Kukan Zuci Book 1

Kukan Zuci book 1 chapter 1

by @lere

���� Kukan Zuci

Written by Novels Elite.


Wannan labarin ƙirƙirarre ne idan kaji yayi da rayuwarka/ki ayi haƙuri domin banyi hakan da

wata manufa ba sai don nishaɗi. Wannan Labarin kuma kajere ne ba mai tsawo ba saboda

wannan shine littafina na farko.


Page 1.

Free page

Misalin ƙarfe 7:20am (na safe) Zaune suke a falo suna karin safe (breakfast) domin su tafi

makaranta Nabil ya Kalli Annan su yace, "Abba idan na girma na gama karatu zan zama likita

idan baka da lafiya Ni zan dinga kula da kai," kallon sa kawai Abban nasu yayi tare da sakin

Murmushi na jin daɗin abinda yaron nashi ya fadi, domin kuwa yaji dadi sosai. Nabil yaro ne

wanda bai wuce shekaru biyar da haihuwa ba, kyakkyawa ne kuma shi kaɗai ne Alhaji Kabir

Mahi ya haifa Bayan shekaru goma (10) da Auren su tare da Hajiya kubrah. Ƙarfe 7:40 Alh. Kabir

Mahi ya kammala cin abincin sa domin shima zai tafi ofis ya ɗauki Nabil da jakar makarantar sa

da abincinsa, Hajiya Kubrah ta taki su har wajen da motarsasa ke ajiye suka shiga Hajiya na ɗaga

musu hannu alamun sai sun dawo.


Suna tafe a hanya suna fira da ɗan nasa wanda ya zama tamkar abokinsa domin kuwa yana

jansa a jiki domin nuna kulawa ta yadda idan yana da wata matsala zai iya samun sa ya faɗa

masa abinda yake damu da, wanda kuma hakan yana da kyau ka ka ɗan ka ko ƴar ka a jiki ta

haka ne zai sa ba zasu dinga fita sosai ba har su haɗu da abokai ko ƙawayen da zasu lalata musu

tarbiya.


Ba daɗewa suka isa ƙofar makarantar su Nabil sai da Alhaji Kabir ya tabbatar ya shiga

makarantar sannan ya ta fi wajen aikin sa.


Nabil yana matakin aji uku na primary kuma ɗalibi ne mai ƙoƙari sosai a cikin abin su domin

daga anyi tambaya shine ke saurin bada amsar abinda aka tambaya, kuma shima ya kanyi

tambaya akan abinda ya ga bai gane ba ko idan ya Lura sauran abokanshi basu gane ba.


Hajiya Kubrah ta dawo daga rakon da tayi ɗakin ta kawai ta wuce domin ta kammala duk wani

abu da yakamata ta yi saura gyaran gida ne kawai kuma dama suna da me aiki, Lauren. Lauren

dattijuwa ce wacce aƙalla ta kai shekaru hamsin da ɗaya, tana da kirki da haƙuri, ta kai kimanin

shekaru huɗu tana yi ma Hajiya Kubrah aiki, suma suna kyautata mata sosai domin kuwa suna

cikin halin babu wanda dole suna buƙatar tallafi. Ƴaƴan Baba Laure biyar (5) wanda mijin ta ya

rasu ya bari.


Alh. Kabir kuwa ya isa kamfanin sa ke nan na Mahi Motors, Mahi Motors Mallakin Alhaji Kabir

Mahi ne inda ake sayar da motoci kala daban-daban dake cikin Garin Kaduna, wanda ake shigo

dasu daga ƙasar waje duk kalar motar da kake nema zaka samu, Alhaji Kabir ya iya kasuwanci da

hazaƙa domin hakan yasa mahaifin su Alhaji Mahi ya fi don sa akan dukkan sauran ƴaƴan sa.


Alh. Kabir Mahi yana da ƴan uwa guda huɗu inda shi kaɗai ne a wajen mahaifiyarsa sauran

suma mahaifiyarsa daban wanda mahaifiyar Alhaji Kabir Mahi itace Karama.

Misalin ƙarfe Uku na rana (3:00pm) Hajiya Kubrah tayi ma Laure Sallama domin ta fita domin

ɗauko Nabil daga makaranta, Laure kuma tana ƙarasa sauran aikin da ba ta gama ba.

Kiran waya ne ya shigo wayar Alh. Kabir, ya ɗauka da Assalamu alaikum, ba sallama na kira naji

ba, na kira ne naji kana Raye ne ko ka mutu?


Shin wanene ya kira Alhaji Kabir kuma me ke tsakanin su.

Kuyi comment, like da share domin cigaba da samun wannan littafin.