WASA DA RAI

15

by @milhaart

*WASA DA RAI*

Fitattu 5

   ©️ *Milhart*

   *Paid Book*


*Free Page*

      *015*

Yana nan a Arewa Books🥰 link ɗin nan kawai zaki danna.

https://arewabooks.com/book?id=650ae9aa3057a0e54cd67f79

Follow me on Wattpad *@milhaart*

Murmushi Prince yayi yana kallon kuliyar ido cikin ido kamar yadda kuliyar ke kallon sa,ɓanɓare ta yayi a jikin sa haɗe da dafe goshin ta nan take ta sulale ta faɗa a ƙasa sumammiya "Ka bayyana kan ka tun kan na illata ka" Prince ya faɗa da wata iriyar murya kuliyar kallon sa kawai take tana kuka, ran Prince ya kai kuloluwar ɓaci nan da halittar sa ta fara sauyawa izuwa wata iriyar dabba Ni kaina sai da na tsorata nan take Ya koma shi ba kare ba kuma ba damuwa sa , wata irin halitta ya koma jikin sa baki ƙiran idanun sa sun koma yellow dai ɗan ɗigon baƙi a ciki , hakwaran sa suka canza suka zama dogi biyu na gaban sun fi ko wanne tsayi kamar na Vampire, a hankali yake takawa yayi gaba yayi baya , Kuliyar bai ankara ba sai ji yayi Ya danne da haɗe da rike shi a wuya nan da nan ya ɓulla wuyar kuliyar, Yana ganin hakan ya wurgar dashi a gefe.


Nan take kuliyar ta canza izuwa suffan Mutum, Shima yana ganin haka ya rikiɗa ya koma Jalal ɗin sa ya nufi kan mutumin, da ƙafa ya taka wuyar mutumin , shi ko numfashin sa kamar zai ɗauke, sai tari yake yana kokarin kwace kansa amma ina Jalal yafi karfin sa "Wa ya turo ka?" Ya tambaya a tsawace kuma da wata iriyar murya mara daɗin ji, ganin mutumin na son yi Magana ne ya sassauta dannewar da ya masa tari mutumin keyi kamar zai sheka, murmushi naga mutumin yayi ɓat ya ɓace a gun.


Naushi Jalal ya kai wa Iska, ya furta "Who is he? Wa yake son ganin bayana?" Ganin ba mai bashi amsa ne ya nufi inda Hafsah take , ɗaukar ta yayi ya lumshe idanun sa ,amma ga mamaki na naga sun ɓace, bai bayyana a ko ina ba sai a ɗakin ta ajiye ta yayi akan gado, ya juya ya fice daga ɗakin , tafiya yake hankali kwance yana taku kamar wanda yake tsoron taka kasar ko kuma kasar zaiji ciwo ne, Part ɗin su ya nufa yana shiga bedroom ɗin sa ya nufa, ban ɗaki ya nufa ya sakarwa kansa ruwa ya fito ɗaure da towel a jikin sa , Kan gado ya faɗa ya kwanta haɗe da rufe jikin sa da duvet ba tare da ya sa kaya ba, Toh asuba ta gari Prince.


Washe Gari

Misalin ƙarfe 8 na safe Zainab na hango a kan sallaya da alama ta idar da sallah,Yayin da Nussy kuma ke kwance tana ta sharar barcin ta, banko kofar da akayi ne ya sanya Zee tayi saurin ɗago kanta a razane , ganin mama hankali a tashe Zee ta mike tana faɗin "Mama Lafiya kuwa?"

"Zainab fito fito Jikin baban ku ya tashi" bata tsaya jin sauran maganar ba ta fice da gudu kai tsaye ta shige ɗakin baban,akan gado ta hango shi sai tari yake da sauri ta nufi inda take ta dafa shi "sannu bana" take ta jera.

"Na shiga Uku" ta furta da ƙarfin ganin jini na fita daga bakin da, Mama da Nussy ne suka shigo a tare suma hankali a tashe, da gudu Nussy ta fita ta ƙira mai gadi , da taimakon sa suka sanya baba a motar Zee, zee tsabagen ruɗewa ta ma manta cewar ba ta wani iya motar sosai ba, a haka ta ja motar suka nufi FTH Gombe, Nussy dage gaba a wurin zamar mai zaman banza sai salati take, Mama kuwa na Baya da baba Kan shi ta ɗaura a cinyar ta sai furta "Sannu malam,sannu malam" take, gudu take shararawa akan titi bata ji bata gani, hankali a tashe ko da ta zo bakin gate na Asibitin ba ta tsaya karɓan card ba ta shige da gudu securities na dagatar da ita bata bi ta kan su.


Emergency ta nuta , tana kwala ƙiran sunan Nurse, da gudu Nurses biyu suka fito da gadon maras lafiya suka ɗaura baba akan gadon maras lafiya, kai tsaye emergency room aka kaishi akayi sa'a kuwa likitan da ya masa tiyata ne ya ƙarɓe shi, kasantuwar ya san cutar tashi hakan ya sa ba ɓata lokaci ya fara bashi taimakon da yake buƙata, Zee duk ta fice daga hayyancin ta sai kai kawo take tana Safa da marwa, , Nussy ce ta riko ta "Ɗan Allah Zee ki Zauna mana ki kwantar da hankalin ki"

"In kwantar da hankali na fa kika ce? Kina ganin baba Yana ciki rai a hannun Allah taya za'ayi na kwantar da hankalina?"

  "Na sani kuma zai samu lafiya insha Allah ki daina tada hankalin ki" Zee gaba tayi abinda ta bar ta tsaye, "Kyale ta Nusaiba haka take yi idan ta ga ciwon baban su ya tashi zo ki yi zaman ki" mama tayi maganar jiki a sanyaye, Yanda mama tace Nussy tayi wuri ta samu ta zauna a gefen mama.


AM

Sai da sukayi breakfast ya matsa akan sai sun zo asibitin , murmushi Mummy tayi tace "Princess Je ki ɗauko min mayafina idan Son ya fara maitar nan nashi baya ji kuma baya gani"

  Mikewa Princess tayi tace "Mummy Nima zan bi ku" a shagwaɓe tayi maganar ,hararar ta AM yayi , buga ƙafa ta fara yi "Ayya Mummy Ya AM na harara ta"

"Kyale shi, maza ɗauko min mayafina yi sauri"

Sai da tayi masa gwalo ta haura sama da gudu "Yarinya zaki zo ki same Ni ne"

Murmushi Mummy tayi don taga abin da Princess ɗin tayi.

"Bari na fito da motar" AM ya furta yayi ficewar sa.


Da sauri Princess ta fito hannun ta riƙe da mayafin Mummy ta miƙa mata, a tare suka jera a hankali Mummy ke takawa sabida ɗan zaman da tayi gwiwar ta ɗan riƙe, har entrance na parlor ya faka motar da sauri ya fito ganin Mummy ya buɗe mata baya ta shiga ta furta "Allah yayi albarka " murmushi yayi ya amsa da Ameen.

Turo baki Princess tayi "Mummy Ni fa?"

"Kema Allah ya miki albarka" 

Murmushi tayi ta buɗe gaba ta zauna, sai da ya bari ta zauna kana ya kamo bakin ta ya murɗa "Ni sa'an ki ne?" Ƴar ƙaramar ƙara ta saki "Wallahi kika min kuka sai na sa wuƙa na yanke miki baki"

"AM ban son cin zali sakar min bakin yarinya"

Turo baki shima yayi kamar yadda Princess take yi yace "To Mummy baki ga abin da take min bane?" Dariya Mummy tayi tace "Allah ya shirya min ku ,muje Ɗan Allah kar mu makara"

"Ai mummy na riga na miki booking appointment muna zuwa zai duba ki"

"Duk da hakan dai muje ,kasan fa ba son asibiti nake ba" key yayi wa motar suka nufi gate, Mai gadine ya buɗe musu gate Yana ɗaga hannun "A dawo Lafiya"

"Allah yasa" AM ya furta haɗe da zuge glass ɗin sama suka fice a gidan.


Tuki yake a hankali, don ya sani sarai idan ya fara gudu Mummy zatayi korafi, lokaci zuwa lokaci yake kallon Princess da tayi shiru ta turo bakin nan ita ala dole an ɓata mata rai, riko hannun ta yayi "Haba My Princess Wai fushi kike da yayan ki?"

  Sake turo baki tayi bata ce komai ba "kinyi shiru"

"Toh yaya ba kai bane ka murɗa min baki kuma da zafi fa"

"Ai dama ba don kiji daɗi na yi ba ,horo ne bakin da ya min gwalo na murɗa" ɗan waigowa tayi tace "Mummy kina jin sa ko?"

Ɗan ɗagowa Mummy dake latsa wayar ta tayi tace "Kinga Kyale Ni kun fi kusa"

Dariya yayi har ƴar dimple ɗin sa suka lotsa ,fizge hannun ta tayi , tana matsar kwalla.

"Am sorry, am sorry bazan sake ba, wallahi idan kika ɓata rai sai kiyi kama da dodonniya"

Murguɗa baki tayi tace "Eh ɗin idan ma ka zagi halitta ta kan ka ka zaga tunda kamannin mu ɗaya"

"Eh amma na fi ki kyau"

"Wallahi na fika" girgiza kai kawai Mummy tayi tana hamdala a zuciyar ta , da Allah ya bata ƴaƴa masu ƙaunar junan su , duk da tazarar shekaru dake tsakanin su amma hakan bai sa ya ja ƙanwar sa a jiki ba. Wani dogon numfashi ta saki a tare suka juyo "Mummy lafiya?" suka furta suna kallon ta, "Lafiya lau, kai dan Allah focus on driving da kake" juyawa yayi ya cigaba da driving din suna hira sama sama, har suka isa asibitin.


Kai tsaye Office ɗin likita suka nufa, dake dama yasan da zuwan su, ƴan rubuce rubuce yayi ya miƙa wa AM yace "Yallaɓai ga wannan , kuje physiotherapist Department , Idan kuka je chan za'a duba a ga mene ne matsalar zuwa yanzu kafar na bukatar a duba shi sosai"

  Godiya yayi masa ya miƙa masa hannu, suka fice daga Office ɗin tafiya suke suna hira gwanin sha'awa , Mummy sai murmushi take.

A waje suka zauna kasantuwar likitan da zasu gani yana da Patient.


Ya ɗauki aƙalla mintuna 30 kana ya fito, Office ɗin sa suka shiga, miƙa masa paper Yayi ya duba kallon Mummy Yayi yace "Hajiya seat here"

Yana mai nuna mata wani kujera , mikewa tayi ta zauna , shima zama yayi kusa da ita "Wani ƙafa ne?" Ya tambaya yana mai kallon kafafun ta ,ƙafar ta na dama ta nuna masa yace "Ammmm.... Am sorry aikin mu da observation ne dole sai na taɓa ta,hakan kuma bazaiyu ba sai da amincewar ku" yayi maganar yana mai kallon AM.

"Go ahead" AM ya bashi amsa.


"Okay ya furta" haɗe da miƙewa wani gado ya nuna mata yace ta kwanta, bayan ta kwanta ne yace da ita ta ɗage zanin, bayan ta ɗaga ne cike da kwarewa ya fara duba ƙafan nata bayan ya sanya hand gloves , duk motsa ƙafar da zaiyi sai ya tambaya ko taji zafi ta girgiza kai, yana yi yana kallon fuskar ta don ganin facial expression ɗin ta, yana juya ƙafar ta hagu yaga ta rintse idanun ta "Does it hurt?" 

Ka ta ɗaga masa tana mai jin zafi, ɗan sake ƙafar yayi

"Kin taɓa bugewa ne ko kin faɗi?"

"A a ban taɓa ba"

"Kin tabbata ki tuna dai"

Ɗan jim tayi tana son tuna wani abu

Nan ta tuno baya a ranar da aka kama Daddy ,ya ture ta yana mai faɗin "Ki fita" a sannan ne ta faɗi ɗan rintse idanun ta tayi ta kuma ware su tace "Eh na taɓa faɗuwa"

AM dake kallon su ya ce "Mummy when kika faɗi ban sani ba?"

Murmushi kawai ta masa bata ce ƙala ba.

Neurogesic ya ɗauko ya fara murza mata a hankali tun tana jin zafi har ta soma jin daɗin yanda yake massaging na ƙafar nata, ya daɗe yana murzawa kana ya cire gloves ɗin yace "Zaki iya tashi" ya koma Kujerar sa ya zauna , prescription script ya ɗauko ya rubuta wasu drugs ya miƙa masa 

"Zaku samu wannan a pharmacy , drugs ne da kuma cream , sannan zata riƙa zuwa kullum safe da yamma ana duba ƙafar har na tsawon sati biyu" yayi maganar yana mai kallon Princess, ɗagowa AM yayi yaga dai Dr na magana amma hankalin sa na wani wurin bin idanun sa yayi yaga yana kallon Princess dake ta faman buga game a wayar ta da alama tana jin daɗin game ɗin take sai murmushi take, AM ji yayi kamar ya shake sa ,ɗan gyaran murya yayi amma ina Dr ya shagala da kallon ta, buga desk ɗin yayi da ƙarfi, Ba iya Dr ba hatta Mummy da Princess sun tsorata sosai

"Zai fi kyau idan ka maida hankali akan aikin ka, ka daina kallon ƴan mata"

Dr ji yayi jikin sa yayi sanyi yace "Sorry sir, anjima da yamma zaku dawo da misalin ƙarfe 5"

Mikewa yayi ya riko hannun Mummy yace "let's go"

Princess kuwa tun buga desk ɗin da yayi bata dawo dai dai ba don ta tsorata sosai kallon yayi rai a ɓaci "And you, zaman me kike yi?" Ya tambaya yana tsare ta da idanu, sum sum ta Mike ta fice suka rufa mata baya.

"Ya Salam what have I done? Ko dai matar aure ce? Amma dai naga suna kama duk yadda akayi ƙanwar sa ce amma Meyasa duk ya ɓata rai har haka?" Dr Bello ya jero wa kan sa tambayoyin nan. Murmushi kawai ya cigaba da duba Patients ɗin sa.


AM ne yace "Mummy ku Zauna anan bari na karɓo maganin sai mu tafi"

To tace sai da ya zaunar da ita ya juya da niyar tafiya , Princess tace "Yaya za bika mu....." Wani irin kallo ya mata hakan yasa tayi shiru haɗe da zama a gefen Mummy ba shiri, girgiza kai kawai Mummy tayi, shi ko AM ko a jikin sa ya wuce pharmacy bayan ya biya ya nufi pharmacy ya karɓo maganin, tun daga nesa ya hango Mummy da Princess zaune a inda ya bar su suna ta hira, murmushi ya saki ba shiri, kan ya karasa ya hango Dr Bello ya fito yana tambayar Mummy basu tafi ba? Mummy ta amsa masa da "Jiran sa muke ya je pharmacy" ɗago kansa yayi ya hango AM dake masa wani irin kallo yana ganin ya nufo su yayi saurin barin gun, Mummy cike da mamaki take kallon sa lokaci guda taga ya ruɗe, ganin AM da tayi ne yasa ta gane dalilin sa na barin gun.


Riko hannun Mummy yayi, ya kalli Princess "Oya Nana let's go" tana jin ya ƙira ta da Nana tasan abun ba sauki , Princess ɗin dama shi ya sa mata kuma sunan ya bita, mikewa tayi suka jera ,yana rike da hanun Mummy Sun Sanya a tsakiya.


Zainab

Dr ne ya fito da sauri ya miƙa mata prescription ,yi sauri ki karɓo wannan" tana karɓa ya juya ya koma ciki da sauri, da sauri ta bar gun ta nufi pharmacy na Emergency aka tabbatar mata da ya ƙare, Nussy na biye da ita taga ta fito tace "Ina kuma zaki ina maganin?"

"Wai babu sai dai muje GOPD" tayi gaba.

Nussy tace "Kiyi tafiya a hankali mana"

"Kin fa san nisan gun kuma kice haka?"

Ta cigaba da tafiyar ta harda haɗa a da gudu , Nussy dai tafiya take duk da saurin da take amma ta kasa riskar ta.


Bata an ƙara ba sai ji tayi ta buge abu kamar dutse da baya baya tayi tangal tangal zata faɗi ,yayi saurin sakin ledan dake hannun sa ya kamata, Zee kam ta sadakar Zata faɗi ,jin an rike ta tayi saurin buɗe idanun ta ta saki ajiyar zuciya,ta furta "Am sorry thank you" ta zare hannun ta , ta gefen Mummy ta bi ta bangaje ta, bata bi ta kanta ba ta cigaba da tafiya da sauri don kwata kwata bata ciki hayyancin ta, AM kuwa ransa ne ya ɓaci , juyowa yayi "Ke stop" ya daka mata tsawa , chak ta tsaya ba tare da ta juyo ba. A hankali ya faro ta ku baiyi wata wata ba ya fuzgo ta ya ɗaga hannun sa sama zai wanka mata mari.

"Don't you dare" ta furta da ƙarfi, ya ɗago rinannun idanun sa yana kallon ta.

____________________


*🆕RELEASE🔰*


  '''FT5'''


    2️⃣0️⃣2️⃣3️⃣


💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *hohoho Allah ya kawo mu qarshen shekara tazo😍, masu iya magana suka ce mai laya kiyayi mai zamani🤸🏼‍♀️, wani kaya sai amale🏇🏼, in kaji ana a marmatsa to giwa ce ta iso🥳,haka in kaji kira ba banza ba🤩...Ina ku ke masoya, ma'abota karatun littafan hausa, kuma masoya littafanmu🥰, Hajiyoyi kun karanta waɗannan littafan ba?, LULLUƁIN BIRI, MUGUN NUFI, CAPTAIN FAWZAN, MATAR UBA, SUNE SILA....To ya ku ka ji salon dukka labaran?😍, sun ƙayatar ba?, sun tafi da ruhika ba😅?, to fa ai su ɗin duk ba komai ba ne, somun taɓi ne cikin shirin da muka yi na nishaɗatar da ku a sabbin labarai masu jan hankali🥰ku shirya kawai ku biyo mu cikin tafiyar TEAM FITATTU BIYAR, salon labaran da suke daban da saura, labarai masu tarin darasi, ma'ana da kuma tsuma zuciyar me karantawa da sauraro😍...LITTAFAI BIYAR A ALƘALUMA BIYAR CIKIN MAFARKI ƊAYA😍...Hajjiyoyi da Alhazawa da kuɗi ƙalilan za ku mallaki littafan da baza kuyi danasani da nadamar siya da karantawa ba💃🏼, akwai tarin ilimi aciki🫶🏼, akwai nishaɗi😹, wa'azantarwa🌝ga uwa uba ƙayatacciyar soyayya mai saka jiki kyarma saboda tsantsar shauqi😍...*


*LITTAFAN SUNE KAMAN HAKA👇🏻*


1- *ƘAYAR RUWA na Halimahz*


2- *FARGAR JAJI na Aisha Abdullahi Yabo*


3- *WASA DA RAI na Fadeela Yakubu Milhat*


4- *LOKACI NE na Fatima Oum Mumtaz*


5- *KWANTAN ƁAUNA na Nana Haleema*


_LITTAFI ƊAYA:- ₦500_


_LITTAFI BIYU:- ₦800_


_LITTAFI UKU:- ₦900_


_LITTAFI HUDU:- ₦1000_


_LITTAFI BIYAR:- ₦1200_


_VIP 2k._


Za ku biya kuɗi ta wannan account...


*6314170140*


*FIDELITY BANK*


*SA'ADIYYA ZAKARIYYA HARUNA*


sai ku tura da shaidar biya tare da sunan littafin da kuke biɗa a wannan number....*Oum Mumtaz(***)*


katin waya zaku tura hoton MTN da sunan littafin ta wannan number...*Milhat(***)*


*ƳAN NIGER KU TURA DA KUƊINKU TA Mkoudi 89356025 airtel, SANNAN KU TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBA...Aisha Yabo(***).*


_LITTAFI ƊAYA:- 350f_


_LITTAFI BIYU:- 600f_


_LITTAFI UKU:- 650f_


_LITTAFI HUƊU:- 750f_


_LITTAFI BIYAR:- 850f_


'''ƳAN KASUWAN DA ZA'A TALLATA MAKU HAJOJINKU DOMIN KASUWANCINKU YA ZAGA IN DA BAKU YI ZATO BA, TALLAN YA KASU KASHI-KASHI:-'''


*_TALLA A KOWANNE PAGE NA BOOK 500, 5pages2k, Complete Book 10k._*


*_•TALLA A VEDIO NA YOUTUBE 1500_*


*_•TICTOK 1500_*


*_•INSTGRAM 1500_*


*_•FACEBOOK 1500_*


*_•WHATSAPP STATUS; 24hrs500, 48hrs1k, 72hrs1500, 168hrs3500._*


'''ku tura da kuɗin ta account numbern da ke sama sannan ku tura da shaidar biya haɗe da details na abin da kuke so a muku talla akai ta wannan lambar...NanaHaleema(***.)'''


*Youtubers da suke son mallakar littafanmu domin ɗorawa a channel sai kuyi magana a wannan lamba...Halimahz(***).*


MUNA MARHABAN DA KOWA CIKIN MUTUNTAWA, A ISO LAFIYA🤩


*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga duk wanda ya siya littafin Fitattu Biyar...son so fisabilillah😍*


________________

Milhart Ce

Ƴar Terawa