WASA DA RAI

14

by @milhaart

*WASA DA RAI*

Fitattu 5

   ©️ *Milhart*

   *Paid Book*


*Free Page*

      *014*

Yana nan a Arewa Books🥰 link ɗin nan kawai zaki danna.

https://arewabooks.com/book?id=650ae9aa3057a0e54cd67f79

Follow me on Wattpad *@milhaart*

_________Hafsah 

Tunda tayi sallar Isha ta kuma yin wanka, a gaggauce take shiryawa Riga da wando na D&D ta sanya a jikin ta Army green Yayi mata kyau sosai , ta ɗauki farin ƙaramar gyalle ta ɗan rufe kanta da shi, ta kwanta tana danne danne a wayar ta, shiru shiru har ƙarfe tara ta gota bai ƙirata ba sannan ta ƙira shi bai shiga ba alamun ya sata a Blacklist, miƙewa tayi ta fice daga part ɗin ummin ta nufi part ɗin Jalal, a lokacin fadar tayi shiru babu kowa a waje sai securities dake ta zaga cikin fadar, bayin kuwa kowa na makamancin sa.


Da sallama ta shige parlor, Shiru babu kowa dama ta san za'a rina don bai fiye zama a parlor ƙasa ba yafi amfani da na sama, saman ta haura nan ma shiru baya nan , kofar bedroom ɗin sa ta nufa ta tura kofar da niyar shiga ciki amma bai buɗo ba mamaki ne ƙarara a fuskar ta "Rufe kofar yayi ko kuma bai dawo bane?" Ganin bata da mai bata amsane ta dawo ta zauna a parlor haɗe da kunna TV "Wallahi ina nan babu inda zanje yadda kace Zamuyi Magana yau sai munyi ko da kuwa kwana zanyi anan ɗin?" (Ni Ko nace aiki ya same ki,iska tana wahalar da mai ƙara a ka).


Nussy

Na jin ance a sake su ,su tafi ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya, kallon ta AM yayi kallo irin na wanda ya san fuskar ta, ita ma shi take kallo tabbas ta san shi "You" ya furta yana kallon ta cire glasses ɗin sa yayi yace "Kamar na san ki a wani wuri?"

Ya tsare ta da idanu, ji tayi cikin ta yayi wani irin ƙara kululuu.

A rarrabe tace "Ni?" Ta na wiki wiki da idanu, murmushi yayi yace "Nevermind, Let the girls go and take the guys to the HQ" ya karashe maganar yana mai kallon John.

Sara masa John yayi yace "Yes Sir."


Takawa ya fara yi kamar yana tsoron taka ƙasan, motar sa ya nufa ya shige haɗe da barin wurin, Nussy tunda aka sauke su a motar aka ce su tafi takalmi a hannu ta ruga da gudu ba ita kaɗai ba harda sauran ƴan matan ,Nussy ko ta kan Hamza ba tayi ba tayi gaba abinta.


Zainab

Tsoro da fargaba sun hana ta motsi ,kuma ba don komai ba rashin sanin halin da Nussy ke ciki , haryanzu hannun su a tsarke da na juna, lokaci zuwa lokaci Prince ke tsaki, Zee dai ƙala bata ce ba.


AM

Driving yake hankali kwance ,wayar sa na ga ya zaro ya shiga dialing number Jameel, Jameel dake driving ya ji karar wayar sa, ɗan rage speed ɗin motar yayi ya cire wayar a aljihun gaban rigar sa , ganin Sunan AM na yawo a kan screen ɗin ya sanya shi ya taka birki ba shiru.

"Wannan wani irin hauka ne haka?" Prince ya faɗa a ɗan tsawace ya maida kallon sa kan Zee ganin duk ta ruɗe na rungumar ta yayi yana shafa bayan ta, ɗan juyowa Jameel Yayi a rarrabe yace "AM ne fa ke ƙira, kaga ma har ta yanke"

Wani ƙira ne ya kuma shigowa "Pick Up kuma sa a handsfree" ya faɗa cike da bada umarni, yana mai sakin Zee amma kuma haryanzu yana riƙe da hannun ta yana murzawa a hankali.

Hannu na rawa yayi picking "Hello Jameel how far?" AM ya furta daga ɗayan ɓangaren.


"Am fine ya aikin?"

"Alhamdulillah kana ina ne?"

Ɗan ɗagowa yayi yana kallon Jalal , da ido ya faɗa masa ya amsa mana.

"Muna gidan mu Ni da Prince amma yanzu haka mun fito zamuje wani wuri"

"Okay to shikenan"

"Amma lafiya ka tambaya?"

"Kamar na ga motar ka ne a Mil Uku Ashe ba Kai bane"

"Ehh...eh bani bane muna gida"

Ɗan shiru yayi yana sauraron yanda Jameel yake magana duk hankalin sa a tashe "Alright we will meet tomorrow then,ka gaida min prince ɗin."

"Alright Yana amsawa." 

Baice komai ba ya katse ƙiran wani irin ajiyar zuciya jameel ya sauke ya furta "That was close"

"wani close Ka kusa ka kwafsa mtsww" ya karashe yana mai jaan dogon numfashi.


AM 

Yana kashe wayar Murmushi yayi ya

Furta "Something is fishy, Muryar ka ta nuna akwai abinda kake ɓoyewa amma muje zuwa, sannu a hankali zan gano koma mene ne kake ɓoyewa."


Prince

Kalon Zee Yayi yace " A wani unguwa kike?"

Zee tayi nisa cikin tunani bata ma jinsa,shafa fuskar ta da yayi ne ya sanya tayi saurin ɗagowa tana kallon sa "A ina gidan ku yake?"

Kallon shi kawai take murmushi yayi ya kuma shafa kumatun ta "What's wrong naga duk bakya cikin hayyancin ki?"

"Am just thinking about Nussy a wani Hali take ciki?"

"Ki kwantar da hankalin ki tana tare da Hamza Am sure zai kula da ita ,now tell me a wani unguwa ki ke?"

"Orji Quarters, ta gate ɗin Abububar Hashidu House" ta furta da siririyar muryar ta haɗe da sunar da kai a ƙasa sabida kallon da yake mata baza ta iya jura ba.


Jameel kuwa mamaki yake sai kallon Prince yake wai yau Prince ke keyi wa mace magana da sanyi haka? Shi a iya sanin sa bayan Ummi da Aunty amarya sai ƙannen sa baya kula kowa bare ma ya kai ga yiwa mace magana ,amma wannan tun daga kallon farko ya sake da ita, ɗan kyasta hannun sa yayi a fuskar Jameel da yayi nisa cikin tunani , kallon Jalal yake amma a zahiri tunanin sa yayi nisa, a ɗan razane yace "Na'am"

"Tunanin me kake haka dude?"

"Nothing me kace?"

"Mu Kaita gida nace"

"Alright" ya furta haɗe da yiwa motar key.

Sai da sukayi nisa ya tambaye shi wace unguwa ce ya sanar da shi.


Nussy kuwa wani mai mashin ta samu ta tara , sai da ta hau kana ta faɗa mishi inda zai kai ta, a gate ɗin gidan su Zee ya ajiye ta ,ta ɗauki aƙalla mintinan goma a tsaye a gun amma ta kasa shiga, ba komai ya hana ta shiga ba bata so a ce ta shiga ita kaɗai gashi tana ta ƙiran layin Zee amma not reachable, tana nan tsaye taga mota ta faka, a kusa da ita kallon motar ta tsaya yi don ganin wane ne da daren nan dan a lokacin ƙarfe 11 na dare ta ɗan gota.


Jameel na Faka motar ya ɗauki wayar sa ya fara latsawa , don yaga abin Jalal ɗin ya fara wuce tunanin sa, Jalal ne yace "Mun iso ko?"

Kai kawai ta ɗaga masa alamun eh, Gani ta yi ya fita a motar, ya zaga ta inda take ,da kanshi ya buɗe mata marfin motar ta fito, Jameel kuwa baki a buɗe yake kallon su, haka ma Nussy, tana ganin Zee ta fito a motar da sauri ta nufi inda suke tana faɗin "Bestie kece hankali na ya tashi"

Ta faɗa tana rungumar ta , shima Jameel fitowa yayi ya kalli wannan ya kalli wanchan, Jalal kuwa hannayen sa ya zura a aljihu.


Da mamaki Nussy ke Kallon shi Nussy tace "Thank you prince Ashe kuna tare? duk na damu"

"No need to thank me ai an zama ɗaya"

Mamaki ne ya kamata "wai an zama ɗaya gayen da na daɗe ina bibiya ko kallo ban ishe shi ba ,sai yau ya kulani shine yake cewa an zama ɗaya?" Ta tambayi kanta ganin bata da amsar tambayar ne yasa tayi saurin faɗin "Toh Allah ya bar zumunci, jameel mun gode" ta faɗa tana kallon Jameel ɗin.

Murmushi kawai ya mata.

Hannun Zee Nussy ta rike tace "Muje ko? Nasan mama na nan gabata jiran mu."

"Nagode" ta furta kana sukayi gaba, murmushi kawai yayi, sai da ya shigewar su cikin gidan kana ya sauke ɗan gutun numfashi, ya zaga ya shige motar ganin Jameel na tsaye bai motsa ba ya ɗan liko yace "Ya dai ko dai baza ka tafi bane na Barka anan?"

Da sauri ya shige motar yayi mata key a high speed suka bar unguwar.


Da sallama suka shiga babu kowa a parlor hakan yasa Zee tura kofar haɗe da sa key, Nussy bata tsaya jiran ta ba ta shige ɗaki, Bayan ta Zee ta bi bayan ta rufe kofar , ƙaran saukar ruwa taji a banɗaki hakan ya tabbatar mata da cewar ta shiga wanka ne, a bakin gado ta zauna tana jiran fitowar ta ,bata wani daɗe ba ta fito ƙirjin ta ɗaure da towel, ita ma miƙewa tayi ta shige wankan ,kayan jikin ta ta cire haɗe da ajiye sa su a inda take ajiye kayan ta masu datti, wankan ta fara yi tana jin daɗin warm water dake sauƙa a jikin ta, runtse idanun ta tayi tana jin sauƙar ruwan ,Fuskar Jalal ta gani yana mai sakar mata murmushin nan nasa mai ɗauke hankali ta kuma tuno lokacin da ya rike hannun ta yana murzawa nan da taji tsigar jikin ta ya tashi da sauri ta buɗe idanun ta tana sauke numfashi, murmushi ta yi wanda ita kanta bata ma san tayi ba tana mai shafa fuskar ta,sauri sauri ta tayi wankan ta fito, hango Nussy tayi tana kwance haryanzu da towel ɗin a jikin ta, taɓe baki tayi ta nufa gaban mirror mai ta shafa haɗe da ɗan gogan turare a jikin.


"Baza ki tashi ki sa kaya ba?"

Zee ta tambaya tana mai nufar walldrope ɗin ta, Zama Nussy tayi tace "Har yanzu ban dawo dai dai bane wallahi, na tsorata sosai"

"Ke kika tsorata ko Ni?" Tana mai zaro wani silky smooth sleeping dress ash color ,gajeren wando ne sai rigar kuma armless, irin sa ta zaro ta wurgawa Nussy amma shi ɗin baƙi ne.

Miƙewa Nussy tayi ta fara sanya kayan "Amma Zee ya akayi kika bar gun? Don a lokacin da sojojin suka shigo ba ganki ba?"

Waro ido Zee tayi tace "Sojoji? Dama sojoji ne suka shigo?"

"Eh mana, dama baki sani bane? ina kika je?"

  "Muna zaune da wannan Prince ɗin aka ƙira shi a waya, ban ji me aka ce masa ba kawai ya riƙe hannu na muka fito"

"Lallai Zee wato tafiya kika yi? Ki ka bar Ni wato nikam ko oho tunda ke kin tsira ko?" Ta faɗa rai a ɗan ɓace.

"Haba Nussy taya za'ayi na tafi na barki? bayan ba sanar dake yanda akayi hakan , nifa ban ma san su wa suka zo gun ba ya dai ce min escaping Zamu yi Ni ban ma fahimci zancen nasa ba wallahi"

 "Kin kyauta ai, don wallahi har a motan sojoji aka sa mu"

 "Police ko Sojoji naga irin wurin nan akace police ne suke zuwa?"

"Nima dai nayi mamakin ganin su amma alamu ya nuna akwai wanda suke nema , shiyasa ma yace a bar mu ,kuma fa lieutenant AM ne fa da kansa ya zo wurin" ta faɗa a dai dai nan ta gama sanya kayan ta zauna tana mai kallon Zee da ita ta gama

"Waye shi ɗin?"

"Yayan Nana Khadija Mustapha Mahdi ne fa"

Taɓe baki"Ke kika san su"

Ta nufi hanyar fita.

Kallon ta Nussy tayi tace "Ina Kuma zaki?"

"Kitchen yunwa nake ji" bata tsaya jin me zata ce ba tayi ficewar ta.


Ruwan Tea ta ɗaura , kana ta dauko kwai guda 6 ta fasa ,ta yanka albasa da attarugu ta sanya seasoning kana to soya su ta ɗaura akan plate, ruwan na tafasa ta haɗa Tea mai ƙauri cup biyu yasha madara da bornvita, ta ɗaura akan ɗan madaidaicin tray ta shige musu dashi ɗaki, akan wani ɗan madaidaicin Table ta ajiye tana kallon Nussy dake ta latse latse a waya tace

"Wai jira kike sai nace ki zo muci?" Ta tambaye ta tana mai ƙafa kofin Tea ɗin a bakin ta.

Mikewa Nussy tayi ta zauna a gefen ta ba tare da tace da ita ƙala ba.


Cin abincin suke babu wanda yake magana, sun ɗauki kusan mintuna 10 a haka Nussy tayi gyaran murya tace "Amma kin san nayi mamaki sosai?"

Zee sai da ta kurɓi shayin kana tace "Mamakin me kenan fa?"

"Da wai Prince ne ya dawo da ke har gida"

"Toh me abin mamaki anan? taimako na fa yayi"

"Baki san Yarima Jalal bane, girman kan tsiya ne da shi, Ni fa tunda nake ban taɓa ganin shi yana dariya ko magana da mace ba amma ke fa har dariya ya ke miki bayan hakan ma kuma ya riko hannun ki ya taimake ki"

"Uhmn" kawai Zee tace

"Kin san shekara nawa nayi da sanin sa?"

"Umm umm sai kin faɗa"

"Shekaru Uku kenan, tun lokacin da ya dawo daga kasar waje nake ta so muyi mu'amala dashi amma yaki bani haɗin kai, ke in takaita miki ma ko kallo na bayayi sai da ga baya na fahimci cewar abokin Hamza ne , da muka je wani club naga sun rungumi juna , tun daga nan nasan na rasa shi kenan"

Dariya tayi ganin yanda lokaci daya Nussy ta zama abin tausayi kamar zatayi kuka tace "Kefa kika ce yana da girman kai to me zai sa ki tada hankalin ki a kansa?"

"Baza ki gane bane , Abduljalal ƙarshene , ga kyau ga kuɗi ga sarauta"

"Bangane sarauta ba?"

"Ɗan Sarkin garin nan ne fa?"

"Dan Allah dagaske kike ko wasa?"

"Mtsww to da ƙarya zan miki?"

Murmushi kawai tayi ta mike haɗe da tattare plates ɗin ta fita dashi.


"Wai Meyasa duk wani abu da nake so Zainab ce take samu? Ko da yake Abduljalal yafi ƙarfin ki nasan ba ƙara haɗuwa zakuyi ba." Ta karashe ta na murmushi ,mikewa tayi ta kwanta.

Zee na kai kwanukan kitchen ta dawo ɗakin, kashe wutan daƙin tayi ta bar bed side lamb da hasken ba sosai ba, tayi kwanciyar ta itama, ba daɗewa barci ya yi awun gaba da ita, Nussy kuwa sai da tayi chart ɗin daren da ta saba da samarin ta kana ta ajiye wayar tayi ba daɗewa itama barcin ya ɗauke ta.


Jameel 

Driving yake lokaci zuwa lokaci yake waigawa yake yana kallon Jalal, Jalal dake an kare dashi yace "faɗi maganar dake bakin ka mene ne ka ke ta kallona haka? Bashi ko tara?"

"Ai dole na kalle ka , me kake nufi da Yarinyar nan? Allah yasa dai ba tarko ka ke so ka ɗana mata ba?"

Murmushi yayi "Wai me ka ɗauke Ni ne? Kawai ta burge Ni ne, bayan wannan kuma babu komai"

"Toh Allah ya sa" dai dai nan suka isa gida ,Horn ya danna a gate ɗin fada, da sauri ya mike ya wangale musu gate ɗin, hancin motar ya danna cikin gidan, dare ne amma ko ina haske hatta allura zaka iya ɗaukawa.


A parking lot yayi parking Motar, Jalal bai tsaya jiran sa ba yayi gaba abinsa, sai danya rufe motar kana yani bayan sa, Jalal na sanya kafar shi a cikin parlor ya saki murmushi Jameel dake tsaye a bayan sa yace "Lafiya kake murmushi kai kaɗai?" Yana mai ɗan lekowa yana kallon fuskar sa.

"Lafiyar ce ta sanya yarinyar nan tana da taurin kai amma zan gyara mata zama nan ba da daɗewa ba"

Cike da rashin fahimta Jameel yace "Wace yarinya kenan fa?"

  "Hafsah" yana faɗa ya fara hawa stairs,da ɗan sauri jameel yabi bayan sa "Me kuma Hafsah tayi?" Tsayawa yayi yana kallon Jameel , wannan shu'umin murmushin nan nasa yayi ya furta

"Tana cikin part ɗin nan"

Baki a buɗe yace "Wa ya sanar da kai? Nifa wasu lokutan kana bani tsoro wallahi"

"Kwantar da hankalin ka mutumina kasan dai bazan taɓa cutar da kai ba ko?"

"Na sani amma ya akayi kasan Hafsah na nan?"

 "Hmmm baka yarda ba ko muje ka ganewa idanun ka" ya cigaba da tafiyar sa.


Yana turo kofar suka hango ta zaune akan 1 seater har barci ya sace ta , daga gani ma baccin na wahala take sabida kwanciyar bai mata daɗi ba, murmushi Jalal yayi yace "See bana faɗa maka ba?" 

"Ikon Allah but how?"

Murmushi jalal Yayi yace "Kaje ɗayan ɗakin ka kwanta , sai da safe"

"Ni fa shigowa nayi na maka sai da safe"

"A daren nan ne zaka fita? Dallah malam kaje ka kwanta"

Ya nufi kofar bedroom.


Jameel yace "Ita kuma fa what will you do with her?" Yana mai kallon hafsar.

"Just go kai kam" yayi shigewar sa ɗaki.

Jameel kuwa ɗan jim yayi yana kallon ta, cike da tausayin ta girgiza kai kawai yayi ya fice ya shige ɗayan ɗakin da ke wajen parlor Jalal ɗin, shima room and parlor ne, ko ina kal kal dashi , yana shiga bedroom ya nufa ya faɗa akan gado ba addu'a ba komai ya kwanta kamar kayan wanki.


AM

Kai tsaye gida ya nufa yana tunanin ta yadda zai ɓullo wa lamarin wannan Empire ɗin, har ya isa gida bai samu mafita ba, a parlor ya Tarar da mammy tana kallon TV ɗan ɗago kai tayi jin sallamar sa miƙewa tayi haɗe da amsa sallamar tasa "Mummy ba kiyi barci ba?"

"Taya zanyi barci AM? Bayan baka dawo ba kai na zauna jira" murmushi yayi sabida kullum haka take ina dai ya fita baza ta kwanta ba har sai ta ga dawowar sa.

"Haba Mom yanzu fa Ni ba yaro bane ya kamata ki daina damin kan ki a kaina"

Murmushi tayi tace "Kai yaro ne a wurina har a bada, kashe Tv nan sai da safe" ta fara takawa ,kallon ƙafa ta yayi yaga tana ɗan ɗingisawa yace "Mom kafar ne? Ya naga kamar kina ɗingishi?" 

"Eh tun safe yau na tashi da shi"

"Kuma shine baki sanar dani ba?" Ya faɗa kamar mai shirin kuka.

Murmushi tayi irin nasu na manya "Naji sauki, kar ka damu" ta cigaba da tafiyar ta.

"A a gaskiya zamuje asibiti gobe"

"Toh Allah ya kaimu" ta sani tunda yace zasu je ɗin bazai kyale ta ba sai sunje ɗin ,ko kaɗan baya wasa da lamarin ta hakan yasa take matukar ƙaunar sa.

TV ɗin ya kashe haɗe da Haurawa daƙin sa.


Jalal 

ne tsaye akan Hafsah ya sauya kaya zuwa Pjs da alama wanka yayi murmushi yayi ya fara tashin ta a hankali yana ƙiran sunan ta, a hankali ta ware idanun ta ta sauke su akan shin, murmushi ta sakar mishi tana miƙa shima ya maida mata da murmushin.

",Ka dawo?" Tana mai gyara zaman ta

"Eh na dawo,dare yayi tashi ki koma side ɗin ku"

"A a Ni gaskiya tsoro nake ji" tana mai turo baki.

"Toh kwana zakiyi anan ɗin?"

"Eh gaskiya nikam kwana zanyi"

"Lallai yarinyar nan baki da hankali" ya ayyana a ransa a zahiri kuma daure fuska yayi kamar ba shi ba yace "Tashi ki tafi nace ko na saɓa mishi" ya faɗa babu wasa a fuskar sa, ai kuwa mikewa tayi da sauri barcin ya watse tace "To dan Allah ya Prince ka rakani part ɗin mu ,kasan fa an fara sace mutane a masarautar nan ina tsoro Gaskiya"

 "Wato maganar ta fara fita, dole na san abin yi" a zahiri kuma yace "Muje" tayi gaba yana biye da ita.


Part ɗin Ummi suka nufa ,basu kai ga isa part ɗin ba wata ƙatuwar kuliya ta bayyana a gaban su, jikin ta fari da baƙi tana wani irin kuka , idanun kuliyar blue ta yi tsaye tana kallon su, Hafsah tsalle tayi ta faɗa a jikin sa tana faɗin "Na shiga Uku." Ta kuma dakin girki wani ƙara haɗe da kankame shi da dukkanin ƙarfin ta.


Ku sani a addu'a plz bana jin daɗi sosai.

*🆕RELEASE🔰*


  '''FT5'''


    2️⃣0️⃣2️⃣3️⃣




💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *hohoho Allah ya kawo mu qarshen shekara tazo😍, masu iya magana suka ce mai laya kiyayi mai zamani🤸🏼‍♀️, wani kaya sai amale🏇🏼, in kaji ana a marmatsa to giwa ce ta iso🥳,haka in kaji kira ba banza ba🤩...Ina ku ke masoya, ma'abota karatun littafan hausa, kuma masoya littafanmu🥰, Hajiyoyi kun karanta waɗannan littafan ba?, LULLUƁIN BIRI, MUGUN NUFI, CAPTAIN FAWZAN, MATAR UBA, SUNE SILA....To ya ku ka ji salon dukka labaran?😍, sun ƙayatar ba?, sun tafi da ruhika ba😅?, to fa ai su ɗin duk ba komai ba ne, somun taɓi ne cikin shirin da muka yi na nishaɗatar da ku a sabbin labarai masu jan hankali🥰ku shirya kawai ku biyo mu cikin tafiyar TEAM FITATTU BIYAR, salon labaran da suke daban da saura, labarai masu tarin darasi, ma'ana da kuma tsuma zuciyar me karantawa da sauraro😍...LITTAFAI BIYAR A ALƘALUMA BIYAR CIKIN MAFARKI ƊAYA😍...Hajjiyoyi da Alhazawa da kuɗi ƙalilan za ku mallaki littafan da baza kuyi danasani da nadamar siya da karantawa ba💃🏼, akwai tarin ilimi aciki🫶🏼, akwai nishaɗi😹, wa'azantarwa🌝ga uwa uba ƙayatacciyar soyayya mai saka jiki kyarma saboda tsantsar shauqi😍...*




*LITTAFAN SUNE KAMAN HAKA👇🏻*


1- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*


2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*


3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*


4- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*


5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*


_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_


_LITTAFI BIYU:- ₦800_


_LITTAFI UKU:- ₦900_


_LITTAFI HUDU:- ₦1000_


_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_


_VIP 2k._


Za ku biya kuɗi ta wannan account...


*6314170140*


*FIDELITY BANK*


*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*


sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*


katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*




*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*


_LITTAFI ƊAYA:- 350f_


_LITTAFI BIYU:- 600f_


_LITTAFI UKU:- 650f_


_LITTAFI HUƊU:- 750f_


_LITTAFI BIYAR:- 850f_




'''ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-'''


*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*


*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*


*_•TICTOK 1500_*


*_•INSTGRAM 1500_*


*_•FACEBOOK 1500_*


*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*


'''ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)'''


*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*




MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩


*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*


________________

Milhart Ce

Ƴar Terawa