NI DA YAYA ARMAN

13-14

by @autarmama

🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏

Hot love story♥️🔐


```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*


📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚


بسم الله الر حمن الر حين


*BOOK ONE*📔

🅿️...............13&14


Cikin zazzak'ar muryarshi Mai cike da kassala a hankali ya ce "My Cutie baki girma har yanzu ko kin manta gaban mutane muke kike rungumeni " ya fada kamar bashi yayi maganar ba murmushi tayi tare da sakinshi ta ce "Sorry yaya murnar ganin kace ta sa na ma manta da mutane a gurin" Aike gimbiyace bakya laifi my cutie "Uhm My yaya ammafa Gaskiya kayi surprise Dina da yawa bantab'a tunanin zaka zoba" Ranar graduation d'in Cutie na guda ace banzoba ai Abu baiyi dad'iba yanzu dai ki shigo mu tafi gida ma ida maganar a hanya ko"to my yaya bari naje nakira Amma Tana barin wajen ya zagaya ya shiga mota.





Aira na komawa khady tayi mata Dariya tace “ummm kwt har anfara love kenan kice mu fara shiri kece bikin farko a mate “harara ta galla mata tace “sa’idinawa kawai yaya nane to sannan tace muntafi sai mun had’e online “tukwana sukayi hug din juna suka rabu Amma na baya Aira na gaba haka suka tafi a hanya sai satar kallonta yake harsuka isa ba mai cewa uffan sunzo daidai bakin gate din inna sukaga fitowar motar Abba ta gate d’in gidansu cikin faduwar gaba Aira tayi k’asa da kanta dan kar Abba yaganta abunda bata saniba tuni yaganta saida taga wucewarsu tukwana ta dago tana sauke ajiyar zuciya Shidai Arman girgiza kai kawai nan ya gyara parking a waje Amma ta fita tare da cewa thnks Aira zata bude motar taji kulle juyowa tayi ta kalleshi saita sakar mai murmushi shima ya mayar mata tare da cewa.




“Ina kika saka wayarki jiya nayi ta kira a kashe”uhm yaya wlh wayarce kasan boyeta nake bana yawo da ita ko tsakar gida dan kar wani yagani shiyasa tana locker d’ita tun jiya sai da zamu sch nadaukota dan muyi hotuna “.



“Ajiyar zuciya ya sauke ya ce “nazata ba lafiya shiyasa na taho saida nazo nan nake tambayar haidar a bangaren inna yacemun kuna sch yau kuke last paper “wayyo yaya wai saboda baka sameni ba a waya kawai ka taho i’m sorry “ta fad’a ta na langabar da kai”Shitttt Kin manta bakya laifi komai kikayi daidaine my cutie “sannan ya dauko wata karamar waya daga cikin kwali tana gani ya daga ya saka wani sabon sim card tukwana ya bude ta yace “amshi wannan karamace saikidinga yawo da ita yanda duk sanda na kira zan sameki “murmushin jin dadi tayi tace Thnks my yaya”banson godiyarnan fa daman kinsan yau kuke graduation shine baki sanar daniba “uhm yaya na manta shiyasa “Allah bada sa a Ya fitar da sakamako me kyau kawai yace sannan yace “zan wuce dear baki bukatar komai”Eh yaya bana bukatar komai ganinka ma ya wayadas Bazaka shiga ku gaisa da inna ba “dazu mungaisa ai zanje na hutane kafin gobe na wuce “kamar zatai kuka tace “yaya gobe kuma yayi kusa ai”Zandawo soon yanzun akwai aikin da na baro shiyasa I am sorry gobe idan ba jirgin Safe zanhau ba zanbiyo muyi bankwana idan kuma na samu na safe na wuce kawai “hawaye ne suka fara zubar mata tace “shikenan yaya Allah ya kiyaye ya tsaremun kai “handkerchief ya d’auko ya fara share mata hawayen ya ce “Idan nazo kinamun kuka idan zan koma zandaina yawan zuwa dan bakisan yanda nakejin kukanki a cikin zuciyata ba “cikin sauri ta had’iye kukanta da take shirin cashews’





“sorry yaya bazan sakeba banson kana nesa dani ne shiyasa idan ka tafi yaushe zaka dawo “shima ji yake kamar yayi kukan yace “nafi kowa bukatarki a kusa dani dan bayanda zanyine next week insha Allah zanshigo na kwana biyu “to my yaya Allah ya maidoka lafiya “ki kulamun da kanki kinji my cutie “murmushi tayi tace “kaima ka kulamun da kanka sun dan taba hira kadan tukwana yayi mata bankwana ya wuce ji suke kamar karsu rabu da juna.





Aira koda ta shiga gida bata iske kowaba sai Ummy da Haidar da amma da suka dawo tare “Ya Ummy ina y’an gidan naga ba kowa bangaren inna ma bata nan”ta fad’a tana Waige waige “Suntafi kai Mamy asibiti “wara idanu tayi tace “Asibiti kuma me ya sameta “Haihuwa zatai “langabar dakai tai tace “wayyo Allah sauketa lafiya ranar bangarensu ta kwana sai addua take Allah sauke mamy lafiya dakyal bacci b’arawo yayi awon gaba da ita.



************


Arman kai tsaye guest house dinshi ya wuce dan yasan ya biya ta gida Mummy saisunji dalilin da yazo to yace musu saboda Aira ko me hakan yasa ya wuce chan bayan yayi wanka t-shirt kawai ya sanya da gajeran wando fresh milk kad’ai yasha tukwana yabi lafiyar gado dan akwai gajiya sosai tattare dashi yau jinshi yake cikin farinciki saboda ya hadu da Airanshi lumshe ido yayi a hankali ya ce “I love her so much Cox she’s beautiful “tunowa lokacin da yaganta cikin unifoam yake kyakkyawar fuskarta kawai yake ta hangowa da yanda take sakar mai murmushinta mai narkar da zuciya tuno lokacin da ta rungumeshi yayi ji yayi tsikar jikinshi ta tashi kamar wanda aka tsunkula haka ya zabura rumtse idonshi yayi sosai kafin ya bude su mikewa yayi ya dauko wani hotonta sosai tayi kyau cikin Wata black laffaya daga gani hoton bai jima ba kafe hoton yayi da idanu bako kiftawa kafin ya fara shafa hoton yana murmushi shi kad’ai yace “I love you my Aira ina sonki sosai Airata ki soni please ko kadan ne yafada yana marairaicewa (🤣nikam nace Arman karfa ka haukace)rungume hoton yayi a haka baccci me dad’i ya daukeshi cike da mafarkin Airanshi.


*********

Washegari Su Aira su na bacci Ummy ta tashesu cikin murna tace ku tashi yanzu mama ta kira Mamy ta haihu “Aira kamar an tsikareta haka ta tashi tace “da gaske Ya Ummy me ta Haifa”nima ban tambaya ba yanzu dai Mama ta kira tace da asuba ta haihu mu gyara gidan tare da Laure(yar aikin su)ba jimawa zasu dawo.



Cikin murna Aira ta tashi da dinga murna nan suka gyara gidan wajejen 12 su Mamy suka dawo gida inna dauke da jaririn mamy ko duk tayi lakwas Aira sai murna take ganin k’anin nata shima fari me kyau dan duka d’iyan Mamy su ukkun fararene Haidar ne ma baiyo hasken mamy sosai ba nan yan barka da yan uwa suka fara shigowa.



Aira ko bayan flowers ta koma domin kiran Arman taji ya tafi ko zaizo dan taga har anyi la’asr tana sand’o ta ciro k’aramar wayar da ya bata daman ta hardace number dannawa kawai tayi saitaga yamayi mata save da My yaya murmushi tayi tanajin karason Arman na ratsa kowani sassa na jikinta saida kiran ya katse kafin ta kara kira taji kiranshi ya shigo murmushi jin dadi tayi tare da kissing d’in wayar tace I love you my yaya tukwana tayi picking..........✍🏿



Manage ba yawa 😊


Share saboda Allah 👏



_*Miss Hajo ce_*🤙🏿