Chapter 5_6
by @kainaat1515
Doctor Shazim
Daga alƙalamin
kainaat... ✍
*_KING AND QUEEN WRITING CHAMBER_*
Season one
free
Episode 5_6
_FRIDAY......._
sauko wa yake daga stairs jikin sa sanye da baƙaƙen coat hannun sa riƙe da briefcase , ammy ce zaune kan sofa ƙaraso wa yayi kusa da ita " Ina kwana Ammy ina fatan kintashi lafiya " ya fada yayin da yake samu wuri kusa da Ammy ya zauna " lafiya lau Shazim har kafito," eh ammy ya bata amsa," ga breakfast din ka nan kan dinning" "to,ammy kinkuwa yi waya da NORAIZ "( kanin sa mai bimasa yayan fatima dayake baya nan yana kasar portland yana masters akan business ) ya fada yayin da yake nufar dinning "eh naji yace yana nan zuwa ranar sunday ( lahadi ) , ammy ta fada " eh ammy haka yake fada man jiya, "to Allah ya kaimu lafiya" Jiya uncle ɗin ku ya kirani, yace kai ka ɗai suke jira" shiru yayi baice komai ba sai da ammy ta sake cewa "da kai fa nake magana, ni ban san mikake nufi ba , da anyi magana sai kayi shiru, tun yaushe ake abu ɗaya sai yawo kake ma mutane da hankali"
"kiyi haƙuri ammy, wlh ban gama abun da nake ba, kuma nifa bani da wata wacce zance ina so, nafi son su barin harsai na samu wacce nake so"
"to bari kaji na faɗa maka ni ba ruwana daga yanzu bazan sake shiga maganar ba duk hukuncin da suka yanke akan ka babu ruwana "shazim yace "dan Allah ammy karkice haka idan kika zare hannunki innah zata iya zuga su su yanke man hukuncin da duk sukaga dama"
"to idan har baka son haka tafaru to dole sai ka nema ma kanka masalaha" "insha Allah ammy"
"to Allah ya yarda, ameen ammy ".
fatima ce ta fito daga bedroom dinta dake kusa da na Ammy jikinta sanye da uniform , dinning ta nufo Ita ma domin breakfast
" Ina kwana Yaya dafatan antashi lafiya " lafiya qlu ya bata Amsa, yana gama breakfast ya mike hadi da daukar briefcase din shi " Ammy ni zan wuce, to a dawo lafiya Allah ya bada sa'a, ameen Ammy fita yayi zuwa parking lot, gaisawa ya tsaya yi da masu aikin gidan tun daga kan maibama flower ruwa Har izuwa kan maigadi sannan ya fuce daga gidan, ABNOOR ya nufa domin yau baya zuwa EKO.
ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN PRIVATE HOSPITAL ( ABNOOR ).
Direct office din sa ya nufa briefcase din sa ya aje akan table zama yayi hadi da bude laptop dinsa Aiki yafara kafin time din daya ke duba patient yayi. sallama a kayi hadi da turo kofar wani matashin saurayi ne wanda zasu yi sa'anni da shazim din.
Amsa mashi sallama yayi, shigowa yayi daga ciki hadi da mikama shazim din hannu suka yi musa baha , sannan ya zauna kan kujerar dake gaban table din " shazim amma yanzu ka shigo ko dan nazo baka nan, eh shigowata kenan nakama aiki , ai ku manya ne agogo sarkin aiki, haka dai kake gani majeed karfin haline kawai, wlh kuwa ai kana kokari, to ya za'ayi, dole a nema"
"hakane dama maganar kayan da suka kusa ƙarewa ne"
"kai ai kuwa gara daka tuna man dan har na manta, zanyi magana da su yau insha Allah "
"to shikenan nibari nakoma office"
"to shikenan nima yanzu zanje duba patient insha Allah sbd da time din sallah nayi zan tashi sai kuma gobe Idan Allah ya kaimu, ameen majeed ya fada hadi da barin office din shima baijima ba ya fita dakin marasa lafiya nufa sai 12:10 sannan ya dawo office yana shiga bawani jimawa yayi ba ya hada kan kayansa ya fito direct gida ya nufa bedroom din ammy ya fara zuwa gaisawa kawai sukayi ya nufi part din sa bedroom din sa ya nufa kayan jikin sa ya shiga ragewa ya nufi bathroom after 10 minutes ya fito kugunsa daure da towel dressin mirror ya nufa mai ya shafa mai dankaran kamshi, comb yasa ya shiga combing din kansa sannan ya shafesa da man aloe da hair spray clothes set dinsa ya nufa shaf shaf ya shirya cikin wata shadda ƴar ubansu milk color ba karamin b
kyau yayi ba sannan ya dauko hula ya daura brown color, feshe jikin sa yayi da turare mai ƙamshi,sannan ya nufi shoe rag dinsa takalmi ya dauko me kyan gaske shima brown color. masha ALLAH kawai zamuce dan ba karamin kyau yayi ba wayoyin sa dake bedside ya dauka fita yayi daga bedroom din yana zuba kamshi, ya nufi down stairs parlorn ammy zaune ya sameta tana karatun Al'qur'an tana kai aya tace " sai masallaci kenan, eh ammy ya bata amsa , to shikenan a dawo lpy nima zanje gida domin na ƙasa duba jikin baba , to saikin dawo Allah ya bashi lfy nima insha Allah yanzu daga masallachi zan biya na gaishe shi saina dawo ya fada hadi da kama hanyar fita Ammy nacewa a dawo lpy , da innah asabe ya cikaro ( mai Aikin su) zata shiga wurin Ammy, gaishe da Ita yayi ta amsa mashi da " Lafiya lau Shazim har za'a tafi masallachi kenan, eh ya bata amsa hadida fice wa daga falon ya nufi parking lot mota yashiga mai gadi ya bude masa gate ya fuce.........
_KATSINA......._
AIRAH
Zaune take bakin gado jikinta daure da towel da alama wanka zatayi .
"sister gaskiya kiyi sauri kifito nima nayi wanka kinsan yau abie zai dawo kuma mom tace muje gidan granny mu gaishe ta har so nake muje gidan aunty safiya ( kanwar MOm wacce suke uwa daya uba daya) mun kwana biyu ba muje ba "Aairah ta fada.
fitowa Aaimah tayi daga bathroom jikinta daure da towel " bawani sis zaki ziyara ne kodai zakije ganin ya MUS'AF dan nasan halinki sarai, Amma wlh Aaimah kin bani da sharri yau she nace maki saboda shi zanje gidan ni dai ziyara zani bawai saboda ya mus'af , dan wlh ki bari karki jaman ya usman yaji wannan maganar , ai kuwa saina fada masa ince bakiji gargadin da yayi maki ba, ni wlh har mamaki kike bani kirasa dawa zakiyi soyayya sai ya mus'af harka duk ta yarin ta, eh naji matar babban mutum sai mi koda ace na girmi ya mus'af ina ruwan ki Aairah ta fada tana huro hanchi, Allah ya baki hakuri Aairah ni nayi nan Aaimah ta fada hadi da nufar dressing mirror bathroom Aairah ta nufa shaf shaf Aaimah ta shirya cikin atamfa super Red color ɗinkin riga da skirt tana nan tsaye tana fesa turare Aairah ta fito sai bata rai take shiryawa itama tayi cikin atamfa color daya data Aaimah tana gamawa ba tai ma Aaimah magana ba taka ma hanyar fita daga bedroom din, murmushi Aaimah tayi hadi dacewa " ki nafa iya cewa kinji haushi, bata bata amsa ba sai tsaki data ja, haba twin sis kiyi hakuri bazan sake ba kinji ta ya mus'af sorry pls Aaimah tafada hadi da matsowa kusa da Aairah sake bata hakuri tayi tare da cewa haba abun gidan ya mus'af kiyi dariya mana dan Allah tafa da yayin da take langwabar da kai, murmushi kawai tayi hadi da cewa wallahi Aaimah ki daina kushe man ya mus'af Indai kina so mu zauna lafiya da ke, kaina bisa wuya na daina insha Allah Aaimah ta fada hadi dajan hannun Aairah suka fita bedroom din mom suka nufa samun ta sukayi zaune gaban dressing mirror tana saka sarka a wuyan ta sanye take da wani hadaden less brown color ta sha daurin ture kaga tsiya hannunta ya sha dan hannu da zobe na gold kalar sarkarta, har suna hada baki wurin fadin masha Allah , Aaimah ce ta ce "kice yau an tashi rikita mana abie kenan , wannan kwaliyya haka mom ai sai ya ka sa gane ki yayi tuna nin sabuwar amarya aka kawo masa, Aairah tayi charab tace ba kiga harda ture kaga tsiya ba, lallai duk wanda ya ture ya taro match ba yan ball, murmushi kawai mom tayi hadi da cewa kun rainani ko, na lura ni kuka maida granny da dadi, Aa wane mu kawai dai munga kin hadu kar abie ya riki ce, ALLAH ya shirya ku mom ta fada ameen suka amsa, Aairah tace daman mom daga gidan granny zamu wuce gidan aunty safiya dan Allah, shikenan Idan kunje kuce ina gaishe ta , to shikenan mom zataji Insha Allah amma sai abie ya shigo sannan zamu tafi , to shikenan mom ta fada..
Ya usman ne ya shigo bedroom din jikinsa sanye da shadda maroon color sallama yayi hadi da shigo wa gaishe da shi su Aairah su kayi hadi da ficewa falo zama sukayi kan sofa suna kallo.
a chan kuma bedroom din mom gaishe sa Ita usman yayi, amsa mashi tayi hadi da cewa har ka dawo daga masallachin, eh mom ya bata amsa, abinci fa, a kai maka part dinka ko zaka sauko kachi a dinning, a'a a barshi nan zan sauko Idan abie ya shigo sai muci tare da ku , dan nayi waya da shi da ina kan hanya wai ashe ya dawo yana gidan dadi (kakar su ta wurin uba mahaifiyar Abee) amma yanzu zai taho, to shikenan bari nasa ajera abinci kan dinning sai muci tare da dashi dama nayi tuna nin basu kusa isowa ba, to shikenan mom ni na wuce part dina kafin ya kai da shigowa ya fada hadi da ficewa itama mom fita tayi direct kitchen tawuce a chan tasa mu baba larai na zuba abinci cikin warmers "yawwa baba kice harkin kwashe kafin nazo, halan kinga najima ban dawo ba sallah nayi sai nace bari kawai nayi har da wanka tun da nasan san da zan dawo nasan a bincin ya nuna kuma barrister na hanya shiyyasa, A'a nima sai da nayi wankan da naga baki sauko bane kuma ya nuna sai nace bari kawai na kwashe, to shikenan bari na jerasu a dinning mom ta fada hadi da daukar warmers din ta nufi dinning bala driver ne ya shigo hannun sa dauke da kaya suna cikin gaisawa mom sukaji sallamar abie daga bayan su sauko wa su Aairah sukayi da gudu jin sallamar abie, nufar sa su kayi da gudu hugging din su yayi yana murmushi sun bi sun makalkale shi mom ce ta matso tana cewa ku sake sa man, kunbi kun makalkalesa , haba mom kwana biyu fa baya nan, to ko baya nan fa , ya kwaso gajiya shine zaku kara masa wata, ku sake sa mana , sakin sa su kayi kan sofa suka zauna, shi kuma up stairs ya hau shi da mom , bala ne ya sake shigowa da wasu kayan na abie, jakar kayan abie ka dai bala ya kai sama sauran kayan kuma kitchen ya nufa dasu .
AFTER 25 minutes........
abie ne da mom ke sauko wa daga up stairs abie har ya chanza kayan jikin shi da alama wanka yayi dinning suka nufa ta sowa su Aairah sukayi suma suka nufo dinning din " Aairah maza kije ki kira yayan ku mom ta fada, tashi Aairah tayi direct part din ya abdallah ta nufa tsit parlorn shi, ba kowa sai kamshi kawai dake tashi ya hadu parlorn golding color ne komai na ciki , bedroom din sa ta nufa nocking tayi tambaya yayi waye, Aairah ce, yaya mom tace ka sauko abie ya dawo ta bashi amsa, gani nan zuwa yace, fita tayi daga part din ta koma wurin su mom , yace ga shinan zuwa ta fada yayin da take samun wurin zama serving din su Aaimah ta shiga yi sai ga ya abdallah shima ya sauko jikin sa sanye da jallabiya karaso wa yayi yana gaishe da abie da gajiyar tafiya, amsa mashi abie yayi tare da tambayar shi ya aiki,amsa ya bama abie da alhmdllh shima serving din sa Aaimah tayi , abinci suka shiga ci ba magana sai dai karar spoon dake tashi, su Aairah suka fara tashi, ba dai har kun ta shi ba, abie ya tambaya yana binsu da idanu, eh abie zamuje gidan granny ne shiyyasa kuma fa mun koshi, Aairah ta bashi amsa, to shikenan sai kun dawo kar dai ayi dare , a dawo dawuri kunji, Insha Allah abie baza mu kai ba, Allah yasa, ameen suka fada hadi da nufar up stairs , abie suna gama cin abinci kan sofa suka koma suna fira shi da ya abdallah ,mom kuma tattare dishes din da su kayi amfani dasu tayi ta nufi kitchen, baaba larai ce ta fito daga corridor din da da kinta yake wurin su abie ta nufo hadi da gaishe da abie tana tambayar shi ya gajiyar hanya amsa mata yayi da, "lafiya lau alhmdllh, ya gida ya kuma muka same ku, alhmdllh muke naga sako nagode Allah ya saka da alkairi, ameen nagode bakomi abie ya bata amsa ( nasan masu karatu zasu ce godiyar mi baaba larai keyi ma abie , kudi ya ba ma mom ta ba ma dukan hadiman gidan dama ya kan yi haka duk In zaiyi tafiya.) Kitchen ta nufa anan ya samu mom na wanke dishes din da suka ci abinci " ah hajiya dakin bari nazo na wanke ai, A'a bakomi baaba kema ki huta mom ta bata amsa, to shikenan bari muyi tare" inji baaba larai, A'a dakin bar shi Allah kinga na kusa gamawa ai, to shikenan , su Aairah ne suka sauko sun sha jalbab har kasa sai bag kalar ta kalmin dake ka farsu kara sowa su kayi wurin su abie hadi da cewa sai mun dawo,abdallah ne ya ce" mudi na nan waje shi zai kaiku" to suka ce hadi da nufar wurin mom sun cewa sai mun dawo a dawo lafiya tayi masu , ficewa su kayi harabar gidan, a nan suka samu mudi na jiran su , motar suka nufa, shiga su kayi, key yayi ma motar suka fice da ga gidan dama me gadi ya bude masu gate labari kawai Aaimah da Aairah keyi shi dai mudi nashi saurare har suka isu gidan granny horn mudi yayi a bakin gate din gidan bude masa gate din a kayi ya shiga daga ciki ya na parking suka fito gidane dan dai dai me kyau cikin gidan suka nufa wata kyakyawar tsohowa ce suka samu zaune a parlor tana kallon SUNNAH TV ( granny kenan mahaifiyar mom ce) sallama su kayi da gudu suka nufi yar tsohuwar, granny tace " karku kuskura ku fado man , salon ku ida kara sa man yan kafafun da nake fama dasu" Aaimah tace "haba granny daga munyi murnar ganin ki sai kice zamu ida karasa maki yan kafafun"ta fada tana turo baki, Aairah ce tace " shiyyasa yau zan zuga tsoho yayi maki kishiya tun da baki da kafafu" granny tace " sai dai ke ayi maki kishiya, amma ba dai ni ba, saboda ni ba wacce zata iya kishi dani, in kuma kece kishiyar inji tunwuri" dariya suka kwashe da Ita su duka Aairah tace " wah wai ni , ai kuwa da kin sha kwar kwasa da kisi si na, murmushi kawai granny tayi hadi da fadin Allah ya shiryeki yan biyu ( dayake haka take ce masu kokuma Hassana da hussainah) gaishe da Ita sukayi suna tambayar tsoho na nan, ( wato mijin granny) granny ce ta basu amsa da "yana parlor da yake ganin dalibn sa, inajin ma karatu suke saboda yau juma'ah ( malamin addini ne shi duk da ya tsufa hakan bai hana shi koyar da daliban sa ba) Aaimah tace" to shikenan granny bari muje gidan aunty safiya mu dawo, kilan time din ya gama, to sai kun dawo ku gaishe man da ita granny ta fada Aairah ce tace zataji insha Allah fita sukayi harabar gidan nan suka samu mudi zaune kan benchi suna fira da me gadin gidan, gannin sun fito yasa shi ta sowa Aairah ce tace "kabar shi kawai ba nisa za muyi ba gidan aunty safiya za muje, to ya fada hadi da koma wa kan benchi ya zauna su kuma fita su kayi daga gidan, tafiya su kayi a kafa ba mai nisa ba suka iso gidan tura yar kofar dake gefen gate su kayi hadi da shiga gidan, gida ne mai girma ba laifi dan har ya kusa girman gidan su, part din masu gidan suka nufa da sallama a bakin su suka shiga parlorn, yan yara suka samu na wasa a parlorn mace da na miji a kalla za suyi kimanin shekara 10, suna jin sallamar su suka nufo su da gudu suna masu "oyoyo aunties ya gida ya mom" su Aaimah suka ce"lafiya lau hisham sai ku ka dai a parlor kai da hibba, wata matashiya ce ta leko daga up stairs jin haya niyar yaran zata yi sa'anni dasu Aaimah tana ganin su Ita ma da gudu ta sauko tana fadi "oyoyo lovely sister da kuka ce kun fasa zuwa" Aairah tace "kedai bari najma, dafa har mun fasa saboda abie zai dawo yau, to da muka koma gida daga school mom take ce ma ai yama kusa isowa, to shine fa muka shirya tana dawo wa muka taho, najma tace "gaskiya naji dadi, da Allah har nayi fushi, Aaimah tace "yanzu dai ba wannan ba naji banji mutsin Ummah ba ( Aunty SAFIYA suke cema Ummah sbd su najma ) ko bata nan ne , tana dakin abba najma ta bata amsa hadi da jan hannun su tana cewa kumu tafi part din abban daga nan sai ku gaisa dashi ko , ok muje, part din abban suka nufa, sallama su kayi yayin da suke shiga cikin parlorn zaune suka same su kan sofa, amsa masu sallamar suk ayi aunty safiya tace "ah lallai yau ina da mn yan baki" abba yace " lallai kam yau muna da man yan baki, ya mom din ku da abie ya kuma school, alhmdllh abba suka amsa mashi, to masha Allah abba ya fada najma ce tace " to ku tashi mutafi daki, da to suka amsa mata hadi da mikewa suka fice direct bedroom din najma suka nufa suna shiga suka yada zango akan bed din ta Aairah ce tace " wai nikam ina Yaya mus'af ne najma,Aaimah ta ce " uhmm dama nasan hali har ni zakiyi ma bariki wai ziyara za muzo bayan nasan karyane, eh din naji komi za kice kice Aairah ta fada tana murguda ma Aaimah baki ,najma ce tace" ya Isa haka inkuka fara sai kuba mutun haushi wlh , ya mus'af ne deko to yana part dinsa bari nakira maki shi a waya koke kikira shi ba shi kenan ba, Aaimah tace aikin san wasa nake maki ko rabin rai , niban wani sani ba Aairah ta fada, to yanzu kinsan shikenan ko ta wuce, bari ni na kira maki shi da kaina a cewar Aaimah hadi da ciro wayarta tayi dealing number sa kiran na shiga ta mikama Aairah wayar picking call din yayi hadi da ce " Aslm, wslm ta bashi amsa, sai cewa yayi" Aaimah ya kike ya gida yasu mom da ya abdallah, ina kuma sweetie nah take, bubbuga kafafu ta shiga yi tana turo baki hadi dacewa" haba Qalbei nice kenan baka gane ba , su najma miza suyi inba dariya ba suna cewa a she soyayyar bata kaiba da har ake kasa gane muryar juna , fa shewa da kukan shagwaba Aairah tayi hadi da cewa ka gani koh Aaimah da najma nayi man dariya, on the other hand yace " sorry sweet heart nayi tuna nin Aaimah ce, kinga ai numberta ce amma kiyi hakuri kinji my, najma na gidan kune, Aa fa kai da nazo nayi surprise dinka, amma sai ka bata komai baka gane ni ba Aairah ta fada, sorry kinji tawan fada man kina ina kinji, turo baki gaba tayi hadi da cewa " Ina bedroom din najma , am coming sweet heart ya fada hadi da kashe wayar,ajiye wayar tayi Ita ma hadi da yima su najma gwalo "oho dai ke da ba'agane ba najma ta fada hadi da tafawa ita da Aaimah" nocking sukaji ana yi da sauri Aairah ta nufi kofar tana bu dewa wani matashin saurayi ne tsaye jikin sa sanye da jeans da T-shirt na kamfanin Gucci farine kyakyawan karshe a kalla zai yi kimanin shekara 20 murmushi Aairah ta sakar mashi shima martanin murmushi ya mayar mata, gaishe da shi Aaimah tayi, ficewa su kayi daga bedroom din, su Aaimah kuwa fira kawai suke har aka kira sallar asr, sallah suka tashi su kayi a lokacin Aairah itama ta shigo domin yin sallar Aaimah ce tace ma Aairah ai nayi tunanin nisa ku kayi da naga kun fita ashe kuna kusa, banza Aairah tayi da ita ta nufi bathroom domin yin alwala, basu ne suka bar gidan ba sai wajen 5:00 sannan suka koma gidan granny najma da Aaimah na gaba yayin da Aairah da mus'af ke bayan su , suna shi ga granny tace a she zaku dawo harna yi tuna nin kun wuce gida a she kuna nan, kallon mus'af tayi tana fadin" kai kuma lafiya kayi man tseye a kai , aure ne dai banyi ehe" dariya mus'af yayi hadi da cewa sai mi, dama ni yarinya nake so me jini a jika ba tsohuwa ba, dariya suka kwashe da Ita su duka, haba kai dai kawai dan ba zaka samu bane , ya safiyar take ina su Hibbatu da hisham ,
lafiya lau suke granny, fira suka shiga yi da granny tana tsokanar su a nan tsoho ya same su, gaishe da shi suka yi , dashi suka taru suna ta firar ba sune suka bar gidan ba sai kusan 5:50 sannan mudi ya mayar da su gida duk da mus'af ya so mai da su, amma suka ce ya barshi tun da da driver suka zo ,da shigar su gida bedroom suka nufa domin time din sallar magrib ya kusa kayan jikin su suka cire suka sanya ma rasa nauyi, sau kowa su kayi down stairs direct kitchen suka nufa wurin mom da baaba larai dake shirya dinner , kama masu aikin su kayi har suka kammala kowa ya nufi bedroom dinsa domin gabatar da sallar magrib wacce ake kira.
KAINAAT
_Lagos....._
Innah asabe ce a kitchen ita da fatima suna girki kiran sallar da a ke yine yasa fatima cewa "Innah kije kiyi sallah zan karasa aikin, to amma kefa, karki damu Innah kitafi kawai ( da yake tana fashin sallah ne) To shikenan, fita tayi daga kitchen din ta nufi dakin ta, shazim ne ya shigo cikin gidan jikin sa sanye da farar jallabiya da alama daga masallachi yake par Ammy ya nufa bai isketa ba sai yawuce bedroom din ta nan ma bata nan fitowa yayi daga part din ya nufi main parlor fatima ya gani ta fito daga kitchen hannun ta rike da food flask " Ammy bata dawo bane, eh bata dawo ba , ok ya fada hadi da Komawa part din sa, sanda Innah a sabe zata koma kitchen har fatima ta gama komai da yake sai da ta jira aka kira sallah isha tayi, kama mata kawai tayi suka gyara kitchen din, falo fatima tafita kiran daya daga cikin ma aikatan gidan tayi a waya domin yazo ya daukar masu a binchin su, sallama a kayi daga kofar falon hadi da turo ta, fateemah ce tace yawwa ilya hadi da shiga kitchen fitowa tayi hannun ta dauke da food flask din masu aikin mika mashi tayi , part dinsu ita da Ammy ta nufa bedroom din ta ta shige kayan jikinta tacire towel ta daura bathroom ta wuce domin yin wanka 10 minutes ta fito daga bathroom din dressing mirror ta nufa mai kawai ta shafa ta nufi clothes set dinta dama ta sanya pad tun a toilet shiryawa tayi cikin pajamas lemon green ta yafa mayafi white mai dan girma feshe jikin ta tayi da turare mai dadin kamshi fita tayi daga bedroom din a falon Ammy ta zauna kan sofa wayar ta dake charge tacire ta shiga chatting wurin 9:00 sai ga Ammy wacce shazim ya dauko falo ta tsaya shi kuwa up stairs ya haura sai 9:30 fatima da Ammy su kayi dinner dan shi shazim cewa yayi takai masa part din sa suna kammala wa fatima ta kwashe kayan da suka yi amfani dasu ta kai kitchen nan falo ta zauna suna fira da Ammy sai wuri 10:00 su katashi kowa ya shige bedroom dinsa
, zaune yake kan sofa dake bakin bed dinsa yana aiki a laptop dinsa sai wurin 12:00 ya rufe laptop din toilet ya nufa bayan 5 minutes yafi to jikin sa da danshin ruwa da alama alwala yayi, wardrobe dinsa ya nufa sallaya ya fito da Ita ya shim fida shafa'i da wutiri yayi ya jima kan sallayar yana adu'oi sannan ya niketa ya maida ta cikin wardrobe, bed dinsa ya nufa hadi da kashe bulbs din dakin bedside ya kunna, zama yayi daga bakin bed din adu'a yayi ya sha fa a fuskar sa sannan ya ida hawa kan bed din kwanciya yayi hadi da jan blanket yarufe iya kugunsa.
To nace Asuba tagari doctor nima bari naje na nemi nawa makwanchi.😴
Washe gari.......
Zaune Ammy da fatima suke kan dinning suna breakfast, shazim ne ya shigo jikin sa sanye da jogging suit black color sai p-cap white hannun sa rike da water bottle wurin su Ammy ya nufa " ina kwana Ammy fatan kin tashi lafiya ya fada Ammy tace "lafiya lau alhmdllh, yau baka zuwa abnoor ne, amsa ya bata da " A'a Ammy zanje, ok naga har 10:30 tayi Ammy ta fada , shazim yace " eh wlh nayi late wurin tashi daga bacci amma yanzu zan shiga ciki nashirya Insha Allah, to shikenan sai ka shirya ga breakfast dinka nan na jiran ka a dinning, to Ammy ya fada hadi da nufar part din sa.............
✨ _Victoria_ . ✨
Anguwace ta christianity irin ta masu kara min Karfi, destiny naga ni ta fito da ga wani gida ta nufi wan da ke opposite din inda ta fito jikin ta sanye da gown iya gwiwarta purple color kanta da kitson kalaba na attachment ka farta sanye da flat shoe, gidan dan karami ne, ko ina ya sha cement dakuna biyu ne a gidan nufar daya daga cikin kofofin tayi knocking hadi dacewa" excuse" daga cikin dakin naji ance "come in" tura kofar tayi hadi da shiga Victoria ce acikin
dakin tana ta faman jan straight gown taki shigar ta destiny ce tace " lallai Victoria a she bakima shirya ba kin kuwa san nisan da wurin ya ke da shi sai fa munfita Lagos kuma fa kinsan yau ana zuwa church da yamma, sorry destiny yanzu zan shirya mu tafi, abun da yasa ma nayi late bari nayi sai momy ( mahaifiyar ta ) ta tafi market sannan domin in tasan inda zamu ba zata bari mu tafi, Victoria naga ma shiryawa suka fita gidan tafiya sukayi sai da suka hau kan titi tukun suka tsai da mai mashin suka hau, tafiya su kayi mai dan nisa sannan suka kawo wani dan karamin kyauye duk duwatsu suna kawowa inda mashin bai wuce wa suka sauka, kudin sa suka bashi su kuma suka cigaba da tafiya nanma sai da su kayi tafiya ba laifi tukun suka kawo wata yar bukka ita kadai a wurin sai mutane jere a bakin bukkar suna karaso wa suma suka bi layi, sun jima a tsaye layi bai zo kansu ba, victoria harta gaji da tsayuwa ta duƙa, lokacin da layi ya zo kansu shiga sukayi tare cikin bukkar, wani mutum ne zaune gaban sa wasu kahuna ne sai kawunnan mutane kwaran gwal jikin sa sanye yake da jajayen kaya fuskar sa duk ta sha digedige fari sai idanun sa kewaye da bakin fenti gaishe dashi sukayi dawani irin yare mara dadin ji shi kuwa kwashewa yayi dawata irin dariya sannan ya tambaye su meke tafe dasu, destiny ce ta kora masa bayani a kan abun da yake tafe dasu, dariya ya sake kwashe wa da Ita sannan yayi yan surkullen shi wani magani ya dauko cikin wani bakin tulu ya basu destiny tasa hannu ta karba ita kuwa Victoria sai zare idanu take kudi suka dauka masu yawan gaske suka ajiye a gaban bokan sannan suka fice daga bukkar ta hanyar da suka biyo ta nan suka bi sai da suka kawo cikin kyauyen tukun suka samu wani mashindin ya dawo dasu gida, gidan su destiny suka wuce dan lokacin kafe 4:15 dakin destiny suka nufa zama sukayi suna huce gajiyar tafiya destiny ce tace" ina zuwa" tana fada ta fice daga dakin batafi 1 minute ba ta dawo da kwano a hannun ajiye shi tayi gaban Victoria fita ta sake yi sai gata ta sake shigowa hannun ta rike da pure water guda biyu zama tayi hadi da bude kwanon sakwara ce da miyar okra ( kubewa) suna cikin ci saiga wani namiji ya shigo dakin sanye ya ke da crazy jeans sai singlet gashin kansa kuwa yasha dada ( yanda yan iska keyima gashin su ya koma kamar lagwani )da kaga yana yin sa zaka san a buge yake, ya na ganin Victoria ya kama washe baki daure fuska Victoria tayi tana ganinsa , kusa da Ita ya matso kamar zai yi hugging din ta ba shiri ta mike tsaye hadi da daka mashi tsawa tana cewa" which kind of this nonsense samuel " bangane wulakanci ba Victoria you are my wife ya fada yana washe baki, destiny dai na gefe tana kallon su bata ce masu kala ba sai da taga Victoria na niyyar fita da ga dakin sannan taba Victorian hakuri shi kuma Samuel ce mashi tayi "ya fita ya basu wuri tun da shi ba shi da hankali , Victoria tace bata son shi to mi yasa zai ta kura ma rayuwar ta, Komawa Victoria tayi ta zauna sai wani cika take tana batsewa, suna kammala cin a binci fita su kayi bakin wani fanfu suka wanke hannu Victoria ce tace "destiny zan tafi gida domin nayi shirin zuwa church din kuma kin ga momy bata san nafita ba kar ta dawo bata ganni ba, kawai dai kinson zuwane amma aikin san bata dawo ba, da ta dawo da mun iske momy ( mahaifiyar destiny ) a gida itama ta dawo tun da wurin business din su daya, kuma tare suke fita su dawo tare, to kawai Victoria tace, komawa su kayi dakin, destiny tace " kinsan fatan da nake kuwa Victoria, Aa sai kin fada Victoria ta fada tana sauraron mi destiny zata ce, so nake wannan wawuyar hidaya ta taya ki bama dr hakuri kamar yarda da tace, a samu sa'a shi kuma ya maida ki uhmmm zata sha mamakin abun da zamuyi mata dan sai munrabata da eko ma gaba daya yan da ba zata sake ganin dr ba, nima haka nake so zata sha mamaki In dai ya mai da ni wuri na, dariya sukayi harda ta fawa suna nan suna shirya yan da za su yima hidaya sai ga mahaifiyar destiny tashi go , suna jin shigo warta suka fito daga dakin gaishe da Ita su kayi yayin da destiny ke amsar kayan da momyn ta ta shigo dasu, Victoria ce tace "ni na tafi" to saina shigo destiny ta fada tana fita gida ta shiga momynta ta samu a dakin zaune cewa tayi" good afternoon momy , afternoon daga ina kike na shigo baki nan momyn tafa da , ina gidan su destiny ne momy, ok kawai momyn tace, wurin 5:00 suka shirya domin zuwa church ( suna zuwa church su duk ranar Asabar domin gyaregyre sbd lahadi ) gidan su destiny , Victoria taje daga chan suka wuce church din.........
_Katsina......_
Mom ce zaune a main falo suna fira da baaba larai abdallah ne ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya wurin su mom ya zu hadi da cewa fira kuke ne nagan ku zaune, wlh kuwa sai ina haka naga kasha jallabiya mom tafada amsa ya bata da cewa zan danje wani wuri ne daga nan zan tsaya sai angama sallah sannan zan dawo, mom tace" ah kace wurin diyata za'a amma sai kaje mata da jallabiya sai kace wani limami, murmushi kawai yayi hadi da cewa " mi za kiyi da wata diya keda kike da yan biyu duk mata a gaban ki, mom ce tace " duk da ina dasu kari ai bai kin dadi koh baaba larai" haka ne kuwa hajiya baaba larai ta bata amsa, Mom ce ta kuma cewa" ni dai yau she zaka kawo man surukata gidan nan" abdallah ne yace " ki bari mom dana samu wacce ta dace dani zan kawo maki Ita har gida, uhmmm Allah ya shirye ka abdallah wata kan har yanzu baka samu wacce tada ce da kai ba ko, nasan maganinka ai sawa xanyi abie dinku ya zabo maka mata tun da kai ka kasa Mom ta fada, abdallah yace" haba mom kamar ni za'a za boma mata, ai kuwa dana bani , yo ai sai abokaina suyi man dariya, mom tace" to In dai baka son auren dole to ka fito da mata kayi aure, kai ko kunya bakaji shekara 30 fa amma ace baka da mata haba ina amfani ' dan Allah mom kibar batun auren, dolenan , In dai aure ne very soon zanyi in Allah ya yarda, Allah ya yarda mom ta fada, ni na wuce sai na dawo ya fada hadi da nufar kofar fita, a dawo lafiya mom ta fada , fira mom suka cigaba Ita baaba larai suna nan zaune sai gasu Aaimah sun shigo da'a lama daga Islamiyya suke dan jikin su sanye suke da hijabi blue color gaishe da su su kayi sannan suka nufi bedroom din su wanka su kayi hadi da alwallar magrib sannan suka sanya kaya marasa nauyi a daki suka zauna har sai da su kayi sallah isha tukunnan suka fita falo fira sukeyi a kan Islamiyya anan mom tasa me su har da abie wanda baijima da dawowa ba daga masallachi nan sukai ta fira har 9:00 sannan su kayi dinner kowa ya wuce dakin sa suna shiga daki wayar Aairah na ringing dauko wayar tayi dake ajiye kan bedside murmushi tayi data dauki wayar taga mai kiran Aaimah ce tace " halan ya mus'af ne, daga mata kai Aairah tayi to sai da safe domin nasan ke ba yanzu ba Aaimah ta fada hadi da hayewa kan bed taja blanket Ita kuwa Aairah zama tayi bakin bed ta cigaba da waya ba Ita bace ta gama wayar nan ba sai wurin 10:55 sannan ta haye bed adu'a tayi ta shafa hadi da shafa ma Aaimah sannan taja blanket Ita ma bayan ta kashe bulbs da bedside lamp.....
Asuba ta gari yan biyu 😴
ayi haƙuri da yana yin typing ɗin na farko ne
share it pls 🙏