SHAFI NA GOMA
by @zeeyabour20
*KULUWA*
*NA ZEE YABOUR*
*DA SADIYA NASIR DAN*
*YAN TAGWAYE BIYAR*
*ZANGO NA BIYU*
*TAFIYAR BIYU TAFI DAYA*
*SHAFI NA GOMA*
Kuluwa zaman dirshan tayi a k’asar dake malale da tsakar gidan nasu, ta saki kukan da bata san tahowarsa ba sai d’umin hawayen da taji suna sauka kan kumatun ta, Bata tab’a riskar tashin hankali irin na yau ba, Umma Habiba dake gefenta itama sai a yanzu hawaye ke zirya kan kumatun ta tashin hankalin rasa mijinta na bin dukkan wata kusurwa ta zuciyarta, tasan ta rasa shi kenan zatayi rayuwar da bata da bambamci da zawarci sunan mijinta na raye ne kawai amma ba zasu cigaba da rayuwa tare ba, dan basu da kud’ad’en biyan bashin dake kansa a sako sa, Dubanta ta kai kan KULUWA ganin yanayinta ya sake hargitsa mata zuciya, a raunane ta kai hannunta kan KULUWA tana rik’ota tace “K’addararmu ce tazo a haka, sai dai mu bi Malam da addu’a amma nasan acan zai k’araci rayuwarsa tunda bamu da yadda zamuyi mu fito dashi”. Furucin Umma Habiba ya sake jefa KULUWA cikin wani irin firgici ba zata tab’a iya jure ganin mahaifinta yana rayuwa a can kulle ba, shikenan an rabasu dashi, har gara su san baya duniyar akan ace yana cikinta amma baya tare dasu yana cikin wahala da takura, ta sha jin labarin irin rayuwar uk’ubar da mutane ke yi a can idan an kama su, Kallon UMMA HABIBA tayi ganin hawayen fuskarta na sake jefata cikin wani irin tashin hankali da damuwa, bata tab’a ganin hawaye kan fuskar mahaifiyarta ba sai yau, “Umma ki taimakeni ki tsayar da hawaye kan fuskar ki, zuciyata ba zata iya jure ganin hawayenki ba”. KULUWA tai maganar muryarta na fita da k’yar saboda kuka da rauni, “Dole nayi kuka KULUWA, Allah kad’ai yasan irin rayuwar da Malam zai fuskanta a can, ba k’aramar azabtarwa sukewa mutane ba, babban tashin hankalina shine yadda zai dawwama a can har k’arshen rayuwarsa cikin uk’uba”. Wani irin kuka KULUWA ta fashe dashi tana k’ank’ame jikin UMMA HABIBA.
*******
Malam Garbati cikin mota tsakiya suka sa shi tamkar wanda yayi sata ko wani gagarumin laifi, Har lokacin ya kasa furta komai sai nadama mai tsanani da yake na kasancewarsa mai cin bashi yana jin ina ma bai tab’a cin ko naira ta wani ba, dukkan bashin da yake ci yanayi ne dan inganta rayuwar iyalansa baya son ganinsu cikin k’unci gashi sanadiyyar hakan zasu dawwama cikin k’uncin da yake gudar musu, yasan bazasu samu farin ciki ba matuk’ar baya tare dasu musamman KULUWA, tausayinta yaji ya mamaye zuciyarsa, k’walla ta tarar masa gefen ido wanda yak’i ba kansa damar da zasu sauka kan kuncin sa har suka iso k’aramar hukumar KURA, yana ji yana gani aka jefasa cell mai d’auke da wasu samari su uku kallo d’aya zaka musu kasan hatsabibai ne, D’aya daga cikinsu wani kallo ya ma Malam Garbati yace “Kai tsoho baka ja tsufanka ba kayi eyane aka kawo ka nan, wa kayiwa wuff da kaya ko kuwa yarinya kai wa fyad’e”. Malam Garbati idonsa ya runtse yana jin d’acin maganar, yayin da dana sanin cin bashi ke sake mamaye sa, tabbas da bai ci bashin kowa ba, ya tsaya ma talaucin sa, da bai jawowa kansa tozarci irin wannan ba, da bai jefa matarsa da yar’sa cikin k’unci da damuwa ba, Gefe d’aya ya zauna, yana jingina da bango, sanyin k’asan sementi da na bango yana ratsa k’ashin jikinsa, ya had’e jikinsa gu d’aya saboda sanyi.
*********
Major Umar yadda baccin daren jiya baiyi sa cikin natsuwa da dad’in rai ba, tashin sa ma babu dad’in rai har yayi sallah wacce a gida yake yi d’akinsa yana da matuk’ar wahala ya fita masallaci sallar asuba, A toilet na d’akin ya shiga yai wanka, akwai komai na buk’ata na wanka ciki, Ya d’auki kusan minti ashirin yana wanka kana ya fito d’aure da towel zuwa d’akinsa wanda a can duka kayansa suke,
Ya kammala shafa mai ya kai hannunsa zai d’auki designer spray d’insa wayarsa tayi k’ara wacce ba kasafai yake sakata silent ba saboda yanayin aikinsa za’a iya masa kiran gaggawa, Waigowa yayi yana duban wayar da ya ajiye kan bedside drawer sam jiya ya manta yaje da ita d’ayan d’akin, D’aya daga cikin yaransa ne, Yayi picking, “HELLO SIR, an kai harin wani k’auye a katsina kuma sun kwashi mutane yanzu haka ma ance suna kan operation”. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”. Major Umar ya furta yana saurin kashe wayar cikin kid’ima, duk da ba yau ce rana ta farko yana jin faruwar hakan ba amma a duk sanda aka sanar dashi labari irin haka hankalinsa ba k’aramin tashi yake ba,
Number wani babban soja da can mazaunar sa ta aiki take kusa da k’auyen ya kira ya sanar dashi abunda ke faruwa kan su shirya motocin sojoji ayi saurin zuwa a rutsa su kafin su bar garin, “OK SIR” ya ba MAJOR UMAR amsa kasancewar yana gaba dashi yafi shi matsayi gun aiki. Yana kashe wayar yace “Ba zanyi kasadar rayuwata naje garin nan ba, idan sun kasheni iyalaina nayi ma asara ba gwamnati ba, ba wanda zai cigaba da dawainiyar da lalurarsu, gashi ba wani biyan arzik’i za’a ma mutum ba ko yaje yayi artabu dasu”. Ya gyara zamansa yana kishingid’a hankalinsa kwance ya zaro tabar wiwi daga aljihu ya fara busawa, ba alamun tausayi ko damuwa da labarin da ya riske sa tun d’azu tun kafin kiran MAJOR UMAR.
********
Wayewar safiya mutanen k’auyen DANHASSAN da zancen kama MALAM GARBATI suka tashi, duk lungun da kabi zancen ake, har mata a cikin gidajensu maganar suke, kai kace wani gagarumin laifi ya aikata, Rabi zancen ba k’aramin dad’i ya mata ba, da tana kwance d’aki ko aiki bata fito tayi ba a cewarta cikinta ke ciwo yanayinta yasa mahaifiyarta yarda ta k’yaleta tana jera mata sannu, Rabi sai da ta fakaici idon mutanen gidan nasu ta fice ba tare da wani cikin yan’ gidan nasu ya ganta ba, bata zarce ko’ina ba sai gidansu KULUWA,
UMMA HABIBA da KULUWA tun tafiya da MALAM GARBATI suna tsakar gidan babu abunda ke cikin zukatansu sai alhini da damuwa shimfid’e tare da tunanin rashin sanin mafita, sai dai KULUWA bakinta bai gushe wurin ambaton Allah ba, Ganin RABI gidan nasu yasa zuciyarta bugawa cike da tunanin me kuma tazo dashi, Rabi marairaice fuska tai alamun tausayawa gare su, ta gurfana gaban UMMA HABIBA ta gaisheta wacce ta d’ago rinannun idonta da suka sauya kala tsabar kuka har tana jin sun mata wani nauyi ta kalli RABI ta amsa gaisuwar, “Allah ya tsare Malam yasa su sako sa”. Umma Habiba kad’ai ta amsa da “Amin”. Sab’anin KULUWA da ta d’auke kai daga kallon Rabi, wacce ta kalli KULUWA tace “YARIMA HALADU ne ya aikoni gun ki”. Take gabanta yayi mugun fad’uwa, Ganin Umma Habiba a gun yasa tace “Muje d’aki”. Umma Habiba bayansu tabi da kallo da suka shige d’aki tana addu’ar Allah yasa wani taimako zai musu akan kama MALAM GARBATI,
KULUWA ba tare da ta kalli RABI ba tace “Dan Allah ki barmu a halin da muke ciki, ki tafi bana buk’atar jin duk wani sak’o daga gare sa”. “Ko da na wanda ya shafi fito daga mahaifinki ne daga hannun hukuma”. Da sauri ta kalli Rabi babu abunda take tsananin buk’ata da buri yanzu sama da mahaifinta ya fito, Rabi ganin Kuluwa ta kalleta yasa taji wani sabon k’arfin gwiwa taja numfashi tace “KULUWA kina da damar kub’utar da mahaifinki idan kin so, kinsan irin azabtarwa da akewa masu laifi idan suka shiga hannun hukuma, hadda mugunta suke had’awa, mahaifinki ki tuna irin muhimmiyar rawar da yake takawa a rayuwarki, bashin da yake ci ma dalilinki ne dan ya inganta rayuwarki, ki cire girman kai ki amincewa YARIMA HALADU ya baki kud’ad’en da zaki tseratar da mahaifinki”. Karon farko da taji hud’ubar Rabi na shiga ranta tana samun muhalli a zuciyarta, idonta ya rufe da son taimakon mahaifinta, zata iya komai dan ganin ta kub’utar dashi, Allah na tuba ka yafe mun bani da wani zab’i da ya wuce bin wannan hanyar, Tai zancen zuci hawaye na bin kumatun ta, Rabi kallon Kuluwa tayi ganin alamun tayi nasara kanta tace “Kin shirya zuwa gun sa, na sanar da MAMMAN”. Kai Kuluwa ta d’aga tana rushewa da wani irin kuka ta kifa kanta kan cinyoyinta, RABI murmushi tayi mai cike da farin ciki tace “Zanje yanzu na sanar da MAMMAN ki zama cikin shiri zuwa dare zai miki jagora gun sa”. Kasa ba Rabi amsa tayi sai kanta da ta sake cusawa cikin cinyoyinta abu mafi daraja gareta yau zata bada shi ga mutumin da bai cancanta ba, Rabi ta fita d’akin ranta cike da tsananin farin ciki tayiwa UMMA HABIBA sallama a tsakar gidan ta fice.
********
MAMMAN na zaune bakin dakalin gidansu, sam duniyar bata masa dad’i sakamakon YARIMA HALADU da ya yanke alak’a dashi fatansa shirinsa ya tafi daidai ta yadda YARIMA HALADU zai dawo dashi cikin rayuwarsa, Hango Rabi tafe fuskarta washe yasa zuciyarsa d’an jin sanyi, ya tashi zaune yana jiran k’arasowarta, Rabi cikin sauri ta taho tana tsayuwa gabansa baki washe tace “Yau dai KULUWA ta amince zataje ga Yarima Haladu, ka shawo kanta duk da kace ka ishi kanka nice dai na maka aikin”. Dariya yayi yana kallonta yace “Kin shawo kanta ko shirina yayi aiki”. “Ban gane ba taya kenan?”. Tai masa tambayar tana kallonsa da mamaki, Numfashi yaja yace “Kina tunanin su DANLADI nada k’arfin d’auko yan’ sanda daga KURA saboda bashi kawai?”. Rabi ta girgiza kai tace “Bani kad’ai ba kowa a k’auyen nan ma yayi mamaki duba da ba wani k’arfi garesu ba kuka bashin nasu duka nawa ne a biyan yan’ sanda ma sai sun biya fin bashin nasu”. Murmushin gefen baki yayi yace “Aikina ne, ni na tsara komai”. “Ka sanar dani yadda zan fahimta”. Mamman yana kallon Rabi yace “Tunda na barki a bakin gidansu KULUWA nake tunanin hanyar da zan bi, shawarar da ta zo mun shine zuwa na tunzara wanda suke bin Malam Garbati bashi, kan suzo tada hankalin cewa sai ya biya su, ni zan d’auko musu jami’an tsaro kuma komai rok’on da zai musu kada su saurare shi, DANLADI da HABU sun sanar dani dama suna son d’aukar mataki kansa, dan haka suka amshi maganata hannu biyu, nayi tunanin matuk’ar aka kama mahaifinta shi zai sa ta amincewa YARIMA HALADU ba ja”. Rabi ta jinjina kai tace “Shirin ka yayi amma sai dai ka sani tunanin haka bai zo mata ba sai da naje na dasa mata nawa karatun sannan ta amince”. MAMMAN yace “Kinci dubu hamsin”. Wani juyi Rabi tai na murna, Mamman ya bata hannu suka tafa ba kunya ba tsoron Allah.
*********
“Mummy munyi missing d’inki yanzu kin daina breakfast damu kullum you are busy”. Aydah ta fad’a tana turo baki, Ayrah ta taso daga kan kujerar dining da take zaune ta taho gun UMAIMA tana cewa “Ni Mummy ce zata bani tea”. Saurin ja baya UMAIMA tayi tace “Tsaya mana Ayrah kada ki b’ata mun jiki”. Yarinyar turus tayi idonta na cika da k’walla, UMAIMA cikin halin ko in kula taja kujera dining table ta zauna, tana jawo kofi ta had’a tea mai kauri, tana sha tana duba wayarta, Ta chab’a ado na gani na fad’a tamkar wacce za taje gidan biki, dining area ya d’auki k’amshinta,
Major Umar dake tsaye bakin k’ofa hannayensa hard’e kan k’irjinsa yana kallon meke faruwa, zuciyarsa ta kai mak’ura gun b’aci da abunda UMAIMA ta aikata, mamaki kuma ya cika sa na ko in kula da ta nuna kan yaranta mafi soyuwa gareta da a ko da yaushe bata da buri sai na inganta rayuwarsu da son kasancewarsu kusa da ita, Zuciyarsa ta fara karkata ko sihiri aka mata, a yau zuciyarsa ke sake tabbatar masa ba yin kanta bane, ya zama dole ya tuntub’i babban malami, Falon ya k’araso wanda Ayrah na ganinsa ta taho gunsa, Tana cewa “Daddy Daddy”. Kofin hannunta ya amsa, yaja kujera ya zauna ba tare da ya kalli saitin UMAIMA ba, ya zaunar da Ayrah kan cinyarsa ya fara bata tea cike da kulawa, Aydah itama plate na chips d’inta ta d’auko ta dawo gunsa, Ya shafa kanta yana cewa “Zauna ki cinye duka kada kiyi late na zuwa school”. Kai ta d’aga masa ta zauna ta fara ci,
UMAIMA tamkar bata san dashi a gun ba, ta tashi tana tafiya tamkar bata son taka k’asa tana jijjiga jikinta, Major Umar bayanta yabi da kallo yadda mazaunanta ke juyawa yasa tsikar jikinsa tashi yai saurin rufe idonsa MAJOR UMAR yana cikin jerin maza masu k’arfin sha’awa, bai tab’a jera kwanakin da ya jera yanzu ba tare da ya kusancenta ba.
UMAIMA jakarta ta d’auko da mukullin mota, ta yafa figigin mayafi ta fito ta wuce abun ta ba tare da ta kalli Major Umar ba balle ya samu gaisuwarta, kishinta ke nuk’urk’usar zuciyarsa na ganin shigar da tayi ta fita, sai dai baya son rigima da ita gaban yaran sa, Dole yana ji yana gani ya barta ta fita, wanda a take zuciyarsa ta sake jagulewa.
****************
Wunin ranar yau KULUWA a d’akinta tayi sa ta kasa fitowa gudun UMMA Habiba ta fuskanci yanayinta wacce da taji ta lek’o d’akin zata lafe tamkar mai bacci, Umma Habiba tayi mamakin baccin KULUWA sanin yadda take saka damuwar mahaifin nata a rai, amma taji dad’in ganin ta samu bacci, KULUWA duk wani shige da fice na mutane dake zuwa musu jaje a kan kunnenta, Alwala kuwa tun ta azahar take rik’e da ita har zuwa magrib, lokacin sallar isha’i ne da ta dakaci lokacin da take kyautata zaton UMMAN ta shiga sallah kana ta fito tai alwala ta koma ciki, tayi sallah, Ta zauna jigum zuciyarta cunkushe babu wata walwala tattare da ita,
Yau ma Rabi tare da Mamman suka zo gidansu KULUWA, Rabi ta shiga ciki a tsakar gida ta samu Umma Habiba suka gaisa take sanar da ita YARIMA HALADU ne yazo yana son ganin KULUWA kan zancen fito da Malam, Umma Habiba a zabure tace “Kina nufin zai sa a fito dashi”. Kai ta jinjina tace “Eh Umma”. A take farin ciki ya mamayeta ta soma kwarara masa addu’o’in alkhairi, wanda duka akan kunnen KULUWA da take jin wani irin raunin zuci, “Umma da kinsan me yake buk’ata daga gareni kafin ya aikata haka, ko kusa ba zaki masa addu’ar alkhairi ba”. Tayi zancen tana share hawayen da suka tarar mata a ido, RABI ce ta shigo d’akin tace “KULUWA tashi muje ko”. Babu kuzari ko kad’an a jikinta tamkar wacce aka zarewa dukkan lakkar jikinta haka ta fito d’akin nata, Kasa kallon Umma Habiba tayi balle ta amsar addu’ar da take mata na dawowa lafiya, gani take kamar zata fuskanci abunda za taje aikatawa,
KULUWA tafiya take k’afafunta sun mata wani nauyi bata san ina take jefasu ba, hannayenta rik’e da na Rabi da take mata jagora har suka kawo k’ofar d’akin YARIMA HALADU, MAMMAN ya k’arasa ya bubbuga masa yace “Yarima nine Mamman yau na cika maka alk’awari na kawo maka KULUWA”. “Bana son maganar banza MAMMAN, yaushe na zama abokin wasan ka”. “Wallahi tare muke da ita YARIMA, idan ka fito kaga ba ita bace na yarda a d’auki ko wane irin hukunci a kaina”. Jin haka Yarima ya tabbatar da gaske yake, Yayi saurin saukowa daga kan gadonsa, Ya bud’e k’ofar ganin KULUWA ya sake tada masa wata zazzafar sha’awarta ya had’iya wasu yawu, Yana dubanta yace “Mu shiga daga ciki ko”. Wata irin mummunar fad’uwa gabanta yayi tana jin tamkar ta juya tace ta fasa, kanta na mata masifar nauyi, RABI tayi caraf tace “Ni dai a sallameni na tafi kafin a shige”. Yarima murmushi yayi ya koma ciki, ya d’auko rafar d’ari biyar ya damk’a mata, Rabi tsabar murna kamar zata had’a hadda hannunsa wurin amsar kud’in, ta dinga zuba masa godiya kana ta tafi, Kallon Mamman yayi ya masa alama zasu had’u, Mamman ya washe baki sanin kyauta ce mai tsoka, Hannunsa ya kai kan na KULUWA ya rik’ota wacce taji tamkar saukar dalmar wuta, zuciyarta na sake yin bak’ik’irin, ya jawota cikin d’akin ya rufe……
HMMMM
TOH FAH
KU DAI BIYO MU CIKIN TAFIYAR YAN TAGWAYE
SADIYA NASIR DAN CE
TARE DA ZEE YABOUR