Chapter 1
by @asmabaffa1
🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA
GARE KI ❤️
AIDA MAMAN TASNIM
1-5
INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA SABON LITTAFIN NAN
INA MIKO GAISUWA DA JINJINA GA MASOYA MASU BIBIYAR NOVELS DINA INA MUKU ADDUA ALLAH YA AMSA MUKU BUKATUNKU BAKI DAYA DA WANDA NA SANI DA WANDA MA BAN SAN SU BA.
Page naki ne
MRS CHIEF
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
***
***
BISMILLAH
GA MASU AUDIO..BAN YARDA A JUYA MIN NOVEL ZUWA AUDIO BA.
Gidane me kyau Dan madaidaici da shi na rufin asiri haka gidan yake a unguwa wacce take ta masu rufin asiri daidai gwargwado,gidan dauke yake da dakuna hudu sai Palo da toilet a tsakar gida guda biyu ko Ina siminti ne Palo da toilet ne kawai da tiles, gidan dai babu makusa Dake cikin birnin Kano, wani matashi ne kyakyawan gaske da shi, fari amma haskensa ba can ba a kalla zai Kai 31yrs,dauke da sallama ya shigo gidan hannunsa rike da Yar yarinya wacce zata Kai 3yrs itama yarinya kyakyawa wacce ke kama da matashin me suna Mohsin.
Yaran gidan ne suka Masa sannu da zuwa Yaya Mohsin,murmushi yayi ya amsa,Hidaya ce tazo ta rike Masa hannu suka shiga palon gidan,bayan sun gaisar da shi yace Umma fa? Hidaya Ido ta runtse sabo da kunya tana danne dariyarta tace Yaya wai ta tafi shako warin gardi kasan cikin da Umma ta samu ita me son wari ne,ban gane ba Mohsin ya tambaya,Hidaya ta sake fashewa da dariya tace kaga Yaya Umma tayi tayi akan lallai Abba sai ya daina wanka sabo da ta samu warin hammatarsa ta shaka Yana sata nutsuwa amma yaki sam sai yayi wanka, bata Jin warin shine take ficewa wajen masu aikin gini ta Dan sinsino sai ta dawo,wlh munyi munyi amma taki dainawa gashi Aunty Naila tana gidan yari, itace dama zata iya taka mata birki, Mohsin shi kanshi mamaki yake yi wai duk cikin da Ummansu ta samu ne yasa ko yaushe ita dai ta shaki warin gardi shine dai dai, suna zancen sai suka ji Muryar Umma tayi sallama ta shugo sanye cikin doguwar riga bubu me Fadi ta silk material ta yafa mayafin sai cikinta kato a gaba, sai wani annuri take yi da nishadi.
Palon ta shugo ta zauna tana furta wash Alhmdllh dadi ya ratsani amma gardin nan kazami ne na gaske malam na shaki irin Wanda nake so,Mohsin ya Kalli mahaifiyarsu yace Yanzu Umma da aurenki da mijinki amma kije shakar wani warin gardi duk da ciki ne ya jawo ai bai dace ba, Kubra wacce suke kira da Umma tace ahhh kaga laifina? Ubanku tsaftar tsiya gare shi nayi nayi ya fasa wanka na kwana uku yaki yarda ai kuwa dole na fice Inda zan samu kwanciyar hankali,tunda nake fita sai yau nayi dace na shaki irin Wanda nake so tun da ya daga hammatarsa mallam sai naji wata nutsuwa,Umma tana labarin har wani lumshe Ido takeyi tana cewa wlh wani ni'ima da salama sai wani ratsani take,duk damuwar da nake ciki ta garkame Naila a gidan yari sai naji ta yaye yau bacci harda munshari,idan Kuma Bakin ciki kake min to ka daina wanka da aske hammata kazo na dinga shakar warin naka,Mohsin ya yatsina fuska yace Allah ya kiyaye min,Umma tace Ina Hanan matar taka? Mohsin yace tana Nan lafiya.
Uhmm wannan matar taka marowaciya ita ko irin kyautar nan da ake yiwa surukai a dan siye suruka bata yi,sisinta banci ba me za ayi da mace irin Hanan,Mohsin yace haba Umma duk irin girmamakin da take yi ai shi ake so...kafin ya rufe Baki Umma tace a'a ai babban girma shine Yan kyaututtuka a zamanin Nan waye yake yayin wani girmamawa ai kawai ace ungo shine girma
Canja zancen Mohsin yayi yace Umma yaushe zamu je ziyarar Naila Kinga ta kusa sati daya a gidan yari ya kamata muje,Umma tace ba Wanda zai je mata da wuri ita tasan me ta aikata dama Naila a rashin jinta nasan zata aikata sabo da haka kar Wanda yaje sai ta gane kurenta,Mohsin yace haba Umma haka ma fa Abba yace bazai je ba ko su Hidaya duk babu Wanda zaije mata,sharri aka mata ni ban yarda Naila zata iya kisan Kai ba,nace babu Wanda zai je duk Wanda yaje ko ban sani ba ban yafe muku ba,Naila da tuntuni take da samari na kirki masu kudi Inda zamu huta wannan solobuyon uban naku dolo ne ba abinda ya iya, nace ta zabi daya ta aura taki ai gashi nan yanzu garin shegen kinibibi da taurin kanta ya ja mata,ni na haifi Naila amma kowa yasan halinta bata ji ga taurin Kai,gaba daya Dana sanin kaita wajen ubana nake,ya gama kashe min yarinya,idan na tuna Alhaji Ibrahim da yake son auren Naila amma ta koreshi mutumi me kudi taki yarda da shi idan na tuna abin nan sai naji Naila ta sire min....Umma ta saki kuka yiiiii.....tace raina baci yake,cikin masifa tana zaro Idanuwa nace sabo da haka ba Wanda zai je mata.
Yarinyar Nan sabo da rashin gaskiya ta fita da atamfa a jikinta suka tafi ashe aski taje aka mata tayi shigar Maza kawai Dan ta siyar da magani,gashi Nan taje gidan yari bangaren Maza a matsayin namiji Dandaudu yanzu so kuke muje a tona mata asiri cewar macece? Billahillazi idan suka gano duk sai kotu taci kwal uban mu
Mohsin Yana mamakin halin Ummansu yace amma Umma da taje Abuja Inda kaddarar ta fada mata ba kece kika ce taje ba tunda Abuja ne zata samo kudi,Sai nace taje ta shiga matsalar me gida? Kaga karka dameni wallahi zan dura Maka ashar tashi ka ja yarka ku bar min gida,Mohsin mikewa yayi Yana gyara Karin gugan shaddarsa milk ya dauki Amal yarsa ya sabata a kafada ya bar gidan ransa a bace.
Direct Inda babansa yake aikin gadin petrol din turawa da suke aikin kwalta da shi,can ya nufa da yamma likis,Babansu irin dolayen Nan Wanda haka Allah ke hallitarsu, wasu gasu nan ne dai,Mutane suna zuwa satar petir din shi yasa suka zuba masu gadi,yau abokan aikin nasa basu zo ba sai dare shi dama da safe yake nasa zuwa yamma,Yan iskan gari ganinsa wani dolo sai suka Masa wayo suka samo aron jaki harda Mangala a Saman jakin sai kace a kauye suka zubo gallon 50ltr guda biyu suka taho Abban su Naila yana can Yana dolancinsa ya wani kwanta a Jikin bishiya ya saki baki har suka zo suka saka tiyo suka ja petir din sai da suka cika jarkokinsu sun Dora tsaf a Saman jakin kenan ya farka,daga nesan ya musu magana Kai lafiya barayine? Matasan barayin petir suka ce a'a dama petir muka kawowa turawa ko zasu siya, da masifa ya dinga korasu da hannaye Yana ku tafi ba'a so ba'a so baza su siya ba shegu sarakan son kudi sabo da a siya da araha ku tafi,suka juya da jakin da jarkokinsu cike da petir din da aka sashi gadi,Mohsin yaga duk abinda ya faru Yana Saman lifan dinsa da yarsa Amal a gabansa shi kanshi wannan abin na Abbansu ya bashi dariya matuka mutane sun saci petir Yana kwance Kuma sun Masa wayo kiri kiri ya kore su da kansu,barayin suma suna barin wajen suka tsaya suka dinga sheka dariya kamar ba gobe gashi motar tank ce ta petir bare a gane an sata.
Mohsin nan ya karaso wajen Abban nasa sannan ya sauka daga kan machine din,Abban nasu ya kalle shi yace Mohsin idan na kalleku sai naga kamar ba ni na haife ku ba kyawawan yara Yan gayu ga nutsuwa kar dai ace na yabi kaina amma na iya tarbiyya,dariya Mohsin yayi yace Abba Kaine mana kana gani muna kama ma,Abba yace a'a yanda nake kamar birin da ake wasa da shi ta ya muka yi kama gaku dogaye charas da ku amma ni kana gani kafata ma kamar fatar Kura,Mohsin Yana ta dariya ya gaida Abban nasa yace Abba wai baza aje wajen Naila bane?
Fuska Abban ya bata sabo da Umma ta zuga shi, yace babu me zuwa yanzu sai Nan gaba,Mohsin yace a gidan yari fa take Abba,ah idan sun kulleta su jefa mukullin a rijiya Dan tani kar ta fito a kulle ta har kwatagwan, uban waye yace ta Maida kanta namiji shedar bata da gaskiya ,Mohsin shuru yayi kawai ya juya zai tafi kenan sai ya tsinci Muryar Abba yace zo ka bani Dari biyar ni,Juyowa yayi tare da zaro dubu daya ya mika Masa ya juya ya tafi,Abba dai kwanciya yayi ya koma baccinsa yace barayi ku kuka sani Kuma, ato idan kuka sata Allah Yana kallon ku ni dai nayi iya yina, ya lumshe Ido sai bacci
Mohsin gidansa ya koma duk ya damu Yana shiga Dan gidansa me kyau madaidaici yasha tiles ko Ina,ga matarsa Hanan me tsafta da ita ko Ina Kal Kal Yana kamshi,sanye take cikin kana Nan kaya ta matse ta tsuke gata da kyan diri Yar gayu ce ta gaske,Yana shugowa Palo ta mike ta rungume shi hannayensa yasa tare da zagayeta tsam a jikinsa Yana shakar kamshinta,fuskarsa ta karewa kallon tana Masa wani kallon so a hankali cikin salo ta furta waye ya taba min mijina,Amal ce ta kwalla ihu tana ture Hanan tana taba mata Daddynta,dariya suka yi Hanan tace Sorry Amal ta matsa gefe Amal ta koma wajen Daddy dinta ta makale,zama suka yi sannan yace kinyi min zobon kuwa? Fuska ta yatsina tace kayi hakuri na gaji ne shi yasa,Ya danji haushinta sabo da bai taba cewa tayi Masa Abu tayi ba sai idan itace taga dama, shuru yayi kawai.
Cikin gidan yari dake garin Kano,lungu da Sako ake tafiya da ita an tasa keyarta gaba sanye cikin Kayan dake jikinta Wanda aka kamata dasu wato wandon jean blue na Maza gashi barmeme katon gaske,sai riga me dogon hannu da wata rigar jean din a sama itama me dogon hannu komai na Maza ne a jikinta har takalmi,sai hula da ta saka irin ta Yan acaba a kanta, sai ka rantse da Allah dan kyakyawan saurayi ne,sai dai ace Yana kalar mace amma ba me tabbatarwa macece.
Ko nononta ba'a Gani ta sa wani yankin kyalle ta dame kirjinta tasa seletape ta zagayo tun daga bayanta har zuwa gaban kirjinta ta manne breast dinta da fatarta dam sannan ta sa vest ta Dora riga ta sake Dora wata rigar me nauyi ta jean da ta tafi da ita.
Suna tafiya amma taki sauri wani jibgegen namiji ne wanda yake Ma'aikaci ne a gidan yarin kana ganinsa kaga rashin mutunci zalla tsawa ya dakawa yarinyar matashiyar burdurwa tunaninsa namiji ne yace sauri mana.
Allah ya taimaketa basu ce ta cire kayanta ba sannan basu mata komai ba har aka gama case din tare da yanke mata hukunci,Allah ya amshi adduar Naila basu ganeta ba,dama tsoronta kenan shi yasa kullum a addua take kar a gano macece ita.
Naila ta fara wani uwar tafiyar kamar Dandaudu tana wani yanga tana doro tana kwambo ta sake rage saurin tafiyar tata tana wani gadara tana ciccije lips,wata mahaukaciyar tsawa Ma'aikacin yayi yace zan sassaba Maka kamanni shege criminal,Naila ko a jikinta tana jin mutumin yana cewa an kaika aiki gidan me kudi ka kashe uban gidan naka kayi asara,gashi hukuncin daurin rai da rai ba fita, ka godewa Allah ma duk bangaren masu daurin rai da rai suna shanawa, yana ta masifarsa.
Ko a jikin budurwar sai juyowa ma tayi fuskarta dauke da murmushi sabo da tsananin kyawun wannan budurwa shi kanshi Ma'aikacin kasa kyafta idonsa yayi yana kallonsa,Budurwar ta kalleshi tayi Muryar Maza tare da furta da Allah akwai Yan Daudau Irina? Ni Dandaudu ne,harka ce ta Takashi akeyinta,ni idan ba Takashi bazan iya rayuwa ba,ni yanzu ma breziyya nake nema haba sai kace muna Maza ne, kirji wani rashanene haka sabo da Allah, Dan kana gidan yari sai a Maida ka akuya sabo da Allah Kalli fa ni Abu ba kyan zubi ba sai kace an dura ruwa a bakar Leda ba a gane farkonsa da karshensa yanzu kafin na fice daga gidan nan ai sunyi muguwar faduwa sun zube a kasa ku taimaka min karku rage min farashi gandroba kuke ko me,karku ganmu Maza ku raina mu ni dai na koma mace tun da dadewa ehe, ku shigar damu wajen gomnati a samo mana brazeyya available mu Yan Daudu,kar a barmu suyi zubar gado gashi Allah ya kawo mu rayuwa cikin gardawa, wallahi Wanda ya taba ni ban yafe ba ehe.
Har ga Allah Ma'aikacin ya zaci Dandaudun gaske ne,yace Kai ya sunanka? Naila tayi fari irin Dandaudu tare da furta Tantiriya nake idan ya Maka wahala zaka iya cewa Terror, sunan da aka yanka min rago Kuma Jamilu
Ma'aikacin sai yanzu ya daina kallon Dandaudun kawai ya kwashe shi da Mari, Naila ta dafe kumatu da sauri ta saki Kara tace ya shige ni wlh Allah ya Isa Idan na yafe Maka Kabila nake,Idan na yafe Maka kace ba Sunana Jamilu ba kace ba Yar Nigeria bace ni,Ma'aikacin kamar Allah ya aiko shi ya samu budurwa ya fara jibgarta tunaninsa Dandaudu ne amma abinda ya bashi mamaki laushi jikinsa,sai yayi tunanin ko Dan yaro ne,tsayawa yayi ya daina dukan ya shiga kallon hannayensa yanda yaji Laushi,sai da ya gaji sannan ya jata a kasa kiiiii.... ya jefata cikin wani daki Wanda yake cike makil da maza ridi ridi ba masaka tsinke, can gefe Naila ta koma,cikin Mazan wani Baki wuluk idanuwansa jajir dasu me suna Mula yace Kai ya sunanka,Naila ta tayi karairaya tare da furta Jamilu, Nickname Dina Kuma Tantiriya,lokacin Ina soya doya a Tafa bakin tasha na samu suna Tantiriya
Wani a ciki shima DanIndo shine yazo tare da make bakin nata yace rufe mana baki ko yanzu na yaga Maka baki gida biyu uban me ka yi aka kawo ka nan Dandaudun banza? Nan bangaren ko wanne ka gani Yan hukuncin daurin rai da rai ne, Naila tace sharri aka min na kisan Kai,DanIndo yaja tsaki yace sharri ai gwara ma da kashewa kayi shine ka yi jarumta amma sharri aka Maka, ko ba komai sharrin yayi irinsa muke so,Amma wallahi da ace bashi kaci aka kawo ka nan babu ruwanmu da yaro ne,ba ruwanmu da Daudunka da sai na kusa kashe ka a gidan nan amma tunda harka ce ta kisa wannan shine dai dai, da Allah zai sa ka fita da na maka hanya an baka bindigar aiki,ka Ganni nan Hirer killer ne ni nan.
DanIndo ya sake dukan kirji yace billahillazi gidan yari da ka gani a wajena ya zamar min kamar gidan gado Kuma muna da yawa irinmu dan uban babanka Jamilu,Naila ta saki baki tana kallon ikon Allah,DanIndo har Yara ne da shi a gidan yarin sai abinda yace suke yi,group group ne kowacce kungiya suna da leader wanda yafi kowa iya shege da Yara a karkashinsa yana bautar da su,a gidan yarin suka hadu kawai Idan anfi karfinka shike nan sai dai ka zauna a kasan wasu Wanda suke bangaren Yan daurin rai da rai kenan.
Naila kuwa tunda aka kawota taga wasu a ciki suna ta fitowa da Maka makan wayoyi ko wanne da tasa suna harkokinsu,suna da freedom zasu iya siyen abinda suke so suci ko su Sha, har su sigari abubuwa da dama duk bangaren daurin rai da rai ana barinsu suna yi,sannan kullum akwai ranar kidan koroso za ayi rawa a cashe ta koroso,akwai ranar da Yan Solo ke zuwa suyi musu wasanni a cashe,duk wani wasanni suna yinsa,ga sana'ar hannu,ga musulmai dole suje makarantar addini Data boko, bangaren mata ma daban na masu ciki daban,duniya guda ce,amma duk Wanda su masu daurin rai da rai ne to sunfi kowa more rayuwa a ciki sabo da su an San har abada ba fitowa,sabo da nishadinsu aka tanadar musu abubuwan nishadi,haka lokacin maulidi ma ba a barinsu a baya.
Naila tana ta Shan kallon Yan iska iya Yan iska,a ranta tace dole na zama tsagera Tantiriya,a Nan sunana na daji Tantiriya zai min amfani,bangaren daurin rai da rai ko ma'aikatan ciki basa shiga wajen sai da dalili sabo da zasu iya kashe wasu iya Kaci dai hukunci daya ne dai Wanda suke ciki daurin rai da rai tunda yanzu in ance Wanda ya kashe a kashe shi to fa ba a kashewar, gomnati bata sa hannu, a haka ma masu kwakwaran hanya da kudi ake fitar dasu ba a sani ba.
Tantiriya dai ganin an dameta da kallo suna nema su ganeta sai daki ta canja na wasu malamai ne Wanda kaddara ta fada musu, su biyar ne a dakin shi yasa ta koma can taga suna da tsoron Allah baza suyi mata komai ba,Bata son cudanya da mazan. malaman ban sai kallon Naila suke tunaninsu Namiji ne Dandaudu,Sallama tayi da Muryar data canja ta dole ta Maza amma duk da haka sai aji kamar ta mata, Malaman Nan tana shugowa duk wanda ya Kalli Jamilu Terror sai yaji gabansa ya Fadi sai yaji Yana wani son Dandaudun,gaba dayansu,basu sake shiga wani hali sai da Naila tayi magana, babban malamin cikinsu a kalla zai Kai 50yrs a hankali ya hadiyi yawu wani tsoro ya kamashi sai istingifari yake Yana furta a ransa Allah na tuba na kamu da son Dandaudu Allah ka kubutar dani,shima Malam Jilani Yana kallon Jamilu Terror sai kuwa yaga ya saki murmushi,wani narkewa yayi a zaune wani matsananciyar kaunar Dandaudun yaji lokaci guda,Malam Usama kuwa har baya son ya kyafta Ido da kallon Yaron Dandaudun,Naila kuwa dariya take a ranta a fili kuwa ta maze,wani gadon karfensu ta ja gefe can karshen bango ta Kai bed din ta kwanta a abinta.
Babban malamin Sharu ne ya Kalli Dan uwansa Malam Usama ya rada Masa kasa kasa tare da dafe saitin zuciyarsa yace Akaramakalla kana jin wani masifa data ke neman fada min kamar ni da tilawata izu sittin naji me kalar Dandaudun can ya birgeni namiji ne fa,Ina kallonsa naji zuciyata ta hau bugawa wani kaunarsa ta kamani yaro namiji Dan uwana kamar Dan cikina ni malam,ku sani a addua Dan Allah,Usama ma kasa kasa yace nima Dan ubanka haka naji gaba daya sai naji ya tafi da imanin....da sauri ya danne bakinsa da tafin hannunsa, yace wannan jarabawa ce Allah zai mana mu halkanta mu dukufa da addua,Naila ce suka hada Ido da Malam Jilani ta saki wani murmushi,Jilani kirjinsa ya dafe ya fado cikin su Malam Sharu shima Murya kasa kasa yace yayi min murmushi wlh sai naji sonsa ni dai na shiga uku barin dakin nan zanyi,shima Alaramma Garzali Yana satar kallon Naila Yana dauke Kai,Naila ta daga Masa gira daya tare da kashe Masa ido,Zuciyarsa ce ta fara bugawa da sauri Kafafunta ya kalla sak irin na mata ya bude baki,abinka da an Dade ba a hadu da mace ba ji yayi kamar ya rungume Jamilu Terror, ai tashi yayi ya fice daga dakin Yana salati a ransa,shi kadai uban zufa ya hada
Yace Ina zan sa kaina yau naji Ina son Namiji,a daren malam Jilani yace saukar Qur'ani ya zama dole, a daren haduwa sukayi kowa ya bude Qur'ani kwana suka yi suna addua Allah ya cire musu son Da namiji Jamilu,Naila tana ta baccinta gefe daya ita hankali kwance ta samu dakin malamai ba ruwanta,su kuwa suna ta surfa addua akan Allah ya tsare su da Jamilu.
Washe gari da safe mazan gidan yarin masu uban yawan masifa Yan matasa dattijai,tsofaffi duk gasu nan iya kallonka da munana da masu kyau duk gasu nan,duk kalan laifinka akwai ubanka a ciki ko wanne da bangarensu, bangaren mata daban na maza daban,haka ranar ziyara sai an gama da maza sannan a bude mata ba Wanda ke haduwa da wani tsakanin mata da maza,gashi Sabo da lalacewar ta kasar mu dakuna sunyi kadan,toilet,komai babu na kirki,haka uniform ma babu sai wata riga da ake bawa Maza lokacin ziyara,sai sutura kayan gida amma basu wuce kala uku ko hudu,haka bangaren matan yawanci basu da bra,wasu Kuma suna da ita,wacce tafi wata karfi ma zata kwacewa wata ko an kawo mata daga gida,Naila dai itace mace daya kwal a bangaren Maza Wanda babu Wanda yasan Hakan har Ma'aikatan kaf a namiji ne Kuma ana zargin Dandaudu ne,Naila bata da ko bokiti ,gashi wai a gidan Yari zata yi gayu.
Yanda take nunawa Dandaudu ne kawai, tana zaune a cikin dakin Malaman tace akwai ruwan zafi? Ya Sheikh bana tsarki da ruwan sanyi sabo da na koma mace ni, na hana kaina amfani da ruwan Sanyi,tana magana tana zuba uban karairaya wai dole Dandaudu ne,gaba daya malaman Nan suka saki baki suna kallon Jamilu duk ya tafi da Imaninsu,cikin rada da tsoro Malam Sharu yace addua bata karbu ba mu sake dukufa wlh, Mallam Garzali ya a hankali ya saci kallon Jamilu sai kuwa suka hada Ido,fari tayi Masa,da sauri ya yayiwa Sharu magana kasa kasa yana yi min fari wallahi,kansa ya sadda kasa duk ya rasa Inda zai sa kansa.
Naila ce ta shiga aika musu da fari tare da dage musu gira,Kasa karatun suka yi,Kamar ruwa ya cinye su ba Wanda yayi motsi,sai zuwa mazan bangaren nasu keyi suna kallonta ana labarin an kawo kyakyawan Dandaudu Dan matashin yaro,kowa yazo sai ya tafi da kaunar Dandaudu Jamilu a ransa sabo da kyau da farin jini irin na Naila,Naila taga suna ta zuwa kallonta ita bata sani ba,tace bayin Allah ruwan zafi nake tambaya zanyi tsarki mu yanda muka koma mata ai mata sai da ruwan zafi harda yin tafi da hannu Irin na Yan Daudu,suka dinga tuntsira mata dariya ganin namiji matashi me kuruciya ta karfi ya koma mace, a dakin malaman ba Wanda ya bata amsa karshe ma kowa Uzurinsa ya fita,Naila tashi tayi tana tafiya tare da zuba hannayenta a aljihun bujen wandonta ta fito
Ko Ina mutane ne lungu da Sako ba masaka tsinke,Naila tace ashe duniya ce guda a gidan Yari,tana zuwa taga uban layin botikai da fanteku harda languna tun na zamanin da,tana zuwa ta dauki botikin wani na roba an cika shi da ruwa ta dauke ta Kara gaba, da tambaya ta samu taga Toilets gasu nan ko wanne ta leka duk an lalata su wasu Kuma Kashi ko Ina dama maza ba tsafta ba wasu,Naila ta rasa inda zata shiga dole sai da ta wanke toilet din sama sama sannan tayi wankan ba sabulu ta, ta daure kirjinta tam tam da yankin Atamfa ta Maida kayanta ta shirya tsaf sannan ta fito ta Maida botikin,wasu shahararrun kartai suka taso zasu yi mata duka Allah ya kawo DanIndo wanda kowa tsoronsa yake a gidan mugu ne na karshe,yana kallon mazan yasan yaran Goje ne,yace me Jamilu ya muku? suka ce ruwa muka ebowa Goje tun safe muke layi kafin muje mu dawo ya dauke yayi wanka,Naila tace ku fadawa Goje din Dan babansa na dauka kayan gomnati ne muna da hakki,dariya wasu suka dinga yi da kyar DanIndo ya kwaci Naila yace ku bari zai zuba masa,wani ya gama buga ruwansa Sabo da zalunci Dan Indo ya dauke ya zuba a bokitin Goje yace kuje,Ya Kalli Jamilu Terror wato Naila kenan yace jeka ka bugawa yaron can wani ruwan
Naila tace bazan buga ba,wani gigitaccen Mari Dan Indo ya hada mata kumatu biyu sai gani akayi Jamilu tuni ya fara buga ruwan tana kuka sai da ta cika botikin sannan Dan Indo yace ware daga nan.
Dan Indo bai taba jin fata me laushin ta Jamilu Dandaudu ba,ya tsaya sai kallon tafin hannunsa yakeyi shima Yana mamaki,Sam ba fatar namiji bace da shi.
Naila tana sakkowa sai ga wani Ma'aikaci ya tari Naila yace kai waye da za a hana Hawa Saman tuka tuka kazo ka hau, uban waye ya aikeka? Naila da taurin Kai take kamar ba ita ke cin duka ba,ta Kalli Ma'aikacin ta nuna kanta da yatsa tace nice Tantiriya Jamilu ko a garinmu haka sunana yake kaina akwai kwari ba a cina da yaki,ma'aikacin ya Kalli Naila an zagaye su ana kallo,yace Zaka ga Tantiriya munga Iyayenka a taurin Kai ma sunyi laushi a nan gidan bare Kai da ka Maida kanka Dandaudu gafalalle, Naila tace banda ni cikakken Tantiri ne ni Ina kallon ku Ina Maida kaina namiji,Kai Ma'aikaci kayi a hankali zan iya tsille ma takashi ato, su kansu ma'aikatan tsoro suke ji,juyawa yayi zai tafi, Naila tace nayi marking dinka sai na sa maka guba,sai na farke Maka takashi,Dani kake zance,ma'aikatan sun Saba da tsagerancin Yan bangaren daurin rai da rai tunda suna gani shine karshen hukuncin,dole ya tafi.
Naila ta fashe da kukan karya tace Allah ka Saka min ni Jamilu Ina ganin rayuwa Yar Takashin ma ban samu ba tunda nazo naki yin farin jini,ana ta kyalkyala dariya,tace Mummy data yi sanadin zuwana gidan nan ya Allah kasa Danta ya mata dukan tsiya watarana.
Akwai Yan Daudu da yawa a gidan Yari da Kuma Yan luwadi wasu ma a gidan suka lalace sabo da rashin mace a kusa, tunda suka ga Jamilu Tantiriya gaba daya sai hadiyar yawu suke gashi kyakyawan gaske komai irin na mace gaba dayansu sai kaunar Naila,har da Wanda ke ciki masu hanu da shuni sai suka fara neman gindin zama wajen Tantiriya Jamilu,Naila a ranta sai dariya take shekawa su sun zaci namiji ne kowa ya kaimu da sonta har Wanda ba Yan luwadi ba.
Rafeeq zaune yake gaban Mahaifiyarsa Mima wacce ke faman kallonsa tana bin Aljihunsa da kallo tana zaro idanuwa tana kallo tace banga Aljihun ya dago ba? Na shiga uku kar dai ace haka kazo hannu yana dukan cinya, Rafeeq ba tare da ya sake cewa komai ba ya jefa hannunsa a aljihu Kudi ya zaro Wanda sun kusa dubu hamsim ya Mika mata,jiki na rawa kamar yau ta fara ganin kudi kamar ba a gidan kudi take ba ,Allah ya maka Albarka wannan waje naka na Shawarma Allah ya karo customers
Sam baka yi kalar me Shawarma ba wlh yaro kamar Dan gidan Salman Khan kalar kudi amma ficika babu,Yan mata sai rububi aljihu ba komai wannan kusan dubu hamsim din wata nawa kayi kana Tarawa? Rafeeq wani takaici ne yake kamashi a duk sanda Yazo gidan iyayensa,mikewa yayi yana Shan kamshi fuskar nan a murtuke da kyar ya iya bude Dan bakinsa yace na wuce ni yana cewa haka ya fice daga daga katafaren Palon Mima din Wanda ya gaji da tsaruwa, compound ya fito motoci ne gasu nan iri iri a gidan masu tsadar gaske gidan ko Ina sojoji ne ke tsaronsa kana gani kasan na babban Soja ne gidan..
Gate aka wangale Khalid babban Da a gidan ya shugo da motarsa lafiyayya,yana yin parking ya fito cikin kakin sojojinsa ya zuba kyau ya nufi wajen Rafeeq dake hanyar fita,Rafeeq Kai dai baza ka canja hali ba wlh kana ganina na shugo zaka tafi ai ka tsaya mu gaisa ko,Rafeeq juyowa yayi da kyar da shegen Iyayinsa ya mikawa Khalid hannu suka gaisa kana gani kasan Yan uwa ne na jini ba karya suna kama sai dai Rafeeq yafi Khalid kyau na gaske,sannan yafi gayu Dan gayu ne shi sumarsa ma askin Yan duniya aka mata,suna gaisawa ya juya yayi tafiyarsa ya bar Khalid a tsaye da mamaki yace yaron nan fa takamarsa ta fara yawa nema yake ya Koma kamar Spark, tsaki yaja ya wuce abinsa.
Shawarma Joint me kyau da shi Wanda ke dauke da katuwar wata rumfa an zuba kujeru da table masu kyau na Passion Wanda Idan mutum na bukatar zama yaci a wajen zai zauna,haka daga ciki ma akwai katon daki ya gaji da alatu Shima ciki kujeru ne da table na Yan gayu na cin abinci ga masu son zama cikin sirri,daga kofar wajen kuma ga hotunan abinda ake siyarwa nan shawarma,burger,chips and chicken da kayan sha Kuma, aikinsa yake yana ajiye Dan littafin Menu karami Wanda ke rubuce da iya abinda ake siyarwa yana bin ko wanne table yana ajiyewa da sauri,sabo da yana da lecture 4 to 5,a hankali wata mota me kyau tayi parking a gabansa da sauri ya barwa yaransa aikin ya koma ciki ya shirya cikin kana nan kaya masu kyan gaske ba karya yayi kyau ya fito rataye da jakarsa ya shiga gaban mota,ko kula abokin nasa baiyi ba,a hankali Abokin yace Rafeeq halina da Kai yanga sai kace masifa magana ma ta gagara wlh har mamaki nake da ake zuwa joint dinka siyen Shawarma Kai da Spark halinku baiyi ba,Spark ma ya fika rainin hankali duk da Yayanmu ne amma shi kake bi wlh Dan wulakanci ne turai ta kwance Masa Kai,mutum kullum ba Rahma ga shegiyar yanga kamar Dan gomna ga bala'i Kuma a gidan ma Spark ba Soja bane kaima haka amma kunfi sojojin ma,kaima ka koyi halinsa sabo da kuna gadara da kyau ko me oho, ka kyale spark yayi ya fika indai kyau ne,gashi da kudi shi idan yayi ba matsala tunda ya fika komai, shi dai Rafeeq ko kala bai ce ba wayarsa ya zaro Samsung yaci gaba da dannawa abinsa,a hankali cikin muryarsa me Dadi ya furta next month zanje Kano,me zaka yi? Ban taba zuwa ba yaron da akace yazo aiki ko ziyara ko me ya sawa Daddy guba an Yanke masa daurin rai da rai,yace kasan lokacin Makaranta sun Kai mu Egyft branch dinsu,so ban San yaron ba ban ma taba ganinsa ba,Islam Abokin Rafeeq yace Kai mene naka a ciki? dama Yan aikin nan Yan iska ne zasu iya gashi ance Dandaudu ne ma,Rafeeq yace Yaya Spark ne zai aikeni can wai yana da ja sabo da yasan Mummy dinsa yasan Halinta,yasan Kuma halin da suke ciki da mijinta Daddy, to me zaka masa Dandaudu na tsani Dandaudu? yace zanje ne nayi masa Yan tambayoyi ance sunansa Naila Hashim naji gidan Jamilu,Islam yace alright amma da mota zaka je? Kasan bani da mota muje ka rakani kawai,Allah ya kaimu no wahala,shi Spark din bazai bamu kudi ba? Yama bamu fa Yana accnt,tun daga haka Islam ne kadai yake labarinsa Rafeeq bai iya magana ba.
Naila tana gidan Yari kwananta biyar taga zalunci iri iri,ma'aikatan ma Idan kayi laifi zasu iya maka duk muguntar da suka ga dama iyakaci Idan ta asibiti ce a kaika asibitin gidan kason,ga wahalar ruwa,sai mutum yayi sati baiyi wanka ba sabo da kasar tamu ba ci gaba,kazanta kadai ya Isa ka kwashi cuta,komai yayi karanci a ciki,ga mutane masu laifi sunyi yawa ba wajen Saka mutane tunda Wanda ya saci akuya ma kaishi ake gidan Yari,a masu kudinmu Babu Wanda zai Kai musu agaji ya gyara musu tuka tuka ko toilet da dakin kwana musamman gomnati wannan hakkinta ne,musamman bangaren maza yafi Muni da kazanta za a hada mutum biyu a sarka daya a daure su ko Ina zasu je tare Idan daya zaiyi Kashi ko fitsari dole agaban daya zaiyi ko mene,Hakan yasa da yawa sun zama Yan gay suna Neman Yan uwansu maza haka matan ma da yawa Neman junansu suke maimakon a samu gyaran Halin sai Kuma a lalace a ciki,harkar daba da rashin gaskiya wasu duk a ciki suke koyowa,rashin kunya,taurin Kai da fitsara iri iri duk koyo akeyi a cikin gidan gyaran hali,Naila tana zaune a jikin wata bishiya sunci aiki sun koshi tun safe suke noma a can wani bangare suna gyara ciyawa,sun hada uban zufa,Basu samu Salama ba sai da suka yi nisa,duk haskenta tayi Dan duhu , jikinsu furu furu,Dan Indo ne ya zauna kusa da ita su ko a jikinsu har kiba ma wasu keyi a ciki,Naila bata San sanda hawaye ya fara zubo mata ba.
Dan Indo ya kalli Jamilu yayi dariya sosai yace ashe dai Jamilu Tantiriya Kai karamin dan iska ne? Da kace baka ji kai Tantiriya ne, Naila tana share hawayenta tace kana gani a haka zan kare rayuwata a wannan masifar wallahi sharri aka min ban aikata niyyar ko kisa ba,DanIndo yace da ka adana kalamanka ba maganin da zan Maka,kawai abinda zan fada Maka tunda baka da karfi sai taurin Kai ka kiyaye yiwa mutane nan rashin kunya,wlh watarana Idan suka gaji zasu karairaya ka su watsar,kayi biyayya,mun fika iskanci,Kai iskancinka na Daudu ne Amma tunda kaga muna musu biyayya to kawai kayi, kana gani dai a gabanka suka sa karfe suka cirewa Hamisu farcen babban yatsa Kuma ko a jikinsu, Naila ta goge hawayenta ba tare da tace komai ba,kafin ta rufe Ido a cikinsu aka zabi shugabanni suna sasu aiki Wanda ya kamata na tsafta da gyaran wajen kamar a makaranta,mazan sun dawo da tsawa da duka sun kora kowanne aiki,Amma Naila kin tashi tayi suka zaneta kuwa Amma ko gezau da uban taurin Kai take,Inda taci Sa'a duka gidan kaunarta suke haka kawai basu San ba gender dinsu daya ba.
Indo ce ta kwala mata Kira da Tantiriya dake yanzu kowa haka yake Kiran Naila da Jamilu Tantiriya domin ita ta radawa kanta sunan gata gata da farin jini Allah ya bata kowa Yana sonta suna daga mata kafa sosai amma bata da kunya ga taurin Kai,ta matsu iyayenta su kawo mata ziyara ko zata samu kayan canjawa da Dan kudin siyen abubuwa,a haka sai da taga dama sannan ta mike ta shiga cikin Yan gidan suka ci gaba da aikinsu amma sun rasa dalili Bata son cudanya da Maza sai ta ware kanta gefe,sannan namiji Bata bari ya riketa sai idan Bata sani ba,Hakan ya tabbatarwa da kowa ta shahara a harkar Daudu.
Naila tana noma ta Kalli wani Dan saurayi matashi kamar sa'anta ne amma ya fita girma da komai namiji da mace ba daya bane ko a halitta, suna Shiri dashi Amjad, tace Amjad ban taba ganin mace ba tunda nazo gashi har na kusa sati,oh ashe kallon mata ma Rahma ne,dariya Amjad yayi yace wlh ai in ba a Yan uwanki mace ta zo Miki ziyara ba baza kiga mace ba,Kai da kake Dandaudu Ina ruwanka da mata,Tantiriya tace to ai munfi Jin dadin rayuwa cikin mata sune muke kama, Allah sai dai irinku Maza haba shi yasa naga maza suna ta Neman junansu.
Ni a dangina ma bamu da mazaje Samari sai wani Dan banzan kanina me tafiyar tolo tolo sai uwata sai ubana, Wanda zai iya zuwar min Yaya Mohsin ne,kaga Ina da saurayi Kuma nasan zaizo, Amjad Baki ya tabe tace Dan uwanka ne fa namiji,Jamilu yace kamar ka sani yanda nake son Gambo beauty sai baza ayi ba ta furta da sugar Yan Daudu,Amjad ya sheke da dariya yace kunyi asara wlh.
Amjad ya sake cewa hala kai Hariji ne ne ko kana sex tun a gida? Yo mu yai muna layin gidan Kashi cewar Naila.
Naila a ranta tace a gidan Nan nasan ma cuta ta kamani ta ciwon sanyi sabo da kazanta wlh har kaikayi nake ji a gabana tabbas na kamu da ciwon sanyi.
Wani shahararren Dandaudu ne da ake kira da Skoler yazo wajen Tantiriya Yana rangwada yace Kawas ya kamata na fada miki kiyi taka tsantsan da toilet mu mata muna kamuwa da ciwon sanyi in kinji gaba na kaikayi sai kiyi magana zasu kaiki asibiti a baki magani ahayye ya tallafe kirji ya zaci da gaske Naila Jamilu ce,suna ta hirarsu har kusan dare sannan suka hau layin karben abincin dare abincin Dan kadan gashi ba Dadi,masu kudi suna ta siyen abinda suke so,a hakan ma Idan wani yafi karfinka ya samu ya masgeka ua kwace ya hade du ya cinye.
Naila tana layi aka zubo mata Miya da Katon sandararren tuwon masara,ta Kalli abincin ta bata fuska tace Kai masu girki kuji tsoron Allah Miya kamar yawun kaza haka gomnati tace kuyi? Wani Ma'aikacin cikin fursunonin yazo zai kwade Tantiriya Naila da duka sai yaji ya wani shiga ransa sai ya koma yayi mukus ya juya, amma Naila harda tana Allah ya Isa wlh ma'aikatan har sun gaji da Halin Jamilu Tantiriya duk abinda akace kar yayi sai yayi, duk mugunta iri iri Amma bata jin magana,rashin kunyar ta da taurin kanta kullum karuwa yake sabo da basa taba dukanta kowa jinta yake a rai tunaninsu ma namiji ne.
Washe gari da yamma yau ta samu tayi wanka Dan Indo ne Ara mata sabulu ta fito gabanta Yana ta mata kaikayi cutar sanyi ta kamata,ta rasa Inda zata sa kanta gashi ba abin ta fada ba a gano ta,Dama kayan Dan Ido ta Ara ta barma a jikinta a wanke suke,ta wanke nata tas ta shanya su,kayanta suna bushewa ta koma toilet ta shirya ta Saka abinta, yau fes take sai kaikayin da gabanta ke mata na hauka cikin dakinsu ta shiga Wanda yake da malamai a ciki,gado ma Babu na kirki wasu duk a kasa suke kwanciya ko shimfida babu a masu kwanciya a gado har Tantiriya Jamilu,,ta Ari bargon malam Sharu tace bani da lafiya bani aro ta kwanta ta lullube jikinta da shi a ciki ta samu ta tattale kafa ta hau sosa gabanta ba ji ba gani,a hankali kasa kasa tana cewa a bani cokali wannan susar sai da cokali.
Naila tana susarta tace yau Bado Yana cin ubansa da Susa,a fili Ashe ta furta Dariya su Malam suka yi sun zaci iskancin Yan Daudu ne kawai,Malam Jilani yace mene Bado? Naila tace gaban mata, ku baku ga yayi kama da Bado ba? Bado wannan Abar da take fitowa a cikin ruwa,Idan baku San Bado ba kuje kuyi bincike,malamai sai kunya ta lullube su,Malam Sharu yace Dan Allah ka koma cikin Yan uwanka Dandaudu Bai kamata kazo cikinmu ba muna malamai.
Rafeeq gida ya shugo cikin takunsa na yana kamshi yayi Sallama a gidan ShimaA wannan gidan da gani kaga gidan me hanu da shuni gidane na gasken gaske komai na more rayuwa akwai duk da gidan da iyayen Rafeeq suke yafi kyau sosai Amma wannan ma ba baya ba,ga motoci nan hadaddu masu tsada daban daban,Rafeeq yana shiga katafaren Palon gidan wata matashiya ce baza ta wuce 50yrs ba da kuruciyarta kyakyawa son kowa kin Wanda ya rasa ga kyan Kira da diri,tana ganin Rafeeq ta saki murmushi tare da amsa sallamarsa,kallonta yayi ya zauna a hankali yace Aunty barka da hutawa,Wacce ya Kira da tace Dana ya aiki ya Kuma school kana garin shine sai yau zaka zo min? Sai da ya dauki lokaci sannan yace kiyi hakuri Aunty Exam muke yi ne,kin San indai lafiya ai zanzo ko? tace na sani to ya school? normal Aunty,bari na kawo maka abinci,me kika dafa ne? Hmmm zai wuce tuwo ne da kyar fa ma ya bari nayi tuwon, kasan komai dai yau ma ko kudin cefane bai bayar ba,ayi mutum kamar talaka Wanda bai gaji arziki ba,Hawaye ne ya zubo mata tace Ina so ko Yaya ne ya so ni ya kyautata min amma Hakan ya gagara sai ma kuntata min da yake kana gani dai, Aunty wai waye naji ance an kaishi prison akan gidan su Spark? Hankalin Aunty ya dawo kan Rafeeq, tace wani Dandaudu ne marar Imani ya kashe shi,daga kawoshi gidan mutane,Aunty ta kwashe labari ta fadawa Rafeeq,Rafeeq yace Allah ya kyauta shi kam a ransa bai yarda ba Sam, yana da ja akan kisan domin yasan tsakanin Mummy da Mijinta irin zaman da suke, tace sunansa ma wai Jamilu Hashim.
Rafeeq yace hmm kawai sannan yace kina da kudi kuwa? tace da kyar ma na samu na siyan kayan Miya Sweetheart, Rafeeq ya mike tare da zaro kudi dubu goma yace kiyi hakuri da wannan kin San Yan Makaranta,ta Mika hannu Zata karba kenan me gidan ya shugo sanye cikin wata peach shadda Yar gaske yana sheki yana kamshi Shima ba wani babba bane,Rafeeq yace Sannu da zuwa wani kallon banza yayiwa Rafeeq yana daure fuska yace bana hanaka bata kudi ba,iyalina ko naka bana son shishigi,wato kana nuna min ban iya ruko ba ko?to baza ta karba ba jeka da kudinka,kafa dameni Karka bari na hanaka zuwa gidan nan,Ina daga maka kafa baka gani, Rafeeq kudinsa ya karba ya Kalli Aunty a sace suka hada Ido ya faki Ido ya tura mata kudin a kasan kujera tana kallo ya ajiye ya fice abinsa,Wanda ta Kira da Abban Na'eem da Na'eema ya fara yayyafa mata ruwan masifa yace wlh ki kiyayeni Rumaisa Ruma ki kiyaye ni banza shashasha,wato tona min asiri kike sabo da kin raini Rafeeq gani kike kamar ke kika haife shi karki manta Dan Yar uwarki ne,Yar uwar taki ma da bata son kike shiga sabgar danta in Banda masifa ma kina juya bakya haihuwa ki hakura da rike Dan wani mana yaja tsaki,tace kayi hakuri abincin fa? Bana ci ya juya ya wuce part dinsa fuuuuuu dama ya Riga yaci nama me rai da lafiya a wani joint me tsada a koshe yake abinsa.
Su Naila ana gobe ranar ziyara dukkansu murna suke musamman Wanda Suke da tabbaci za a zo musu daga gida,ita kuwa Naila bata murna domin Iyayenta Basu yarda da ita ba shi yasa suka ce ba ita ba su Kuma babu Wanda zaizo wajenta ko an kaita can,tasan halin Ummanta ,Amma haka suke ta tsafta suna gyara jikinsu kar azo a gansu cikin kazanta,Naila tana Kallonsu ta zuba tagumi a inda ta idar da Sallar la'asar Sallar ma a boye take yinta,a haka ma da ya ta shugo da Karamin mayafin a cikin wandonta a boye,duk Allah ya tsallakar da ita ba a kamata ba,Addua take Allah ya rufa mata asiri kar a tarfa ta,sai ta bari an fita makaranta take buya tana yi ba nutsuwa sabo da tsoro, kullum itace karshen fita school tace ya Allah karka bari a kamani ko a ganta da mayafi kowa yasan iskancin Yandaudu sunyi Imanin baza a kawo musu Mace gidan ba shi yasa duk suka amince Dandaudu ne,Allah yasa ma basu kamata ba har yanzu,kullum addua take kar a kamata har ta fice a gidan,kullum cikin faduwar gaba take.
Wani Wanda ake kira da Skoler Dandaudu baki har kunne ya samu Dandaudu me kyau kamar mace,wajen Naila ya karaso Yana rangwada ya furta budurwata ke wai baza kiyi wankin ba? Ai ko sabulu sai na Ara Miki ki wanke kayanki, ga wando da t-shirt Dina ki Saka,Naila tace ni ai ba Wanda zaizo min wa nake da shi Babana da Ummata sunce baza su zo min ba,nafi sa rai ma da Yaya Mohsin amma nasan halin Ummanmu ko zan mutu baza su kawo min ziyara ba,Dandaudu Skoler yace iyyee ke ki bari Dan Manzo, ai shike nan amma baki sani ba ko sun huce, kinyi fa sati daya da zuwa nan Jamilu ki samu dai kiyi tsafta ga farcenki nan sunyi Zako Zako haba Jamilu ta ,gashinka buzu buzu,ga kaya sunyi dirty gashi kina fama da susar Bado abin ai yayi yawa,sai yanzu Naila ta tuna hannunta na gabanta da sauri ta cire,Skoler yace ahhh karki ji kunyata ai daya muke nima macece irinka sosa abinki kafin Nan gaba ki aminta Dani na dinga lashe pole din naka,Ahhh ranar akwai harka ahayye chass Chass heyyyyy nanaye, fito dan Allah Jamilu Baby mu wuce.
Hannun Naila ya rike ta fisge da sauri,ya saki da mamaki yace ahhhh wannan laushi kamar auduka, billahillazi kinji za ayi bantan bala'i Dani a kanki Yar uwa,I love you Jamilu,Dan Allah ni dai Jamila zan dinga kiranki please
Naila ta Kalli Skoler tana hawayen karya gwanin ban tausayi tace nifa ba a sani sannan ba a hanani Iyayena ma hakuri suke Dani shi yasa ma da akace na kashe wani suka yarda kije kawai zanyi tunani akan soyayyar, Skoler yayi tafi tare da bugar cinya Yana fari yace shike nan Ina jira tawan ,Naila tace ba gwara ma na mutu na huta ba,gwara kazantar cuta ta kashe ni, zuciyata ta buga kawai na huta,ba na Jin magana ni yawwa ba a sani sannan ba a hanani,Suna jinsu kowa ya rabu da su,Shi kuwa Skoler ya dage lallashin budurwarsa yake Jamilu,tana ta shagwaba ,gajiya yayi ya zaro dubu daya yace ungo Baby je ki Sha lemon kwalaba ki sanyaya makoshinki,Naila taji wani dadi ta karbe tace thanks ,yace wow yimin fari Jamilu na,Naila tayi Masa fari da Ido,Kirji Skoler ya dafe yana karairaya yace zan suma bar ni haka, shi a dole ya samu budurwa namiji irinsa Dandaudu.
Washe gari bayan mata an gama zuwa ziyararsu sannan aka bude maza suma aka dinga zuwa musu suna ta murna yau sun samu abincin gida suna ta ci amma banda Naila ko kare bai zo wajenta ba ko ma fitowa bata yi ba sabo da sai Wanda aka zo wajensu suke fita,kusan kowanne anzo masa suka dinga dawowa da sabulai da omo,rezo,shaver da tarkace daban daban amma banda Naila me kaya kala Daya,ana koya musu Karatun addini Dana boko a ciki,ga sana'ar hannu iri iri,Itadai Naila sakar hannu ake koya mata a ciki da Saka kayan sanyi,Sai filin wasa Idan sunyi niyya,Naila ranar wasa tana can daki bata zuwa,duk sanda ta tuna iyayenta da Yan gidansu Kuma taci kuka ta koshi,hankalinta bai sake tashi ba sai da ziyara tazo taga kusan kowanne kato anzo masa banda ita,a Hakan ma su Dan lIndo da Yan Daudu ne suke taimakonta da sabulu da omo gashi wani satin zata fara period ta rasa Ina zata samu pad duk da sanyi ya kamata bata San ko zaizo ba ko bazai zo ba oho.
Dare na yayi sauro kamar zai cinyesu sauraye ne na hauka kamar yayi gomnati bata dauki mataki ba Yana zubawa mutane cuta,Naila sai Susa take ga cizon sauro gashi yanzu duk tunani da bakin ciki ya hanata ma yin tsaftar ba sosai ba,gashi ba wuta ma bare su samu suga haske ba kullum ake kunna musu inji ba,cikin duhun daren kowanne a kwance yake, kasa kasa take jin maza Yan gay suna numfashi suna ihunsu na Dadi ga wasu Kuma suna biyawa kansu da kansu bukata,Ko wanne daki haka suke yi Idan dare yayi,Yan Iskan karshe sai kalaman banza sukeyi suna ihu da Nishin Dadi,duk sanda Naila taji Hakan hankalinta tashi yake taji a duniya bata bukatar komai face Namiji,macece me bukata amma yau dake ciwon sanyin nata yayi nisa bata ji sosai ba ta mike sum sum ta koma dakin malamai Inda yafi mata mutunci, su na kirki ne basu aikata alfasha baccinta tayi a can.
Kafin sati biyu farcenta sunyi mugun Zako Zako duk ta fita a hayyacinta ta rame tayi duhu duk haskenta amma sai da ya ragu,ana gobe Ziyara Rafeeq da abokinsa Islam a Kano suka kwana a hotel kowanne da dakinsa,washe gari da safe bayan sunci lafiyayyen Kari ,Islam ya fito shirye cikin hadaddiyar Shaddarsa me kyau sea blue Dinkin Yan gayu na Yan zamani yana kamshi ya Saka hula kalar kayan yayi knocking dakin Rafeeq yayi yana tsaye yana fesa turaruka shi sanye yake cikin kana nan kaya masu mugun kyau na Yan gayu Riga me dogon hannu me tafe da hula bata da nauyi Sam sannan ya sauke hular a bayansa,da wandonsa fari cif cif shi ya tsuke, gashinsa ya gyara bai wani sharce ba sabo da an wani murmude sumar ne gata da yawa an kwashe bayan keyar duka ba gashi sai kadan,gefe da gafe ma an kwashe anyi wani irin gyara wajen yayi shape sosai daga tsakiya zuwa gaba sai tarin sumar me shegen tsayi an murmurdeta a tsaitsaye gyaran fuskar ya fito ras gashi da sajensa me kyau kadan sai gemunsa dan chass da shi Wanda ya kawata farar fuskarsa,abunka da me kyau gashi yana da Dan haskensa baza ace Masa baki ko wankan tarwada ba Kuma hasken ba me yawa ba,mutum gashi da cikar zati da kyan sura kana ganinsa kasan zai wahala ace ba ruwa biyu bane, yana bulbula kamshi ya fito,Islam ya Mika masa hannu suka tafa irin na Yan zamani yace let's go mun makara fa,suka fito a tare zuwa cikin motar Islam wacce ta sha wanka ta hadu suka saki kidan zamani tare da Jan motar, Rafeeq ke driving, da tambaya sannan suna duba location a waya map a haka suka Isa gidan yarin,Dan cin hanci Islam ya Mikawa masu tsaron gidan aka bude musu ana girmamasu aka basu shedar shiga ciki, suka yi parking sannan Wanda suka bawa cin hancin suka tambaya ya shiga da su har inda ake ganin Yan gidan yarin maza da aka zowa ziyara,suna ta fitowa gasu nan iri iri dattijai da Yan matasa ba kalar da Babu,Suna shiga suka fadi sunan Jamilu,Rafeeq yace Jamilu Hashim,akwai wani Ma'aikaci nan yake ya gane yace wani me kama da mata ko,ya bada Umarni aje Azo mata da Tantiriya Jamilu,Nan take Rafeeq da Islam suka Kalli juna mamaki ya kamasu,su gashi basu San waye bama Jamilu Tantiriya bare su tabbatar,gashi gidan yarin duk Wanda aka zowa ziyara a gaban kowa za ayi hira a gaban masu tsaro da sauran da ake zuwarwa ziyara suma suna ta hirar su ana jin na kowa.
Naila tana zaune ita kadai a dakinsu tayi tagumi aka zo akace Kai Jamilu fito Yan uwanka sunzo,ihu ta saki da murna tace nasan Yaya Mohsin ne,ni sanan Abba ma zai hakura ai nasan Umma ma dole zata huce,gaskiya Iyayena suna so na,gashi banyi tsafta ba haka ta fito tana uban sauri itama baki har kunne zata ga Umma,har ta fito inda ake ganin mutane Naila ta shiga zare Ido bata ga kowa nata Wanda ta sani ba,Amma kallo ya dauke mata Ido tace wai yaushe rabon da na ga mota kunga yau na hango motoci ta window,Mika tayi da hamma tace Allah mun gode maka da ka halicci Nasara ka Bawa bature ikon kera mota, ashe Kallonsu ma Rahma ne amma da kullum sai Maza kartai nake ta kallo Yan banza sai kayan wari,yau maza Kun shiga uku a wajena,ta fara zare Ido tana washe baki tace ga maza Yan gayu ba masu wari ba yau,maza mutanenmu,ana jinta ana ta dariya a wajen Banda masu tsaro duk dariyarsu sai dai suna gazawa suna danneta suke yi wai ba raini.
Kai baka ga Wanda ke jiranka bane wannan yaron baka ji wlh,Rafeeq Yana zaune yana ta danna waya ko kallon Naila baiyi ba Yana dai jin surutun kamar mace kamar namiji bai sani ba ko shine sai da Islam yace gashi fa yazo,sai lokacin Rafeeq ya dago a hankali ya Kalli Naila ya ganshi yaro ne ma matashi,da riga da wando manya na maza kayan dukun dukun wandon ma ya dan yage,Islam yasan Rafeeq bata musu lokaci zaiyi kawai shi yasa yayi magana yace kaine Jamilu?
Tace ae nine Tantiriya Jamilu mana,wajenka muka zo,ta dawo benchin da suke zaune ta zauna a gefen Rafeeq,kamar an tsira masa Allura haka ya tashi tsam ya tsaya a tsaye,cikin masu tsaron ne sunga kalar kudi harda sake mikawa Rafeeq kujera ta daban ya zauna shi daya tare da harde kafa Daya kan daya kamar yana Palon ubansa,ko kallon Naila baiyi ba,Islam ne yayi magana yace kaine Jamilu Hashim ko? tace ae a sanyaye ganin kyamar da Rafeeq ya mata,yace kaine ka je Abuja ka kashe me gidan ko? Naila tace aka yi min sharri dai sannan ni Kuma ina da gata na ba aiki naje ba,labarin Zaka bamu Muji ko zamu iya wani abu akai,sai lokacin Rafeeq ya dago yana kallonta sabo ya gane labarin nata karya ne ko gaskiya ne,mamaki ya kamashi ganinta kamar mace haka.
Amma kafin ta fara labarin wani kaikayin ciwon sanyinta ya hada ta gaba daya ta rasa inda zata Saka kanta gashi so take ta Sosa gashi maza ne a wajen sannan tana tsoro kar a kamata, a ranta tace Kai uban wa na ajiye wai in Sosa abina,a ranta tace ai da kunya Kuma a gaban maza,Zullo tayi tana daga zaune tare da Jan yaji shiiiiiiiii.......kafarta ta dora kan daya tana mutsu mutsu,taji kaikayi ba sauki dai ta mike tsaye ta sake komawa ta zauna tana so ta Sosa, duk sai kallonta akeyi banda Rafeeq da Islam ba kikawai har ma'aikatan, Naila tace gashi ba a komawa ciki a dawo Kai wannan rashin yanci da yawa yake Susa ma ba dama mutum yayi.
Bakinta ta toshe da sauri ashe maganar a fili ta furta,tunawa tayi a cikin gidan kaso su Kam Babu kunya ba shayi,Islam waya ya daga ya mike ya matsa gefe,ganin Islam ya tashi ta saci kallon Rafeeq tunaninta baya kallonta ta saci kallon mutane taga kowa harkarsa yake
Baki ta tamke kamar me tsotsar alawa tasa hannu a gabanta Saman wando ta haka ta Sosa kadan ta sake satar kallon Rafeeq da mutane ta sake sosawa da karfi,harda lumshe ido taji Kam Salama sai ta manta ma taci gaba da susarta,Rafeeq yana ta kallonta dariya ta cika masa ciki a ransa yace yaron nan bashi da lafiya,dagowa yayi da sauri ta cire hannunta,cikin muryarsa me kasa kasa da gadarar gaske yace me kake sosawa?
Kai mene haka kaikayi?a wajen neman mazan ka kwasowa kanka? ya tambaya, ko kunya ya daga masa Kai a hankali yace ance sanyi ne ya kamani Dan Allah baka taho da Dan wani karfe ba? Wani mugun kallo ya mata Wanda ba Shiri tayi mukus tana tsiri tsiri da Ido
A hankali yace sabo da kana da infection sai ka dinga Susa a gaban kowa baza ka iya hakuri ba,Naila tace a'a wlh bani da shi ya jumbo Yana kaikayi ace bazan Sosa ba kasan kuwa bala'in da nake ji,Kuna da asibiti kaje mana shuru tayi yace karka bata min lokaci ka bamu labarinka,lokacin Islam ya dawo Shima ya zauna yana Sauraren labarin Jamilu,tiryan tiryan ta basu labarinta kaf amma suma binne su tayi ta barsu a namiji ce ita Kuma sun yarda.
Wace Naila
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM
❤️❤️❤️
FREE PAGE
WANNAN NOVEL NAIRA 300 NE
Account number
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
KATIN MTN
***
'YAN NIGER GA NUMBER
+22790795939
Kar a manta da Sharhi fans please.
Ina godiya gare ku masu godiya da masu addua
AsmaBaffa