Mutum Mugu Ne

27

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*


                     27


Hoto suke yi a k'ofar gida su biyar Gbenga, Timothy, Ziha, Ronke da Azra. Motar da tayi parking ne ya ja hankalinsu, Azra ta nufi motar da gudu tana kiran "Dad".

Tim ya sak'ala hannunsa a k'ugun Ziha yace " let's have a last cute selfie" ta d'an yi murmushi kafin Tim ya d'au hoton ya kissing kumatunta wanda a haka ya snapping hoton.

Dai dai Sajid ya fito daga mota, Azra dake ta masa surutu ma bai iya kulata ba sai kawai ya rik'e hannunta suka fara tafiya idonsa k'ur akan Naziha.

Har lokacin da suka iso wajen still hannun Tim na k'ugun Ziha. Sannu da dawowa suka mishi ya amsa k'asa k'asa, zai wuce cikin gidan Azra ta rik'e shi "Dad wait please, let's take a pic together" da kamar ba zai tsaya ba ko me ya tuna sai ya juyo. Gbenga ne ya musu hoto shi da Azra sai kuma Tim da Ronke suka shiga hoton, Ziha komawa gefe tayi tana kallonsu tana dariya. Gbenga ya mik'a mata wayar yace ta d'aukesu shima ya shiga group pic d'in sai da ta d'au kala uku sannan Tim yace ta zo ta shiga ayi selfie. Ta girgiza kai. "Come on Nazzy, take a pic with my Dad" Azra tace da ita. Had'a ido suka yi da Sajid ta ga wani kallo yake mata da batasan ma'anar ba.

"No Baby some other time"

Azra ta zo da gudu ta rik'e hannunta "I won't take no for an answer, Nazzy"

A hankali ta dinga janta har ta k'arisa wajen da yake tsaye ta d'an tsaya gefenshi, Timothy zai d'aukesu hoton wayarsa tayi mishi warning babu space, " Oh shit, Gbenga jor Funmi ni phone re"

Gbenga ya laluba aljihunsa babu waya ya sa ta chargy cikin gida.

Sajid ya ciro wayarsa ya mik'a wa Timothy dan ya fahimci mi Tim d'in yace. Tim ya k'ar'bi wayan.

Juyowa tayi ta kalleshi wasu abubuwa take rayawa a zuciyarta "yanzu mutumin da ba ta ta'ba mafarkin zata had'u da shi ba shine yau a gefenta har zasu d'au hoto, just like in movies"

Azra ganin yadda suka tsaya kowa daban daban akwai space tsakaninsu yasa ta tura Ziha dan su had'u da Sajid. Unfortunately bata ankara ba saboda duniyar tunani da ta shiga. Shirin fad'uwa take yi Sajid ya grabbing ɗinta hannunsa d'aya a kafad'arta d'ayan a hips d'inta. Gaba d'ayansu wani yanayi suka tsinci kansu mai wuyar fassarawa. K'irjin Ziha bugawa ya shiga yi buk buk buk. Sajid ya tsura mata idanunsa ita d'inma shi take kallo, gyara mata tsayuwa yayi yace "careful with your legs"

Ita dai tsayawa kawai tayi amma zuciyarta baya wajen, dad'in k'amshin turarensa, lallausan hannunsa har yanzu current daya flowing tsakaninsu bai saketa ba, batasan ya akayi ba kawai ta kama hanya ta shige cikin gida tana dai jin muryansu Tim sama sama suna cewa zasu sake d'aukan wasu hotunan saboda wayar Sajid ta fi d'aukan hoto mai kyau. A center table d'in falon ta zauna tana sauke ajiyar zuciya " Don't even start it Naziha, he's like a mountain whilst you are like a pebble. Ya fi k'arfinki Naziha, ya fi k'arfinki"

Muryansa ta ji ya doki kunnenta " is like free kiss kike bayarwa yau d'in nan, Timothy, Gbenga, who else kissed you today?"

"Uncle... free kiss kuma!"

Zama yai gefenta har kafad'arsu na gogan juna yace " don't deny it, da idona na gani"

"Uncle ba kiss bane ba fah, it's just a peck, and gobe Tim zai koma school shine muke hoton k'arshe"

"hmmm! I see, Nima idan na tashi tafiya zan samu goodbye peck kenan"

Rufe bakinta tayi da gyalenta tana dariya...

"Ziha seriously ya kamata ki yi k'ok'arin hana Gbenga da Timothy abinda suke miki, yes I understand ku cousins ne amma kin san ke musulmace kuma musulunci bai basu dama su dinga ta'ba ki anyhow ba, da ace su musulmai ne kin san akwai aure tsakaninku. Amma kin barsu suna ta'ba miki jiki anyhow, then yanzu kissing, baki san gaba mi zasu kuma nema a wajenki ba, you need to be very careful" yadda yake magana da fad'a yasa jikinta yai sanyi maganarsa na k'arshene yasa hawaye suka fara zubo mata cewa ya yi " or may be you really enjoy it when they touched you, shiyasa baza ki iya hanasu ba"

Ranta ya 'baci matuk'a ' mi uncle yake nufi?'

Azra ce ta shigo da gudu biye da ita kuma Zaytunah, tsam Ziha ta tashi jin k'as k'as d'in takalmin Zaytunah. Ita Zaytunah batama kallesu ba dan tana dafe da goshinta saboda wani mugun ciwon kai da take ji.

Ganin Zaytunah yasa tayi saurin wucewa d'aki. 

Yanayin yadda ya ga Zaytunah na tafiya yasashi k'arasawa wajenta da sauri duk da yana fushi da ita amma bak'aramin tausayi ta bashi ba. Baya cikin maza da basu damu da matansu ba idan suna fad'a. Kama hannunta yayi ta fad'a jikinsa tana cewa " my one ka kaini d'aki"  d'aukanta yayi ya shiga d'aki da ita, ya kwantar da ita kan gado, goshinta ya ta'ba ya ji zafi sosai "mi ya sameki?" Ya tambayeta

K'ank'ameshi tayi tana fad'in "my one jikin nawane ya tashi, I'm sorry I shouldn't have gone out" ta san idan tace masa maganar kishiya da aka yi ne ya ja mata zazza'bi ba kulata zai yi ba k'ila ma ya mata fad'a.

"Ko muje asibiti ne?"

Tayi saurin cewa " a'a kawai ka kwanta kusa da ni zan ji sauk'i"  gyara mata kwanciya yai shima ya kwanta gefenta ya ja musu bargo, abin mamaki Zaytunah na fama da zazza'bi amma zuciyarsa Ziha take tunowa abinda ya faru d'azu a haka barci ya saceshi.

Kuka tayi a d'aki sosai tana tunanin maganganun Sajid, abu biyu ya tsaya mata a rai maganar Sajid yana nuna kaman he's jealous, na biyu kuma yana zarginta da bin maza.

'Babu dalilin da zai sa Sajid yai kishinki Naziha' zuciyarta ya tabbatar mata.

Azra data shigo d'akin yasa tayi saurin goge hawayenta.  Ta mata murmushin yak'e...

Kiran wayar Zaytunah da aka yi ya fargar da shi daga baccin da yake yi da sauri ya tashi ya d'au wayar amma harta yanke, agogo ya duba ya ga k'arfe biyu ta wuce yai saurin tashi ya shiga band'aki yai alwala. Yana fitowa ya shimfid'a sallaya yai sallah bayan ya idar yai addu'o'i. Zaytunah ya tayar ya tambayeta ya jikin tace da sauk'i yace mata ta tashi tayi sallah lokaci ya wuce. Fitowa yai daga d'akin zuwa falo Ronke ya samu tana kallo ya tambayeta ina Azra tace masa sun je kasuwa da Funmilayo, suna bacci shiyasa ba a gaya musu ba. Ta mik'a masa wayar sa ashe har Barrister ya kirashi kusan awa d'aya daya wuce.

Ronke ta ce masa abincinsu yana dining table ya amsa da toh sannan ya kira Barrister sun jima suna magana kafin ya kashe. D'aki ya shiga ya samu Zaytunah ta idar da sallah ya tambayeta ko zata ci abinci ko kuma ya mata order tace masa tea kawai zata sha.

Fitowa yai ya tambayi Ronke inda ake saida provisions a anguwarsu ta tambayeshi mi zai siya yace mata kayan tea. Caraf Mama ta fito daga kitchen tana cewa kuma kayan tea shine sai ya siya. Ta yiwa Ronke magana da yare ta tashi da sauri. Jim kad'an ta kawo masa tray da kofuna guda biyu da kayan tea akai ta bashi ya amsa ya shiga dashi d'aki,ya fito ya k'ar'bi ruwan zafi. Shi da kanshi ya had'awa Zaytunah tea d'in ya bata. Ya jawo laptop yana duba sak'onni da barrister ya aiko masa.

K'arfe hud'u Ishola ya zo ya d'aukeshi suka tafi.

Zaytunah wanka tayi ta saka wani material red, d'inkin riga da skirt, wani gyale bak'i ta sak'ala a kafad'a ta fito falo babu kowa ta zauna tana chatting a wayanta. Naziha da Azra suka yi sallama suka shigo. Da mamaki Zaytunah ta kalli Ziha dake sanye da hijab bak'i dan ta d'auka duk 'yan gidan Christians ne.

Ziha ta gaisheta bata amsa ba saima wani kallon walak'anci data bita da shi, Ziha simi simi ta nufi d'aki muryan Zaytunah ne ya tsaidata " why are you wearing hijab? Are you a Muslim?"

"Lallai ma matar nan" tace azuciyarta sannan ta shige ba tareda tace mata komai ba, Azra uwar surutu ta gaya mata ai musulmace, ta kuma bata labarin inda suka je.

Naziha ta fito daga d'aki dan ta kai sauran kayan da ta siyo kitchen. Zaytunah tace "Ke zo nan"

Abin ya 'bata mata rai amma ta share ta tsaya ita bata cigaba da tafiya ba ita kuma bata juyo ba " shine ashe kina jin Hausa ki ke wani yi kaman baki jin abinda nake cewa tun jiya ko, to ki bud'e kunnenki da kyau ba wai kunga mun zauna muku a gida ba ku d'auka mu matsiyatane irinku, munfi k'arfin zama a irin wannan gidan kawai dai k'addara ce tasa ki ka ganmu anan, sannan banaso ki sake fitamin da yarinya kalan kuje ku sa mata maita ana zaune lafiya"

"Kiyi hak'uri, na san kunfi k'arfin zama damu, kuma In Allah ya yarda ba zan kuma fita da Azra ba" daga haka ta shige kitchen.

Sajid bai samu dawowa ba sai kusan k'arfe tara na dare. Bai ga Ziha a falo ba Kuma yaso ya ganta d'in, saboda ya bata hak'uri d'azu ya mata gyara cikin fad'a.

D'aki ya shiga ya samu Zaytunah zaune kan gado tana chatting tana ganinshi ta taso ta rungumeshi, wata rigar bacci ne ajikinta shara shara iya rabin cinya k'ok'arin cire masa riga take yi ya rik'e hannunta "Azra ta ci abinci ta sha magani?"

Tayi wani far da ido tace " na mana order lasagne d'azu munci, my one kasan me? I can't believe it's taste very delicious, kamar daga Italy aka kawo mana"

" Ya jikin naki ?" Ta amsa da sauk'i

Taimaka masa tayi ya cire riga "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oon, my one miya same ka anan?" Ta fad'i tana nuna wajen da aka harbe shi, Zama yai gefen gado yana cire takalmi yace " I was shot Zaytunah, and this people helped me, musamman Naziha without her k'ila da yanzu kina cikin takaba"

Hannu tasa ta rufe baki sai ga hawaye cikin kuka tace " haba my one yanzu sai a harbe ka amma ka kasa gaya mini, why didn't you call me nazo nayi jinyarka?"

" No cewa za ki yi miyasa ban saka labarin a media ba saboda na samu masu jinya da yawa"

Ta kwantar da kanta a k'irjinsa tace "my one gaskiya baka min adalci ba, ina matarka amma mummunan abu ya sameka ka kasa sanar dani, that's so mean"

" Ya riga ya wuce Zaytunah, abinda nake rok'onki shine respect this people, domin sun min abinda ba zan ta'ba iya biyansu ba"

Janye jikinshi yayi ya shiga band'aki ya watsa ruwa koda ya fito kwantawa gefe yayi, Zaytunah tazo ta rungumeshi tace "my one please be very careful, idan wani mummunan abu ya sameka mutuwa zan yi"

"Allah ya kiyaye, ki dena magana irin wannan"  

"My one I miss you so badly, kai ko irin marmarina ba kayi" ta fad'i tana kissing wuyanshi

"Zaytunah sleep, jikinki bai warke ba nima ban warke ba we'll do it some other time" kukan sakalci ta saka masa yai kaman baya jinta, haka ta gama kukanta bai kulata ba ta hak'ura tayi bacci.

Washe gari tun da asuba yakejin k'anshin Masa, Zaytunah ma saida ta fito fili tai magana "my one k'anshin masan nan ya burgeni dama yarabawa suna cin masa ne?"

"Ki fita ki tambayesu" ya amsa mata.

K'arfe bakwai aka k'wank'wasa k'ofar d'akinsu da sauri ya tashi ya je ya bud'e dan azatonsa Ziha ce, sai dai yana bud'ewa ya ga Ronke da tray d'in abinci ya amsa ya mata godiya.

Duk kinibibin Zaytunah da ta bud'e kulan abincin sai da ya burgeta, masan shinkafa ne da miyar taushe, sai ruwan tea. Ta d'au guda d'aya ta kai bakinta, wani dad'i ya ziyarceta haka ta zage ta fara cin Masan ta manta cewa jiya ita ke zaginsu cewa su k'azamai ne.

"Zaytunah jiya da kika order lasagne kin had'a dana mutanen gidan nan?"

"Rabani da asara, su je chan su ci bak'in amalarsu sunfi amanna dashi mi zasuyi da Lasagne ina ganin ko sunan basu ta'ba ji ba"

kunya ce ta kamashi, mutanen nan hannu biyu suka rik'eshi amma gashi matarsa na musu rowa.

"Kin bani mamaki Zaytunah" abinda ya iya cewa kenan.

Gaskiya shima ya ji dad'in masan ga miyanma tayi dad'i sosai.

Bayan sun gama karyawa yace Zaytunah ta fito su yiwa su Daddy godiya, bason ranta ba ta biyoshi suka fito. A falo ma suka taddasu kowa yai shirin zuwa church Tim da Ziha ne kawai basa wajen.

A gadarance Zaytunah ta gaidasu tareda musu godiyan kula da mijinta da sukayi.

Daddy yace wa Sajid zasu wuce church kuma zasu jima sannan Funmilayo da Gbenga zasu raka Tim makaranta, so idan zasu fita su kulle gidan ya mik'a masa key.

Bayan ya shiga d'aki ya d'auko wata brown envelope mai d'an fad'i ya fito lokacin harsu Daddy sun fita daga gidan, d'akin su Tim ya shiga ya samu Gbenga na kwance kan gado shi kuma Timothy yana shiryawa, gaisawa suka yi sannan Sajid yace shine tafiyar ta ka ba sallama. Tim yace "I'm sorry Sir" Sajid ya mik'a masa envelope d'in yace gashi asha ruwa a hanya, k'in k'ar'ba yayi, Sajid ya ce idan bai k'ar'ba ba ya nuna masa cewa shi barene a gidansu. Tim yai godiya ya k'ar'ba.

Kamar zai duba d'akinsu Ziha sai kuma ya ji muryan Azra tana kuka a nasu d'akin, yai sauri ya k'arasa.

Tana ganinshi ta zo da gudu ta fad'a jikinsa, Zaytunah dake kwalliya tace "gara da ka shigo kukanta ya isheni dama"

Cikin kuka Azra ke ce masa Nazzy tace bazata fita da ita ba. Hak'uri ya bata sannan ya mata alkawarin zai kai ta shan ice cream. Ihun Tim sukaji yana fad'in "OMG Uncle Sajid you are the best"

"Wannan kuma wace k'wayar ya sha da safiyar nan" Zaytunah ta fad'i tana tsaki.

Murmushi yayi dan yasan kyautar daya masa ne ta girgiza shi.

......Ziha ta shigo d'akin da gudu dan ihun Tim ya birkitata, rawa ta samu yanayi hannunsa d'auke da waya iPhone 7. Ta kalli Gbenga da yake rik'e da bunch d'in kud'i a hannunsa tace "Boda Gbenga ki lo s'ele?"

Tim ya rik'o hannunta yana juyawa da ita yana wak'a.

Ta fincike hannunta " Tim stop this drama and tell me what's happening"

" Uncle Sajid gave me this and that ya nuna kud'in hannun Gbenga" ta kar'bi wayar a hannunsa tana dubawa iPhone 7 ce sabuwa dal ga ma kwalinta can gefe. "Funmi he gave me this phone and 50k, isn't that wonderful"

Ta d'an girgiza kai "he's a very generous man"

A take ya kira Daddy ya gaya mishi Daddy yace yaje ya masa godiya.

Yana shiryawa wayarsa tai ringing Zaytunah ta d'auka ganin Mr David ajiki tayi saurin mik'a masa, godiyar abinda ya yiwa Tim ya masa tareda cewa kyautar tayi yawa, Sajid yace ba komai ai Tim kaman d'a ne awajenshi, Mama ma ta kar'bi wayar ta masa godiya.

"My one akwai laundry fa, za'a fara biyawa damu wajen masu dry cleaning"

Kallon mamaki ya bita dashi kwata-kwata kaya nawa ta 'bata da bazata iya wankewa ba. Ashe Ziha na k'ok'ari da take wanke masa kaya ta goge masa tunda yazo gidan. " Ba nida time ki wanke da kanki ko kuma ki kai da kanki"

"Haba my one ni ina na san wajen dry cleaning anan ka bawa driver ya kai mana"

" In kin gama shiryawa ki sameni a falo" daga haka ya fice a d'akin

A falo ya zauna yana danna waya.

Gbenga ya fito zai je taro taxi ya tsaya ya yiwa Sajid godiya sannan ya wuce.......

......."believe me my hipsy, Uncle Sajid is jealous, it's not what you are thinking"

Naziha ta ce " it's a lie, he wasn't jealous he has no reason to be"

Ya d'an dafa kafad'arta ya rad'a mata a kunne " believe it or not he's over protective because he likes you"

"Liar" tace,

Tim yace " true"

"Liar"

"True"

"Liar" gaba d'aya suka kwashe da dariya.

Dariyarsu ya jiyo daga inda yake zaune duk ya ji wani haushi ya kama shi, wato Ziha ba ta ji fad'an daya mata jiya ba.

Fitowa suka yi tare kowa fiskarsa d'auke da murmushi. Tim saboda kyautar waya da aka masa, dama gashi da uban son gayu gashi kuma an bashi iPhone 7, zai je ya ci takunsa a school da dalili. 

Ita kuwa Ziha maganar Tim ne ya sa hankalinta ya kwanta ko ba komai yanzu ta d'an rage jin haushin Sajid d'in.

Har k'asa Tim ya tsugunna ya masa godiya, Sajid yace masa kar ya sake masa godiya ba komai ya masa ba.

Zasu koma fitar da kaya Sajid yace "Ziha ba gaisuwane" murya k'asa k'asa tace "Uncle good morning"

Kafin yace wani abu ta riga ta shige d'aki. Galala ya bita da kallo yana mamakinta kodai Zaytunah ta mata wani abu ne yasa take gudunshi yanzu. Azra da Zaytunah suka fito Zaytunah d'auke da kayan wanki data had'a a leda.

Minti biyar da fitowarsu Ishola ya iso, suka fita bayan ya yiwa Tim sallama.

Dole dai sai da aka tsaya suka bada kayan wanki kafin suka wuce gidan Barrister. Ko minti ishirin basuyi ba Zaytunah tace zata je gidan k'awarta. Ce mata yai Allah ya kiyaye. " My one baza kasa driver ya kai ni ba"

Hararanta yai yace " ba aikinsa bane ya kaiki yawo" da shike da Hausa suke magana barrister bai san mi suke faɗa ba.

Zaytunah ta tashi ta musu sallama ta fita, Azra kam suna chan da yaran gidan suna wasa a waje da shike akwai yaran Barrister guda biyu da k'anana, d'aya 7yrs d'ayar kuma 9yrs......

Bayan ya bar Gidan Barrister, amusement park ya kai Azra, Salim da Mistura yaran Barrister d'in sun jima kafin ya mai dasu gida abinka da yarinta Azra har ta saba dasu da suka nemi ta kwana tace zata kwana. Barrister ya tambayi Sajid, ya ce masa ba matsala zai taho da kayanta....

**

Nickolas yana kishingid'e kan gado Irene tana bashi abinci a baki, kallonta yake yi cike da so da k'auna.

"I love you, Irene" ya fad'i yana kallon k'wayar idonta

"Just eat and get well soon"

Sai da yace ya k'oshi sannan ta tattara wajen.

"Irene please end this case, testify against Uncle Joe and let those innocent boys be free"

"I can't Nickolas, uncle Joe is still out there he will try and harm my family"

Ajiyar zuciya yai sannan yace mata "ki dena tsoro ba abinda Uncle Joe zai iya yi yanzu, without Uncle Joe Mommy B ba ta da wani k'arfi sannan Uncle Joe greediness nashi ya sa ya betraying ɗinta ya kwashi dukiya yana so ya gudu, kinga shi da yanzu ake nemansa k'asa ko sama ina zai iya harming family ɗinki or even Yamin"

Ta d'ago ido ta kalleshi da mamaki yace " yes Irene, na san kina son Yamin and by keeping quiet you're protecting both your family and Yamin"

Ajiyar zuciya tayi tace " I'm scared Nick"

Hannunta d'aya ya rik'e yace " don't be my Angel, Nicholas Evans is here for you" .

Ce mishi tayi zata tambayi Daddynta idan ya amince zata bada shaida a court gobe.



***

.....BAUCHI.....

Washe gari tare suka had'a breakfast da Anty Zahra bayan ta karya ta wuce gidan radio na BRC dan interview da aka kirata. 

Abba zai fita Nazira ta ce " Abba dan Allah maganar jiya...."

Cikin tsawa yace " kar na sake jin maganar nan a bakin ki"

Bayan ya fita ta shiga d'akinsa dan ta gyara masa taga ya manta babban wayarsa da shike lokuta da dama ma baya fita da ita ya fi amfani da k'aramar wayarsa da kuma laptop. Wani tunani ya fad'o mata tai murmushi sannan ta d'au wayar ta saka numbar Anty Zahra sai ta ga ashe yanada numbar, Zahra Isma'il ta ga ya saving da shi ta goge ta maida sunan zuwa 'My dear Wife'

Ta tura mata message da numbar Abba kamar haka:

*Dear kin isa wajen ne? Ina miki fatan Allah yasa ki samu wannan aiki, domin ki dawo kusa dani nan Bauchi saboda komai ya zo da sauk'i. Ina neman alfarma ki jirani agida idan kin dawo akwai maganar da zamu yi*

Lokacin da Zahra ta ga message d'in ta karanta ya fi sau goma, tambayar kanta take yi mi Yaya Sulaiman yake nufi?. Kiran sunanta da aka yi yasa ta tashi ta shiga d'akin interview d'in.

Koda ta fito daga office ɗin waje ta samu ta zauna ta sake bud'e message d'in ta karanta. Ta daure dai ta tura masa reply * Yaya Insha Allah zan jiraka d'in*

Nazira na kwance wayar Abba na gefenta ta ji message ya shigo ta duba ta karanta ta yi murmushi......