WAZEER!

Adviceful

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®AS-2023.






*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*





           *♡WAZEER¸.•💥*

          (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)





Bʏ.

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

https://www.arewabooks.com/u/realsmasher

 ••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

 


    



                25

 


#Adviceful



     Shiru Wazeer yayi yana kallonta,he could feel how the words came from the bottom of her heart,Safwa ta sake cewa "i really do love u" kasa cewa komai yayi saboda yanda kalamanta suka wani irin ɗaɗɗaure shi,Safwa tai kamar za tayi kuka tace "love me Aley ko da kaɗan ne,love me back please,tun kafin mu fara haɗuwa wallahi zuciyata ta kamu da sonka,na yi shiru ne ban nuna maka ba,na bari naga ko za ka fahimce ni,amma kamar baka san ina yi ba,ina sonka wallahi har ban san dame zan kwatanta ba.. Let's break the layer da yake tsakaninmu,ni ba abota nake nufi muyi ba tun farko,na ce haka ne saboda tunanin wata rana za ka gane ka so ni" lumshe idanunsa yayi a hankali har yayi shutting nasu off ya wani irin runtse su yana jin zuciyarsa na bugawa da sauri²,Safwa ta marairaice tace "will u love me Aley? Za ka iya bani guri a zuciyarka? Za ka iya bama soyayyata gurbi da muhimmanci? Har ka karɓeni as a girlfriend please?" Rasa me zai ce mata yayi,yanda take magana ya isa bayyana masa da gaske take,ya san mene ne son abunda bai san kana yi ba,ya ɗan ɗana so duk da ya yi ne a inda ba'a san da shi ba,a hankali ya numfasa kafin ya buɗe idonsa da sukai laushi,maganganunta sun sanyaya masa jijiyoyin jikinsa,kuma sun sa tunaninsa kullewa,bai taɓa zaton haka za ta faru ba,bai taɓa tunanin a matsayin da Safwa take,za ta iya buɗe baki tace tana sonsa ba,though ya fahimceta since from the very beginning,amma bai yi zaton a matsayinta na ɗiya mace za ta iya furta tana son namiji ba,even though ya san ba haram bane yin hakan,amma bai ma taɓa kawo tunanin za ta iya yin haka ba. Ganin ya yi shiru idanunsa kuma a kanta yasa ta kauda kai tana share idonta da ƙwalla ya taru tace "if baza ka so ni kwatankwacin yanda nake sonka ba,ko da kaɗan ne ka mayar min son zan ji daɗi,kuma zan yi farin ciki,zan san cewa ban yi so a banza ba,ban kuma so wanda bai san mutucina ba" numfashi me ɗumi ya sake saukewa still ya kasa buɗe baki yayi magana,tabbas Safwa ta bashi tausayi a yau,but 1 thing da ya yarda da shi kuma yake kallon kansa shi ne,ba zai taɓa cutar da wani ba,shi ɗa ne halastacce da ya san halacci,tun da har ita da take mace da aka sansu da kunya ta iya buɗe baki ta faɗi tana sonsa,to shi me zai sa yace ba ya sonta? Ko da ba ya sonta akwai hanyoyin da zai bi ya fahimtar da ita,ba tare da ya cutar da zuciyarta ba,ba kuma tare da yasa ta yi tunanin aikata wani abu na badai² ba,sai dai yana buƙatar lokaci ya yanke hukuncin abunda yake ji game da ita,lokaci ya ɗan kalla da idanunsa,a hankali yana furzo iska daga hunhunsa yace "i think lokacin tafiya na ya yi" Safwa na kallon ƙasa ta ɗan gyaɗa kanta,a hankali muryarta yai ƙasa² tace "ok! Sai yaushe?" Yayi ɗan shiru kafin yace "za muyi waya idan na isa gida" ta sake gyaɗa kanta tace "ok! Allah ya tsare.. Na gode" yace "a gaida Mom" ta gyaɗa masa kai,tana tsaye ya wuce ya tafi,yau kam ko get bata iya yi masa rakiya ba,yana fita gidan ta sauke wani kafirin ajiyar zuciya,a hankali fuskarta ya cika da wani irin miskilin murmushi,kafin ta haɗa chairs ɗin ta ɗauki tray ta fara mayarwa sannan chairs ɗin then ta wuce cikin gida.




*SAFWA* 



   Tana shiga parlour Umma dake kallonta cike da takaici tace "ki je Babanku na kiranki" Safwa ta kalli Umma da sauri tace "ni kuma? Me nayi?" Umma ta wurga mata wani kallo tace "sai dai kije ki titsiyesa sai ya sanar miki da kansa" waro idanunta Safwa tayi sai kuma ta wuce ɗakin Baba,tana yin sallama Baba dake ciki ya amsa yana cewa "yes shigo" Safwa ta buɗe ƙofa jikinta a sanyaye ta ƙarasa ciki tare da durƙusawa tana faɗin "Baba sannu da hutawa" Baba ya ɗago ya kalleta kafin yace "ina mahaifiyar taku take?" Safwa tace "tana can parlour" kafin Baba yayi magana Umma tayi sallama,Baba ya amsa yana faɗin "yanzun nan nake tambayarki" Umma tace "wallahi na tsaya ne na kwantar da su Asim" ta ƙarasa ta zauna tana sauke numfashi,Baba ya kalli Safwa data takure gefe yace "Safwah!" Yanda ya kira sunanta kawai sai da ƴaƴan hanjinta suka kaɗa,tace "na'am" Baba yace "kin san dalilin da yasa nace ina son ganinki a daren nan?" Safwa ta girgiza kai,Baba yace "na samu labarin akwai wanda ke son aurenki,ke kuma kince akwai wanda kike so,right?" Safwa ta sake gyaɗa kanta tace "ehh Baba" Baba yace "good.. Kin san me yasa nake miki tambayoyin nan?" Safwa tace "a'a" Baba yace "da fari na baki dama ki tsaya da samari ne saboda me?" Tace "idan na samu miji ku min aure" yace "kin san da haka?" Ta gyaɗa kai tace "ehh!" Baba yace "Safwa bazan miki auren dole ba ki san da wannan,saboda ni ma ba'ayi min ba,kuma ba zan yiwa ƴata ba,u are my only child mace a duk duniya,saboda me kina da wanda kike so kawai zan tauye farin cikin ƴata? Wannan dalilin yasa nake so ki sanarwa shi wanda kike so,idan har da gaske yake sonki to yazo muyi magana ya aiko magabatansa ayi maganar aurenku,idan ba haka ba ni da kaina zan dakatar da shi,am i clear?" Safwa tace "toh! Baba" Baba yace "shi kenan tashi ki tafi,Allah yayi muku albarka" Safwa tace "ameen.. Sai da safe" Baba suka amsa. Tana fita ta haura sama,bedroom ɗinta ta shiga tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya,kafin tasa hannu ta ɗauki sabuwar wayarta,missed calls ɗin Hamood Waziri was abunda ta gani a kai,bata fara kiransa ba ta shiga kiran Malama Gaaji ta sanar da ita abunda ya faru tsakaninta da Aley a daren da kuma abunda Baba yace mata,kan maganar turo Aley da yace tayi yana son ganinsa,yanda take mata bayani cikin damuwa,yasa Malama Gaaji ta ƙara mata ƙwarin guiwa then sukai sallama tana sanar mata a taimaka ayi mata taimakon da aka saba,ta yanda bai isa ya kalleta yace bai sonta ba kuma zai zo yaga Baba suyi maganar aurensu,suna gama waya ta shiga kiran Radhiya,tana ɗauka Safwa tace "hello ƙawata! Ya kike? Ya yau?" Radhiya tace "lafiya lau wallahi.. Ya Umma da su Bilal?" Safwa tace "kowa lafiya.. I have a gist fa" Radhiya na dariya tace "ok! Gist me,me yake faruwa?" Safwa tace "yau na sanarwa da mutumin fa" Radhiya tace "wane mutumi? And me kika sanar masa?" Safwa tace "na faɗa masa ina sonsa.. And u know what?" Radhiya da mamakin Safwa ya kashe tace "kin faɗa masa? But why ƙawata? Idan yace miki a'a fa? Kin san bazai miki daɗi ba,ni dai ina jiye miki abunda zai faru wallahi,da kin bi ta tawa wallahi baza ki taɓa faɗa masa kina sonsa ba,ko da zai yi ajalinki" Safwa ta zaro ido tace "what? Haba ƙawata,baki ga son zai ajalina bane,ai ko ke da kanki sai ki nemosa ki faɗa masa" Radhiya tace "yanzu duk ba wannan ba,yaya kuka yi da shi?" Tas Safwa ta kwashe yanda suka yi ta faɗa mata,Radhiya ta sauke ajiyar zuciya tace "to Allah yasa muji alkhairi" Safwa tace "ameen.. And kin san wani abu kuma?" Radhiya tace "nope" Safwa tace "na fa sake waya" Radhiya tace "ke don Allah?" Safwa tace "wallahi.. Wani muka haɗu da shi rannan a school,bamu haɗu bane ai da kin sha labari" Radhiya tace "wallahi fa tunda muka je gidan su Muniba" Safwa tace "yaushe zan sa rai da ganinki? I want to see u fa,akwai case da ya taso min ina so ki bani shawarar yanda zanyi,yaushe za ki shigo dai kawai muyi maganar?" Radhiya tace "do u want to see me ne haka da gaggawa?" Safwa tace "of course yes,akwai fa labarai ne,kuma idan ba haɗuwa muka yi ba babu yanda za'ayi kiji" Radhiya tace "shi kenan zan shigo in sha Allah" Safwa tace "sai kin zo.. A gaida Ammi" Radhiya ta amsa da "za ta ji.." Safwa na ajiye wayar kiran Hamood Waziri yana sake shigowa,ɗan taɓe baki tayi kafin ta ɗauka tana yin ƙasa da muryarta tace "hello! Good evening" Hamood Waziri ya amsa yana sakin ajiyar zuciya kafin ya shiga tambayarta "ina gimbiyar mata ta shiga?" Safwa ta zauna bakin gadonta tana sauke veil tace "i have a guest ne yau,shi yasa ban samu lokacin kaina ba" yace "ok! Mace ko namiji? I want to know,because i don't want u kina mu'amala da wasu mazan idan ba ni kaɗai ba,ina da tsananin kishi sai kin yi haƙuri da ni" Safwa ta zaro ido tace "laaaa! Mace ne" yace "mace ce dai ko?" Tace "anyways haka nake nufi" Hamood ya sauke ajiyar zuciya yace "ok! Yanzu hankalina ya kwanta.." Hira suka ɗan yi kafin Hamood Waziri yace "Baby ina son zuwa na ganki,and i want to see Dad,ina son gabatar da kaina.. U know na faɗa miki ba da wasa nazo miki ba,idan kin amince min cikin ɗan lokaci za'ayi komai a kaiki gidana" Safwa da gabanta ke wani irin faɗuwa ta fara kame² jin maganar da yake,jin ta kasa magana yayi ɗan murmushi yace "kina buƙatar lokacin yin shawara,right?" Ta gyaɗa kai kamar yana gabanta tace "ehh!" Yace "hope it won't take long?" Ta sake cewa "ehh!" Yace "ok! Yaushe zan zo to?" Tana kallon nails ɗinta da suka taru a yangance kamar tana neman amsar a gurin tace "gobeeee!" Yace "hakan ya yi miki nazo babu matsala?" Tace "ehh" yace "ok! Thanks.. Sai mun yi waya?" Ta gyaɗa kai tace "toh" sanda sukai sallama shiru tayi tare da ɗaure fuska,a fili ta furta "ni fa bance maka zan aureka ba,ni gaskiya kuɗinka nake so kuma shi ya jani,shi na bi.." Tashi tayi ta shiga bathroom tana fitowa tayi shirin kwanciya,tunanin maganar Baba da na Hamood Waziri ta dunga yi,da ƙyar bayan ta gama tattara hankalinta akan tunanin ta yanda za ta sanar da Aley kiran da Baba yake masa ta sauke ajiyar zuciya. Kusan 3 days Safwa basu haɗu da Radhiya ba,ga maganar na cinta,gefe ɗaya kuma Hamood Waziri kullum sai ya tambayeta shawarar data yanke,sai dai tace masa ya ƙara mata lokaci. Yau tunda ta tashi kasancewar bata je islamiyya ba,da wuri ta gama shirinta ta fito,Umma dake zaune parlour ta ɗaga kai ta kalli wall clock da yake nuna 12pm,then ta waigo ta kalli Safwa tace "toh! Sai ina kuma?" Safwa tace "wallahi gurin Radhiya nake son zuwa,mun yi da ita za mu haɗu yanzu ga shi har 3 days kenan" Umma tace "haka dai kullum sai dai ke kije gurinta" Safwa tace "kaiii Umma uzurina ne fa zai kaini dama" sallamar Radhiya yasa dukansu kallon entrance suka amsa,Safwa ta saki dariya tace "ƴar halak! Yanzu fa shirin fita nake naje gidan na sameki" Radhiya tayi murmushi tace "wallahi nima na gama aikin da nake nace bari dai nazo,ina ta jan lokaci yau nace gobe" Safwa tace "Allah ya hutar da ni" Radhiya ta durƙusa ta gaida Umma,ta amsa tana faɗin "ai yanzun nan nake mata ciwon bakin bakya zuwa sai dai ita tace min za taje" Radhiya tayi murmushi kawai,Umma ta tashi tana faɗin "bari na baku guri" Radhiya tace "laa! Umma da kin yi zamanki wallahi" Umma tace "um'um! Kitchen zan shiga na ɗora sanwar rana,ni da ba matayi nake da shi ba,ai dole nayi na gama da wuri kafin rana yayi a kaima yaran nan abinci" Radhiya tace "toh Umma a fito lafiya.." Tana kallon Safwa data zauna kusa da ita tare da ajiye mayafinta tace "baza ki tayata bane kika samu guri kika zauna? Ai nan zan wuni yau" Umma da har ta juya ta waigo tace "attoohh! Gara dai kiji kema ko kya yi mata faɗa,kina ganinta nan babu tsiyar da ta iya,komai ni nake yi a gidan nan.. Yanzu idan akai mata aure fisabilillahi me za taje gidan mijin tayi?" Radhiya ta kalli Safwa da buɗaɗɗen baki tace "ƙawata! Anya kin kama hanyar dai² kuwa?" Safwa ta tsuke fuska tace "kin ga ba na son haka,zuwa kika yi muyi magana ko kuma kin zo ne ki gaggaya min magana?" Radhiya na dariya tace "duka biyun" Umma ta taɓe baki tace "ai ba ta son a gaya mata gaskiya.. Shi kenan sai kiyi ai,amma dai ki sani akwai ranar ƙin dillanci.. Da ya za ta ɗakin ƙanwa" daga haka Umma tayi wucewarta kitchen,Radhiya za ta sake magana Safwa tai kicin² tace "wallahi Allah kika ƙara cewa wani abu akan wannan maganar za mu samu matsala dake" Radhiya ta gyaɗa kai kawai tace "shi kenan tunda ba kya so,amma don ina sonki ne da alkhairi,in ba ni ba kin san babu me gaya miki gaskiya,ko da za'a ganki kina shirin faɗawa wuta" Safwa tace "to ki adanata maybe tayi amfani nan gaba" Radhiya ta gyaɗa kai ba tare da ta sake cewa komai ba,hira suka shiga yi har sanda suka gangaro kan zancen haɗuwarta da Hamood Waziri,bata ɓoyewa Radhiya komai ba da ya faru tsakaninsu,Radhiya tace "to shi yanzu ba kya sonsa me yasa kika yarda har yazo gidanku? A ganina da baki ma fara bashi fuska ba bare number ki" Safwa tai mata wani kallo tace "whatttt? Haba Radhiya kin ga kuɗinsa kuwa? A'a wallahi bazai yiwu ba.. Ni kawai maganar auren da yazo min da shi ne bai min ba,kin riga kin san akwai wanda nake so fa" Radhiya ta buɗe baki tace "ban gane ba!? Idan bai zo miki da maganar aure ba da me kike so yazo?" Umma da ta gama jinsu tas ta fito kitchen tana faɗin "bar sha³.. Ke a wannan zamanin har za ki samu mutum yace yana sonki zai aureki,sai ki tsaya shashanci kina hauka da kidahumanci,gara da Allah yasa naji maganar nan tun da wuri" Safwa ta turo baki tace "ni fa Umma ina da wanda nake so kin sani" Umma tace "son banza da wofi,ga mai sonki da gaske kin tsaya hauka da shirme kina wani maganar ga wanda kike so" Safwa tace "aahh! Umma dama na faɗa miki tun farko kuɗinsa nake so" Umma tai mata wani kallon takaici kawai ta ɗauke kanta,ba tare da ta sake ce musu komai ba ta juya ta bar parlon.



*MUNIBA*



     A hankali lokaci ya fara tafiya,kwanaki suka fara turawa,biki na sake matsowa Mami sai shiri take yima yaranta,tunda aka tsayar da maganar aurensu,duk weekends Khalidah da Aunty Wahidah basa zama sai sun fita siyayya,su ne aminan Mami ko'ina za'a kuna ko me za'a yi ko siya su take sawa suje su siyo,duk abunda za ta bada biyu² ake kawo mata iri ɗaya hatta color,duk da Muniba da Baniynah suna zuwa school amma kaga wani extra kyau da suka ƙara za ka sha mamaki,sai dai bayan school ɗin babu inda suke zuwa,sai gidan me gyaran jikin da Mami ke kaisu da kanta,kowa a family shiri yake da gaske,sai count down ake na kwanakin da sukai saura,saboda ɗokin bikin kowa yake. A gefen Lieut ma dai da Khalifa suma shirin suke,duka gidajen babu zama don maganar kai lefe ake ta yi,a yanzu shi ne next move wanda daga shi abunda zai yi saura a fara biki bai da yawa. On the other side su kansu amaren ba'a barsu a baya ba,duk wani shawara da za suyi basu da ƙawar data wuce Khalidah sai ko Safwa,duk abunda ake ciki suna kiranta su sanar mata,kuma da ita ake tsara komai,biki ya rage saura 1 month duk wani shiri kusan an gamasa,sai abunda baza'a rasa ba. Kiran da Mama ta yiwa Mami a waya,yasa Mami dake zaune ta sha lulluɓi da babban veil,gefe ga haɗaɗɗen tsadadden handbag ɗinta,hannu ta kai ta ɗauka suka gaisa then suka shiga maganar da za suyi,bayan sun gama ta ɗan yi murmushi,lokaci ɗaya ta ɗaga kai ta kalli ƴan matanta da suke saukowa tace "hurry up muje kuna ɓata mana lokaci" Baniynah da ta taho da veil a hannunta tana yafa take cewa "Mami za mu biya ta gidan?" Mami tace "um'um! Gida za mu dawo,me za kuje kuyi a can,bayan duk week sai kunga Maman naku.. Ni ku wuce muje kada yamma yayi mana,kun san Abba zai dawo yau,banda dai na gama abunda ke gabana kuma Khalidah bazai yiwu nace tazo ta kaiku ba saboda kada mu shiga hakkin mijinta da aurenta,ai da ita zance ta kaiku,to na san shiririta za kuje kuyi na haɗa ku" Muniba tayi ƴar dariya kawai ba tare da ta ce komai ba suka fice Mami na masu magana cikin sauri². Cikin week ɗin wanda ya rage 4 weeks to the wedding aka kawo lefe da komai na aure,kayan da aka zubawa both of them zai baka mamaki,set ɗin boxes masu shegen kyau da tsada kowa 4 sets banda wasu adudi da akayi suma cike da kaya,lefe sai kace na ƴar shugaban ƙasa,kuma kamar baza'a mutu ba,kana kallo za ka san kowane gefe sun kashe makudan kuɗaɗe,kuma bikin ba wai na gama garin mutane bane,haka ƴan uwa da ƙawaye sukaita zuwa ganin kaya,Safwa da Radhiya da suka je kallon kayan nan kamar kada su tafi sai santi suke,sun fitar da ankonsu daban² Mama dake harkarta ne ta musu order,zuwa yanzu cards ma da komai sun iso an fara rabonsu ma ƴan uwa na nesa.



*SAFWA*



  Since ta fito masu da chairs biyu ya zauna ya ɗan zame ba normal zama ba ya yi kamar ya kwanta haɗe da miƙa ƙafafuwansa,a hankali Safwa da ta zauna tana kallonsa tayi shiru kamar yanda shima ya zauna ba tare da ya ce komai ba,bayan ɗan lokaci Safwa ta sauke wani ajiyar zuciya mai nauyin gaske and began to say "baby ya kake?" Idanunsa a lumshe ya amsata da "alhmdllh" gyaɗa kai tayi,sai suka sake yin shiru su duka,while Safwa na tunanin yanda za ta sanar masa maganar lefen Muniba da aka kawo yau da kuma kiran da Baba yake masa,idan da hali buri take ace ta samu kamar lefen nan ko sama da haka,but looking at his ɗan madina slippers da jallabiyar jikinsa yasa ta haɗiye wani yahu mai mugun kauri da ɗacin bala'i,tana runtse idanuwanta da suke wani mugun zafi,kamar mai fizgar maganar da ƙyar tace "Baby baka mana murna ba fa,yau an karɓi lefen friend" the way tayi maganar yasa shi fahimtar yanayinta,but duk da hakan ba tare da ya ɗago ya kalli fuskarta ba yace "Allah ya sanya alkhairi" Safwa da idanunta ke kansa tace "ameen.. Saura na mu" ɗago gaze ɗinsa Wazeer yayi ya sauke ƙananan idanunsa a kanta ya kalleta a bit,kafin ya janyesu daga kanta ya sake yin ƙasa da su kamar mai shirin bacci,ba tare da ta yi tunanin zai ce wani abu ba sai kuma taji ya ce "Allah ya kaimu lokacin" cikin ɗan yanayin rashin kuzari ta furta "ameen.." Underneath kuwa cewa take "uhmn! Lallai kuwa.." Suka sake yin shiru kafin tace "yawwa Baby.. Baba fa yace na sanar maka yana son ganinka" Wazeer ya ɗaga idanunsa tare da tsareta da kallo me cike da tuhuma yace "hope ba laifi nayi ba?" Tana girgiza kanta tace "i don't think so.." Yace "when yace yana son gani na? Or kin san dalilin da yasa yace yana nemana?" Safwa ta girgiza masa kai tace "i don't have an idea akan komai.. Kawai dai idan ka samu lokaci sai kazo lokacin da yake nan,almost 1 month fa kenan da ya faɗa min maganar na kasa sanar maka" ya gyaɗa kansa kaɗan yace "ok! Allah ya kaimu.." Suna ta zaune gurin babu me cewa wani komai sai ga Baba ya yi horn,Bilal ne ya fito da keys a hannunsa ya tafi ya buɗe get,Baba ya shigo da motarsa yayi parking,Bilal ya rufe get ɗin da ɗan gudunsa ya ƙarasa gurin motar Baba yana faɗin "Baba sannu da zuwa" Baba ya amsa yana kallon inda su Safwa suke yace "buɗe booth ka shiga da kayan da suke ciki gida" Bilal yace "to Baba" excuse Wazeer ya nema gurin Safwa yace "let me greet Baba" tace "ok" ya tashi ya ƙarasa gurin motar ya yiwa Baba sallama,Baba ya amsa yana kallon yanda ya durƙusa ƙasa yana cewa "barka da dawowa Baba" Baba yana kallonsa yace "barka dai" suka gaisa a mutunce kafin yace "kai ne kake son Safwa?" Wazeer yayi ƙasa da kansa kafin ya ɗan gyaɗa kan nasa yace "ehh Baba" Baba yace "toh! Dama ina ta son ganinka,Allah bai nufa ba sai yau,but duk da haka na bada saƙo a sanar maka almost a month,sai dai na ji shiru,shin ya iso maka ko?" Wazeer yace "ehh! Ka yi haƙuri ban zo ba,ban jima da samun saƙon ba" Baba yace "toh babu damuwa,idan ka samu lokaci,kazo akwai maganar da za muyi" Wazeer yayi shiru kafin ya gyaɗa kansa yace "toh Baba" Baba yace "idan kuma kana da lokaci yanzunma sai muyi maganar" Wazeer ya ɗan gyaɗa kansa yace "toh Baba" Baba ya ɗaga kai ya kalli inda Safwa take yace "Safwa shiga gida ki jiramu za muyi magana" da sauri ta amsa tare da tashi tabi Bilal sukai cikin gida,Baba ya kalleshi yace "mu ƙarasa can mu zauna kada ka gaji da tsuguno" Wazeer yace "toh Baba.." Shiru ne ya ɗan ratsa tsakani bayan sun zauna kafin Baba ya nisa ya fara masa magana cikin taushin murya da kalamai yace "da fari mene ne sunanka ne?" Wazeer da kansa ke ƙasa kamar mace yace "Aliyu!" Baba ya gyaɗa kansa yace "maa sha Allah.. Ashe babban suna ne da kai" Wazeer ya ɗan saki fuskarsa kaɗan sai dai bai dai ce komai ba,Baba yace "Malam Aliyu.. Shin ka san dalilin da yasa nace ina son ganinka?" Wazeer yace "a'a" Baba yace "haka ne.. To dai duka ba kan komai bane illa game da alaƙarka da ƴata,ba zan ɓoye maka ba,akwai wanda yazo yake son aurenta yanzu haka,and he's ready ayi komai cikin taƙaitaccen lokaci.. Sai dai abunda ya hana ban amshi maganarsa ba har yanzu shi ne,saboda ta sanar mana akwai wanda take so,a zamanin da muke ciki ba ka ɗauki ƴarka kayi mata auren dole ba,don kawai mun damu muna son aurar da yaranmu mata,ba sai mun hura musu wuta sun kasa tsugune sun kuma kasa tsaye ba sannan zai sa ka samu abunda kake so.. A'a! Bawa zaɓin yaranmu muhimmanci yana daga cikin abunda zai sa ɗanka yaji daɗi kuma duk abunda kace ta zauna,zai maka biyayya.." Wazeer yace "haka ne" Baba yace "Toh! Alal haƙiƙa Malam Aliyu,matuƙar kana son ƴata Safwa da gaske babu yaudara,lokaci ya yi da ya kamata ka sanar da magabatanka su zo ayi maganar aurenku,idan kuma baka shirya bane ko ba yanzu za kayi aure ba,to ina ganin ya kamata ka dakata da zuwa haka nan,sai a bawa wani cikin masu nemanta dama suma.. Wannan shi ne saƙon a taƙaice,saboda haka don Allah a ƙoƙarta,idan har da gaske kake ba lokaci kazo ka ɓata ma ƴata ba na baka nan da 1 week,ina jira naji daga gareka,idan haka ta gagara to sai dai ayi haƙurin da na faɗa.. Allah yasa mu dace" Wazeer ya numfasa tare da gyaɗa kansa yace "in sha Allah Baba.. Na gode sosai,Allah ya ƙara girma" Baba ya amsa sannan suka yi sallama ya tashi ya shiga cikin gida. Not too long Safwa ta sake fitowa,sanda ta zauna tana kallonsa a sanyaye tace "huh! Ya kuka yi da Babanmu?" Wazeer yayi shiru kafin ya sanar mata abunda ya faru,ta ɗan gyaɗa kanta kaɗan tace "to yanzu ya kake ganin za'ayi? 1 week ɗin da Baba ya faɗa wallahi na san shi bazai wuce haka ba.." Wazeer ya ɗaga idanunsa ya kalleta a hankali yace "and this is ok for me too.. Zan sanar da Babana in sha Allah" Safwa ta gyaɗa kanta tace "ok!" Bai jima sosai² ba yace zai tafi,sukai sallama ta rakashi bakin get. 



*WAZEER*



    Tunda ya dawo gida ya shiga gurin Daada yai mata sai da safe ya wuce ɓangarensu,yana shiga bedroom ya wuce ya ajiye wayar da Safwa ta bashi,kafin ya wuce bathroom,sanda yayi wanka da shirin bacci then ya hau gadonsa tare da janyo bedside drawer ya ciro farin eye glasses da yake amfani da shi,then ya ɗauki MacBook da wayarshi dake kashe ya kunna,abubuwa da yawa yake ji suna damunsa a rai amma ya rasa wanda zai tunkara ya sanarwa,ko even Mimi bai jin zai iya maganar da ita saboda bai saba sharing dakuwarsa da kowa ba,for long yake cikin damuwa da kaɗaici,bai da abokin hira,bai da abokin shawara bare tattauna matsaloli da damuwoyi,bai ma san ta ina zai fara tunkarar wani da maganar ba,aikin da ya ɗauko MacBook da niyyar yi,sam bai iya yinsa ba,haka ya mayar ya ajiye tare da dilmiyewa kogin tunani,ga Dad bai nan ya tafi Lagos shigo da wasu kayansu da suka iso cikin satin,a hankali ya numfasa tare da buɗe idanunsa da kyau,wayarsa ya kalla kamar zai ɗauka ya kira Dad ya sanar masa amma bai iya yin hakan ba,wata zuciyar ta taushe shi ya jira har zuwa sanda Dad zai dawo. Cikin wannan yanayi kwanaki suka fara tafiya,tamkar cinyewar wutar kara haka ranakun sukaita gudu,sanda aka share kwana huɗu,har sannan babu Dad babu alamarsa,on one side kullum kuma Safwa sai ta kira shi kamar za tayi masa kuka tana cewa "Babe ka ƙi zuwa,kuma ka ƙi ce min komai,shin bakai magana da Baba bane har yau?" Cikin wani irin yanayi yake sanar mata "Baba baya nan ya yi tafiya ƙauye ziyara,and zai duba wasu cikin harkokinsa na can,da zaran ya dawo zan sanar masa,u don't have to worry,zan zo kuma Babana zai zo ya yi magana da Baba" haka kullum zai lallasheta da kalamai masu nuni da tayi masa uzuri,ranar da aka yi 5 days Safwa ta matsa masa lamba sosai² har da kuka kamar warce akaiwa rasuwa tana faɗa masa "i can't leave without u Aley.. Idan har kana sona da gaske kamar yanda nake sonka,ko da Baba baya nan ai u have other relatives da za ka iya ka kawo su suyi magana da Baba,ba fa kuɗin aurena Babana yace lallai sai ka kawo a cikin 1 week ba,magana yake so magabatanka su zo ayi,su tabbatar masa kana sona kuma u are ready ka aureni" Wazeer yace "i know dear,but.. Duka ƴan uwanmu basa nan,kin san mutumin dake ƙauye,babu yanda za'ayi ya bar sana'arsa ya taho miki nan" Safwa cikin damuwa tace "amma ai yini ɗaya ya yi yawa an gama magana sun juya.. Kawai idan baka shirya aurena ba,Aley ka sanar dani don Allah,sai na cire rai na da samunka,na kuma bawa zuciyar da ke sonka da gaskiya haƙuri.." Tana faɗin haka ta katse kiran tare da kashe wayarta off,yanayin yanda tai magana tana kuka cikin damuwa da tashin hankali yasa Wazeer kiranta back,amma sai yaji wayar switch off,abun ya bashi mamaki sosai,yanda Safwa ke nuna masa so har tsoro yake ji,sometimes ko kiranta ya gani ko ya tuna sunanta sai gabansa yaita faɗuwa,lumshe idanunsa yayi underneath yana tunanin rashin dawowar Dad,shi da yace bazai wuce 3-4 days ba,amma gashi har ana maganar 5 days,he's trying hard not to call him,don maganar ba na waya bane,he's not sure yana son Safwa 💯%,kuma bai jin yana ƙinta,ace wai irin heated ɗin nan da za tasa yaji bazai iya rayuwa da ita ba,kawai shi kansa bai san me yake damunsa ba in between,wani lokaci yana jinsa somehow,kamar dai ba asalin shi bane,to amma bai san wa ya kamata yayi maganar ma da shi ba,Dad bai da lokacinsa sam,ta businesses ɗinss yake,harkar neman kuɗinsa da shahara yasa a gaba,Mimi kuma bai ma kawo yayi magana da ita ba,saboda tunda ya dawo tun bayan maganar da yayi mata akan rabuwarsu ita da Dad,da ya fahimci basa son maganar yayi shiru bai sake ɗaga zancen ba,ya ƙyalesu har zuwa sanda zai gama tattara hujjoji da bayanan da zai sanar musu su duka. 



*SAFWA*



    Da gangan kamar ta san zai kirata ta kashe wayarta,sai da ta kintaci lokaci kafin ta kunna wayar ta shiga kiran Malama Gaaji,cikin damuwa Safwa ta shiga zayyana mata abunda ke faruwa da abunda take son ayi,Malama Gaaji ta amsa tana kwantar mata da hankali tace "toh Safwa ai da kin bari an bincika miki yanayin yanda zaman naku zai kasance da shi,tunda kin ce ke baki ga alamar ɗan wani bane,kuma Ummarki ma mun yi wannan maganar da ita,abunda nake so ki fahimta yanzu shi ne,idan har da ace Aliyu yana da yanda zai yi,da ba'a kawo yau ba,Babanku ya bashi 1 week just because ya kawo iyayensa ayi magana,aji idan da gaske yake sonki zai aureki,but bai zo ba kullum sai dai yayi miki ƙaryar Babansa is not there,bla bla bla.. Which is all lies,to bari kiji ƴata na baki shawara,a yanzu a zamanin da muke tuni aka daina auren soyayya,muddin za kaje ka sha wahala haƙura ake da duk wani so,kowa auren rufin asiri yake fatan yi,ka tafi inda za kaje ka huta ƴan uwanka ma su ji daɗi.. Na san kin sani ko a cikin ƙawayenki,shin yanzu idan nace miki waye sukai auren soyayya,suka auri wanda bai da shi,za ki iya faɗa min mutum 5 da suka auri talaka futuk,suka zaɓi soyayyarsu akan jin daɗi?" Safwa tai shiru kafin ta girgiza kai kamar tana gabanta tace "a'a" Malama Gaaji tace "to ke me yasa kike son zuwa inda yake ƙasa da gidanku sosai²? Ba kya sha'awar ki samu mijin nunawa sa'a?" Safwa tace "ina so" Malama Gaaji tace "toh! Safwa indai kina son rayuwar jin daɗi,sai kin yiwa kanki faɗa tun yanzu,ki tuna kyau yana disashewa,haka soyayya tana raguwa,da kije inda za ki wahala kizo daga baya kina da kin sani,gara kije inda nan gaba za kiyi ta faɗin,kai Allah ya taimakeni lokaci kaza da nayi kaza,na godewa Allah da yasa na bi shawarar Ummata,da tuni ina can ina surfau,wankau da dakau.." Safwa ta zaro idanunta waje tace "Aunty surfe fa?" Malama Gaaji tace "yes!" Safwa ta kalli hannunta ta jujjuyasa tace "Allah ya tsare ni da yin wannan" Malama Gaaji tace "ameen.. Toh! Yanzu ya kike gani? Ayi wancan aikin ko na bari kiyi shawara?" Safwa ta gyaɗa kanta tace "ehh! Zan yi shawara" Malama Gaaji tace "toh! Babu damuwa,Allah yasa muji alkhairi" Safwa ta amsa sannan tayi mata sallama. Number Radhiya ta shiga kira kai tsaye,bayan sun gaisa Safwa ta ɗan yi shiru,cikin damuwa Radhiya tace "what's up ƙawata?" Safwa tace "ina cikin damuwa ƙawata,wallahi ban san ya zanyi ba,kin san na faɗa miki Baba sun yi magana da Aley,tun ranar yau kwana 5 fa bai zo ba,idan na masa magana sai yace min Babansa baya gari ya je ƙauye,imagine Radhiya mutumin da nake so yake min yawo da hankali haka,i don't know what to do,idan deadline na Baba ya cika ya tambayeni shi me zan ce masa? Ga Hamood Waziri ya buɗe wuta so yake na bashi dama yaje gurin Baba" cike da dauriya Radhiya dake gyaɗa kanta ta numfasa tace...








*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*


  _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

  _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


*Infection*

  _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_


  _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*****

*****






#Follow

#Comment 

#Vote

#Share fisabilillah!

#ASLI-SMASHER.