NI DA YAYA ARMAN

5_6

by @autarmama

🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏

Hot love story♥️🔐


```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*


📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚


بسم الله الر حمن الر حين


*BOOK ONE* 📔

🅿️...............5&6


Cikin ta ne ya d'uri ruwa jin Abba na kiranta Cikin kuka ta kalli Haidar ta ce "Na shiga Ukku Haidar Abba Duka na zaiyi ko" Sai yaji yayar tashi ta bashi tausayi girgiza mata kai yayi ya ce "A a ya Aira nidai kawai cewa yayi kizo kuma kinsan Abba bayason yayi kira a bata mai lokaci ki taho muje " shahada tayi ta mik'e tare da Jan kafafunta Wanda dak'yal suke daukarta tsabar tsoro.






Sosai ta tsorata ganin Abba na safa da marwa a palour tana shiga gabanta ba abunda yake sai fad'uwa juyowar da zatayi taji Abba ya d'auke ta wani gigitaccen mari da saida hankalinta ya gushe na d'an wani lokaci kafin ta d'ago ya k'ara kifa mata mari wani irin ihu ta fasa tare da durk'ushewa ta na kuka.








Cable d'in wayar wuta ya d'auko ya nufeta tare da lafta mata daya azabar da taji ce ta saka Kara sakin wani karan "Na shiga ukku zan mutu" Mama ce ta taso hankali tashe ta rik'e cable d'in ta ce "Dan girman Allah Alhaji kayi hakuri karka daketa DA Wannan Abun" Abba ya juyo ya Kalleta ya ce "Zainab ki rabu dani wannan yarinyar bata jin magana ki barni na koya mata hankali" .






"A a Alhaji Dan girman Allah kayi hakuri ka zauna Tukunnama me tayi Abba na huci ya zauna ya dubi Aira da ta ke kuka wiwi ya ce "Had'iye kukan nan yanzu yanzu nan Dan gidanku " Cikin Sauri ta Had'iye kukan sai shshsheka da take cikin tsawa ya ce.








"D'ago ki kalleni Munafuka " Idonta jab'e jab'e da hawaye ta Kalleshi ya ce "Sau nawa Zan rabaki da d'an iskan yaron nan,ban rabaki dashi ba?tana shasheka ta d'aga kai " Bud'e baki zakiyi kimun magana "k a ra ba mu " ta fad'a a rarrabe "Fine Kinsan da haka kuma shine kika cigaba da mu'amula dashi ko Watau bakijin magana ta ko rainani ne kika yi?" Cikin kuka ta fara girgiza kai ta ce "Dan Allah Abba kayi hakuri Bazan sakeba".






" wannan ya zama.last warning da zan k'ara ganinki da yaron can duk irin hukuncin da na yanke maki ki kuka da kanki kina jina"cikin Sauri ta d'ago ta ce "Naji Abba"ki tashi kiban wuri sakarai wacce batasan ciwon kanta ba "hada gudunta Aira ta Ruga tayi dakinsu ta na zuwa ta baje a gado taci gaba da rera kuka Amma Da Ummy su sukayi ta Lallashinta anma kamar k’ara zugata suke.






Mama ko da Mamy sosai basajin dadin wannan al'amarin nasu musamman Abba da ya fi d'aukar zafi , ba Wanda ya kumayin magana cikin su Mamy ta tashi da tsohon cikinta ta tayi d'akinta ta jima ta na hawaye tasan Duka itace silar raba wannan y'an uwa Gashi kuma batajin dad'in yanda Kullum y'arta ta zama kamar jakka akan Arman kullum Abba cikin dukanta yake amma kamarma Kara tunzurata yake Haidar ne ya shigo maza tayi ta Goge hawayen ta Kalleshi ta ce.








" Haidar jeka kiramun Hajara"to Mamy yafada yaje ya samu Aira na Kuka Amma na Lallashinta yace "ya Aira Mamy na Kiranki a d'akinta Gyada mai kai tayi ta tashi ta na Goge hawaye ta bishi ta na zuwa ta zaune gefen Gado Mamy ta kalli Haidar ta ce " Bamu wuri zamuyi magana "Yana fita ta kalli Aira ta ce " ke yanzu Hajara Haka zakiyi ta zama kin maida kanki jaka a gida ko,?kowa ya na zaune lafiya amma banda ke,tunda kika San mahaifinki bayason tarenki da shi meye na likemai Ubanki ne shi da bazaki iya rabuwa dashi ba ko kullum kinfison ke kad'ai ake jinki da mahaifinki na rasa uban me yake baki duk kinbi kin lik'emai sakarai Saikije kiyi tayi ai tunda bakison ciwon kankiba"Aira Abu dukya chunkushe mata ga Abba ya gama laftarta ga Mamy ta hauta da fad'a tashi tayi ta na kuka ta fita tayi waje ta ma bar part din gaba d'aya ta koma part din inna.








Gadon ta ta hayaye a abunda take inbanda kuka shin ya zatayi da rayuwarta ,meye laifin ta ida da Arman akan gabar dake tsakanin iyayensu ga Abba ya gama jibgarta itama Mamy zata hauta da fad'a saida ta gama kukanta harta gode Allah tace "Gashi Shima Ya Arman din yayi fushi dani ya kukeso nayi da rayuwata tafada tana wulli da pillow Ta Kara fashewa da kuka ta ce.






" Tun bansan kaina ba na shak’u da kai yaya ARMAN wacce bazan tab'a iya misalta ta da komai ba ,tun bansan kaina ba ,shakuwar dake tsakaninmu babu wanda zai isa ya rabamu koda za a dinga tsaga naman jikina ana barbada attarugu da barkono bazan tab'a iya rabuwa dakai ba " kuka ta k'ara fashewa dashi ita wai yazatayi da rayuwarta Daren ranar bacci kauracewa idanunta yayi banda kuka ba abunda take sai wajen Asuba bacci ya d'auketa.






©©©©©©©©©©©©©©©




Arman kai tsaye guest house d'inshi ya nufa kwance yake kan makeken gadonshi da komai na d'akin pink ne dakin gabaki dayanshi manne yake da hotunan Aira wasu tun tana yarinya wasu kuma da girmanta wasu tare suka dauka daga shi sai T-shirt da gajeran wando banda tsaki ba abunda yakeja ya ce "Wannan tsoron na mahaifinta da nagani k'arara a kwayar idanunta Tabbas wataran zata iya ruguza alak'armu abunda bazan tab'a jura ba kenan ko sama da k'asa zata had'e ana ruguguwar tashin k'iyama bazan tab'a yarda a rabamu ba my cutie Aira I love her so much,ina jinta har cikin kokon zuciya ta ,i can't live without her inajinta a jinin jikina,tunaninta bai tab'a barin kwakwalwata ba daidai da second d'aya why Abba yakeson rabamu me mukai musu,ina ruwan mu da rigimarsu" Chan ya numfasa saboda bai saba doguwar magana ba ya ce.






" Karfa Aje kuma ita Har yanzu Kallon yaya kawai takemun kartace kuma bata sona wulli yayi da laptop d'in dake gabanshi ya ce "Inaaaaa bazaiyuba haka yayi ta zirga zirga ya k'ulla can ya since can ganin kanshi ya fara kullewa ya tashi tare da daura alwala ya fara jera salloli duk adduarshi akan Allah ya bashi Aira Dan shi kanshi ya kasa gane wannan wace irin jarabtar so ce Allah ya d'ora mishi ta yarinyar nan........✍🏿


Hmm muje zuwa






A gaskiya ina Jin dadin comment dinku sosai masoyan asali kuma ina godiya kwarai da gaske 💃🏾💃🏾💃🏾




*Comment*


*vote*


*Share fisabilillah*#





*_Miss Hajo ce*_🤙🏿