KULUWA

SHAFI NA TARA

by @zeeyabour20

*KULUWA*


*NA ZEE YABOUR*

*DA SADIYA NASIR DAN*


 *YAN TAGWAYE BIYAR*

  *ZANGO NA BIYU*


*TAFIYAR BIYU TAFI DAYA*


*SHAFI NA TARA*


Idonsa damtse suke, hak’oransa cije da labb’ansa na k’asa zuciyarsa cunkushe da tsananin b’acin rai suka iso gida, Kafin maigadin sojan ya rufe gate motar UMAIMA ta kunno kai ciki, wacce ganin motocin MAJOR UMAR a harabar gidan bai sa ta tsorata ba, 


Major Umar idonsa ya bud’e da yake jin sun masa wani nauyi tamkar mai jin bacci, ya zura k’afafunsa waje ya fito daga motar, Yaji shigowar motar UMAIMA sai dai ko saitin inda take bai kalla ba, baya son yayi abunda zai ji kunya ko ya jawo mata raini gaban yaran sa, yasan tabbas ya kalleta ba abunda zai hana shi reacting hakan yasa ya shige ciki, UMAIMA hankali kwance ta shiga cikin gidan itama, Kacib’us tayi da Major Umar kanta ya daki k’irjinsa ba tare da ta ankara dashi ba, tayi saurin ja baya tana kallon sa tsaye yake hannayensa zube cikin aljihunsa zata iya rantsewa tsawon shekarun da sukayi tare bata tab’a ganinsa cikin yanayi irin na yau ba, fuskarsa tamke take sosai har jiyoyin kansa na nunawa sun fito rad’au kan goshin sa idonsa sun canza launi suna nuna tsantsar b’acin rai, Gabanta ne ya shiga duka, duk yadda take k’ok’arin danne tsoron sa tayi masa tsiya taji ta kasa sai ma wani irin tsoron sa dake shigarta, “Daga ina kike?”. Yayi mata tambayar cikin amon maganar da bai tab’a yi mata ba, duk zafin MAJOR UMAR a wurin Umaima mai sanyi ne, sab’anin yau da hakan yaso bata mamaki, amma tuna cikar burinta yasa ba gargada tace “Lunch naje tare da abokan aikina”.Ransa yaji ya sake harzuk’a da amsar ta basa cikin tsawa yace “Da izinin wa?”. Baya taja sosai gudun kada ya kai hannunsa ga jikinta duk da tasan ba d’abi’arsa bace dukan mace amma yanayinsa na yau ya sakata shakku tace “Please ka barni na samu yan’cin kaina, yanzu fah duniya ta canza ace lunch ma dan zanje sai na wani tambayeka please let me be”. Tayi maganar tana k’ok’arin barin falon, MAJOR UMAR cikin zafin rai ya kai hannu zai fisgota sai kuma yayi saurin sauke hannun, wani irin so yake mata da yake kasa d’aukar mataki a kanta, hannun sa kawai ya dunk’ule zuciyarsa na wani irin zugi, daga tsaye bai san sanda ya kai zaune kan kujera, tare da yin baya ya jingina bayansa da kujera, yana damtse idonsa ya kai hannunsa ya shafi goshin sa, “Me ya canza UMAIMA? Me na mata?”. Ya tambayi kansa yana cizon labb’ansa na k’asa, Idan a da akace Umaima zata canza d’abi’unta na baya zuwa na yanzu to tabbas zai ƙaryata hakan, lallai ya yarda da cewar na miji yana samun natsuwa ne idan yayi dace da mace ta gari, a kwankain nan da Umaima ta canza sam baya jin wata natsuwa a tattare dashi, Idonsa ya bud’e ya mik’e ya shiga d’akinsa, yadda ya fita ya barsa haka ya dawo ya tarar dashi hatta agogon da ya manta dashi kan gado yana nan yadda ya barsa, sab’anin lokutan baya da sai dai ya gansa a ma’ajiyarsa, UMAIMA macece mai kula da killace masu dukkan abubuwan sa masu muhimmanci da ma marasa muhimmanci, iska ya fusgar mai zafi ya d’auki agogo ya ajiye, ya bud’e drawer da yake ajiye magungunansa saboda k’ananun rashin lafiya da yawan ciwon kai da jiki da yake saboda yanayin aikin sa, panadol ya d’auko ya b’alla, ya d’auki ruwa a k’aramin fridge dake kusurwa d’aya ta makekekn d’akin yasha, Ya cire kayansa ya saka a laundry basket dake toilet wanda har ya soma cika da kayan datti, tun aurensu da UMAIMA bai tab’a cire kaya ya dawo ya tarar dasu ba, sai a yanzu da ta sauya d’abi’a, Ya fito toilet d’in ransa babu dad’i, wurin closet d’insa ya nufa ya bud’e gefe d’aya dake shak’e da designer kayan gym kala kala, ya zaro set d’aya ya saka sun masa kyau sosai a jiki, ya fesa turaren sa mai dad’in k’amshi yana sake bin d’akin da kallo, Tsigar jikinsa yaji ta d’an tashi, Major Umar mutum ne mai son tsafta yana jin ba zai iya kwanciya a d’akin ba idan bai samu gyara ba, ya fita d’akin yana nufar k’ofar da ta sadashi zuwa sashen Umaima, A falo ya tarar da ita zaune hankali kwance ba wata damuwa tattare da ita, hannunta rik’e da remote tana k’ok’arin saita murya na tv taji shigowarsa, k’amshin turaren da takun sa ya sanar mata amma tayi tamkar bata ji ba, Kallo d’aya ya mata ya kawar da kansa gefe cikin dakakkiyar murya yace “Na umarceki kije ki gyara d’akina”. Remote d’in ta ajiye gefenta ta waigo ta kallesa tace “Gaskiya naje aiki na gaji”. “Kada ki bari naje gym na dawo ba tare da kin gyara ba”. Yayi maganar cikin amo mai sauti ya juya ya fita falon ransa b’ace, UMAIMA baki ta tab’e tace “Wallahi bazan gyara ba, ni ba jakar ka bace yanzu”. Ta sake gyara zama tana d’aura k’afa kan d’aya ta cigaba da kallon ta, ba tare da tayi ko dogon motsi na tashi ba. 


MAJOR UMAR b’angare d’aya ya ware a gidansa inda ya zuba kayan motsa jiki da jini, kullum ya kan ware lokaci da yake exercise, dan k’ara gina lafiyar jikin sa musamman shi da yake soja, shiyasa ko da yaushe jikinsa baya nuna shekarun sa haka kana ganinsa kaga karfaffan lafiyayyan namiji mai cike da kuzari, 



********************


Magriba da ta gabato yasa KULUWA fitowa ta kwashe wankin da tayi ta shiga dasu d’aki tana ninkewa, KULUWA yarinya ce mai tsafta duk da babu da suke ciki haka bai hana mata tsaftace suturarta ba, ba guga suke samu ba amma ko da yaushe tsaf ba zaka ga gansu da datti ba, tana jera kayanta cikin jakar buhu tana tunanin yadda zata b’ullowa lamarin YARIMA HALADU, 


*********


“Kwana uku suka rage mun na koma makaranta, kuma duka kwanakin ina son kowacce rana na kasance tare da KULUWA”. Yarima Haladu yai maganar yana kallon MAMMAN, Cikin bada girma yace “Zanyi iya k’ok’arina yau na kawo maka ita”. “Idan ka kuskuren yau baka kawo mun ita ba, bana jin alak’armu da kai zata cigaba”. YARIMA HALADU yai maganar babu alamun wasa kan fuskar sa, A razane Mamman ya kallesa har wata zufa na ratso sa, da Yarima ya dogara duk wasu kud’ad’e da yake samu ta hannun Yarima ne, bazai tab’a son abunda zai sa Yarima ya barsa ba, Yawu ya had’iya yace “Zan kawo maka ita yau YARIMA bazan kuskure ba”. YARIMA bai sake cewa komai ba ya juya ya shige cikin gida zai shiga gun mahaifiyarsa, Mamman bayansa yabi da kallo tare da jinjina yace “Lallai Yarima ba k’aramin jaraba yasa akan KULUWA ba dole kowacce hanya ce nabi dan ganin na kawo masa ita”.


***********


Rabi ta gama tsara dukkan shirinta akan KULUWA, Da Mamman yazo mata da zancen yadda sukayi da Yarima hankalinsa tashe, Dariya tayi tana kallonsa, Wani kallo ya mata yace “ Ina fad’a miki matsalar da zan shiga idan ban kai masa ita yau ba, kina dariya”. Murmushi tayi tace “Saboda nasan yau d’in dole ta shiga hannunsa”. “Me kika shirya?”. Ya tambayeta cikin zak’uwa, “Idan munje zaka gani”. “Kinga ki sanar dani naji idan shawarar tayi idan batayi ba a canza wata, dan wallahi yau bazan runtsa ba sai na kaiwa YARIMA yarinyar nan”. Rabi tsayuwa ta gyara tace “Kayan abincin da muka kai gidan su, zai sa yanzu idan munje muka aika yaro akan cewar YARIMA ne yazo ko batayi niyyar fitowa ba iyayenta zasu tilasta mata, idan ta fito na samo wata hoda ta gusar da hankali ita kawai zamu busa mata ta fad’i mu kai masa ita”. Kai ya jinjina cikin gamsuwa da shawararta yace “Amma taya kike tunanin zamu wuce da ita ba tare da wani ya ganmu ba”. Rabi ta kallesa tace “Ni da nake mace ma nafi ka wayo”. Yace “Naji ni dai mafita yake nema kawai sanar dani dabarar taki”. “K’auyen nan bai wadatu da wutar lantarki ba, a yadda take tsaye zan kwanto da ita kan kafad’ata na rik’eta, kai kuma ka biyomu a baya, mu bi ta baya wurin shagon Danjummai babu yawan mutane da dare kasan mutane basa bi hanyar saboda tsoron maciji”. “Amma idan ta dawo hayyacinta fah zata gane mune muka kaita wurinshi”. Dariya Rabi tayi “Ko ta gane mune kasan dai bata isa jayayya da Yarima ba, kuma ma ai kanta zata tonawa asiri kasan k’auyen nan yadda ake d’aukar macen da aka ma fyad’e ko aure sai ya gagareta”. Mamman murmushi yai cikin gamsuwa da zancenta a yanzu zuciyarsa ta rufe neman farantawa YARIMA kawai yake dan kada ya yanke alak’a dashi.


***********


Gumin da ya tarar masa kan goshi yasa hannu ya jawo k’aramin towel dake jere gefe d’aya an musu hanger su, ya goge zufar, Ya matsi ruwa a dispenser ta wurin ya sha, Yana sauke ajiyar zuciya, ya mik’ar da hannayensa biyu, kana ya soma taku yana barin gun, ba abunda yake buk’ata yanzu kamar kwanciya ya huta d’akinsa ya shige kai tsaye cike da tunanin yaji k’amshin turaren wutan da ya saba ji sai dai ga mamakinsa alama bata nuna wani ma ya shigo d’akin ba, Idonsa ya runtse yana jin yadda zuciyarsa a take ta mamaye da b’acin rai, ya dunk’ule hannayensa, tabbas idan yaje gun UMAIMA a yanayinsa yanzu ba abunda zai hana ya kai hannunsa jikinta, k’ok’arin danne zuciyarsa yake yana tausasawa kansa, Lallai Umaima ta fara crossing limit d’inta, har ya umarceta ta tsallake yake zancen zuci wanda zuciyarsa ke sake harzuk’a, Babu mai aikin da ta tab’a shigowa sashen sa, amma ya zama dole yau ya buk’aci mai gyara masa d’akin, ba zai iya kwana cikinsa ba, har ya fito zaije kiran d’aya daga cikin masu aikin sai ya tsaya cak yana ganin hakan tamkar tonon asiri ne gare sa, Juyowa yayi zuciyarsa na karkata zuwa d’ayan d’akinsa, Haka ya shiga ya kwanta ransa babu dad’i.



Ta b’angaren UMAIMA da ta gama kallo, d’akin yaranta ta lek’a daga bakin k’ofa taga an shiryasu cikin kayan baccinsu, kowacce na kwance kan gadonta tana bacci, bata damu ta shiga ciki ta sake tabbatar da lafiyarsu ba taja k’ofar ta wuce d’akinta, Cike da tunanin Major Umar zai zo ya tuhumeta kan rashin gyara masa d’aki, ita kuma ta shirya amsoshin basa, sai dai har bacci ya soma d’aukarta bata ji ko alamun motsin tab’a k’ofa da zai nuna shigowar wani ba, ba haka taso ba, tayi da gangan ne dan ta sake harzuk’a sa yazo ta fad’a masa maganganu.


(Hmmm ko meyasa Umaima kike haka🥹🥹)



*******


Malam Garbati, Umma Habiba tare da KULUWA zaune suke tsakar gida kan tabamar sak’a suna shan iska mai cike da sanyi da dad’i, suna hirar rayuwa, Kuluwa ba kasafai take saka baki ba tafi maida hankali kan sauraren iyayen nata, Sallamar yaro suka jiyowa daga waje, Malam Garbati cikin d’aga murya ta yadda zai jiyo yace “Waye?”. “Wai ana sallama da Kuluwa inji Yarima Haladu”. Kuluwa gabanta ne yayi mummunan fad’uwa, UMMA HABIBA DA MALAM GARBATI kallon juna sukai suna murmushi kowane zuciyarsa na cika da farin ciki, Malam Garbati yace “Kace tana zuwa”. Yaron yace “Toh”. Yana komawa ya sanar da Rabi da Mamman wanda suka zak’u da fitowar tata, Malam Garbati ya kai dubansa ga KULUWA yace “Tashi kije Kuluwa, ki sanar dashi kuma ina son ganin shi”. Ta bud’e baki da zummar sanar dasu manufar Yariman sai kuma taji zancen ya nauyi a baki tamkar an saka k’aton dutse an danne harshenta ta kasa magana, Jiki sanyaye ta shiga d’aki ta d’auko babban hijabinta cikin hijabai uku da ta mallaka a duniya ta saka, ta fito tana karanta dukkan addu’o’in da ta iya dan neman kariya daga sharrin YARIMA HALADU,


******


Ba k’aramin mamaki ya bayyana kan fuskarta ba ganin Mamman da Rabi, waigawa tayi ko zata hango YARIMA HALADU daga gefe sai dai babu shi babu alamar shi, ajiyar zuciya ta sauke wacce sautin ta ya fito a fili, Rabi na murmushi ta kalleta tace “Godiya kike wa Allah ba Yarima bane ko”. Wani Kallo KULUWA ta mata na baki da amsa, D’an matsowa tayi kusa da Kuluwa, tana d’ago hannunta wanda ta zuba hodar, wurin masu shaye shayen k’auyen nasu ta samu, da k’yar suka bata bayan ta musu alk’awarin dubu biyu, KULUWA kallon RABI take cikin rashin yarda, ganin ta d’ago hannunta tana neman k’arato fuskarta tayi saurin sa hannu ta bige na Rabi da k’arfi wacce hodar ta b’are a k’asa, Rabi da Mamman wata irin muguwar razana sukayi, Duhun da ya mamaye sararin samaniya ya hana KULUWA ganin hodar, amma jikinta ya bata tabbas wani abu ne a hannun RABI, Ta kalleta kallo mai cike da haushi da k’yamatar halayyarta tace “A da idan zan kira masoyana a cikin k’auyen nan zan saka sunanki Rabi amma a yau na shaida bani da makiyiya kamar ki, kiji tsoron Allah”. Tana fad’ar haka ta juya ta shige ciki,


Mamman wata irin zufa ce ta keto masa, ita kanta Rabi hankalinta ya mugun tashi taga samu taga rashi, Mamman yace “Wane irin sakaci kikayi Rabi da har ta ganki”. Tsaki taja tace “Kada ka d’aura laifin kaina, ni ai nayi k’ok’ari ma da na kawo shawarar nan kai fah kanka sam baya kawo wuta ai”. Ransa yaji ya harzuk’a yace “Daga yanzu bana buk’atar taimakon ki zanyi da kaina”. Ya juya ya barta tsaye, tana jin kamar ta tsunduma ihu tsabar bak’in ciki da takaici, tasan yanzu KULUWA ba zata sake yarda da ita ba, wacce hanya kuma zata bi.


MAMMAN tafiya yake ba tare da yasan ina zaije ba, gaba d’aya tunaninsa wacce hanya zai bi, wani tunani yazo ransa wanda yake ganin shine mafita, Ya jinjina kai cike da gamsuwa da kansa, zuciyarsa na saka masa yak’inin zaiyi galaba


***************

Malam Garbati da Umma Habiba sunyi mamakin saurin dawowarta cikin gida, Malam Garbati yace “Yariman har ya wuce ne”. “Eh Malam”. Ta fad’a tana saurin shigewa d’aki gudun su sake mata wata maganar da ta dangancen sa, Malam Garbati da Umma Habiba sun d’auki hakan da tayi kunya ce, dariya kawai sukai a tare suka girgiza kai, Malam Garbati yace “KULUWA sarkin kunya”.



Daren ranar KULUWA ba tayi wadataccen bacci ba, kwana tayi juyi zuciyarta babu natsuwa, damuwar yadda Yarima yaci burin lalata mata rayuwa na sakata tsoro da fargaba, tana ji a jikinta kamar wani abu zai faru wanda bata san menene ba, sai zuciyarta da ta kasa jin natsuwa, a haka take ta juyi har asuba, Yau ta riga Malam fitowa wanda a kullum yake riga su, Tana zaune wajen tana alwala ya fito, yana dubanta yace “KULUWA har kin tashi yau”. Tace “Eh Malam na tashi, barka da asuba”. “Yawwa barka”. Ya d’auki buta yai alwala ya fice masallaci.




Dawowar Malam Garbati ba jimawa daga masallaci, Kuluwa na zaune kan d’ankwalinta da tai sallah akai, tana bitar karatun qur’ani sukaji sallama ta karad’e tsakar gidan nasu, muryoyin sama da mutum uku na tashi, Gaban KULUWA ne ya fad’i zuciyarta na shaida mata DANLADI ne yazo kamar yadda ya furta yau ce cikar ranar wa’adin kwanakin da ya d’ibarwa mahaifinta, ayar da ta d’auko ta k’arasa karantawa tayo waje, tayi turus k’iris ta fad’i ganin jami’an tsaro sanye da kakinsu, abunda bata tab’a gani ba tsawon rayuwarta , hasalima yan’ sanda basu da ofishi a k’auyen nasu sai kaje KURA wanda k’ark’ashin garin k’auyensu maisuna DANHASSAN yake, tashin hankalin bai sake kamata ba sai da taji furucin DANLADI yana cewa “Ku tafi dashi, kada a sake shi har sai ya biyani kud’ina”. Habu da wasu su biyu suka fad’o cikin gidan ba sallama a tare suka ce “Muma sai ya biyamu namu sannan a sake sa”. KULUWA zuciyarta taji tana barazanar tarwatsewa bata tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba, ganin an kama mahaifinta ana k’ok’arin saka masa ankwa, zubewa tayi k’asa ita da Umma Habiba, Cikin tsananin tashin hankalin da ya hana hawaye zuba kan fuskar su suka soma rok’on su Danladi da jami’an tsaro, sam suka k’i saurarensu, suka tasa MALAM GARBATI gaba wanda tsabar shiga tashin hankali komai ya kasa furtawa.



Allah sarki KULUWA🥹🥹🥹



SADIYA NASIR DAN CE

TARE DA ZEE YABOUR