TANTIRIYA A GIDAN YARI

Chapter 4

by @asmabaffa1

🏫 TANTIRIYA🏫

    A GIDAN YARI




       16-20



Official


By

AsmaBaffa




SADAUKARWA

GARE KI❤️

AIDA MAMAN TASNIM





Page naku ne

Najida Aliyu Bicca

Mhiz Awwal







*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka  kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

***

***






     Yau ma akwai kidan koroso da rawa kusan kullum sai an musu kidan koroso da rawa a gidan yari amma iya bangaren masu daurin rai da rai watarana harda Yan solo ana kawo musu domin nishadinsu,wani lokacin Kuma akwai ranar Yan drama suma suna zuwa ciki bangaren Yan life in prison a musu sabo da nishadi,yau ranar koroso ce za ayi da yamma har zuwa magriba.


   Ko wanne yazo Inda Tantiriya Naila yau tazo tayi kallo itace bakuwa, Naila tace ba kidane a gabana ba in fita daga gidan nan shine target dina,duk kansu Jin Jamilu suke a shashasha,Dan Indo Yana Shan sigari yace idan ka fita kayi magana na baka babban aiki wlh,kaje a baka bindiga banza ka zauna ana maka sharri a banza kayi na gaske akwai binda Dan kutmar...kai Allah, Naila dariya tayi tace Allah ya tsare ni da kisan Kai tana maganar Yan Daudu harda shanye hannu, tace ni Jamilu duk wani iya shege Dani ake farashi,ai mune wakilan shedan ehehehayye...Dan Indo zuciyarsa ta buga wani birge shi Jamilu Dandaudu yayi,haka kawai yaji Yana masifar kaunar Jamilu,a ransa yace Ina ma mace ne Jamilu,ko ace ni Dan neman Maza ne da na kwashi harka a wajen Jamilu.


  A hankali ya faki idon Naila Tantiriya ya rike damtsenta tare da jawowa,yaji wani laushin masifa ya wani jawo shi talau,ashar ya dura tare da ja da baya ya dafe kirji Yana kallon Jamilu yace amma Kai tun a cikin uwarka dama Dandaudu ne?, Naila ta tsuke baki tare da furta tunda na fado duniya ni dama babarmu tace kukana da nake yi maimakon aji Inya Inya sai aji Ina cewa Zaniiiiii....Zaniii....idan na shide sai aji kukan ya canja sauti Dan.....Dankwaaaaaa......liiiii....DanIndo ya kwashe da dariya, Muler Dake gefensu Yana Jin hirarsu Yana ta dariya yace Kai Jamilu amma uwarka ta haifo Dan iska,Naila tayi fari da Ido tare da shanye hannu tana tsuke baki ta wani lashi labbanta sannan tace ya ranka ka daina gatsa sunana kamar kana gatsar rake ka kirani da Jamilu Tantiriya haka nake,sai ta dauki mintuna kafin tayi magana sai ta tsaya ta gama karairaya da wani lankwashewa sannan take magana.


  Wani me suna Farau Farau shine ya Kalli T.k ya Masa rada yace nifa tunda aka kawo yaron can Jamilu wlh na fada matsananciyar kaunarsa ni ba me neman Maza ba abin nan Yana damuna,Tk yace abinda zan fada Maka ka rigani kenan wlh abin Yana damuna,kusan duk mutanen gidan Nan kaunar Jamilu suke anya ba asirin farin jini ne da shi ba kuwa,Cikin rada Farau Farau yace kaga kaga kalli Yana murmushi Kalli... Dan Allah baiyi kama da mace ba? Tk yace a macen ma full option,ance jikinsa laushi kamar me,muje mu taba Muji,Muler da Tk suka taso da niyyar taba hannun Jamilu su ji,sai kuwa Dan Indo yaji wani uban kishi ya make hannun Muler yace wlh kana taba Jamilu sai na rushe Maka hakora,sun san DanIndo sai suka koma Inda suka taso,Naila a ranta taji dadi Sam DanIndo ya tsaya mata ba Wanda ke kawo mata wasan shirme sabo da suna ganin abokin Dan Indo ne.


  Naila ta juya ta Kalli Dan Indo tace Ina baka labari abokina,yace Ina jinka,ai Ina fada Maka ni idan nazo waje shedan ya kan bace yace oga tazo har gisuwa yake kawo min ida na shirga wata tsiyar,badan gidan yari ba da yanzu na kashe auren Yaya na, amma kisan Kai bada ni ba,Dan Indo ya furta mene a cikin kisa ai kawai Wanda yayi akuya kawai ka caccaka Masa wuka,ai ni billahillazi da me zarto nake amfani cewar wani me suna Baballe da ya tsomo musu baki, shi da yake babban Dattijo ne ma,ya kunna sigari yace maganin shege sai Dan Banza Tantiriya Jamilu,ai karka sake a kawo ma raini ko a gidanku ne,Naila tana Jin halin kowa iri iri.


   Tunda tazo gidan yari Dan ragowar tsoronta ya gudu, Uban Dawa yana wajen yace ni ka san daga Ina tsiyata ta fara? Maza nakewa fyade,in ketawa Namiji haddinsa ba komai bane duk girman gardi nayi niyyar lashe Masa Timber karya yake ko ubansa waye,Baki suka hada suka yi wata shaharriyar shewa da ihu harda,suna da masifar yawa a wajen sun hada uwar daba,wani da ake kira da Goje yace ke Tantiriya wanne tsiya kika yi a kasar Nan ta alfahari? Wacce kai da kanka Jamilu idan ka tuna kake jinjinawa kanka? Naila tace Ni Jamilu nine wanda na saka Budurcina a caca tun farkon fara Daudu nawohoho suka furta kamar Wanda suke shuka abin arziki haka suke hirarsu,


   Fitsara da rashin mutunci a cikinsu ba a magana,akwai Yan iskan da su tsirara ma sukeyi watarana a ciki uban kowa ya gansu,duk wani sabon me laifi da aka kawo shi gidan yari Wala mace ko namiji tofa kowa sai yaji labarin an kawo sabo, sai Kuma an San waye,duk iskancin mutum akwai Wanda ya ninka shi sau dari a ciki,suna zaune Naila taja DanIndo da Goje wanda suka fi mutunci tace kwana nan zan bace a gidan nan,Goje yace ta wacce hanya Tantiriya? Naila tace ta bangaren Mata zan koma nayi shigar mata,dariya suka saki,tace wlh da gaske nake,ta bangaren Mata Anfi samun damar guduwa idan ta kama,daga part din Mata sai bayan Daji Kunga kuwa sai fecewa,Goje yace ai kuwa kana haurawa zaki karairaye, ka Kalli uban katangar gidan,tunaninka katangar banza ce,a banza zaka ga kartai sun kasa tserewa, gashi yanzu an Kara kwalabe da wayoyin shocking kana tabawa sai mutuwa,Naila tace bazan yarda daku ba,to munji yanzu ta ya zaka shiga bangaren matan har ka zauna ba a ganeka ba,Bari zaku gani bari yayana yazo zai kawo min kayan Mata ku gani.


  Bikin Spark an saka rana an saka bikin a kurkusa, babu bata lokaci Mummy ta matsa Masa ba yanda ya iya,sai masifa yake yi,yau gidan su Asmau yaje har gaban iyayenta ya musu warning yace idan kuka aura min yarku ba ruwana da Yar uwa ce zan iya kashe ta nine ajalinta gwara ma ku janye ato ba abinda zai hadani da ita ya fada ne Dan ya tsorata su a fasa auren,yaci gaba da furta me zanci da yarku bana sonta ko dole ne ana so dole ne Dan kawai Kuna Yan uwana sai ku takura min.


  Baban Asmau kuwa masifar son 'ya'ya ne da shi,sai abinda yaransa suka ga dama shi suke yi ba a yiwa yaransa fada bare ace ba a sonsu,shi indai kana son yaronsa to ka gama da shi,tunda ya fuskanci Spark baya kaunar yarsa shike nan ya tsani Spark yake mugun Jin haushinsa,sabo da yaga iyakarsa shi yasa ya dage ayi aurensa da yarsa ko tsawa idan yayi yarsa ya sa a ransa sai ya daure shi,sai yayi amfani da mukaminsa da hanya da kudinsa yaga karshen Spark a duniya, Suna jin Spark ya gama masifarsa ya fice ya bar gidan tare da shiga motocinsa suka bar gidan,Baban Asmau yace ni Kuma bari naga karyarsa bari a dawo da bikin nan da sati daya idan ya isa ya mata ko tsawa ya gani ni Kuma ba rangwame wallahi sai ya kare rayuwarsa a gidan yari Kuma bazan ma barshi a gidan yarin Abuja ba kar ma suje suyi cin hanci,l,Lagos zansa a batar da shi,ni dama bana son yaron nan tunda ya taba kwace min wata Kwangila da gomnati ta bani. 


  Kawai Baban Asmau sabo da shima babban Soja ne sai yace a dawo da bikin sati daya,Spark sai labari yaji wai an dawo da bikinsa sati daya,a fusace ya tafi gidan Mummy, shi yayi driving shi daya yana shiga ya samu Mummy a palonta tana takaba amma Dan masifa sai tayi bikin kamar ba me takaba ba har lallenta take yi, ya durkusa a kasa a gabanta,haka kawai ya fashe da kukan karya,yana hawaye yace wlh bana sonta Dan Allah karku aura min ita,bazan iya rayuwa da ita ba,ni bata min ba,Mummy ko kissing nata bazan iya ba bakinta ya min girma sai ta hadiye min bakina Kinga nawa Mummy ya turowa Mummy karamin bakinsa,yace ki tuna na Asmau kamar kofar ShopRite ya sake fashewa da kukan karya tare da Dora kansa a cinyar Mummy,a boye Kuma Dariya yake, Dariya Mummy tayi ta rike hannayen Spark tace yau Spark da hawaye akan mace,yace wlh bana son ganinta ko a hanya bare ace zan aureta,ni Spark ace za a min auren dole wlh bazan shiga gidan ba ko an kaita gidana.


  Mummy tace ka makara ka koyi sonta wlh yau saura kwana shida zaka ganta a gidanka,mikewa yayi Yana cika Yana batsewa hakarsa bata cimma ruwa ba,sai ya koma spark dinsa ya daure fuska Yana kunkuni ya fice cikin fushi dama kukan karya yayi ko za a tausaya Masa sai gashi ba nasara.


  Spark Yana ta bincikensa akan Case din Naila ya zaiyi ya fitar da Jamilu a gidan yari ga matsalar aurensa,kamar wasa biki yazo ranar Friday za a daura Kuma a ranar za a Kai amarya ba wani biki za ayi ba sabo da Mummy tana takaba,Spark har ya hakura ma yace Allah yasa haka shine Mafi alkhairi ya zaiyi.


  Ana gobe daurin aure tare suke da Kamal suna Hira, Spark yace na kyale yarinyar Nan sabo da son da take min,taci darajar Sona da take yi amma fa bazan ko hada room da ita ba wlh har ta gaji tace na sake ta shine kawai adalcin da zan iya,ni zan hada jiki ne da wacce zuciyata ke so wacce ta kwanta min a rai wacce bana kyankyami, Kamal zamuga wace Yar sa'ar Nan Yar gidan waye idan Kuma Asmau ce zata sace zuciyar to,Spark yace hmmm ya Kalli Kamal yace zaka Gani inshaallah,ai Asmau bazan taba sonta ba,ni ba abinda ta min kawai Allah bai sa min ko digon sonta ba,hasali ma a duniya ba wacce na tsana irinta.


   Asmau kuwa Banda murna ba abinda takeyi,itakam shagali take matukar zata zauna gida daya da spark to rayuwa ta mata dadi ko da bazai kulata.

  Washe gari Friday daurin auren Spark dukkan Yan uwa da abokan arziki sun hallara har abokinsa Kamal duk sun dauki wanka amma ba ango yace bazai je ba wlh,mahaifinsa da Mima mahaifiyarsu sunyi iya yinsu yaki zuwa,haka aka daura aure ba ango,shi Yana Office ma aikinsa yake ya kashe waya kar ma ayi Masa Allah sanya Alkhairi,haushi yake ji in akace Allah sanya Alkhairi, zuwa Yamma aka Kai Masa Amarya sai kace dole,amarya anci gayu an hade,har aka watse ango bai zo ba,shuru shuru haka Amarya ta mike tayi alwala tare da gabatar da sallah sannan tayi Shirin bacci ta kwanta abinta,Nawwar a ranar a Office dinsa ya kwana ma bai je gidan ba.


   Asmau kuwa bayan ta kwanta bacci, sai da safe dangin Amarya suka zo zasu mata sallama zasu tafi garinsu amma sallamar duniya a palon ba a bude ba,har suka gaji tare da shiga ciki suka zauna a Palo nan ma shuru shuru,suka fara duba bedroom dinta sai kuwa suka hangota a kwance ta Kalli sama idonta a kafe,da sauri suka isa kanta suna tabata shuru har ta sandare ta kame, Dake akwai dattijai a ciki suka tabbatar ta rasu,wuyanta ga shatin igiya Nan da alama igiya aka sa tare da shake mata wuya har ta mutu,sai kuka da kuka suna cewa dama angon yace sai ya kasheta to kuwa da gaske ya kasheta shike nan sai bige bigen waya azo ango ya kashe Amarya ya gudu baya gidan ma.


  Hankalin kowa ya sake tashi a family gaba daya,iyayen Spark kowa suka tattaro sai katafaren gidan Spark, Kamal ma da gudu yazo gidan,iyayen Asmau kuka suke suna cewa wallahi baza mu yarda ba,mahaifiyar Asmau ta fada kan gawa tana kuka tace Asmau...Asmau na....wayyo ya kashe min Yata bai San zafin haihuwa ba, Mummy da gudu ta shugo gidan tana wallahi Dana bazai yi kisa ba ban yarda ba karya ne sharri ne ta Fadi a kasa tana kururuwa,Mummy a duniya tana son spark ko uwar data haife shi baza ta fada mata son Spark ba,kamar ranta haka yake,tace wallahi da nasan haka zaku ce bazan daure gindin Spark ya auri Asmau ba.


  Mutane ba Wanda ya yarda da Mummy duba da halin Spark da Kuma furucinsa Kuma an San baya karya shi yasa har iyayensa na gaskiya suka yarda, Baban spark shima Soja ne ya Kalli Baban Asmau yace kuyi bincike ku dauki mataki akan Ashraf ya girbi abinda ya shuka,Mima uwa to fa uwa ce amma Mummy ta fita son Spark itama tace idan an tabbatar shine a hukunta shi, sai kuka take tana cewa tabbas yara haihuwarsu jarabawa ce,mu iyaye muna ganin jarabawa akan yaran da muka haifa, Rafeeq zuwa yayi shima Yana ta al'ajabi amma bai yarda Spark zaiyi haka ba sabo da yasan halin Spark.


  Baban Asmau dama kadan yake jira yasa aka Kai gawa asibiti duk wani gwaje gwaje anyiwa gawa amma komai normal bata ci wata guba ba da wire ko igiya aka shaketa har ta mutu,Spark aka shiga nema lungu da sako babu Wanda yayi zaton Yana Office,sai da Yan sanda suka dangana da Building dinsa,gashi Baban Asmau ya musu alkawarin mahaukatan kudade na mamaki shi yasa suka dage.


Suna shiga ciki ko Ina a bude yake sabo da ma'aikatansa duk sun zo aiki,har Office dinsa suka shiga sai kallon tsaruwar office din suke,akwai Palo a ciki suka karasa a Nan suka same shi Yana ta bacci hankalinsa kwance kasancewar jiya baiyi bacci da wuri ba Yana ta aiki.


  Tashinsa suka yi sun san da kudi shi yasa ba raini suka tashe shi,a hankali ya bude idonsa ya kallesu da uban yawa a kansa sun zagaye shi,kallonsu ya sake yi yace lafiya? daya daga ciki yace matarka Asmau....kafin ya rufe Baki Spark yace Allah yasa ta mutu na huta da mayya,me ya faru? Sheda ta Kuma tabbata sai suka fito da sarka tare da furta You are under arrest, ana tuhumarka da kashe matarka,Idanuwa Spark ya zaro yace kisa Kuma ni? Yaushe ma na kwana a gidan? Mamaki ya kamashi,Asmau ce ta mutu? Su dai yanda suka ce zai raina musu hankali ne kawai suka sakala Masa sarka a hannaye yace ba sai Kun sa min sarka ba zan iya binku normal cire min chain,ba musu suka cire Masa.


 Spark yana furta innalillahi wa innailayhirrajun yaci gaba da cewa ko a lahira Allah karka hadani da Asmau, ya Allah ka gafartawa Asmau ka yafe mata,Allah ka gafarta mata irin shiga hakkina da tayi ta aure ni bada izinina ba l,Allah na yafe mata ka yafe mata,kansa ya jinjina yace uhhmmmm su Asmau an matsa min lamba Allah ya yafe miki,Sadakin ma sai da Papa ya biya min,Allah ya miki Rahma uhmm rabo to..dama ance rabo Yana kisa,sai da nace a hakura rabon wata ne aka ki ji, Yana magana ya tattara documents dinsa da kudadensa da duk wani Abu nasa me amfani ya fito dasu tare da Yan sandan motocinsu sunfi biyar suna ta jiniya.

  Manager dinsa ya mikawa yace ka kaiwa Mummy kace ta ajiye min ba Mima ba Mummy nace,yace angama sir,ya shiga mota yaransa masu aiki a karkashinsa suna kallo Yan sanda suka tafi dashi.


 Yana can aka sallaci Asmau tare da kaita makwanci,Yana motar Yan sanda ya Kalli Inspector guda yace iceko takaba bata hau kaina ba? sabo da tsabar ya raina musu hankali,Kuma wulakanci Spark ne,Yana da kudi to ba uwar da suka iya Masa,dama duk jaraba akan talaka take karewa, Spark sai kallon raini yake musu,suna ta Shan wulakanci iri iri.


   Inspector yace Kai nifa Inspector ne,Spark yace no Inspectataatatatataaaa,yaja wani tsaki Kuma ba uwar da suka iya yi,shuru ya musu fuskar nana hade, har suka kaishi tare da tsare shi,ko tambaya suka Masa baya basu amsa a mutunce,shine ya Kara basu haushi sosai.

  Duk wasu bincike an fara yinsu akan Spark amma ba hujja shi ya kashe Asmau,Baban Asmau kudi yake dannawa Yan sanda akan a Masa duka to shima Spark Yana da kudi Kamal Yana kawo kudi dole basa iya dukansa ko farcensa basa iya tabawa gashi tsagera Yana da kwarjini,Inda Allah ya saukaka ma da wuri Baban Asmau ya Kai Kara kotu ta can Lagos,ana ta faman bincike yaga zasu bata Masa lokaci ya Maida karar Kaduna,Nan ma yaga Spark ya fishi hanya ana ta daga sharia gashi ma za a bada bailing Spark,tsoro yaji kar ya cale kasar waje,yasa aka sake tsare shi sosai aka Maida case kotun dake Kano state.


  Yayi hakane Dan ma kar Ashraf ya bada cin hanci a sake shi,duka dangi ma sai labari suka ji ai an Maida shi kano.

  Wani mugun azzalumin Alkali ya samu sannan da lauyoyi azzalumai, Spark Yana tsare ba dama yayi katabus,Mummy duk kulla kullarta Baban Asmau ya fita gashi babban Soja ga kudi kamar yayi, gashi namiji ya fita basira,iyayen Spark da danginsa sunki shiga cikin case din sabo da spark ba Wanda ya kyale shi yasa suka kyale shi.


  Suna ji suna gani aka Masa sharrin kisa ta karfi tare da yanke Masa daurin rai da rai shima a gidan yari.

  Spark yaga masifa ana kawo shi ciki gidan yari Naila ce ta fara ganinshi tace wow, sai data tsaya ta kare Masa kallo Yana wani gadara da kyar yake tafiya fuskar nan a hade ba mutunci dama ya lafiyar Kura bare tayi zawo, sai kallonsa akeyi sabo da kyansa da gadararsa ana ganinsa an San Dan gidan wani kusa ne a kasar, Naila ce ta fito tana tafiyar Yan daudunta tabi bayansa tana kiransa tace wannan zaka dace da Daudu,ni Kam nayi budurwa,ta fara kiransa da Asabe....Asabe....ko Tabawa ce ne? Tabawa...ahhh Ashe ba tsohuwa bace sannu ko sunanki Kamariyya? Jin Muryar mace sosai yayi mamaki ya juyo ba shiri,gashin kawai ya kalla yace a ransa Ashe Dan daudu ne,Naila ce ta katse Masa tunaninsa da cewa Kaiiii gaskiya kina kama da Lady Gaga, jar Uba I love you, shike nan ga suna na Yan gayu Iklima ai yafi?,ni sunana Dahara,wani takaici ya kama Spark,Sam shi ya tsani mutum dandaudu wani tsanar mutum yake yi,ga wannan gaba daya suffar mata gare shi, Naila kuwa ta jera dashi taci gaba da cewa,Sunana Dahara sunan ya samo asali ne tun Ina karama Allah ya sa min yin tsarki,kullum ni dai na dauki buta nayi in tsarki shine aka canja min Suna Dahara, Kuma fa Ummata sanda tana da cikina ance Bata iya rike fitsarinta shine kullum ta dauki buta shine ana haifo ni nima kullum da buta a hannuna dole aka gaji Dani aka sa min Dahara.


  Look ni ba wani abu nake so ba,kawai abokina zaka zama sabo da ba karamin girma bane a ganni tare da Kai,kawai ma ace Ina Dating naka ai ni na zama kadara, duk Inda ya sa kafa Naila tana biye da shi,mutanen gidan sai daga mata hannu akeyi a matsayin Dandaudu ne kowa sai yace su Jamilu Terror anyi sabon kamu, Naila tace harka ce ta Uhmm humhum,hankalinta ta Maida wajen Spark tace to shike nan da sunanka zan na kiranka, ya sunan naka? Ko kulata baiyi ba, ganin Dandaudu y matso kusa da shi hannu yasa ya ture Jamilu,ai Naila rikicif sai gata wanwar a kasa, lebenta na kasa ya fashe kadan,Mamaki ya kama Spark namiji guda daga Dan ture shi yayi wannan uban faduwar haka,Bai San macece ba,a ransa yace wannan ya gama kashe kansa ya zama macen gaske,wait tsayawa yayi Yana tunani da yasa hannu a jikinsa yaji Laushi haka,wani sabon mamakin ya dira a zuciyarsa,kallon jamilu a kasa Yana goge bakinsa, haka ya wuce bangarensa na masu kudi wajensu daban dakinsa shi kadai harda tv da fridge harda kujeru sai dai rayuwa kawai a waje daya musamman ga namiji akwai wahala.


  Naila tashi tayi da kyar ta goge jikinta tana dingishi ta koma dakin su Alaramma Jilani,samunsu tayi suna Hira ai suna Ganinta ta shiga gaba daya suka jawo Qur'anansu kowa ya bude ba shiri,dariya suke Bata.


 Gefen bed ta zauna Malam Garzali ya dago Kai ya saci kallonta ai kuwa karaf suka hada Ido Naila ta kashe Masa ido daya,da sauri ya duka karatunta Yana yiwa sauran magana kasa kasa yace kaiiiiiii wallahi Ido yake kashe min Kuma ya birge ni,Malam Garzali shima yace nima haka zuciyata 


  Naila Hanata akayi shiga indai ba da izinin me kudin ba to ba Wanda zai shigar musu sai da izini,shima ba kwana ba idan da kwana to Wanda ya shiga shima sai an biya Masa kudinsa daban,yini ma sai an biyawa mutum zai yini a wajen,bangaren masu kudin ma shi ba wani me kyau can ba kawai Dan akwai kujeru da fridge ga toilet ko Ina tiles sannan har wanki ma da guga yi musu akeyi zasu iya dauka a cikin Yan gidan yarin suna biyan mutum hakkinsa Yana musu. 

  Spark da wayarsa da komai amma ya canja layika gaba daya sai in shi ya Maka magana sannan kasan shine,in banda Kamal da Rafeeq da ya nema ba Wanda ya nema sai Mummy dinsa me kaunarsa itama ya kirata amma sauran ba Wanda ya kira sabo da duk sun yarda zai iya kisan Kai.


   Spark bakin ciki ya taru ya Masa yawa ya rasa Inda zai sa kansa,Naila kuwa tsabar bala'i sai da ta bada cin hanci aka barta ta shiga dakin Spark,tace wato ita duniya dai ko Ina me kudi yake akwai banbanci a lahira ne kawai kowa zaici kwal ubansa Kai daya muke, ranar ba wani me kudi,palon ba kowa bedroom ta shiga a zaune ta hango shi ya hada Kai da gwiwa Yana hawaye shi daya.


  Naila tana shiga a hankali take sanda,ya ganta tun shigowarta,a ransa yace wannan Dandaudun ko maye shege tsinanne,Naila da karfin hali zama tayi a gefen gadon nasa, cikin Muryar Maza mazanta da take amfani da ita tace Allah sarki hakuri zakayi kaddara ce,wallahi ka saki ranka idan sharri aka Maka zaka fita watarana,Allah zaka fadawa kawai,gidan yari idan ka saki ranka akwai dadi ma itama wata rayuwa ce ta musamman Kuma zaka yi nishadi,ka kwantar da hankalinka ka saki ransa idan sharri aka Maka uban Wanda ya Maka sharri yaci... dan me..Kai Dan kut...nace durun....kai...duk bata karasa zaginba idan ta dakko sai ta saki ta kama wani.


  Ka tsaya kana kuntatawa kanka kana namiji aradu ka fito a dama da Kai,karka bari kanka ya kulle,gidan yarin bata rago bace aradun Allah,gidan Maza malam anan zaka tabbatar da namiji ne kai, anjima kadan yau za ayi gala rawar solo ka fito kayi nishadi karfe biyar za a fara har dare, Spark a ransa yace iyyeee a gidan yarin? Bai San a fili ya furta ba,Naila tayi dariya tace ai har koroso kullum sai anyi da wasanni kala kala kazo muje na nuna Maka komai ka huta da bacin rai, tunawa yayi da Dandaudu yake magana sai ya bata ransa ya daure fuska,Naila tace wasa nake Maka ni ba Dan daudu bane kawai Ina kama da mata ne shine Yan gidan yarin Nan suke fada min haka,amma wlh ni ba Dan Daudu bane sunana na gaskiya Jamilu,Spark ya Kalli Jamilu wato Naila sosai,murmushi ta saki a ransa salati ya saki kawai yayi shuru shi Kam wannan mata Maza ne gaskiya bai yarda ba sai dai Matamaza.


  Tashi tayi ta fice,tana fita ta koma wajen su Goje har hudu tayi taje tayi sallah a boye malaman dakinsu jam'i baya wuce su,suna fita take yin tata kafin su dawo, suna mamaki Bata zuwa jam'i iya wuya a daki take sallarta,wanka tayi a toilet din ta shirya tsaf ba Wanda ya taba ganin jikinta,kaya ta canja suma sai masu kauri burma burma na Maza,harda shafa turaren da Scoler ya bata sai wajen da ake musu wasan Solo lokaci zuwa lokaci,Yan solo sunzo harda Yan film an kafa kida an fara cashewa kowa ya zauna ana kallo wasu suna ihu suna liki,sai ga Spark kamar ba a gidan yari ba ya Sha kana Nan kaya sai shining yake dake sabon zuwa ne gashi kyakyawan gaske fari,ga kyan sura da diri,ga kwarjini da cikar haiba,Jamilu abokinsa ya fara dubawa a wajen can ya hango Naila zaune a gefe daya bata shiga gwamitsin kartai,kujera ta nuna Masa a gefenta,wasu munafukai harda gulma dama tunda naga kalar guy Nan nasan shima Yana harkar Daudu,Terror an samu Dan uwa,Spark hannu ya mikawa Naila yayi sallama,Naila ta kalle shi kawai ta basar ta share,Yan Solo suna cashewa wata Yar bariki har da zuwa zata rungume Spark Naila tace ke dalla matsa na saka miki guba ki shaka ki mutu bar Nan Dan uwarki tana zaro ido ta koma Yar Zara,tana zare Ido tana magana ta Maza ta Yan Zara,amma duk da haka mace sak.


  A hankali Spark ya dago Kai ya Kalli Naila,dariya ta kusa kama shi,a ransa yace ikon Allah namiji ta karfi sai ya koma mace to naga Dan ubansa ta ya zai canja Banana dinsa,ai sai ya yanketa kawai idan ya isa,shi kadai Yana tunani sai ga scoler yazo Yana rangwada yace da Naila Tantiriya ta? Jamilu Naila ya kalle shi yace Na'am my love Ina ka shige ne Ina ta missing naka.


 Dandaudu Scoler yace ahayyeeeee Yana tafi yace Dan ma har yanzu kinki yarda kiji dumin jikina,Naila tana shagwaba tace ai karka damu Darling tana so tayi kuka,Scoler ya dafe kirji yace na shige su ni Yar Nan karka bari hawayenki ya zubo tawan mene ne? Jamilu Yana rangwada yayi fari sannan yace ba Kaine ba sabo da Allah haka ake saurayin kaki zuwa zance bare ko kudin zance ka bayar gashi Dan liki ma bani da kudin yi,Scoler yace Dan Allah daina fada jiya aka turo min kudi ungo yasa hannu a aljihu ya zaro Yan Dari bibiyu na dubu biyu ya mikawa Naila,badan yau Saturday ba Alqur'an sai na rungume ka cewar Naila,amma anyi rashin sa'a yau cikar shekarar kakata ta wajen uwa goma Sha biyar da mutuwa,ranar bakin ciki ce sai nan gaba.


  Scoler yace kiyi hakuri amma gaskiya kakarki ta cuceni data mutu ranar asabar ai sai ta bari zuwa lahadi Sunday yanzu je kiyi liki,Yan wasan kwaikwayo suna ta uwar rawa a fili, Naila ta mike tace zaku ci ubanku sisi bazan lika muku ba,caca zanyi muku,ta wuce ciki filin rawar,Dj harda fadar sunanta ana ta cewa Jamilu Tantiriya Allah ya tsare mana Kai,Naila ita da kanta dariya ta kamata ta dinga dariya,mazan Nan sai kallonta suke ana ta son Jamilu sai kuskus ake yi.


  Naila ta zaro Dari biyu tayi mata rikon tsauri ta tsaya kusa da budurwar me tikar rawar tace a duwawu zan lika miki taje ta manna Dari biyu a duwawun budurwar Nan,da karfi tace aradu ciko ne ciko jama'a,Kuma ta rike kudinta Kam sai ta manna sai ta zare kudinta Yana makale a hannunta, mc Yana ta zugata Dan ta lika tace na ki wayon wlh ficikata baza tayi ciwon Kai ba akan me duwawun ciko ba, ana kallo ta fice tana cewa ciko ne wlh kar Wanda ya lika sisi gwara muci tsire ciko take mirgudawa,na taba maimakon naji wajen Yana karkarwa sai naji yayi dubush baya motsi kar kuyi asarar kudinku,suna ta dariya Yan gidan yari,amma sai da wasu suka lika kudin sosai,Scoler ya Maida kudinsa aljihu ya fasa likin yace asararru


  Ba'a wasa da Yan daurin rai da rai ko sun kasheka to fa su hukunci daya dai gashi Nan shi yasa budurwar Yar film sum sum ta koma wajen rawarta bata ce kala ba duk tijarar da Naila tayi mata,kamar ba gidan yari ba yanda ake likin kudi ana zuba naira Banda Spark bare Jamilu Naila da ba gatan kirki shi yasa yaki lika sisi,Scoler ne yazo yace me yasa wai Baki yi likin ba? Allah ya hana likawa irin wannan masu yada badalar kudi haka Malam Jilani suka ce Kuma na dauki wa'azinsu,Scoler yace munafukan malamai Allah yasa kar su kashe Maka zuciya ka daina Daudu,Naila tace a'a wannan ko Sudais ko shureim na Makkah ne suka zo bazan daina ba Daudu yanzu na fara,Scoler yaji dadi yace yawwa ko Mufti Menk ne karki dauki wa'azin,Naila tace hauka nake Daudu for life.


 Spark Yana jinsu ko harkarsu bai shiga ba.

  Tunda Spark ya zauna baiyi Magana ba daka kallo sai danna waya har ya gaji ya mike zai tafi abinsa Naila bata kulashi ba itama,sai da ya tafi tace Dan iyayi wai shi me kudi dan ya samu ma Ina kulashi sai nayi maganinka.

Tashi tayi ta koma dakinsu Inda kasa kasa tana jiyo surutun mata dakin wasu a Jikin dakinsu yake,Naila ta Dora kanta a Jikin bango tace da karfi Ina son daya a cikinku,Mata ta bangarensu sukaji magana,wata a ciki ana ce mata Beauty tace Ina sonka nima sunana Beauty.


  Kasa kasa Naila taji tayi tsalle tana murna,tace Inama da kofa da na Kalli fuskarki,sunana Beauty aka bawa Naila amsa mata sai shewa suke a dakin,Naila tace mashaallah zamu dinga zance ta Nan sunana Jamilu me zamani,Beauty tace daga Jin Muryarka ka hadu,Naila tace da zaki Ganni sai kin dalalar da yawu na hadu,Wata a ciki tace nima Ina sonka,Naila tace duk ku taho Ina sonku ni na mamajo ne ko wacce zan iya da ita,ya aka ji da rashin da namiji a kusa? Beauty da karfi tace muna fama wlh duk gamu taron balagaggu,Naila tana dariya itama da karfi tace iceko bakwa warin balaga? Malam Garzali suna dakin suna jinsu su tunda suke ma basu taba Jin Muryar mata ba sai yau,Kunya duk ta kamasu manya dasu gasu malamai Jamilu duk ya takura musu,ga kaunarsa duk ta kamasu sun rasa sukuni,Beauty tace Kana da waya? Naila tace me kika ce? Banji ba,kana da waya? Naila tace Allah sarki maraya ne ni,Beauty Yar gidan me kudin gaske ce itama kaddara ta kawota tace karka damu zaka yi waya me tsada zansa Daddy ya kawo amma sai munci gaba da soyayya Naila a ranta tace dole na dage naci kudin Beauty, Su Malam Jilani suna jinta sun kasa karatunsu da suke faman yi,Beauty tace da dare zamuyi free call ta jikin bangon nan,Naila tace karki damu sai anjima bye.


  Ta Kalli Malam Jilani tace ku malamai ba a morarku sai dai ku Mori mutum wato tunda nazo Kun San maraya ne ni amma ko sisinku ba a ci haka aka koyar daku a Islamiyya,Malam Sharu ya zaro Dari biyar yace ita kenan gareni ungo Dan Allah ka canja wani dakin Jamilu,Naila tace tab Ina nan so kuke ayi min fyade,Malam Garzali a hankali yace mun shiga uku mu dai.


   Umma ita kadai ce a gidan yara suna Islamiyya da yamma lis sai Abba yayi sallama ya dawo a gajiye Yana Nishi ya zauna Saman kujera,tace Kai Kuma lafiya? yace yau Nasha aiki jarkar Mai biyar na dauka a wajen aiki duba min kaina na fara sanko ko? Umma ta watsa Masa harara tace yanzu sabo da lalacewa akan ka dauki jarkar mai biyar shine abin gajiya haka har wani sanko zai fito Maka,Abba yace ke kinji nauyi ni gaskiya idan haka zan dinga yi zan bar aikin Nan bazan iya ba,Umma ce ta fashe da kuka,da sauri ya kalleta da Dan cikinta a gaba sanye take cikin riga da zani na atamfa,yace lafiya taki magana sai kuka take yi,yace haba Kubra menene? ta sake fashewa da kuka,Abba duk ya rude Yana tambaya menene? Sai da kyar tace Dan cikina nane yace a dauke shi,Abba ya bude Baki yace ta Ina yayi maganar? ya akayi ni banji ba, through placenta ya fada min uwa ce kawai ke gane yaren danta,Abba ya kalleta yace yanzu Kubra na gaji amma baza ki tausaya min ba,taya zan dauki jaririn Dake ciki? tace ai idan ka daukeni to ka dauke shi,Kubra gata me kiba Abba Dan tsurut haka ya Mike ya yunkura Yana Nishi ya dauke ta da kyar suka tsaya a tsaye,tace kaji wai a zaga da shi yace,Kubra nauyi ne Dake wlh kamar buhun sugar kiyi hakuri kuka ta fara ya fara zagawa da ita a hankali da kyar Yana Nishi,sai da taga ya Sha bakar wahala sannan tace yace a cinyarka zai zauna shi,Abba ya ajiyeta da sauri Yana Nishi kamar me,ya zauna ta zauna a cinyarsa yayi zuru da Ido ransa a bace sai da taga yara zasu dawo sannan tace to danwake zaka yi min yau yace shi zai ci,Abba ya kalleta kawai ya Mike ya shige daki tare da kulle kofar ya sa key shi bazai iya cewa bazai yi mata ba tunda ya Saba Yana yi mata watarana.


   Mummy tunda aka kama Spark hankalinta fa ya tashi matuka kuka ba dare ba rana,duk ta rame ta lalace burinta taje taga Danta,sai lokacin ta tuna da Jamilu fa Yana can shima ta dalilinta,share zancen tayi duk da suna waya da Spark amma Sam hankalinta baya jikinta, Mima Kam abin a ranta yake dukanta Wanda ba Wanda ya gane Hakan sai dai a ganta duk ta fige ta rame,Daddyn su Spark shi kansa abin Yana damunsa amma ba yanda zaiyi.


  Mima tana dakinsa ya kalleta a hankali Sam bata hayyacinta duk ta rame,tambayarta yayi yace meke damunki ne ko tunanin Spark ne? Mima murmushin karfin hali tayi tace a'a...idonta ya ciko da kwalla sai kuka bata San sanda ta fashe da kuka ba,Daddy ya kalleta cikin shigarsa na kayan manyan sojoji Yana Shirin fita,yace sai hakuri fa kaddara ce sai dai addua.


 Rafeeq ne ya shugo ya same su a haka da sauri Mima ta goge hawayenta ta nuna ba komai shima Rafeeq duk da yaji zancen su bai nuna yaji ba,gaishe su yayi kawai sannan Mima tace ya school din? yace Alhmdllh,Kuna waya da Spark kuwa? yace dazu ma munyi waya da shi ai shi baya cikin wahala part dinsa ma daban,Mima tace yayi kyau na kira shi yaki dagawa ai,dole yaki dagawa ni banga laifinsa ba Yana da gaskiya,Ku Baku bari anyi bincike ba Kun kasa tsaya masa Wanda Kun San gaskiya bazai aikata ba amma kuka goyawa iyayen Asmau baya an bata Masa suna sabo da Yan uwantaka,dama Aunty ce ta aiko ni tace ki bata sakon na Kai mata,Mima tace to tana wani bata rai ta dakko sakon ta mika Masa a leda tace yaya kudin baka kawo ajiyar ba, fuska ya daure yace na bawa Aunty ya juya tare da ficewa abinsa.


   Mohsin zaune yake Saman Sallaya Yana addua cikin tsakiyar dare Naila yake ta yiwa addua,Hanan ta farka tace wai har yanzu adduar ce kazo ka kwanta karka kashe kanka akan wata,ko kallonta baiyi ba,haushi ya kamata tace wannan Naila din kwai tsinanniya ta Hana mijina sakewa,a fili tace yau kwana nawa kaki kazo ka sauke min hakkina Kuma kasan Ina bukatar namiji a kusa,bai ko saurareta ba,ta ja tsaki tace wlh bazan yarda ba sai na kaika Kara wajen iyayenka kazo ka min abinda nake bukata, mikewa yayi ya bar mata dakin ya dawo Palo,tashi tayi tace wlh baka isa ba akan Yar iskar kanwarka ka wulakantani tazo Yana sallah ya tada sallah ta fado gabansa, ai kuwa ya Kifa mata Mari ya makar da ita gefe ta Fadi can gefe wanwar, sallarsa ya tayar, sabo da ta hanashi sallah ta dinga kururuwa amma bai fasa sallarsa ba har ta gaji.


  Washe gari da safe ta riga shi tashi sai gidan su Mohsin Yana bacci Bai San ma ta tafi ba,tana zuwa ta samu Umma suna karyawa da yara yau ba school, tunda Umma ta ganta tasan ba lafiya ba,dama ta tsani Hanan bata mata kyauta kadan take jira,Abba kuwa Yana zaune abinsa ya gama karyawa Hidaya tana aikin gida yara suna wasansu.


  Hanan ta gaishe da su Umma tare da fashewa da kuka,Umma tace in kin gama kukan Kya Fadi abinda ya kawo ki,ai ni kukanki farin cikin ganinsa nake yi Hanan Maza ci gaba wlh Inda kisan Ina kallon film din India sabo da nishadi,Hanan sai ta daina kuka Jin furucin Umma ta daure tace karar Mohsin na kawo,Abba ya mike zai tafi wajen aiki yace ki fadawa matar gidan gata Nan ta isa komai ya fice abinsa ya barsu,Hanan tace Umma Mohsin Yana zaluntata kawai hakuri nake zama da shi,Umma tace da ubanki zakiyi idan ba hakuri ba kowa hakuri yake ai nima da kika ganni me wari nake nema ban samu ba haka na hakura sannu shafaffiya da Mai, Hanan tace ai nawa yafi na kowa domin baya biya min hakki na kullum sai Sallah cikin dare,idan cikin dare yayi shuru Yana yiwa Naila Addua Kuma ko kema ai naga ba haka mijinki ke miki ba, Umma salati ta saki tace laaaaa wayyo sannu ai ni macece ta kwarai ni haka nake Masa irinki mahaukaciya shi yasa kika Ganni Ina shanawa sai abinda nace to na cika mace,ke fa? zaki min iskanci idan ke surukar zamani ce nima itace dai dai nake dake,marowaciya ko Dan kwai baki taba dafowa kince a kawowa Tsohuwar Mohsin taci ba,bare Dan sabulun wanka da wanki,kije ki tambayi tarihina a kauye kiji har saniya na taba bawa surukata kyauta Dan kawai na samu shiga,ke kuwa ko cinyar kaza daga ke sai danginki, Kun takurawa Dana sannan dare ma bazai huta ba ubanki zai miki cikin daren? 


  Duk fitsararki na haifi Wanda suka fiki ke idan da Naila tana Nan kin isa ma kizo har gida ki fada min kice wai mijina ba haka yake min ba,in Haifa miki yaro ki aura kizo Kuma ki ci min mutunci Yar matsiyata,Hanan tace to wallahi idan na fada halaka shi ya ja ai Ina ganin Maza gasu nan,Umma ta daga hannu sama tace ya Allah ka fito min da 'yata Naila tazo taci ubanki har gida, wayar Umma ce tayi ringing ta daga sai taji Muryar Naila,ta manta haushin Naila take ji sabo da Hanan taci mutuncinta, tace Naila ce wai? Naila tace ae Umma itace Jamilu ba,yawwa a dinga gyarawa sabo da tsaro ko kice Tantiriya is better Umma,ya gida ya kowa Ina Yar bakin ciki Hidaya? duk kowa lafiya Naila,iceko kina lafiya? tace to gashi nan dai a fadawa Yaya my love ya kirani da wannan number din,Umma tace to ga matarsa ma tazo ta kawo kararsa,Naila tace ki fada mata na saketa saki uku Umma ta kwashe kayanta na saketa,tana jinki ma ai na sa a handsfree,Naila tace yawwa ai da Allah yasa Ina Nan da tuni na kashe auren Yaya, Umma tace wai baya biya mata hakkinta,Naila tace ai da nasan gidan yari zanje da kafin na tafi zan bawa Yaya magani na kwantar da Hallare wanwar a kasa bata sake motsi sai ya sake aure na tashe ta,Umma dariya ta kamata da kunya sosai amma bata yi dariya ba kunya ta hanata dariya ga suruka na Ji ga Naila yarta,share zancen tayi tace idan ya shugo zai kira,Naila tace to a gaida su Aslam da Hidaya Yar bakin ciki da Zarah,sannan a cewa Darling ya kirani,Umma tace to sai munzo ziyara.


 Naila tace ko baku zo ba ma I can survive, Allah Yana kula da halittarsa, tururuwa ma Allah na kula da a barsa bare Dan Adam, Tausayin Naila ya kama Umma sosai harda kwalla ta datse wayar da sauri tasan magana Naila ta fada mata da suka ki zuwa mata.


  Hanan tuni tayi waje ta fice ta tafi gidansu tana kuka tace Mohsin da iyayensa ne suka ci mutuncinta, Mamanta tayi mata nasiha aka maidata gidan Mijin,Mohsin baya gidan bai san ma ta koma ba,Yana dawowa daga wajen aiki ya ganta a gidan tana girki,ransa a bace yace yanda kika tafi ki tattara ki koma gidan naku ai Umma ta kirani a waya ta fada min karata kika Kai musu sannan kika wuce gidanku sai ki koma gidan naku Kuma karki sake ki daukar min 'yata,Wani takaici ya kama Hanan tace ai dai muna da gidan ko,sabo da kaje gidanku an zugaka shine zaka dawo ka raina min hankali dadin abin dai ubana Yana da gida,Mohsin yace kije dai ku kwana da yara su tsula miki fitsarin kwance a jikinki,lokacin da nake zuwa zance gidanku in kika fito mayafinki zarnin fitsari yake ko kina tunanin ban gane ba to hanci na ya jiye min shuru nake miki kawai Ina dauke kaina gefe,Hanan zuciyarta har suya take sabo da bacin Rai,bedroom ta shige ta dakko mayafinta ta saka tana tsaki tace gidan naku ai ba fin namu yayi ba,ubana na ma yafi naku,naku sai yanda tsohuwa tayi da shi,ta juya zata tafi ya fisgota yace me kika ce? taji tsoro amma duk da haka tace na fada gwara ubana...ai kuwa Mohsin ya hau jibgarta tana ihu har makwafta sai da suka shugo,da kyar aka lallaba Mohsin ya kyaleta amma mayya Hanan ta San ta kan Mohsin,sai tace bazan tafi ba ai nayi wanki gashi Nan a Saman igiya yanzu zan kwashe zan tafi.

 

 Mutane kowa ya watse sai wata dattijuwa Mohsin yana cewa Baba sakinta zanyi,Tsohuwar tana cewa kayiwa Allah Dan girman Allah ko Dan darajar yarku karka saketa,bazan zauna da ita ba Baba,Baba tace karka ce haka Dan nan,Hanan ta koma bedroom ta cire kayanta ta fito da daura kirji ta shiga toilet ta fito ta sake komawa,ta fito karo na uku ta shiga kitchen sai ta sauke zaninta a iya kugunta ba bra ba riga daga samanta sintir sai kayan uban nonuwa suna ragaje ragaje ta fito a haka ta wuce su tana girgiza ta shige Palo ta sake fito tana girgiza kirji tana cewa duk abinda mutum yake ji nima Ina ji,Baba tsohuwa tana ta dariya a ranta tasan iskancin Hanan tasan dalilinta,Mohsin sai kace tsohon maye duk Inda Hanan tayi sai kallo Yana mika wuya Yana Cewa Baba zan sake ta fa? Iya tace a'a kayi hakuri,Hanan ta fito tana waka ahayee dawo dawayya....tana girgiza....Mohsin yace to Baba ance rayuwa sai da hakuri musamman ga ma'aurata ko? Baba tasan batun tace ae yi hakuri kaji,yace to na hakura yanzu tunda dai nima na zageta shike nan 1-1 idan ta sake sai ta bar gidan nan,Baba tace ae Hakan yayi ayi hakuri ya wuce ,yace sabo da ke Baba Ina ganin mutuncinki na hakura,Baba ta bar gida tana ta dariya.


  Hanan kuwa Kwata kwata yini tayi tana zagade a gidan tana wake wake taki saka riga a haka tayi wanka ta saka Dan skert ba ko riga ba bra ta sake fitowa kamar karuwa,a Palo ta zauna tana girgiza tana wake wake,Mohsin Yana ta kallonta kamar maye hankalinsa ya gama tashi matuka,Amal dama tana gidan su Hanan,Tashi Hanan tayi tana murguda duwawu tana tafiya ta shige daki ta fito daga ita sai pant ta zauna suna facing juna da Mohsin ta baje kafafu tana tauna chewgum tace zama daram,Mohsin a nutse yace dama ai kece kika jawo ni ai bance karki zauna daram ba,idan aka yi hakuri duniyar nawa take eyeee, rayuwa dole sai anyi hakuri da juna ki daina taba min iyaye wallahi akan iyaye na ba abinda bazan yi ba,Hanan tace ni ai ka zagi nawa taya bazan rama ba daga na nemi hakkina sai kuyi min taron dangi, Mohsin yanzu Kam dama a matse yake yace indai akan pleasure stick ne ake wannan tashin hankali gata nan,ai ita ba bakuwar zafi bace,Hanan taji dadi ya sakko tace to yanzu naji zance nima ka yafe min mu tafi Downstairs, yace sai kinje kin bawa Umma hakuri,tace zanje ai ba komai,yace to suka yi cikin bedroom.



Sharhi please fans


Book 1

Free page


Accnt no

0175487861

Asmau Garba Muhammad

 Gtbank


Katin MTN

***


Yan Niger

+22790795939




AsmaBaffa