Beseech
by @realsmasher
💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*
*♡WAZEER¸.•💥*
(A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)
Bʏ.
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*
```Wishing myself the happiest of birthdays.. On this special day,i just want to thank Almighty Allah for the priceless gift of life that He has given me and for the wonderful people He has put in my life. I'm a happy celebrant today! Happy birthday to me.. Happy birthday to me! Happy birthday dear me..```🥂🎂🦋
21
#Beseech
Lokaci ɗaya mood ɗin Safwa ya sake canjawa,Wazeer dake kallonta ya ɗan lumshe idanu kamar bai san me ke faruwa ba,cikin gajiya da magana yana yatsina fuska yace "an min rowan digits" Safwa tayi shiru ta kasa cewa komai,bata manta maganar da suka yi da shi ba akan number Muniba da ya tambayeta ranan,ɗauke kansa yayi tare da sake lumshe idanunsa,for about 3 minutes babu wanda ya sake magana,can a hankali ya buɗe idanunsa da kyau ya kalli Safwa da tayi shiru tana kallon motar Abba da ya shigo gidan yayi parking ƙasan tent,ana kashe motar Mubasshir ya buɗe ya sauko daga front ya buɗewa Abba dake back seat,yana fitowa ya kallo balcony sai kuma taga sun tsaya suna magana,tunda suka sauko motar Safwa ke kallonsu gabanta na ɗan faɗuwa,duk da bata san me suke magana akai ba amma haka nan taji ta tsargu,for about 2 minutes kuma sai Abba ya wuce ya nufi get driver ya sauko daga motar ya rufa masa baya,while Mubasshir kuma ya nufo balcony fuskarsa a haɗe yayi musu sallama ya wuce ya nufi entrance,Wazeer dake kallon Safwa ta gefen ido ya amsa tare da ɗago kansa da niyyar su gaisa da Mubasshir,sai dai bai samu damar hakan ba don ya riga ya shige,ɗan gyara zamansa yayi kafin ya buɗe baki kamar yana magana da kansa yace "tunanin me kike?" Maganarsa ya taimaka wajen dawo da ita hayyacinta,ta girgiza kai tana ƙirƙiro murmushin da iyakacinsa saman lips ɗinta tace "babu komai" yace "are u sure?" Ta gyaɗa masa kai tace "yap!" Ya ɗan taɓe baki yana kauda kansa yace "ok! I think zan wuce yanzu" tana gyaɗa masa kai tace "ok!" Yace "sai wani lokaci,a gaida Mom" tace "za ta ji" tana sakin murmushin da kamar don dole take yinsa,miƙewa suka yi kusan tare tace "muje na maka rakiya" yace "oh no! Ba sai kin wahala ba,thanks" tace "alright! Na gode sosai da ziyara" ya gyaɗa mata kai yana sauka balcony yace "sai mun yi magana" daga haka ya wuce cikin ɗan sauri,Safwa na tsaye gurin tana kallonsa har ya kai get,yana fita gidan ta ɗauki tray ɗinta ta fito zuwa gida ranta babu daɗi. Tana yin sallama parlour Umma ta ɗago tana kallonta tace "me zan gani?" A kumbure cike taf da haushi Safwa tace "ya tafi" Umma tace "to ya ci abincin?" Zama Safwa tayi jagwab tana kyaɓe fuska tace "a'a bai ci ba" Umma tace "me ya faru to na ganki haka wani iri?" A hankali ta zame ta kwanta saman kujera tana kallon tray data ajiye ta kwashe labarin komai ta sanarwa Umma,Umma tai tsam da ranta tace "toh ni yanzu abunda ban gane ba,ke ya sani ko ita Munibar? Sannan cikin ku biyu wa yake so da yake tambayar number ta bayan yana da taki?" Safwa tace "ni ya sani,amma ni gani nake kamar so yake yace min yana sonta,which is abunda bazan bari ya taɓa faruwa ba,dama tun ranan da ya tambayeni number ɗinta nake zargin haka.." Umma tace "toh! Yanzu na fahimceki,amma me yasa tun farko kema kika nuna masa Munibar? Sakancin da kika fara yi kenan,ke baki san ko miji ne da kai a yanzu ba'a nuna masa ƙawaye ba bare koɗa halayensu a gabansa?" Faɗa sosai Umma tai mata tana faɗin "ko don gaba kada ki kuskura ki ƙara bari ba saurayinki kawai ba koma waye ya san wata ta dalilinki,don haka za'ayi ta yi miki ƙwace da fin ƙarfi kina kallo babu yanda za kiyi" Safwa ta gyaɗa kai ranta a jagule tace "toh Umma yanzu ya za'ayi ni wallahi sonsa nake tun sanda na fara ganinsa,shi kuma ya bijiro da maganarta" Umma ta kalleta tace "a'a babu wannan maganar,ki sha kuruminki ke dai kawai zan san abunda za'ayi akai,amma ko da zai sake yi miki maganarta,kada ki nuna masa ba kya maraba da alaƙarsa da ita,kiyi ta lallaɓasa har mu san nayi" Safwa ta gyaɗa kai tace "toh! Amma Umma bazan sanar da Aunty Hilda ba?" Umma ta girgiza kai tana faɗin "a'a ba sai kin kirata ba,ai wannan aikin bai fi ƙarfina ba nima,akwai warce na sani dake bada taimako kan irin wannan matsalar,Hjy Baturiya ta haɗani da ita,in Allah ya kaimu zan kirata na sanar mata abunda nake so ayi,ba dai kina sonsa ba?" Safwa tai saurin gyaɗa kai a shagwaɓe tace "ehh Ummana!" Umma tace "shi kenan an gama.. Za kiga abunda zai faru,ke dai za ki sha mamaki.. Shi da sake tuna wata Muniba bare yayi maganarta sai idan kin so" Safwa tai zumbur ta tashi zaune tana washe baki tace "da gaske Umma?" Umma tace "ahaf! Kuma dai ba ni na faɗa miki ba? Ke dai tsaya nan kiyi kallo" Safwa tayi ihun murna tace "wayyo Allah daɗi,ai kuwa wallahi Umma da kin gama min komai idan kika sa hankalinsa ya karkato kaina,don baki gansa ba kyakkyawan gaske,na aureshi na gama yin sa'a wallahi,don kaf cikin friend ɗinmu babu wanda ta auri haɗaɗɗe kamarsa" Umma tace "shi kenan.. Tashi kije maza ki kai kayan can kitchen kafin Babanku ya shigo ya dasa min tambayar wannan mene ne? Na waye?" Safwa tayi dariya tare da tashi ta wuce kitchen da tray ɗin data shigo da shi,tana fitowa ta wuce sama tana kiran number ɗinsa taji ko ya kai gida. Not too long ago da tashinta Baba ya shigo da sallama fuskarsa babu walwala,bayansa Awwal ne da Bilal ɗauke da manyan ledoji,Umma data ɗago ta kalleshi sanda yasa taji shakkarsa,ta daure ta amsa da faɗin "sannu da zuwa Baban Bilal" yace "yawwa!" Yana kallon yaran da suka nemi guri suka zauna,then ya sake kallonta tare da jefo mata tambayar "ina Safwa?" Umma tace "tana sama ɗakinta,yanzun nan bata jima da barin nan ba" Baba ya kalli Umma sai kuma ya wuce sama yana cewa "kice mata tazo ta sameni ina son ganinku ke da ita yanzun nan a ɗakina" Umma tai kasaƙe tana faɗin "lafiya dai Baban Bilal?" Baba bai tsaya ba yace "kuzo ku sameni ina son magana da ku" Umma ta gyaɗa kanta tace "toh shi kenan gamu nan" ta dafa kujera tare da yunƙurawa ta miƙe,bata bi ta kan su Awwal ba ta wuce tabi bayansa,tana hawa sama ta ƙwanƙwasa ɗakin Safwa tare da kiranta "Safwa!" Safwa dake kwance tana chat happily tace "na'am" Umma ta buɗe ƙofar daga bakin ƙofar da take tsaye tace "kizo Babanku na kira" Safwa ta tashi da sauri tana zaro ido tace "ni kuma? Ya dawo ne?" Umma tace "sun shigo yanzun nan,da alama sun je wani waje ne da su Bilal" Safwa ta dafa ƙirji cikin zullumi tace "na shiga uku,me nayi?" Umma tace "toh taya za ayi ni zan sani? Ki taso muje maza kada kisa faɗansa ya shafeni" Safwa ta taso da sauri gabanta na wani irin tsinkewa,duk abunda take ba ta mantawa Babanta na iya taka mata burki,baiƙi yasa bulala ya zaneta ba,dan bai da wasa ko kaɗan,a baya tabi Umma har ɗan madaidaicin ɗakinsa,suna shigowa Baba ya ɗaga kai ya bisu da kallo ita da Umma,Safwa ta raɓe gefen kujerar da Umma ta zauna tana faɗin "sannu da zuwa Baba" a daƙile yace "yawwa!" Umma dai kallon Safwa kawai take,ita kanta duk ƴan abubuwan da take don ta shawo kansa a wasu lokutan takan ji shakkarsa,Baba na kallonsu fuska babu wasa yace "yaushe Safwa kika fara tsaiwa da samari ban sani ba? Did i gave u chance ko damar kula wani namiji bayan ƴan uwanki su Awwal da ni nan mahaifinki?" Safwa tayi shiru saboda yanda maganar yazo mata bagatatan,Baba ya juya ya kalli Umma ransa ɓace yace "Maman Safwa kin san yarinyarki na kula samari har ta kai su wani gidan saboda kada na gani ko kuwa kema baki sani ba?" Umma ma tayi shiru,Baba da shirunsu ya fusata yace "zancen banza zancen wofi,ina magana kun yi min shiru dukanku,me kuke nufi? Da saninku kenan komai yake faruwa,ni ubanta aka rufe har sai maƙota ne za su tareni su sanar min abunda ke faruwa a gidana?" Kallo ɗaya za ka yiwa Safwa data kasa kallon Baba ka san a tsorace take,Umma ta karyar da kai kaɗan cikin sanyin murya kai baza kace ta iya hayaniya da ɗaga murya ba idan tana magana tace "ayi haƙuri Baban Bilal.. Amma ban katse maka hanzari ba,a ganina yanzu a shekarun Safwa idan bata tsaya da saurayi ba sai yaushe? Ba tun yanzu ba ake ta yiwa sa'anninta aure,wasu na gidajensu har da rabon haihuwa,idan ba ta tsaiwa ƴar hiran nan,a ina za ta samo mijin aure? In da ace a ƙauye ne yanzu tuni tana da ƴaƴa 3-5,kuma kai da kanka ka sha faɗa min dangi suna ta tambayar yaushe ne aurenta? Na san cikin abokan wasa kuwa baza'a rasa masu yar maka magana akan ta yi nauyin jini ba" Baba yayi tsam yana sauraren maganganun Umma,cikin kwantar da murya tace "ya kamata a duba maganata ranka shi daɗe,ba da wata mummunar manufa nima na goyi bayan ta tsaya da saurayi yanzu ba,illa dai fatan ace ta samu mijin aure mu kawar da ita daga gabanmu" Baba ya ɗan gyaɗa kai cike da gamsuwa kafin ya nisa yace "ban ƙi ta maganganunki ba,amma me yasa idan za tayi zancen baza tayi a ƙofar gidan mahaifinta ba sai ta tafi can gidan mutane? Ni ban isa da gidana bane? Ko kuma raini da kuma ban isa nasa doka abi bane sai dole an karya? To ni bana son haka,idan an raina arzikina ne sai naji,amma kada a sake raina ya ɓaci,zance ne tunda kin kai munzali za ki iya yi,amma ki san da su waye² za ki tsaya,ba ko wane kalar namiji za ki kawo min gida ba.. And daga yau kada wani abu ya sake faruwa ace sai a waje zan ji,idan ba haka ba rai zai ɓaci,am i clear?" Safwa tai saurin kallon Umma ta kasa magana sai ɓari bakinta da jikinta suke,Umma ta gyaɗa kai tace "ai haka ma bazai sake faruwa ba,kuma ko kusa ba raina arzikin gidansu tayi ba,tana dai zuwa can ɗin ne saboda gudun ka ganta kai mata faɗa" Baba yace "to daga yau duk wanda yazo ki kawosa gidanku,kina jina ko?" Da sauri Safwa tace "to Baba" yace "tashi ki tafi,Allah ya bamu alkhairi" tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta miƙe da sauri tace "sai da safe" Baba yace "Allah ya kaimu lafiya" a hankali tace "ameen.. Umma sai da safe" Umma tace "Allah ya kaimu.." Safwa na fita ɗakin Abba ta tsaya tare da dafe ƙirji ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya,wani irin farin ciki ne ya mamaye duka zuciyarta,badon komai ba sai saboda samun damar zance data samu daga mahaifinta,da tana yi ne a ɓoye saboda gudun abunda zai faru,amma yanzu za tayi me licence tunda baba ya cire takunkumin daya sa mata,sai dai abu ɗaya zuwa biyu ne bata ji daɗinsa ba,yanda Baba yai maganar duk da bai fito ya faɗi wanda suka sanar masa ba,ta tabbatar bazai wuce Abbansu Baniynah ba,shima kuma ba wai haushinsa taji ba,tunda ga shi a dalilinsa ta samu damar tsaiwa da ko waye babu shakkar wani abu zai faru,abunda bata ji daɗinsa ba a duka maganar shi ne hanata yin zance da Baba yayi ba'a gida ba,amma babu komai hakan ma da ta samu har ya amince,za ta ci gaba da lallaɓawa amma underneath ta ƙudurce ba kowa za ta bari yazo gidansu ba,saboda akwai wanda take ganin kamar idan ta kawo su tace nan ne gidansu ajinta zai zube.
*MUNIBA*
Su Husniyah na tafiya after ta tabbatar sun isa gida ta kirasu tare da tambayar yanda suka koma,tana ta sake yi musu godiya suma suna mata,har suka bata Mom a waya suka gaisa tayi mata godiya,yanda Mom ɗin Lieut take amsa maganar Muniban ya isa tabbatar maka cewar ba Lieut. Abuu Turab kawai yayi sa'ar samun karɓuwa gurin family ɗinta ba,itama ta samu gurbi a zuƙatan family ɗinsa,after sun yi sallama ta ajiye wayar tare da sakin murmushin dake fitowa daga ƙasan zuciyarta,Baniynah ta ɗago ta kalleta kaɗan kafin tace "hey! What's up? Me Mother in-law ɗin naki ta faɗa miki ne da ya baki nishaɗi haka?" Muniba ta ɗan waro almond eyes ɗinta tana sake murnusawa tace "na sa miki ido ne idan kuna maganarku da Mami?" Baniynah ta fara dariya tace "ahh! Me kike son cewa?" Muniba tace "abunda kika fahimta mana" Baniynah na dariya tace "amma kin san Mami is not my in-law,ni Mami uwata ce dama can" Muniba tace "nima haka" Baniynah ta buɗe duk girman idonta tace "awwnnn! Gaskiya na ji daɗin yanda kikai maganar nan Sweetheart,Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" Muniba tace "ameen².." Suna nan zaune suna hira,har aka yi kiran ishaa suka yi,Mama data tafi sama bata sauko ba har sanda Safwa ta shigo,sanda za ta fita Baniynah ta bita da kallon mamaki,tana ganin sanda Safwa ta ɗauki tray ta fita,a hankali tayi murmushi tace "ni dai na san banza bata kai zomo kasuwa" Muniba dake danna wayarta ta ɗago ta kalleta tace "me kenan?" Baniynah tace "zance ta shigo yi" Muniba ta ɗan yi jim tana kallonta kafin tace "i don't get u?" Baniynah tace "a nan mana" Muniba ta yatsine fuska tace "nan ina?" Baniynah tace "i mean nan gidan" Muniba ta ɗan buɗe baki da mamaki tace "really?" Baniynah tace "auu! Wai baki sani ba dama?" Muniba ta girgiza mata kai tace "um'um" Baniynah tace "i think Baba bai san tana tsaiwa da samari ba gaskiya,shi yasa ba ta yarda ta kai su gidansu" Muniba ta gyaɗa kai a hankali tana jinjina maganar a ranta da mamakin me yasa Baba zai hana Safwa tsaiwa da saurayi at her age? Buɗe ƙofar da aka yi yasa ta waiga don ganin waye ya shigo kuma,Mubasshir ne ya shigo da sallama ciki² fuskarsa ɗaure,Muniba dake kallonsa ta saki murmushi ta amsa da faɗin "sannu da dawowa Yaa Mubasshir" ya kalleta ba tare da ya zauna ba yace "yawwa dear! Yaa school and exams?" Tace "alhmdllh! Mun gama yau" ya gyaɗa kansa yace "Allah ya taimaka.. Mama fa?" Muniba tace "she's upstairs,ta je sallah tun ɗazu bata sauko ba" suna maganar sai ga Mama na sakkowa tace "ƴan mata kun yi sallah ne?" Muniba ta juya tana kallon staircase tace "ehh" Mama tace "to muje muyi dinner" lokaci ɗaya kuma tana kallon Mubasshir dake tsaye har lokacin tace "a'ahh! Yaushe ka shigo gidan?" Yace "yanzu.. Ina yini?" Mama tace "lafiya lau.. Ya aikin?" Yace "alhmdllh!" Ta gyaɗa kai tace "Allah ya taimaka yayi jagora" yace "ameen.." Har sun wuce za su bar gurin Mama ta ɗan waigo tana kallonsa tace "toh! Kai baza kayi dinner bane? Ko are u full?" Ɗan shiru yayi sai kuma ya girgiza kai yace "a'a" ta kalleshi tace "to nan abincin zai zo ya sameka?" Ya sake girgiza kai yace "a'a" ta taɓe baki ganin kamar bai son magana ne,da alama miskilanci yake ji yau ko kuma maganar ya zamar masa babban aiki,wucewarta tayi ta barshi tsaye a gurin,suna zaune dining bayan su Baniynah sun yi serving kowa ta ɗibi abunda take son ci itama Mama sun zuba mata,Mubasshir ya iso gurin yaja kujerar kusa da Muniba ya zauna,cikin tsare gida yace "Baniynah kawo min ruwa mara sanyi" Baniynah da har ta ɗauki plate za tai serving ɗinsa ta kalli Mama kafin ta kalleshi tace "abincin fa?" Yace "serve" ta ɗibar masa yanda zai ishesa,sannan ta ajiye then ta tafi ta ɗauko masa ruwan da yace,tana ajiye masa ta koma ta zauna inda ta tashi,Mubasshir ya ajiye cup ɗin ruwan dake hannunsa,a hankali yace "Mama!" Mama tace "ka san ba na son magana a table ko?" Mubasshir ya gyaɗa kai yace "i'm sorry! But.." Sai kuma yayi shiru,Mama ta kallesa tace "what are u trying to say kuma kai shiru? Mmm?" Mubasshir yace "Mama kin san Safwa na shigowa gidan nan da samari suyi hira?" Mama ta kalleshi tace "samari?" Ya gyaɗa kai yana ajiye spoon ɗin hannunsa,yace "yanzu haka na shigo na sameta da wani,and ba yau ta fara kawo maza gidan nan ba,Abba ya ganta ba sau ɗaya ba,maganar da yayi min idan a compound suke zama da sauƙi,amma fa har balcony take zama,abunda ko Khalidah kafin tayi aure ba ta zama nan,me yasa ita baza ayi mata magana ba? Abba ya sha tambayata me yasa sai nan gurin za su zauna? Wasu lokutan ganinsu da yake ne yake hanashi shigowa" Mama dai mamaki ma ya hanata kai spoon bakinta ko ta mayar da shi ta ajiye,Muniba kam was busy abincinta kawai take ci kamar ba ta gurinma,Mama tace "yanzu ina Abban?" Mubasshir yace "ya sake fita" Mama tace "kenan tare kuke da shi?" Mubasshir yace "ehh!" Kamar wanda akai playing ɗinta Mama ta mayar da spoon ɗin ta ajiye da sauri,fuskarta na bayyanar da mamaki tace "ina ya tafi kuma?" Mubasshir ya girgiza kansa yace "don't know.. Amma na ji kamar yana cewa zai yiwa Engr. Maganar,ba ya tunanin ya san abunda ke faruwa" Mama tai shiru tana tunani,lokaci ɗaya ta tashi daga dining ɗin,Muniba tai saurin ɗaya kai tana kallonta,sai sannan ta ji za ta iya yin magana,tace "Mama abincin fa? Ki zauna ki ci tukuna" Mama tace "i'm coming Sweetheart" da sauri ta wuce ta bar gurin. Kallon Mubasshir Muniba tayi tace "Yaa Mubasshir da baka yi maganar nan yanzu ba" Mubasshir bai kalleta ba yace "da sai na bari har yaushe?" Muniba tace "ko da idan muka gama dinner ne.. Kuma ai think cin arziki Safwa tazo" Mubasshir yace "cin arziki? Idan wani abu ya faru kuma fa? Shin kin san me zai iya faruwa idan Babanta ya sani daga baya?" Muniba tayi shiru,Mubasshir ya ɗan fesar da numfashi yace "samari take kawowa anyhow,yau idan ka ganta da wannan gobe da wani zaka ganta,and duka babu wanda take yarda ta tsaya da shi a ƙofar gidansu,idan wani abu ya sameta zancen ya koma kunnen iyatenta,cewa za suyi mun sani bamu sanar musu ba,maganar zai iya girma ya zama babban abu,gara a yiwa tufkar hanci tun bai nisa ba,samari da yawa da take kawowa gidan nan ba mutanen arziki bane,suna neman damar da za suyi amfani da ita ne kawai a gurinta,ita kuma saboda yarinya ce me high test take kulasu" Baniynah da bata ce komai ba tace "kwaɗayi dai yasa take tare da su har yanzu,amma ai Ummarta ta sani,ita take bata damar tsaiwa da duk samarin" Mubasshir ya taɓe baki yace "is left for them.. In baza ta daina tsaiwa da su ba,sai taje can gidansu ta ci gaba da kulasu a gaban iyayenta,ta bar kawo mana su nan" yanda yake magana duk da ba da faɗa yake yi ba,amma za ka tabbatar ransa a ɓace yake,kuma ciwon abun ke damunsa,babu wanda ta sake yin magana cikinsu har suka gama,Mubasshir da ransa ke ɓace ya miƙe ya nufi ƙofa zai fita sai kuma ya juyo yana kallonsu yace "duk wacce na gani da wani saurayi cikinku ba wanda iyayenmu suka amincewa ba wallahi sai ranku ya ɓaci,ko wane kare da doki sai ya biyo yarinya don rashin sanin ciwon kai ku tsaya da shi" Baniynah ta waro ido waje tace "Yaa Mubasshir mu fa bama kula kowa" yace "kuma yi ku gani" yana faɗan haka ya fice.
*SAFWA*
Kamar yanda Umma ta sanar da Safwa da safe bayan duk sun wuce islamiyya,ya rage sai ita kaɗai a gidan,tana zaune parlour ta ɗauki wayarta ta shiga kiran wata number da tayi saving da *Malama Gaaji*,kiran na tafiya tasa wayar a speaker,sai da kiran ya kusan yankewa sannan aka ɗauka da sallama,Umma ta amsa tace "ina kwana Hjy Gaaji?" Hjy Gaaji ta amsa da faɗin "lafiya lau Hjy Murja,ya gida da yara? Ya me gidan?" Umma tace "duk suna nan lafiya,ya aiki da fama da jama'a?" Hjy Gaaji ta amsa,sukai shiru na some seconds kafin Hjy Gaaji tace "akwai wani matsala ne Hjy? Ina tare da baƙi yanzu,ko za mu bari zuwa anjima?" Umma tace "Malama wallahi wata matsala ce tasa na kira ki" Hjy Gaaji tace "to akan mene ne?" Umma ta kwashe komai ta sanar mata,Hjy tace "duk na ji bayaninki,yanzu me kike so ayi akai?" Umma tace "don Allah irin taimakon da aka saba dai nake nema yanzu ma,duk abunda ya kama ayi babu matsala" Hjy Gaaji tace "toh Hjy Murja,in sha Allah za'a yi duk ƙoƙarin da ya kamata,amma idan akwai abunda kike so ayi kuma sai ki sanar min" Umma tace "ehh to idan sona ne zuciyar yaron da hankalinsa nake so a karkato kan Safwa tunda har tana sonsa,don Allah ko me ya kama ayi mu samu hankalinsa ya dawo kanta" Hjy Gaaji tace "to shi kenan Hjy,in sha Allahu za ayi,da zaran na gama haɗa abubuwan sai ki turota ta karɓa,ko kuzo tare da ita" Umma tace "ai sai mu zo tarenma Malama,nima ina ta son kira nace a ɗan ƙara zafin abubuwa,kwana biyu na fara samun matsala da Babansu Malama,ba kamar kwanakin baya ba gani nake kamar abubuwa sun fara yin sanyi" Hjy Gaaji tace "toh babu matsala,Allah ya bamu dacewa da mafita,ki samu lokaci ki shigo sai mu tattauna sosai,ai na faɗa miki dama akwai ayyukan da suke buƙatar a sabunta su" Umma ta amsa da "ameen Malama.. In sha Allah zan shigo ko zuwa next weekend" Hjy Gaaji tace "toh shi kenan sai kin zo ɗin" then sukai sallama. Yamma sosai Safwa suka shigo gidan,Umma da bata jima da fitowa kitchen ba ta kammala girkin dare ta ɗago ta kallesu tare da amsa sallamar da sukai,Safwa tace "sannu da gida Umma" Umma tace "sannu ƴan makaranta" Safwa tai rau² da ido tace "yawwa!" Umma tace "to inji dai babu wata matsala na ga kina ta ɓata rai?" Safwa ta gyaɗa kanta tace "a'a babu kawai sai dai akan maganar nan na jiya" Umma ta kalleta kafin ta kalli su Bilal tace "Bilal ku wuce ɗaki ku cire uniform kuyi alwala kafin Babanku ya shigo" Bilal ya tashi ya ɗauki jakarsa ya wuce,Aasim da Usman da suke faɗa ta kalla tace "to kajin nawa sun dawo za su sa ni tsinin baki,kun fice min daga nan ko sai na saɓar muku" Aasim ya shagwaɓe kamar zai yi kuka yace "Umma shi ne yake dukana fa tun a islamiyya" Umma taiwa Usman wani kallo tace "akan wane dalilin ka dokeshi? Ban hanaka yana dukansa ba Zunnu?" Zunnu yace "Umma wallahi abuna ya ɗaukar min a jaka tun sassafe kafin mu tafi islamiyya" Umma tace "Auta me ka ɗaukan masa?" Aasim ya ɗauki jakarsa zai gudu,Umma tace "uhumn! Ba ka da gaskiya kenan,zo nan Jerry" Aasim ya tsaya bakin ƙofa yana ɓoye jakarsa na Spiderman a baya,yana turo ɗan bakinsa yace "ban ɗaukan masa komai ba fa" Umma tace "a'a Auta ƙarya kake,zo nan ka kawo min jakar na gani" Aasim yace "ai na basa" Umma ta kalli Zunnu tace "ya baka abun naka?" Yace "ƙarya yake be bani ba,har sawa yayi Mu'allimarsu ta dokeni" Umma tace "lallai wannan shi ne ga mari ga tsinka jaka,zo maza ka bashi abunsa a gabana" Aasim ya maƙale bakin ƙofa ya ƙi zuwa,Umma tace "baza ka zo ba ina kiranka?" Ya gyaɗa mata kai,Awwal da ya shigo lokacin da fito Umma ta ɗaga kai ta kalla tace "Awwal miƙo min Aasim" babu wata² Awwal ya cirashi sama yana takowa cikin parlon,wani irin ƙara Aasim ya kwaɗa ya wurgo jakarsa yace "zan bashi ai" Awwal ya diresa gaban Umma,tasa hannu ta damƙeshi da kyau tace "ni sa'ar wasanka ce ko? Don ka ga ina cema Babana,ina lallaɓaka za kai min iskanci? To ubanka zan ci wallahi,duk ranar da ka sake ɗaukan masa abu,kazo kace min ya dokeka ni da kai na zan zaneka kuma ka bashi abunsa.. Maza buɗe ka ɗauki abunsa ka bashi ina kallo,ko na ɗora maka cinya yanzun nan,sai numfashinka ya daina fita da kyau" ta ɗaka masa duka a baya ta turashi,kuka ya tsanyara tare da gantsarewa har wani shiɗewa yayi kafin ya iya sosa bayansa,cikin tsawar da sai da parlon ya amsa Umma tace "ɗauko abunsa ka bashi nace" a guje ya buɗe jakar ya ɗauko shirin kyauro ya wurga ma Zunnu,Umma ta buga masa tsawa tace "ɗauki da hannunka ka kai masa,kafin na kamoka na zane" a guje ya sunkuya ya ɗauka ya miƙawa Zunnu,yana amsa Aasim ya wuce da gudu zuwa ɗakinsu yana kuka,Umma tace "ka yi na jini ma,ai za ka gamu da ni ne" ta kalli Zunnu tace "yi haƙuri Zunnu,maza kaje ka cire uniform" yace "toh!" Ya wuce yabi bayan Aasim,Umma ta kalli Awwal dake niyyar zama tace "to babban banza ka shigo gida kamar mace,ka san dai in Babanku ya shigo ya ganka zai maka maganar masallaci ko? Ka san lokacin sallah ya yi kake neman zama cikin mata" tashi yayi ya fita yana cewa "nima fa ba zama zan ba" tace "ai shi yasa naga har sai da aka maka magana" lokaci ɗaya ta juya tana kallon Safwa tace "Yawwa! Wai ni a ina Babanku yaji maganar nan ne ma har yazo ya titsiyemu jiya?" Safwa ta kyaɓe baki tace "nima ban sani ba,amma ina jin Abbansu Baniynah ne ya faɗa masa" Umma ta zuba mata ido tana kallo tace "kin tabbatar shi ya faɗa masa?" Safwa tace "ehh! Muna tare da Aliyun nan suka shigo gidan,sai kuma shi ya fita,kuma dama ba jiya kawai ya taɓa ganina ba" Umma tace "toh! Ai kuwa inma shi ne,munafurcinsa zai koma masa,da yardar Allah abunda suke jifanki da shi zai koma kan ƴaƴansa,mutane baza su taɓa faɗin alkhairi akan ƴaƴan wani ba,kullum nasu shi ne shiryayye na wani kuma watsattse,to duk suyi su gama ai mun san komai,ƴaƴan da Allah na tuba cushensu ake yi gurin ƴaƴan ƴan siyasa.." Safwa ta taɓe baki ta tashi tana cewa "Umma ai in ma da niyyar gulma ya faɗawa Baba,to gulmarsu bai yi aiki ba" Umma tace "a'a ke dai baki gane bane,amma gidansa ne ba ya so kina shiga hiran,kuma daga yau baza ki sake zuwa ba,zakaran da Allah ya nufa da chara,ai ko ana muzuru ana shaho sai ya yi,mijin da basu yi tsammanin za ki samu ba za ki samo shi in sha Allahu,ko ƴaƴansu kuwa albarka duk taƙamar da ake da kyawunsu" Safwa ta washe baki tace "Allah yasa Ummana" Umma tace "ameen.. Yawwa! Na yi waya da Malamar nan,in sha Allahu za muje gurinta akan matsalarki" Safwa tace "to Umma,yaushe za muje?" Umma tace "sai wani weekend ɗin in sha Allahu,kafin nan ta gama haɗa mana abunda ya kamata" Safwa tace "ok!"
*MUNIBA*
Cikin ɗan lokaci suka fara fahimtar juna tsakaninta da Lieut Abuu Turab,yayin da wani irin tsaftatacciyar soyayya da shaƙuwa ya sake samun gurin zama,dama can ba ta kula kowa,bata bawa wani ɗa namiji damar da zai zo gurinta ba,bare yanzu da ta san akwai maganarsa a ƙasa kuma har iyaye sun san da shi,ita mutum ce me ra'ayin kanta,rashin son hayaniyarta ba iya kan al'amuranta na yau da gobe kawai ya tsaya ba,hatta akan alaƙarta da mutane ta kan zauna ta ƙididdige yawa da kuma halayya,idan ta tantance then sai ta saki jiki da kai,haka nan a ɓangaren alaƙarta da Lieut Abuu Turab ma bata yi ƙasa a gwuiwa ba,sanda ta gama fuskantarsa ta karancesa tas kafin ta sakankance ta bashi ragamar kanta da zuciyarta,a rana yanzu ta kai ko da bai kirata ba ita da kanta za ta ɗaga wayarta ta kirasa,cikin dangi babu wanda bai san maganar tsakaninsu ba,Mom ɗinsa da siblings ɗinsa kuwa kaga yanda suke nunawa Muniba so baza ka taɓa cewa basu san juna ba tun da can,duk ranar Friday sai sun gaisa da Mom,idan taga tana jin kunyarta taita cewa "ki saki jiki da ni Daughter,ni matsayin ƴa na ɗaukeki ba suruka ba,yanda su Abrar suke haka kike a gurina,ki ɗaukeni matsayin Mom ɗinki kamar yanda nake kallonki as a daughter" a kunyace Muniba take amsawa tace "toh Mom" su Husniyah ma duk Friday sai sun mata Friday wishes da prayers,ta ko wane ɓangare ba ta da matsala da family'nsa,tun kafin alaƙarsu yayi nisa ta shiga cikinsu,sun gama mayar da ita matsayin ta su,idan kuwa suna waya da gogan kamar za su cinye juna ta wayar saboda so,duk wanda ya san Muniba da,a yanzu yaga yanda take kashe murya ba ta nan ba ta can duk sanda suke waya da shi,zai ce ba ita bace,duka² bai fi 2 months da ƙulluwar alaƙarsu ba,amma za ka iya rantsewa kace sun fi 3yrs,idan yaji za taje gidan Khalidah da suka dawo daga yawon shaƙatawar da suka tafi,duk abunda yake zai yi ƙoƙarin bari yazo ya sameta,sai ko idan ba ya garin shi ne kawai dalilin da zai sa kaga bai zo ba,sai dai zai kirata vid call,haka kiran waya ma duk bayan mintuna yake aiko mata shi,sam basa gajiya da kasancewa tare da juna,basa gundirar juna,ko sau nawa zai kirata za ta ɗauka cikin farin ciki,Baniynah da Khalidah a yanzu kam sun zama ƴan kallo,don yanda soyayyarsu yake tafiya cikin tsari da salo me narka jini da ɓargo,wani lokaci idan Baniynah ta gaji sai kaji tana yada musu habaici cikin wasa da raha tana cewa "mu dai wannan love epic ɗin mun gaji da shi,don Allah kuyi² ayi auren nan mu huta,duk walls ɗin gidan nan love words ɗinku ke displaying,saboda haskensu da dare ba sai mun kunna bulbs ba muke gani muna kuma sauraren yanda ake poem ɗinsu" Lieut sai dai yayi murmushi yace ma Muniba ta bashi ita,da zaran ta karɓi waya zai ce "Ƙanwata! Kada ki damu lokaci muje jira,akwai promotional exam da zanyi in sha Allah,shi ya dakatar da ni yanzu,da zaran na gama da wannan matsalar za kiji headline me ƙarfi" Baniynah tayi dariya tace "toh shi kenan Yayana,Allah ya kaimu lokacin yasa a dace.." Tashinta a bacci kenan tana sanye da nightwear ɗinta riga da wando masu ɗan kauri saboda yanayin weather dake bada iska cikin dare,wayarta dake ajiye kusa da shades was the first data ɗauka ta duba time,sai tunanin ko ya kirata tana bacci,ganin babu komai da ya danganci missed call ko text ɗinsa yasa ta mayar ta ajiye,sauka daga gadon tayi ta nufi bathroom,tana shiga ta ciro brush ɗinta ta tura cikin toothpaste dispenser ya matsa mata mouth wash,brush tayi tana yi tana kallon kanta a mirror,tana gamawa ta cire kayanta ta wuce tare da ɗaukan shower cap ta rufe gashinta sannan ta kunna shower,ruwa na fara sauka jikinta ta sauke ajiyar zuciya,tana gama wanka taja bathrobe light pink tasa tare da wucewa ta fita,dai² tana tsayawa gaban mirror ɗinsu wayarta ya fara beeping,ƙayataccen murmushi ta saki kafin tai sauri taje ta ɗauki wayar,ba ta buƙatar tsaiwa ta duba waye,daga ringtone data sa mata ta san shi ne,tana kai wayar kunnenta tayi sallama shima yayi mata,sai kuma suka amsawa juna followed by gaisuwa,cikin taushin murya Lieut yace "what are u doing now? Ina son kiranki vid naga how Mata ta take,is she doing well?" Murmushi ne ya bayyana a fuskarta,a hankali tana lumshe idanunta tace "i'm fine alhmdllh" yace "are u sure?" Tana gyaɗa kai kamar tana gabansa tace "absolutely love" yace "ok! But ina son ganinki" tana sakin murmushi tace "Mmm! Zan gama shiri,yanzun nan na tashi.. I will call u idan na gama" yace "ok! Take care of urself for me" tace "and u too" yayi murmushi yace "ok! I will" tayi murmushi itama tace "me too.." Suna yin sallama ta ajiye wayar tana sakin kyakkyawan murmushi,a gurguje ta ɗauki lotion ɗinta ta shafa,tana gamawa ta ɗan yi applying farar powder da kwalli sai lip balm data shafawa lips ɗinta nan suka fara ƙyalli suna ɗaukan ido,wani green ɗin atamfa ta ɗauko a press doguwar rigar A-shape da veil,tana gama shiryawa ta ɗaura ɗankwalinta ya zauna das,tana shirin fita bedroom ya sake kiranta,kamar zai mata kuka a shagwaɓe yace "me matar Abuu Turab take yi har yanzu? I'm eager na ganki,i have something to tell u,but na fi so ki fara gani" ta ɗan buɗa ido surprisingly tace "can't u just tell me?" Yace "no! Idan kin gama let me call u yanzun nan" ta ɗan gyaɗa kai tace "na gama" yace "ok!" Yana katsewa ta buɗe network ɗinta,babu jimawa kiransa ya shigo,a hankali ta kai hannu bottum ɗin answering ta ɗauka,call ɗin na connecting Lieut Abuu Turab ya bayyana sanye da khakinsa na sojoji kansa babu hula,ya bala'in yin kyau kwarjininsa da cikar kamalarsa sun bayyana,murmushi was the first abunda yayi mata da ya bayyana dimples ɗinsa,yana kashe ido yace "hey!" Muniba da kunyar yanda yake kallonta ya saukar mata yasa ta ɗan sauke idanunta ƙasa tace "hello! How are u doing?" Yace "alhmdllh! And u?" Tace "same.. Ya su Mom?" Yana sakin numfashi yace "huh! Mom ai kin fini kusa da su.. And u look damn good,kin yiwa idanuna kyau sosai" ta ɗan gyaɗa kai tana dariya kafin ta daure tace "u too. Ehem! What surprise kake cewa za ka sanar min?" Yayi murmushi tare da cewa "albishir na kira na fara yiwa Mata ta" tayi murmushi me ƙayatarwa tace "ok! Akan mene ne?" Ya ɗan karkata wayar zuwa saman shoulder ɗinsa dake ɗauke da 2 silver stars and a silver eagle on each shoulder kafin yace "i got a new rank,mijinki yanzu ya hau matakin Colonel" Muniba ta ɗan rufe bakinta fuskarta na bayyanar da farin ciki tace "maa sha Allah! Wow!! Allah ya tabbatar da alkhairi yasa afi haka love,ina taya murna da addu'ah,Allah ya yayi jagora" daga yanayinsa za ka fahimci ya ji daɗin addu'arta,yace "ameen² Sweet" har sun yi shiru kuma Muniba tace "can i ask?" Yace "why not? Yi tambayarki Baby" tana sakin murmushi tace "mene ne bambancin rank ɗinka na da dana yanzu? I know ka samu promosion ne,but ba na gane differences na ranks ɗinku" yayi murmushi kafin yace "wannan ai ba wani abu bane" here ya shiga yi mata bayani yace "da ina matsayin Lieutenant Colonel ne,ma'ana deputy Colonel shi kuma single silver star ne and eagle,yanzu kuma na dawo Colonel stars ɗin sun zama 2 each shoulder" ta ɗan gyaɗa kai tace "ok! But mutum nawa suke sama da kai kenan and how many suke under ur rank?" Yace "mutun 4 suke sama,and ƙasa kuma suna nan da yawa" tace "wa da waye mutum 4 ɗin?" Yace "Brigadier general,Major General,Lieutenant General sai General" tana ɗan gyaɗa kanta tace "idan na fahimta da kyau daga rank ɗinmu na yanzu,next za mu hau Brigadier general?" Ya gyaɗa mata kai yace "sure love" tace "ok! Allah ya tabbatar da alkhairi.." Ya amsa da ameen,sun yi hira sosai kafin cikin muryarshi da idan yayi mata magana ta tabbatar maganar da zai yi ba na wasa bane,yace "Baby me kike yi yanzu?" Tana girgiza kai tace "babu komai" yace "ok! I want to talk to u ne,i don't know ko kina free yanzu" tace "yeah! I'm free" yace "za mu iya yin magana?" Tace "why not?" Yace "ok!" Yana mata murmushi yace "ina son tambayarki ne wani abu" tace "Allah yasa na sani" yace "i want to talk to Daddy akan maganar aurenmu this soon.. So ina so naji daga gareki idan kin shiryawa aurena kamar yanda ni na shirya,ba na son shigowa Kano har sai na tabbatar na ci ƙarfin yaƙin nan,should i call him na sanar masa yanzu kin amince?"
#Alhamdulillah alaa kulli halin! Guy's i'm so so so sorry da tsaikon da muke ta samu,last week mun yi biki ne and mun sake samun rasuwa a dai week ɗin,so ayi min afuwa da jinkirin da aka gani.. And na san some za suji surprise sanda suka ga update ɗina and say,ohh! Yau an tuna da mu kenan,after all this while kuma sai a bamu single chapter? (Smile),to kuyi haƙuri dai ba yin kaina bane nima,and ba da son raina muka kawo yanzu babu update ba,yanayin al'amuran da suketa faruwa ne,and this single chapter da wasu za su raina,tana ɗauke ne da 12 read mores..
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
*Infection*
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*****
*****
#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.