WAZEER!

Strangerlike

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®AS-2023.






*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*





           *♡WAZEER¸.•💥*

          (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)





Bʏ.

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

https://www.arewabooks.com/u/realsmasher

 ••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

 


    



                23

 


#Strangerlike



      Tas Wazeer ya ɗauke wuta a gurin,banda zafi babu abunda yake ji a jikinsa,gumi ya wani irin fara yanko masa,yana jin babu daɗi kuma yana son yayi magana but he couldn't,even ya buɗe baki ya kasa,Safwa tana dariya tace "kuma ka san har an tsayar da ranar auren in the next 2 months?" Wazeer ya runtse idanunsa sosai,lokaci ɗaya fuskarsa ya sauya,kamanninsa suka jirkice,face ɗin yayi wani irin ja,a rayuwarsa bayan mutuwar Mysha da rabuwar iyayensa da zai iya cewa bai ma gane me yaji ba a lokacin,tabbas bai taɓa shiga yanayi na tsoron rasa wani abu ba kwatankwacin wannan ba,sun ɗauki tsawon lokaci a yanayin shiru har sannan ya kasa magana,Safwa ta katse shirun ta hanyar aiko masa tambayar "when are u coming? Sai muje musu Allah ya sanya alkhairi?" Cike da ƙarfin hali da dauriya ya buɗe idanunsa da sukai jajir,ji yayi gaba ɗaya tunaninsa ya kulle ya kasa cewa komai,yana sauke numfashi me zafi kawai ya katse wayar ya ajiye tare da yin shiru,a hankali wani irin sanyi ya fara shigarsa,bai taɓa kallon ƴa mace da wani nufi ba,bai taɓa tsaiwa da wata ba tun tashinsa,ko a can California bai kula matan turawan nan,bama suga fuska ba bare suyi masa magana,maza ma ba shiga harkarsu ya cika ba bare wasu mata duk saboda khuɗubar Dad,mutumin da ba kowa ya sansa bama saboda yanda yake ɓoye kansa,kullum fuska rufe yake fita,da yawa basu san kamanninsa ba bare sunansa sai dai Mr mask,ko kwatancensa za ayi kana cewa Mr mask za'a san wa kake nufi,kaɗan ne suka san sunan Wazeer,suma dalilin Dad ne saboda nacinsu da son lallai sai sun yi mu'amala da shi,sababin ziyartarsa da suke gida yasa suka jiyo sunan,amma idan za ka shekara kana faɗan Aliyu,babu me ce maka ga shi,ita ya fara gani kuma zuciyarsa ta nutsu,har yaji yana son ya samu kusanci da ita,tun a kallon farko yaji zuciyarsa na masa waƙe akanta,yanayin fitar numfashinsa ya sauya,but kwatsam sai akai masa shigar sauri,shi bai ma san me zai yi ko yace ba akan maganar nan,ya tabbatar abunda yaji ɗin nan babu ƙarya ciki,amma ta yaya zai tabbatar da maganar Safwa? Duk da ya tashi wani ƙasar kuma cikin mutanen da ke da ƙarancin ilimin addini,ba zai ce bai yi karatu ba kwata² domin kuwa mahaifinsa shi ne malaminsa,duk wanda yasan gidan Waziri ya san gidan karatu ne,yana ji Safwa na sake kiransa ko kallon wayar bai ba bare ya iya amsa kiran nata,daren nan sosai yazo masa a hagunce,bai taɓa kawowa wani abu kwatankwacin wannan zai faru da shi ba,bacci kuwa sai dai in yana cikin nutsuwarsa,ko da ake cewa ɓarawo bai iya ya sace shi ba,haka ya kwana juye² da tunani,guraren asubah ana kiran farko tunani ya sakeshi,cikin yanayin mutuwar jiki ya tashi ya sauka gadon ya wuce bathroom,alwala kawai ya iya ɗaurowa saboda sanyi²n da yake ji da yayi masa kama da na wanda zazzaɓi ke son kamashi,ko masjid bai iya fita ba yayi sallah tare da yin addu'o'insa kafin ya ɗan samu nutsuwar zuciya,ya jima a zaune doing nothing banda tunani kafin yaja jikinsa da yai masa nauyi ya koma saman gadonsa ya kwanta,a hankali yana sauke numfashi ya lumshe idanunsa da suke azabar zafi,al'amari da yawa suka taru suka haɗe masa,nan da nan kansa yayi azabar ɗaukar charge,ganin damuwa na neman sawa ya fita hayyacinsa ya juya idanunsa da ƙyar,then a hankali ya tashi yasa palm a ƙafarsa ya fita bedroom ɗin,wani room da Dad ya mayar tamkar clinic ɗinsu ya shiga,bincike² yayi tayi yana hargitsa manyan kwalayen maganin da suke ciki,bai fita ba sai da ya gano abunda yake nema,ya fito ya wuce parlour ya ɗauko ruwa sannan ya koma bedroom ɗinsa,sai da ya rage gudun AC dake aiki ɗakin sannan ya ƙarasa gaban gadonsa ya zauna a daddafe,maganin da ya ɗauko ya ɓallo ya watsa bakinsa ya korasa da ruwa,jijiyoyin kansa da suka firfito sun yi wani raɗa² a saman forehead ɗinsa,kana kallonsa za ka san he's not fine,a hankali ya wuce ya kwanta tare da lumshe idanunsa while hannunsa ɗaya yana kan goshinsa yana murzawa,ya jima a haka kafin wani irin wahalallen bacci yazo ya ɗauke shi a gurin.



*SAFWA*



    Yana katse kiran wayar ta fashe da mahaukaciyar dariya har da ƙyaƙyatawa,sanda tayi iya tsayin cikinta kafin ta saurara,ba kaɗan ba yanda yayi shiru ya mata daɗi,don ta fuskanci komai da ya faru,dama da biyu ta kira shi ta sanar masa zancen,dalilinta na farko duk wata hanya da za tabi ta nuna masa tana sonsa ta yi,amma ya kasa kallonta ya amshi tayinta,kuma ba wai don bai gane bane,kawai ta fahimci ra'ayinsa ya tafi can wani waje na daban,abu na biyu kuma don ta cusa masa haushi,tasa yaji kwatankwacin abunda ita taji da ya kasa kallonta har yau,tsakaninsu kawai sai dai wani abu daban,ko da kuwa zuwa yayi gidansu,in ta tambayeshi abubuwa game da rayuwarsa ma dai ba ya taɓa sanar mata,har ta gaji ta bar tambayarsa,sai dai kullum ta yiwa Radhiya ƙawarta complain. Kamar ko wane lokaci yanzuma kiran Radhiya tayi a waya,tana ɗauka Safwa tace "ƙawata hau online za muyi magana" Radhiya na dariya tace "ok!" Tana katse kiran ta shiga WhatsApp,number Radhiya ta shiga tace "hey! U know what?" Radhiya da tayi online lokacin tace "hello! Nope.. What's happening?" Safwa da taji baza ta iya yiwa Radhiya bayani a haka ba kawai ta kirata video call,Radhiya na ɗauka Safwa tace "wai kinji labarin an kawo kuɗin auren su Muniba kuwa?" Radhiya ta waro ido tace "ke don Allah? Yaushe?" Safwa tace "yanzun nan Umma take sanar min wai Maman su Baniynah ta shigo ta faɗa mata not too long,har an sa rana in the next couple months" Radhiya tace "maa sha Allah! Baniynah fa ko ba yanzu ba?" Safwa tace "dukansu ne" Radhiya tace "kai na musu murna wallahi,Allah ya kawo na ƴan baya,ya kawo namu lokacin" Safwan ta taɓe baki tace "ameen.. Amma kin san basu iya su faɗa min ba kuwa har yanzun?" Radhiya ta girgiza kai tace "a'a ƙawata kada kiyi gaggawa za su sanar miki,ni na san ko kowa bai faɗa miki ba Muniba will call ta sanar miki,bare Baniynah ma baza ta ƙi faɗa miki ba" Safwa ta taɓe baki tace "ok! Let's see.." Sai kuma ta buɗe ido tace "yawwa kin san wani abu kuwa?" Radhiya tace "nope!" Safwa tace "ni da Aley ne fa yauma,dalilin da yasa na kiraki kenan" Radhiya na dariya tace "ok! What happened again?" Safwa ta ɓata fuska tace "ni ban san ya zan masa ba,duk ta inda na biyo masa ya kasa fahimta ta,ban san ya yake so nayi ba" Radhiya na girgiza kai tace "um'um² Ƙawata" Safwa tace "please Radhiya don't backed him up,wallahi ya san me nake nufi,idan baze fito fili ya faɗa min ba,i think zan sauke ego na nace ina sonsa,ai da kunya ya kalleni yace bai sona ko?" Radhiya na sauke numfashi tace "ni dai kiyi haƙuri kawai zan iya cewa,amma wata rana zai sanar miki da kansa,ba dai kina sonsa ba and he knows that?" Safwa tace "i dearly love him Radhiya,wallahi ban taɓa son wani kamar yanda nake sonsa ba,he's the full definition of beauty,ko ke wallahi nasan kinji inama ace saurayinki ne,ni kaina ya fini kyau wallahi,and banga da wanda zan iya miki kwatancensa ba a mutanen da na sani" Radhiya tayi dariya tace "um'um! Ke ɗin dai.. But don't mind ƙawata in sha Allah,Aley belongs to no one illa ke kaɗai" Safwa tace "Allah yasa" Radhiya tace "ameen.. Bari na kammala aikin da nake,za muyi magana anjima,sai musa lokacin da za muje yiwa su Muniban Allah ya sanya alkhairi ko?" Safwa tace "a'a ki jira dai har su fara sanar mana,ni babu inda zanje yanzu wallahi har sai idan sun sanar min da kansu" Radhiya na dariya ta gyaɗa kai tace "ok²! In sha Allah za su sanar miki" Safwa tace "later.. A gaida Ammi" Radhiya tace "za ta ji,a gaida Umma da Bilal" Safwa tace "ok! Bye.." 



*MUNIBA*



    Kwance take a parlour bayan saƙon Lieut ya iso mata,wani irin farin ciki yau take ji,ba don komai ba sai maganar aurensu da ya hau saiti,har kuma iyaye suka shiga aka tsayar da lokacin da take ganin kamar yau ne,Safwa was the first person da tazo ranta a kaf wanda suke tare,sanin bambancin halayensu yasa ta waro ido,da sauri ta kai hannu ta ɗauki wayarta ta kira line Safwa,sanda wayar ya kusan yankewa kafin Safwa ta ɗauka da faɗin "hello! Babe" Muniba tayi murmushi tace "hey! Ya gida da su Umma dearest?" Safwa tace "suna nan lafiya,ya Mami?" Muniba tace "Mami na nan lafiya alhmdllh" sukai ɗan shiru kafin Muniba tace "albishirinki" Safwa tace "goro fari tass" tana dariya,Muniba tace "yau fa an kawo kuɗin aurenku da sa rana" Safwa da tayi kamar bata san zancen ba tayi wani ihu tace "awwnnn! Ina ta son zuwa ma mun kwana biyu bamu haɗu ba,ashe da na zo na tarar da labari me daɗi.." Muniba tace "wallahi fa mu kuma bamu shigo ba,school ya ɗauki zafi mun zo final year" Safwa tace "ai fa babu sauƙi,Allah ya bamu sa'a.. How many months akasa,ya kamata mu fara shiri?" Muniba tace "2 months" Safwa tace "in sha Allah zan shigo yima Mami Allah ya sanya alkhairi,sai muyi magana kuma na yanda abubuwa za su tafi" Muniba tace "Allah ya kawo ki lafiya,ki sanar please a group na islamiyya" Safwa tace "alright! Maybe mu shigo tare da Radhiya,ko zuwa gobe ne idan na samu lokaci" Muniba tace "it's ok dearest,Allah ya kawo ku lafiya,na gode sosai,a gaida kowa" Safwa tace "za su ji.." Suna yin sallama Muniba ta sauke ajiyar zuciya,yanzu kam she's safe ba ta jin damuwar rashin sanar da kowa. Mami ce ta sauko tana waya da Sister ɗinta Wahidah,fuskarta da murmushi akai tace "to shi kenan sai kin shigo,a gaida me gidan da yarana" tana ɗan gyaɗa kai tace "ga ta a kusa.. Ok" ta kalli Muniba tace "Sweetheart ga Aunty'nki" da sauri Muniba ta tashi ta amshi wayar ta kai kunnenta tana faɗin "assalam alaikum.. Aunty ina yini?" Aunty Wahidah ta amsa tana faɗin "Amarya!" Muniba na dariya cike da jin nauyin sunan tace "kai Aunty kema haka za ki kirani?" Aunty Wahidah tace "ai yanzu ba ni kaɗai ba,kowa ma haka zai kiraki,sai kin tsufa a gidanki ko kin haihu kafin a bar kiranki da sunan" Muniba tace "a'a ni dai na yafe Aunty ki faɗawa Baniynah" Aunty Wahidah tace "laaa! Tana ina ne ma mutuniyar tawa?" Muniba tace "suna can garden" Aunty Wahidah tace "auuu! Khalifa na gidan ne?" Muniba tace "ehh! Bai jima da dawowa ba" Aunty Wahidah tace "ok! Bari zan kirasa,shi dan gidansu ansa ranar aurenma bazai bar yarinya tayi shirye² ba" Muniba ta fara dariya,sun yi magana cikin kulawa da soyayya kafin suyi sallama,ta miƙawa Mami wayar tana dariya tace "Mami ga wayar" Mami ta ɗago ta kalleta tana sakin murmushi tace "wani abu kuka yi ke da Aunty'n naki?" Muniba na dariya tace "ta ce za ta zo" Mami tace "Mmm! Haka tace min" Mami na kallonta tace "zo nan Sweetheart muyi magana kafin ƴar uwarki ta shigo" Muniba ta zauna kusa da Mami,tace "toh Mami" Mami na kallonta tace "kun yi maganar inda za ki zauna da Abuu Turab ne?" Muniba ta girgiza kanta tace "a'a! But ai ba zai wuce nan Kano ba" Mami ta girgiza mata kai tace "kenan gurin aikin nasa zai na tafiya ke ya barki a nan?" Muniba tace "ina jin" Mami tace "shi ya faɗa miki haka?" Muniba tace "Mami to ai kowa fa yana nan,ni na fi son na zauna a Kano gaskiya,ya dunga zuwa weekends" Mami na girgiza kai tace "um'um! Ki fara tuntuɓarsa dai kuyi magana,tunda kuna final year yanzu,ko da za ki zauna sai in kuna school ne,amma idan kun samu holidays kibi mijinki" Muniba tace "Mami ni dai gaskiya na fi son na zauna kusa da ku" Mami tace "zaman me kenan za kiyi? Idan kina so ki zauna kusa da gida shi mijinki kuma sai ki barsa ya zauna can shi kaɗai? Mene ne amfanin auren da zai yi idan baza ki kasance tare da shi ba a kowane hali da lokaci?" Wani irin magana Mami ta dunga mata me kama da jirwaye,sanda ta cire mata tunanin zaman a nan kafin tayi murmushi tace "i'm happy zan aurar da yarana 3 lokaci ɗaya,saura Mubasshir in sha Allah.. Banda ya tsaya wasa ai da dukanku za mu haɗa mu aurar da ku,ku tafi can gidajenku sai dai ku dunga zuwa kuna gaishemu ni da Mama" Muniba ta zame ta kwanta saman cinyar Mami tana dariya,a hankali tace "Mami kun gaji da ganinmu ne a gida?" Mami tace "a'a Sweetheart,kawai dai fatan ko wane iyaye ne idan yaransu suka kai munzalin aure suga sun aurar da su,muma bamu da buri bayan haka.. And alhamdulillah Allah ya amsa mana addu'o'inmu,muna ta fatan mu haɗa ku biyu ke da Baniynah,Allah kuma sai yai mana tagomashi har da Yayanku" Muniba tayi murmushi a hankali ta lumshe idanunta,suna cikin hira da Mami kiran Abrar ya shigo wayarta,Muniba ta ɗauka da sauri tana ƴar dariya tace "hello dearest" Abrar tace "Aunty are u home?" Muniba tace "yeah! Ina nan" Abrar tace "ok!" Muniba tace "ya akayi dear?" Abrar tayi dariya kawai tace "wait a minute please,i will call again" kafin Muniba ta sake magana ta katse wayar,Muniba ta bi wayar da ido sai kuma ta ajiye tana cewa "ko me Abrar za tace min?" Mami dai na jinta amma bata ce mata komai ba,ba'a jima sosai ba har ma ta manta da kiran da Abrar tayi mata,sai ga knocking anyi,Muniba ta tashi ta tafi dubawa,tana buɗe entrance sukai ido biyu da Abrar tare da Husniyah,Muniba ta buɗe ido da mamaki,Abrar na dariya suka haɗa baki ita da Husniyah gurin cewa "hello Aunty" Muniba na kallon Abrar tace "u never told me kuna hanyar zuwa" Abrar tace "it's surprise" Muniba ta gyaɗa kai tana murnusawa tace "ok! Welcome.. Ku shigo" suka shiga ciki da sallama,Mami ta ɗago tana amsawa,ganin ƴan matan yasa ta saki murmushi tana faɗin "welcome dearest" suka amsa fuskokinsu a sake suka tsuguna tare da gaisar da Mami,ta amsa musu da kulawa tana tambayar Mom da Hammad don bata mancesa ba saboda suna zuwa wani lokaci har su shigo gaisheta,Lieut ne dai bata taɓa gani ba har yau,Mami ta tashi tare da ɗaukan wayarta ta wuce sama ba tare da ta ce musu komai ba,hira sukai ta yi har gurin maghreeba lokacin Baniynah ta shigo ta samesu,suka gaisa da su tana tambayar In-law ɗinta da Hammad,then suka tashi sukai sallah. After they had dinner together sun yi sallar ishaa,Abrar suna shirin tafiya kiran Lieut ya shigo wayar Muniba,ta ɗauka suka gaisa kafin tace wani abu yace "tell Abrar su jira idan na zo sai mu tafi tare" tana gyaɗa kanta tace "ok love" yace "till we meet" tace "Allah ya kawo ka lafiya" ya amsa da ameen,tana sauke wayar tace "dear ya ce ku jira gashi nan zuwa" cikin tsokana Baniynah tace "waye?" Muniba tace "ban sani ba" Abrar tace "Yayanmu?" Muniba ta gyaɗa kai,Husniyah tace "Allah kuwan ba yanzu za mu tafi ba tunda yace zai zo" Baniynah dake dariya tace "ko dai kina da AP ne?" Husniyah tace "a'a wallahi kawai na san sai zai tafi sannan za mu wuce,kafin nan na yi bacci ai" Muniba dake kallonta tace "ok! Sai kice min kin gaji da ganina" Husniyah ta waro idanunta waje tace "a'a Aunty ni ban isa na faɗi haka ba" Muniba tace "to yaya ne?" Husniyah ta girgiza kai tace "ok! I will wait until yace muzo mu tafi" Muniba tayi murmushi ta ɗauke kai tana kallon wayarta dake beeping,answering call ɗin tayi tace "hello love" yace "i'm outside" a hankali ta gyaɗa kanta tace "ok! I'm coming" yace "ok!" Tashi tayi tana cewa "dearest zan sanar da Mami na dawo" Baniynah tace "gaskiya Sweetheart kiyi mana kwalliya" Muniba ta juyo ta maka mata wani kallo tace "abunda yafi haka dai" Baniynah tace "ke don Allah baki ji kunya ba yanzu ki fita a haka?" Muniba tace "ban sani ba.. Banza kawai" Baniynah tace "banzaye dai" Muniba bata sake kulata ba tai wucewarta upstairs ta bar su Abrar suna musu dariya,bedroom ɗinsu ta fara shiga ta ɗan gyara face ɗinta sannan tasa perfume a jikinta masu sanyi,tana gamawa ta ɗauki veil da plat shoe ta fito,can ɓangaren Abba ta wuce don ta san Mami na can tunda ta hawo bata ganta a parlon sama ba,sanda tayi knocking kafin ta buɗe ta shiga,Mami na kallonta tace "za su wuce ne?" Muniba ta girgiza kai tace "a'a ya ce za su tafi tare" Mami tace "ok! Shi ne yazo?" Muniba ta gyaɗa kai tace "ehh" Mami tace "alright!" Muniba tace "Mami na fita wajensa" Mami tace "a gaishesa" Muniba ta fice tana dariya ba tare da ta ce komai ba. Tana saukowa downstairs Baniynah ta bita da kallo,ganin ba yanda ta tafi ta dawo ba yasa tayi dariya tace "ko ke fa" Muniba ta wurga mata wata uwar harara tace "ki fita idona na rufe" Baniynah tace "dilla can jeki mu kada kija mana aji,haka kika ga ina yi wai?" Muniba ta ɗauki throw pillow ta jefa mata,Abrar da Husniyah sai dariya suke musu,kafin Husniyah tace "wait guys.. Aunty wai don Allah waye babba cikinku?" Da sauri Baniynah tace "ni ce babba" Muniba tace "sannu gyambo iyayen son girma" Husniyah tace "Aunty wai haka?" Muniba tace "itace ƙarama sai son girma kamar me" Husniyah tace "amma dai ba shekaru ne tsakaninku ba ko?" Muniba ta gyaɗa mata kai tace "2 months and half" Baniynah tace "don Allah Sweetheart wuce ki tafi kin barmu muna jiranki" Muniba tace "ɗauke ni ki kaini mana kawai idan kin gaji da ganina" Baniynah tace "a'a sai dai na rakaki" Muniba ta kwaikwayi yanda Baniynah tayi magana kafin ta wuce tana cewa "dearest ina zuwa please.." Tana fitowa balcony taga motarshi a ƙasa dake kunne an buɗe ƙofar gefen me zaman banza,sanin ɗabi'arsa ne yin haka yasa bata tsaya ba ta sauka,yanda take tafiya kamar tana counting steps hasken dake gurin kamar da rana,saukowa Lieut dake cikin mota yayi yana kallonta,yanda yayi kyau cikin yadin ambassador me launin sararin samaniya kamar ba shi ba,ya riƙe ƙofar motar tare da sauke idanunsa a kanta fuskarsa cike da murmushin daya sake bayyana asalin kyaunsa da kwarjininsa,Muniba na isowa ƙamshinsa ya wani cika mata hanci,a hankali ta lumshe idanunta tare da yi masa sallama,Lieut da duka hankalinsa ke kanta ya amsa yana faɗin "barka da fitowa matar Abuu Turab" murmushi ta saki cike da kunya tace "barka da zuwa mijin matarsa" ya saki kyakkyawan murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa,yace "na gode love,ya gida da Mami?" Muniba tace "lafiya lau alhmdllh,ina yini?" Yace "lafiya lau dear" tace "ya Mom da kowa?" Yace "Mom na nan lafiya,she said ma a gaisheki" Muniba dake murmushi tace "ina amsawa.. Ya hanya da aiki?" Yace "alhmdllh" ta ɗan gyaɗa kanta tana juyawa ta kalli garden da parlon baƙin Abba,Lieut dake ta kallonta yace "what are u looking?" Ta juyo da ɗan sauri kafin tace "Mmm! Ina tunanin inda za mu zauna ne,palour or garden? I don't know ina ne zai fi maka?" Yace "don't mind ba jimawa za muyi ba,mun zo gaisar da Mami ne" Muniba ta buɗe ido surprisingly,yayi murmushi tare da juyawa ya ɗan sunkuya ya kalli cikin motar yace "Mohan get down ku gaisa" Muniba tace "ahh! Dama tare kuke?" Mohan da ya fito motar yana murmusawa yace "do u think he had wani aboki bayan ni?" Muniba ta girgiza kai tana dariya tace "Allah ban yi zaton tare kuke ba,ni na ma yi tunanin Yaa Hammad ne,ina shirin na tambayesa ne ma fa.. Ina yini Yaa Mohan?" Mohan yace "ehh to ai yanzu lokacin nawa ne,tunda anzo inda ya kamata.. Lafiya lau ƙanwata,ya gida da su Mami?" Tace "lafiya lau alhmdllh,ya Aunty'na?" Yace "tana lafiya,sai muka ji abun alkhairi kuma" tayi murmushi kawai,yace "Allah ya tabbatar da alkhairi ƙanwata" Lieut dake jinsu yace "ameen.. But da kake cewa mene ne? Da ba'a inda ya kamata muke ba kenan?" Mohan yace "kaima ai ka san bazan rakoka zance ba,wannan sai dai Hammad ɗin ni ai na wuce wannan ajin,ka ga ya ɗauki course a gurinka.. Yanzuma ka san banda ka ce Mami za kazo gaisarwa bazan zo ba ko?" Lieut yace "ok! I understand.. Ai da ka ce baza ka zo ba tun farko ma,ka san zan iya zuwa ko na samu wani ya rako ni,ance maka sai lallai kai ne za ka min rakiya?" Mohan yace "amma dai ka san ba ka da kamar ni ɗin" Lieut ya wani yaƙune fuska yace "haka kake gani?" Mohan yace "to faɗi mana idan ba haka bane" Lieut ya ɗauke kai ya ƙi kulashi,yana kallon Muniba da tai bala'in masa kyau yace "love ya za'ayi a sanar da Mami zan shigo gaisheta?" Muniba dake murmushin drama ɗinsu tace "ok! Bari na kira ta on the phone" yana girgiza mata kai yace "um'um! Just go ki sanar mata" tace "amma.." Ya sake girgiza kansa yace "i said um'um.. Je ki sanar mata,iyaye suna da girma a gurinmu,and girmanta ya wuce a sanar mata ta waya" Muniba ta gyaɗa kanta tana masa sanyayyan murmushi,har ranta ta ji daɗin yanda ya nuna mahaifiyarta na da muhimmanci da girma,a hankali ta nemi excuse ta wuce,shi kuma ya rufe motar ta jingina bayansa suka ci gaba da magana da Mohan. Muniba na shiga ta wuce upstairs ta sanar da Mami,babu jimawa suka sauko tare da Mami,Muniba ta wuce Baniynah na tsokanarta bata saurareta ba tai ficewarta,bata jima ba suka shigo tana gaba sai Mohan,Lieut na baya sai sunkuyar da kai yake tun ma bai ga Mami ba,Abrar ta wani zaro ido tana dariya tace "Yayanmu" Lieut ya wurga mata kallo cike da kashedi,fuskar nan nasa ba kamar yanda suke sako masa wasa ba,Abrar ta kame kanta da sauri tare da riƙe lips ɗinta,ya ƙarasa tare da durƙusawa zai zauna saman rug,Mami tai saurin kallonsa tace "a'a don Allah tashi ka koma sama" Lieut yayi murmushi ya kasa tashi sai da ya gaisheta,Mami tace "bazan amsa ba gaskiya idan baka koma sama ba" ya sake yin murmushi cike da kunya ya tashi ya zauna saman lafiyayyen chair kusa da Mohan,suka gaisa da Mami a mutunce,ta amsa musu da kulawa tana tambayar Mohan Khalidah,yace "think za ta shigo gobe" Mami tace "Allah ya kaimu" suka gaisa da Baniynah,kafin lokaci ɗaya Mami ta kalleta tace "Baby come here" Baniynah ta taso da sauri ta tafi kusa da Mami ta zauna,Mami tace "a kawo musu drink da abinci" Baniynah ta tashi ta wuce kitchen,bata jima sosai ba ta dawo da tray taje ta ajiye saman center table,Mami ta tashi tana faɗin "eat please,bari na baku guri ku gama" ta wuce sama abunta,tana barin gurin Lieut ya ɗago kansa,haɗa ido suka yi da Muniba dake masa dariya,yayi murmushi tare da kallon staircase,ganin Mami ba ta nan ya juyo da sauri yace "u ask for it.. And zan rama,sai ranan da kika je gaisar da Mom" su Abrar duka suka fara musu dariya,Mohan ya saki jiki kamar a gida ya ci chops da aka kawo,sun yi hira sosai a nan kafin suyi shirin tafiya,har sannan ruwa kawai Lieut ya iya sha,Muniba dai jinsu take dan kusan hiran tsakanin Mohan ne da su Baniynah,Lieut da ya gaji da zaman yace "dude! Ya kamata mu wuce kafin Abba ya dawo ya samemu" Mohan yace "Muniba sanar da Mami za mu tafi" Muniba ta amsa tare da tashi ta tafi sama,tare da Mami suka sake saukowa,hannun Muniba da wani babban leda me kyau na super market,godiya sosai Mami ta yiwa Lieut da addu'o'i,kafin suyi sallama suna wucewa za su fita yace ma Abrar "ku fito mu wuce" Abrar ta amsa tana ƴar dariya,bai tsaya ba yayi waje da sauri,su Abrar basu jima ba suka fito tare da Muniba da Baniynah da suka rakosu,a nan ma sai da suka ɗan jima suna magana kafin su wuce,Muniba suka juya ciki suna hiran zuwan Khalidah da Aunty Wahidah. Washe gari kusan tare Khalidah da Aunty Wahidah suka iso,can kuma sai ga Mama itama,ranar yini sukai a gidan ana hira da tattauna yanda biki zai kasance cike da farin ciki,Safwa da bata samu zuwa ba ta kira Muniba ta sanar mata baza ta samu zuwa yau ba,Muniba tace "babu damuwa dear,duk sanda kika samu lokaci kya shigo,idan kuma mun fito za mu zo in sha Allah" daga nan sukai sallama,sai dare sannan duk su Khalidah suka wuce,gidan ya rage Mami da ƴan matan ta. Safwa bata samu zuwa ba sai ranar Friday,kasancewar bata je school ba ranar nan suka yini ita da Radhiya sai hira suke,har Mami ta taso aiki ta samesu,bayan sun gaisa suna yi mata addu'ar Allah ya sanya alkhairi,Mami na murmushi tace "Safwa ai ku za'a yima murna,mu sai dai mu taya ku" Safwa na dariya tace "wallahi fa Mami" Mami tace "Allah ya kawo naku lokacin,ya haɗa ku da abokan zama na gari" Radhiya da Safwa suka amsa,Mami har ta ɗan yi musu nasiha akan su mayar da hankali su fahimci wanda ke sonsu da gaske,kada su tsaya wasa ko sakewa wanda suka san ɓata musu lokaci zai yi,suka amsa da "in sha Allah.." Basu tafi ba sai after maghreeb.



*SAFWA*



   Yau ma dai sauri² take ta isa school saboda semester ɗinsu da yazo ƙarshe suna kan haɗa CA,Ayuba dake ta gudu da tricycle ɗinsa saboda yayi ya kai Safwa school ya tsaya dai² titin Hauren wanki da ɗan Karota ya tsayar da su,Safwa dake danna wayarta ta ɗan juya a hankali kamar warce taji an kirata,rantsattsen motar ƙirar Toks Benz E300 da yayi parking kusa da napep ɗinsu ta ɗan bi da kallo,ganin duka glasses ɗin was tinted yasa take ta kallon motar underneath tana faɗin "see wealth a nan gurin,gaskiya masu kuɗi sun ji daɗi,Allah ya musu ni'imomi da yawa,Allah muma ka bamu namu.." Sun ɗan jima a gurin kafin a basu hannu su wuce,har suka kai BUK new side tunani take,sanda ta sauka bakin faculty ɗinsu tace ma Ayuba "sai an jima" yace "toh Hajjaju sai kin dawo,Allah ya bada sa'a" Safwa ta amsa da "ameen" Ayuba yana napep ɗinsa ya tafi,tana shirin barin gurin aka buɗe motar da yayi parking gurin,cikin kamilalliyar huskey voice ɗinsa yace "sannu ƴan mata,baki ji ba please" da sauri ta waiga don bata kula da mutum ba sam...






*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*


  _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

  _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


*Infection*

  _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_


  _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*****

*****






#Follow

#Comment 

#Vote

#Share fisabilillah!

#ASLI-SMASHER.