15-16
by @autarmama
๐ *NI DA YAYA ARMAN* ๐
Hot love storyโฅ๏ธ๐
```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*
๐ *JARUMAI WRITERโS ASSOCIATION * ๐
ุจุณู ุงููู ุงูุฑ ุญู ู ุงูุฑ ุญูู
*BOOK ONE*๐
๐ ฟ๏ธ...............15&16
Daga dayan bangaren Arman ya ce "Hello Cutie ykk " lfyqlau yaya harka tafi ko"ta fad'a cikin sigar shagwaba "Yanzu haka ina Abuja my cutie jirgin 9 nabi shiyasa bansamu nazo nayi maki bankwana ba".
"Ayya to Sannu ya gajiyar hanya "Alhmdllh ya fad'a yace Yadai Naji kamar kina cikin farinciki my cutie Shakomun " Dariya tayi jin ya ce Wai shak'omun ta ce "Yaya Mamy ta haihu fa ".
Daga bangarenshi kamar tana ganinshi ya zaro ido ya ce "da gaske cutie Ah dole muyi farinciki me muka samu" Namiji ni nama zaci mace zata Haifa na samu y'ar uwa kawai sai ta haifi namiji"ta fada tana turo baki .
Dariya yayi har tana jiyowashi cikin waya sosai k'uruciyarta ke burgeshi komai ya fito daga bakinta fad'a kawai take cikin shagwaba ta ce " Dariya ma kakemun ko"Sorry my Beauty Kece kikaban Dariya kince ke mace kikeso ko?"Eh yaya ni mace nakeso " To yanzu shikenan tunda Mai faruwa ta faru saimuyi addu'ar idan Kikayi Aure Haihuwarki ta farko ki haifo mana mace mai kama da ke ko?wara idanu tayi kamar yana gabanta kunya duk tabi ta lullubeta ga yanda yayi maganar ya d'an kulle mata kai "Ki haifo mana?sai muyi addua?Aranta take maimaitawa me yake nufi ?
tsinkayar muryarshi tayi da cewa " Yadai cutie kikayi shiru"Uhm "kawai tace duk kunyarshi ma takeji" Shiko bangarenshi da gangan yayi mata har yanzu yana so ya furta mata Kalmar so amma ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar nuna mata k'arara yanda zata gane ko baice yana sonta ba ta d'auko hanya.
Jin tayi shiru ya sanyashi sauya maganar da cewa"Ki d'auko mun hoton kanan namu ki turoman"Ajiyar zuciya ta sauke jin ya sauya maganar ta ce "To yaya Anjima zand'aukarma" Hango Ummy tayi na nufo wajen cikin Sauri ta ce "Yaya sai anjima Ga ya ummy nan ta maza ta katse wayar ta boye bayanta.
" Ummy ko tab'e baki tayi Dan ta ganta sarai ta ce "Kidaibi A Sannu rawar kan nan taki karta kaiki ta baroki Manya ma Abba ya bida bare ke tsirit" Aira ko kauda kai tayi ta na gunguni Saida taga wucewarta tukwana ta mik'e ta sanya k'aramar wayar a jikinta tayi bedroom d'in Mamy ta k'ara yimata ya jiki ganin d'akin da mutane ya sanya ta juya ranar duk sanda taso ta dauki jaririn hoto a wayarta ta turamai gagara tayi.
Sai washe gari wajen 11am taje gaishe da Mamy ta tarar da Ita ta na Toilet ga Alamun wanka take kuma jaririn na kan Bed shi kadai cikin Sauri ta Ruga part din inna ta ciro wayarta dake locker ta boyeta a jikinta koda ta koma tayi sa a har lokacin Mamy wanka take cikin Sauri ta fiddo wayar ta shiga d'aukar babyn hoto a snap sosai yake yin kyau.
Cikin Sauri ta bud'e data ta shiga ta turama Arman hotunan Sannan ta shiga status tayi status daman bata d'auki number kowa na gidansu ba Dan haka ba Wanda yasanma tana da waya bare har Susan tana chat tana gama dorawa ta sauka ta maza ta kira Arman tana lek'awa Kar wani ya shigo ta na kara wayar a kunne yana d'auka cikin Sauri ta ce .
"Na tura maka hoton ka hau ka gani " rikicewa tayi ganin Fitowar Mamy tayi tsaye bakin bathroom d'in ta na kallonta maza tayi cikin Rashin gaskiya ta kashe kiran Tare da Boye wayar a bayanta "Wace waya ce na gani a hannunki?ta tsinkayi muryar Mamy " .
kafin kace me idonta sun cika da hawaye ta fara in ina karya ma take so tayi abun bata saba ba ta kasa "Mamy ta daka mata tsawa ta ce " nace wayar uba waye na gani hannunki mik'omun wayar Mamy ta fad'a ta na nufota Tashi tayi tana ja da baya ta ce"I m sorry Mamy bazan Sake ba"me nace kinyi da zakice bazaki sakeba kuma wlh na k'ara magana baki mik'omun wayar nan ba zanmiki abunda baki tunani"Tuni Aira ta fara Kuka.
tsawa Mamy ta k'ara daka mata ba arziki ta mik'a mata wayar ta na yayyarfa hannu kamar wacce aka daka "jujjuya wayar Mamy ta fara cike da mamakin ganin wannan tstsadar wayar Dan taga a Instagrams ana tallarta kudinta sun haura 700k " Kallon tuhuma ta kalli Aira dashi ta ce "Wayar wacece?Tawace Mamy Dan Allah kiyi hakuri kar Abba yaji " .
ta fad'a cikin kuka "Salati Mamy ta rafka ta salamce ta ce " Na shiga Ukku ni Rahama Aira lalacemun kikeso kiyi Ki rik'e har wayar kusan 1 million a gidan nan batare da sanin kowaba Aira kunyata ni kikeson kiyi uban wa ya baki wayar wannan me tsada kuma banason kimun k'arya wlh kika kuskura kikamun k'arya saina lillisaki kuma na kira babanki na fad'a mashi maza fad'amun ubanwa ya baki yanzunnan " Tuni cikin Aira ya fara d'urar ruwa kuka ta k'ara fashewa dashi to ita me za tacewa Mamy Arman zatace ya sai mata kowa ..........โ๐ฟ
*Tofa Fans ku taimaka ku bawa Aira shawara ta shiga matsala wa zatace ya saya mata waya ๐ฐ๐ขgaskiya ni harta bani tausayi*
*_Miss Hajo ce_*๐ค๐ฟ