilda tace shi baza tayi amfani da shi ba,sai ta ji ance ana sallama da ita tukuna,wanda yake cikin ƙaramin kwalbar tasa hannu ta ɗauko tayi rolling a saman goshinta,bala'in ƙamshin da turaren yake yasa ta lumshe ido ta buɗe ta saki dariya,da sauri ta tafi gaban mirror ɗinta ta shiga kallon fuskarta tana shafa forehead ɗinta,yanda take dai ko yaushe yanzuma haka ne bata ga wani canji ba,but Aunty Hilda said turaren zaisa tai ta sheƙi kamar tauraron da yafi kowanne haskawa a cikin tsananin duhun dare,so take taga hasken amma bayan farin fatarta babu wani abu daban,a saɓule ta ɗan yi jim kafin ta juya ta ɗauki handbag ɗinta na school tai waje da sauri zuciyarta na mata saƙe²n ko dai ba gaske bane? Lokaci ɗaya duka jikinta ya yi sanyi saboda ganin saɓanin abunda kunnenta suka ji,imanin da tai da abubuwan a hankali ya ragu,tana saukowa taiwa Umma sallama ta fita gidan fuskarta ya ɗan sauya,tsaye bakin get ɗinsu ta samu me napep ɗin da ke kaita makaranta yana jiranta,tana shiga tace "mu tafi please Ayuba,amma kada ka bi da ni ta gurin da yake da traffic jam,zan shiga test ne 9am" Ayuba me napep yace "toh Hjy" daga haka yaja suka kama hanya,PDF na course ɗin da za suyi test ta buɗe tana karantawa,tana kula da inda me napep ɗin yake bi da ita,tun da suka hawo state road maimakon da suka zo ta ƙofar Nassarawa su hau BUK road kamar yanda suka saba kullum,sai kawai ya wuce ta emir palace ya ɗauki hanya ta wuraren tudun wuzirci,dai² sun kawo gidan Wazirin Kano aka tsattsayar da hannunsu da wancan motocin da suka fito kan line gidan Waziri suka hau titi sukai gidan Sarki,kamar ance Safwa ta ɗaga kanta sukai ido biyu da kyakkyawan mutumin dake cikin mota yana magana da wani,Safwa da son mutane masu kyau ta ɗauke kanta tana zancen zuci,gaba ɗaya zuciyarta ya lula ta shiga fasaltasa a rai,a hankali ta sake ɗagowa ta dunga satar kallonsa shi kuma ya kafeta da ido duk da yana magana ne,motocin suna gama wucewa me napep ɗinta ya tayar suka wuce,tunda suka bar gurin ta shiga tunani,sam ta manta ma da wani karatun da take yi,ta shiga tunanin duniya da abunda ke cikinta har suka kai BUK bata dawo duniyarta ba,me napep ɗinta ya shigar da ita har gaban faculty ɗinsu yayi parking,a hankali Safwah tayi ajiyar zuciya sannan ta kalli inda suke,ganin sun iso ta sauka Ayuba yai mata sallama kafin yaja napep ɗinsa ya tafi.
*MUNIBA*
2 days sosai suke waya da Lieut. Abuu Turab,a hankali kuma ta fara ɗan sakin jiki da shi,duk sanda zai kira ba ta ƙasa a gwuiwa za ta amsa masa,cikin ɗan lokacin nan babu abunda bai sanar mata ba da ya shafesa,sai dai abunda ya manta kawai,yau da ya kasance Thursday and ya sa rai zai zo Kano gobe,da dare lokacin ya kirata after sun gaisa,cikin hira da hikima yace "Muniiy!" Cikin sanyin yanayinta tace "na'am" yace "i want to ask u something ina so ki amsa min please idan kin sani" ta gyaɗa kanta kaɗan tace "ok! Allah yasa na sani" yace "ameen.. Do u like me? I mean za ki iya aurena? Na yi miki as irin mutumin da kike burin aure ki zauna da shi tsayin rayuwa?" Tayi shiru ta kasa cewa komai,yace "feel free ki sanar min abunda ke ranki,bazan so kaina ba idan kika ce ban yi miki ba zan yi haƙuri,ko wane mutum yana da zaɓi,kuma yana fatan samun abunda ransa ke so,idan ka samu wanda kake so yake sonka,shi ne zai sa kuji daɗi rayuwa tare,soyayyar tsagi ɗaya ba zai taɓa wadatar da kai ba,idan kana so ana sonka shi zai sa kiga baza'a tauyeka ba,kuma kaima baka tauye kowa ba.. If there's something da bai miki ba just tell me" jin maganganunsa yasa gaba ɗaya suka kashe mata jiki,cikin tausasa harshe da lafazi yace "Muniiy! Please say something,shirunki a yanzu ba zai mana amfani ba,tell me duk abunda kike ji ko mene ne,and i promise u duk abunda kika faɗa,ba zai sa naga laifinki ba,zan ɗaukesa as my ƙadar" yanda yake mata magana cikin tarin nutsuwa,ya isa tabbatar maka yana faɗan haka ne ba don komai ba sai saboda yasa ta fito ta faɗi ra'ayinta,sun ɗauki tsawon minti ɗaya shiru kafin cikin sanyin yanayinta tace "ni.. I don't have choice akan anything,duk abunda Allah ya tsara kuma ya zaɓar min it's ok for me" cike da wani irin confidence yace "yeah! Duk abunda Allah ya zaɓar mana,as a good servant yana da kyau mu karɓa with our own good hands,but atimes mu ƴan Adam muna da buri daban²,shin mene ne burinki?" Tana girgiza kai tace "a'a ni dai gaskiya ba ni da shi,if akwai ma ban sani ba gaskiya in dai a irin wannan gurin ne" yayi ɗan murmushi yace "alright! Yanzu dai let me ask u again.. Ina da rival ko babu? Kada na saki jiki a shammaceni ai min ƙafa" Muniba tayi murmushi shyly ta girgiza kanta kamar tana gabansa,cike da son ta waske ma tambayar tace "ban gane tambayar ba" yace "da Hausa fa nayi magana kika ce min baki gane ba" Muniba dake dariya ciki² tace "da gaske ban gane ba" yace "ok! Do u have boyfriend bayan ni?" Ta girgiza kanta kafin tace "um'um" yace "really?" Tace "Mmm" yayi shiru kafin yace "but! Kamar ki? Da mamaki kice min ba ko da sauri fa kuma na yarda" idonta ta lumshe a hankali tace "who am i? Yanzu fa ka gama faɗan duk abunda Allah ya tsarawa bawa dai² ne,kuma saboda ya san za ka iya karɓa ne yasa ya jarrabeka,and this is my fate too.." Yace "Mmm! Haka ne" tace "ina addu'ah Allah ya bani ikon yin haƙuri da juriya akan duk abunda zai faru da ni" yace "ameen.. This sounds good! But let's not to skipped,mu koma kan maganar da muke yi" tace "toh!" Yace "kin amince min a ko wane irin lokaci na sanar da parents ɗina su zo nema min aurenki?" Shiru tayi saboda yanda maganganunsa na yau suke mata nauyi,yace "please kiyi haƙuri kada kice na dameki fa,haka Allah ya yi ni wani irin mutum,idan ina son abu ko mene ne shi ban iya jira ba,sauri² nake naga na mallakesa" Muniba tayi murmushi tace "amma ai aure ba'a yi masa gaggawa kuma" yace "i know dear.. But ina so a san da ni a gidanku,duk wanda zai zo daga baya ne and na riga na yi masa shamaki da wani abu,idan kin amince zan sanar da Dad suzo nemar min izinin zuwa na ganki" Muniba ta fiddo idanunta waje tare da dafe ƙirjinta,yace "uhumn! Ke nake sauraro" a hankali kamar tana yi masa raɗa tace "ok!" Yace "kin amince su zo?" Ta gyaɗa kanta kamar tana gabansa tace "Mmm" yayi sanyayyan murmushi yace "wow! Thanks so so so much dear,in sha Allah zan sanar da Dad,and at any time na san za su iya zuwa suyi magana da Abba" Muniba ta gyaɗa kanta kawai,basu wani jima ba bayan nan sukai sallama,tana ajiye wayar tayi addu'o'inta ta kwanta tana tunanin yanda al'amarin zai faru,a haka wani irin bacci yazo ya ɗauketa cike da mafarkin abubuwan da sukai waya da shi.
*WAZEER*
Ranar Monday kamar wasa ya gama shirinsa,ka kalleshi baza ka taɓa cewa wai he is corper ba,saboda duk kakhinsa bai ma tsaya kallonsu ba,normal kayansa ya saka kamar yanda ya saba,sai ID ɗinsa da p-cap kawai ya ɗauka ya fita,8am sharp a cikin AKTH yayi masa,ya samu guri yayi parking motarsa,sanda ya ɗauki wayarsa da p-cap ɗinsa sannan ya sauka motar yayi locking,tun daga hanya yake ta haɗuwa da corpers irinsa sun sha well ironed kakhi ɗinsu dake nuna they are corpers,ya kallesu kawai kamar wasu ƙauyawa ya wuce abinsa,kasancewar babu mask a fuskarsa yana jin yanda idanun mutane suke yawo a kansa,sosai ya wani irin ɗaure fuska saboda yanda ya tsani yaga ana kallonsa,Medical Department ya nufa kai tsaye kamar yanda Mimi tai masa kwatancen,yana isa ward ɗin ya kalli office na medical superintendent,shi ma likita ne who has control over all medical department,bai shiga kai tsaye ba sai da ya fara zuwa gurin secretary yai sallama,yarinyar ta ɗago da sauri ta kalleshi kafin ta amsa,ya ɗan kauda kai a hankali yace "sannu! MD na nan?" Yarinyar ta wani kafeshi da ido,ya sake ɗaure fuska yai mata wani kallon da ya tsoratar da ita,kwarjininsa ya cika mata ido,da sauri ta gyara zamanta cikin in'ina tace "ehh! Yana nan,do you have an appointment ne da shi?" Bai kalleta ba yace "yes!" Gaba ɗaya ta rikice tace "to bari na sanar masa" tana faɗan haka ta ɗauki telephone ta kira cikin office ɗin,ana ɗauka respectfully tace "sir! Akwai wanda yazo ganinka yanzu" sanda ta gyaɗa kanta sannan ta kalli Wazeer tace "wa za'a ce?" Bai kalleta ba yace "Dr Hooriyah Aliyu's Son.." Da mamaki ta dunga kallonsa,underneath tana faɗin "ɗan Dr Hooriyah? How? Dama tana da ɗa da aure?" Babu shakka domin ga kama nan ta gani,tunda ta ganshi take son gano inda ta san me kama da shi ta kasa,sai yanzu da ya faɗa sannan ta tabbatar,MD ta sanarwa abunda yace kafin ta katse kiran tace "he said ka shiga ciki" Wazeer ya wuce tare da cewa "thanks!" Entrance na office ɗin Medical director ya isa yayi knocking,daga ciki aka bashi umarnin shiga ya buɗe ya shiga da sallama,MD ya amsa tare da ɗago kansa yana kallon Wazeer,a hankali ya tsaya tare da gaishe shi respectfully,MD ya amsa yana nuna masa gurin zama yace "sit please" Wazeer ya zauna kamar yanda ya buƙata,cikin sakin fuska MD yace "Dr Hoor ta yi min bayanin komai da inda aka kaika,but abunda ban tambaya ba shi ne me ka karanta?" Wazeer da idanunsa ke ƙasa yace Doctor of medicine (DM)" MD ya kalleshi yace "akwai guraren da ya kamata a kaika,me yasa sai lalli delivery suite? Ban san me yasa idan na bada umarnin ayi attending corpers da masu practical sai a kaisu this suite ba,kuma suna yin yawa a gurin" yana maganar yaja paper yayi ƴan rubuce² cikin ƙwarewa da gogewa a aiki sannan yayi sign ya buga stamp yace "ka tafi OT (Operation theater complex),sai ka tambayi incharge ko Dr Sudais ka sanar masa ni na turoka" Wazeer ya ɗago ya kalli Medical director,sai kuma yasa hannu biyu ya karɓa tare da yi masa godiya,sannan ya miƙe sukai sallama MD na yi masa fatan nasara,ya fice office ɗin zuwa OT,direct HOD na department ɗin ya kaiwa paper,yana gama dubawa yai directing ɗinsa inda zai kasance,sai ɗan ƙarin bayanin da yayi masa na theaters ɗin da za'ayi ranan tunda ya zo a kan lokaci,after then ya gabatar da shi ga sugeons ɗinsu kafin ya haɗasa da Dr Sudais suka gaisa,daga nan ya nemi guri ya zauna tare da kiran Mimi suka gaisa,kafin ma yayi mata maganar haɗuwarsa da MD ta fara yi masa maganar "ka samu shiga hospital ɗin ne?" Yace "yes Mimi" tace "ka je gurin MD ɗin?" Yana ɗan lullumshe idanuwansa kamar me jin bacci ya sake cewa "yes Mimi" tace "ya kuka yi da shi?" A hankali yace "ya tura ni OT" Mimi tace "alright! Ai nan baka da matsala ko?" Ya ɗan gyaɗa kansa kamar yana gabanta,sai kuma ya ɗan buɗe idanunsa da kyau yace "delivery suite ɗin ma ai zan iya zama" Mimi tace "kana fama da miskilancin za ka duba matan mutane?" Maganar yazo masa bazata,a hankali ya saki miskilin murmushin da ya bala'in ƙara masa kyau,shi kansa bai san ya akai ya yi shi ba,tuna inda yake yasa ya wani irin ɗaure fuska gudun kada wani ya ganshi ya rainasa,suka gama magana da Mimi ya kashe wayarsa. 8am sharp suka shiga theater,tas suka gama da ta farko aka fito da ita da Baby'nta,kafin a shigo da ta biyu Dr Sudais ya fara masa tambayoyi akan abubuwan da suka faru,Wazeer ya ɗan kalleshi a miskilance,Dr Sudais yayi murmushi yace "don't worry my friend,if akwai abunda baka gane ba,let me know sai nai maka bayani kafin turn ɗin da zan barka kayi theater,ka san bazan ce maka komai ba until naga za'a samu matsala,so let's talk before a shigo da 2nd person" Wazeer yayi ɗan shiru lokaci ɗaya kuma yace "no need!" Dr Sudais yace "u really understand everything da ya faru?" Wazeer yace "sure" Dr Sudais yace "ko yanzu na barka za ka iya yin operation without na taimaka maka?" Wazeer ya sake cewa "sure" Dr Sudais yayi murmushi yace "alright! Let's see.. Idan da gaske za ka iya,ka san wani lokaci ana samun problems da masu practical,sai kayi bayani ka tambaya suce maka ai an gane komai,when it comes to kace ayi maka a aikace sai kaga an fara rawar hannu da ƴar murya,hope you are not irin wannan type ɗin?" Wazeer ya kalleshi sai dai bai ce komai ba,kusan 3 persons Dr Sudais ya yiwa operation,duka mata ne masu ciki,idan sun yi kuma sai yayi masa bayani,Wazeer dai saurarensa kawai yake bai ce masa ya bari ko tambayarsa anything ba,sanda aka shigo da 4th person,Dr Sudais ya kalleshi ganin ba ya cewa komai,cike da son kunyatasa a gaban nurses yace "alright! Yanzu kai za kayi fa,i think ka gane komai,u don't want my explanation,bismillah Malam Aliyu" the way yayi maganar Wazeer ya fahimci manufar da yasa shi cewa haka,bai dai masa um bare um'um ya amsa,cikin hukuncin Allah ya shiga aikinsa,Dr Sudais duk yana ankare da shi,babu ɓari babu rawar jiki,sai wani irin tarin nutsuwa da yaga ya sake shiga,cikin ɗan taƙaitaccen lokaci yayi tiyatar ya gama nurses suka fita da matar,Dr Sudais ya yi mugun mamakin Wazeer tun daga first place har zuwa ƙarshen aikinsa,komai ya yi shi cikin ƙwarewa kai baza kace wai shi ɗin bai jima yana aikin feɗe mutane ba,Dr Sudais yana gyaɗa kai kafin a shigo da wata ya kalleshi yana shigar da report yace "Aliyu ka bani mamaki matuƙa,irinku ake buƙata gaskiya wanda suka tsaya sukai karatu kuma suka maida hankali wajen sanin aikinsu,Allah ya ƙara taimakawa yayi jagora" Wazeer yace "ameen.. Thank u!" Tun daga nan Dr Sudais ya tsinke da lamarinsa,kusan gaba ɗaya sai suka koma aikin 50/50 idan aka shigo da wannan yayi,in the next sai Wazeer yayi,a haka sukai aikin ranar suka gama,lokacin sallah kawai ya tsayar da su sai cin abinci. Dr Sudais ya kira MD cikin jin daɗi ya sanar masa ya aiko masa wanda ya san me yake,yana ta yabon Wazeer da irin yanda ranarsu ta yau ta kasance,MD yayi murmushi yace "Dr Sudais kana so dai kace min ka ji daɗin aiki da Yaron nan?" Dr Sudais yace "sure Sir.. Ya bala'in ba ni mamaki ne kuma ya burgeni" MD yace "maa sha Allah.. But ba abun mamaki bane don jinin Dr Hooriyah Aliyu ya kasance haka" Dr Sudais yace "jinin Dr Hooriyah?" MD yace "ƙwarai kuwa.. Za kace min baka ga kamar da suke ba?" Dr Sudais yace "wallahi Sir tunda na ganshi nake tunanin da wanda yake min kama,sai dai ko kusa ban taɓa kawowa Dr Hooriyah tana da ɗa kamarsa ba,in fact ba na jin akwai wanda ya san tana da aure ma bare akai ga maganar ɗa" MD yace "to Yaronta ne wannan da na turosa gurinka" Dr Sudais yace "ana cewa like father like his son,shi kam wannan sai dai ace like his Mom.. Dr Hooriyah ai babu wanda bai santa ba,mace ce me kamar maza" MD yayi murmushi sannan sukai sallama.
*MUNIBA*
Kasancewar yau Friday kuma da yake lecture ɗaya ne ya kawosu wani course mai 3 credit,11am na yi suka fito suka bar school,kai tsaye daga MA'AUN gida suka yo,suna shigowa duka suka zube a parlour sai bacci,ba su suka farka ba sai da Abba ya sakko part ɗinsa zai fita masjid sannan ya tashi Muniba,ta buɗe ido da ƙyar tana murzawa tace "Abba good afternoon" yace "afternoon how are u Sweetheart? Ya school?" Tace "alhamdulillah!" Yace "maa sha Allah.. Zan fita masallaci,idan Maminku ta dawo before na dawo ki sanar mata tasa a shirya abunda ya kamata akwai baƙin da za su zo anjima" Muniba ta gyaɗa kai respectfully tace "toh Abba.." Yayi mata sallama da faɗin "sai na dawo" tace "Allah ya tsare hanya,a dawo lafiya Abba" ya amsa tare da fita. Ganin lokacin sallah ya kusa yasa bata iya komawa ba,jikinta duk haka ta dunga ji yai mata nauyi,baccin ya yi mata daɗi sosai,upstairs ta wuce tai wanka da alwala sannan ta dawo parlour,lokacin tana jiyo sanda aka tada sallah a masjid Umar bin Khattab ta fara tashin Baniynah tace "Sweet ki tashi lokacin sallah ya yi" Baniynah ta buɗe idonta da suka sauya tace "ƙarfe nawa ne yanzun?" Muniba tace "past 1 fa" Baniynah ta tashi tana cewa "bari nayi wanka tukuna" ta wuce upstairs. Guraren 2pm Mami ta shigo ta samesu a parlour suna cin abinci,duka sukai mata sannu da zuwa ta amsa,tace "kun taso school kenan?" Baniynah tace "tun 11am muka dawo" Mami tace "Abbanku ya dawo ne?" Baniynah ta girgiza kai tace "a'a!" Muniba tace "ya je masjid,and he said akwai baƙin da za su zo" Baniynah tace "yaushe kika gansa kukai magana?" Muniba tace "muna bacci ya tasheni ɗazu da zai fita masjid" Baniynah ta gyaɗa kai,Mami tace "alright! Bari nai wanka na sauko,sai naga me za'a shirya" Muniba ta amsa sukai mata fatan saukowa lafiya. Suna kitchen tare da maids ɗinsu da Mami suna aiki da hira,Abba suka shigo gidan tare da ƙaninsa around 5pm,jiyo kiran Abba yasa Muniba fita da sauri,Abba na kallonta bayan ta gaida Uncle ɗinta ya amsa,yace "ina Mamin naku?" Muniba tace "tana kitchen" Abba yace "to babu laifi yi kiranta muyi magana,ki sanar mata kada ta jima baƙin sun iso" Muniba tace "to Abba" tana shiga kitchen tace "Mami Abba na kiranki" Mami ta kalleta tace "ok!" Ta juya ta wanke hannunta ta goge tace "ku ƙarasa bari naje gurinsa" bata jima sosai da fita ba ta shigo tana faɗin "ku je ku kai musu parlon baƙi" Baniynah suka amsa sannan suka ɗebi komai suka zuba a trays,ganin security sosai a compound fiye da yanda suka saba gani ya basu mamaki,parlon baƙin Abba sukai sallama ita da Baniynah,daga ciki su Abba da suke hira da zolayar juna suka amsa,respectfully bayan sun ajiye komai suka gaisar da baƙin da suka tarar su 3 sannan suka fita. After ishaa Abba da tun tafiyar guess ɗinsu suka fita shi da Dr Sulaiman ya shigo gidan,a downstairs parlour ya samesu har Khalifa suna hira,duka sukai masa sannu da dawowa ya amsa,bai zauna ba ya wuce part ɗinsa,Mami ta tashi bayan ta haɗo masa abinci da fruits data gyara ta tafi kai masa,tana yin sallama parlonsa Abba da har yai wanka ya sauya kaya zuwa Moroccon jallabiya ya amsa,Mami ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin tana zaunawa tace "barka da hutawa yallaɓai" yayi murmushi yace "barka dai Hajiya,ya gida da yara?" Mami ta zauna ta shiga zuba masa abinci tace "alhmdllh.." Suna ta ɗan hira har ya gama cin abinci,Mami ta manta ma sun yi wasu baƙi sai da Abba ya kalleta yace "baki tambayi baƙin da suka zo ba fa yau Hajiya" Mami tai shiru tana kallonsa,ita da dama ba ta tambaya idan ba wai bayan baƙin sun tafi yai mata bayani ba,mene ne nata yau na tambayar su waye ko da me suka zo? Abba da yaga Mami ta yi shiru yayi murmushi yace "ina Mamana?" Mami tace "wacce a ciki?" Yace "Muniba" Mami tace "suna can downstairs" Abba ya gyaɗa kansa ya ɗauki telephone ya kira ƙasa,Khalifa dake kusa ya ɗauka yayi sallama,Abba na amsawa yace "ka turo min ƙanwarka" Khalifa yace "to Abba" yana ajiye telephone ɗin ya kalli Muniba yace "kije Abba na kiranki" ta amsa tare da tashi tai sama,kafin ta isa ɓangaren Abba yayi briefing Mami abunda ya faru da baƙin da suka zo musu,Muniba na isa parlour tai knocking sannan ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama Abba suka amsa mata,ta ƙarasa ta zauna tace "Abba ga ni" Abba na kallonta in a serious note yace "Mamana!" Muniba da haka kawai taji gabanta ya faɗi ta amsa "na'am!" Abba na kallonta da kyau yace "kin san Lieut. Aliyu Tameem Alƙali?" Sanda gabanta ya sake bada rass saboda jin sunan wanda bata taɓa zato ba a bakin Abba,da sauri ta juya ta kalli Mami dake kallonta ta marairaice fuska,Abba yace "kin sansa ko a'a?" Kanta ta sunkuyar ƙasa jiki a sanyaye tace "ehh!" Abba yace "ehh as in? Kin sanshi?" Ta gyaɗa kai tace "ehh" Abba yace "maa sha Allah! Mene ne tsakaninku?" Muniba ta sake yin ƙasa da kai tace "babu komai" Abba yace "babu komai?" Ta gyaɗa kai,yace "anya kuwa babu?" Muniba tayi shiru,Abba yace "amma babu komai ya turo iyayensa gurinmu su nemar masa izinin zuwa wajenki?" Kanta a ƙasa ita dai ta kasa sake iya cewa komai,tunda take bata taɓa tsintar kanta a irin yanayin da ta samu kanta yau ba,ji take kamar wanda aka ɗaɗɗaure da sarƙa a gaban iyayen nata,maganar ya yi mata mugun nauyi,Abba yayi murmushi kafin ya shiga yi mata nasiha kamar wanda zai kai gidan miji yau,sanda ya gama tas yace "u can go.. Yaron zai zo gurinki ku ga juna,ki basa lokaci har Allah yasa ku fahimci juna kin ji ko? Idan kuma akwai wani wanda kike so ne sai ki sanar mana" Muniba ta gyaɗa kai tace "to Abba" Abba yace "Allah yai miki albarka" ta amsa sannan ta tashi tayi musu sai da safe ta fita.
*WAZEER*
Wazeer bai san meke going round ba cikin Hospital,kullum zai je aikinsa zai ga ana kallonsa ana magana,sai dai yaita faman ɓata rai yana tamke fuska,magana idan ba ya zama dole ba ko akan aikinsa ba ya taɓa yi,a ganin farko ma in kai masa ba lallai ka iya fahimtar yana magana ba saboda masifaffen miskilanci,ƙarƙarinsa da mutane sallama idan zai wuce,yana barin guri za kaga an bisa da kallo ana mamaki da tambayar wai yana magana dama? Mutane da yawa na son shiga harkarsa su kulashi,ko don suji shin da gaske ne Dr Hooriyah ce Mom ɗinsa ko ya ya alaƙarsu yake? Azababben kwarjininsa ke hanasu tunkararsa gaba da gaba,a haka week ya zagayo Mimi ta shigo morning duty,ranar Monday da sassafe ta iso,dama indai zuwa aiki ne ba ta taɓa makara,kowa ya shaideta akan sammakonta,Wazeer bai shigo ba sai guraren 8am saura ƴan mintuna,lokacin kuma ko da ya shigo bai iya zuwa office ɗinta ba saboda suna da theater,sanda ya kalli agogon dake ɗaure wrist ɗinsa ya wuce OT kai tsaye. Guraren zhuhur suna fitowa ya tafi masjid yayi sallah,ko da ya fito hanyar Medical department ya nufa while yana kiran Mimi a waya,tana ɗauka yace "good afternoon Mimi" Mimi tayi murmushi ta amsa,Wazeer yace "kina office ne?" Tace "ehh" yace "ok! Zan zo gaisheki" tayi murmushi tace "alright!" Suna ajiye wayar ya iso ward ɗin,ya yiwa metrons da suke ta hira sallama ya gaishesu,wata dattijuwa tana kallonsa ganin ya ɗan tsaya kamar zai kira waya tace "shiga babu kowa Daktar tana ciki" Wazeer ya kalli ƙofar sai kuma ya gyaɗa kansa yace "na gode" then ya isa yayi knocking,daga ciki Mimi ta amsa masa ya buɗe ƙofar tare da yin sallama,Mimi dake zaune da waya a hannunta kamar tana wani uzurin ta amsa tana sakin murmushi,cikin zolaya tace "thought baka samu shigowa ba yau" yana zaunawa yace "um'um! Na shigo" Mimi tace "amma tun safe nayi expecting zuwanka" ya ɗan gyaɗa kansa yace "mun shiga theater ne,ban shigo da wuri ba sai dai² lokacin" Mimi ta ɗan gyaɗa kanta tace "kana zuwa kare kenan.. So ya aikin naku? Hope babu wani matsala?" Ya gyaɗa kansa yace "sure!" Tana kallonsa da kulawa tace "idan akwai dai ka sanar min" ya girgiza kai kaɗan,Mimi da duk motsinsa akan idanunta tace "alright! Allah ya taimaka,yanzu kun fito kenan?" Yace "mun fito sallah" tace "have u eaten?" Ya kalleta da sauri kamar zai yi magana sai kuma ya ƙi cewa komai,tace "ka ci ko kuma sai yanzu za ka nemi abunda za ka ci?" Yana ɗauke idonsa yace "nahh!" Mimi dake ta kallonsa tace "nahh as in? Answer my question" yace "sai na koma gida" tace "kana azumi ne?" A hankali ya gyaɗa kansa,tace "shi ne abunda baza ka iya faɗa ba sai ka bi long process salon ka wahalar da shari'a?" Strictly yace "i'm sorry" Mimi tace "a'a ni bance ka min laifi ba ai.. Azumin me kake?" Yace "taɗawwu'i" tace "dama can kana yi ko daga baya ka fara?" Yace "muna yi" tace "kai da wa kuke yi?" Yace "Dad!" Kallonsa ta dunga yi ba tare da ta sake cewa komai ba,ya ɗago a hankali ya kalleta da idanunsa jin ta yi shiru,da sauri ta ɗauke kanta ta ɗauki wayarta tana operating,kallo ɗaya yayi mata ya fahimceta,abunka da wanda ya karanta psychology,shi kaɗai ne kuma rai ɗaya ne a gangar jikinsa amma he had a 3 degrees,a hankali ya ɗauke kansa tare da miƙewa tsaye,kafin yayi magana akai knocking,Mimi tace "shigo" yana tsayen bayan an buɗe ƙofa yarinyar nurse ɗin ta shigo yace "i'm going Mimi" Dr Hooriyah ta kalli ɗan nata tace "OT ɗin za ka koma?" Ya ɗan gyaɗa mata kai,tace "alright! Allah ya bada sa'a sai kun fito" ya amsa tare da cewa "sai an jima" ya juya a nutse ya nufi ƙofa,Mimi ta kalli yarinyar dake ta kallonsa tace "Halisa ya akai?" Da sauri yarinyar ta juyo sai kuma ta fara ƴan kame²,dama musu suke akansa da alaƙarsa da Dr Hooriyah,ana tambayar wanda zai iya zuwa ya binciko idan da gaske ne maganar da ake ta faɗa,wasu sun ce ba ta da aure a saninsu da ita,wasu kuma suka ce a girman da Wazeer yake da shi bai ci ace Dr Hooriyah ce ta haifeshi ba,sai dai in ace ƙaninta ne,amma dai a haife ko na kaji baza ta haifeshi ba,musun da ake ya janyo kowane side suka sa 10K in har aka faɗa musu saɓanin abunda su suke gani,sai kuma aka rasa wanda zai iya zuwa shi ne ita tace za taje tazo da labarin. Mimi na kallonta fuskarta a ɗan ɗaure ta sake kiran sunanta "Halisa!" A ɗan firgice tace "na'am Dr" Mimi tace "what brought u into my office?" Halisa tace "ana buƙatar ganinki ne a nursery" da sauri Mimi ta tashi tana cewa "me yake faruwa a nursery ɗin?" Halisa tace "a'a nima haka aka ce min na sanar miki" Mimi ta wuce da sauri ta fita ta barta tsaye,Halisa tayi murmushi ta fita,tana isa gurin da suke aka fara mata tambayar "ya akai? Kin gano yanda suke?" Ta kalli masu zaƙalƙalewa akan Dr Hooriyah bata haifi Wazeer ba tace "ku fara bani 10K ɗina tukuna,in akai ɗinyar makaho sai kuji komai" ɗayan side ɗin suna dariya tace "ai har ku sai kun kawo" sai kuma duk sukai shiru suka fara cewa ya za'ayi haka? Tace "oho dai ku bani" haka aka lale mata kuɗinta cas kafin ta shiga yi musu jawabi...
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
*Infection*
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAIđź’Ż*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*****
*****
#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.