SAƁANIN TUNANI
SAƁANIN TUNANI
Aysha D Fulani
7&8
Ashe rabuwa za mu yi? Me yasa da zaka fita da safe baka faɗamin cewar shikenan ba? Wai ma yaushe ka dawo gida? Wa ye ya shigo ya kashe ka? Ina zan sa raina! Ahmad ka tafi ka bar ni da abin da zuciya da gangar jiki baza su iya ɗauka ba. Sun ce na kashe ka, ba su san cewa nima a haka nazo na sameka ba. Me kamin da zan kashe ka ni Fatima? Ta ya ya zan kashe uban 'ya'yana, to nace musu me ne idan sun zo duniya? Inallilahi wa'iinna inaili raji'un! Allah kana ji ka na gani, ka fi ni sanin dalilin faruwar al'amarin nan, kai ne mamallakin kowa da komai, ka shimfiɗa adalci a gare ni, ka da wanda ya kashe mijina ya ci bulus."
Sambatun da ta dinga yi a fili kenan, ta kamo wannan ta saki wancan, gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta birkice sai wasu maganganu take. Jin ƙarar buɗe ƙofar da jami'ar tsaron ta yi ne ya sa ta kalli wurin da sauri.
"Ki fito, ana son magana da ke." Ta faɗa fa kakkausar murya tana muzurai, ta tsaya a bakin kofar tana jiran miƙewar Fatima.
Dafa hannuwanta ta yi a ƙasa ta miƙe da ƙyar tana rike cikinta wanda keta mutsu-mutsu. Ganin tsayuwar na neman gagararta ya sa matar saurin riƙota don ta taimaka mata.
Jerowa suka yi, har ofishin Insipector Bashir yana zaune a kujerarsa yana rubuce-rubuce a cikin file ɗin da ke gabansa, jami'ar tsaron ta sara masa.
"Yallaɓai gata nan."
Ya ɗago kansa yana jinjina mata "Za ki iya tafiya."
Ta sake sara masa ta juya ta fice a ofishin tana mai ja masa ƙofa.
A lokacin ne Insp. Bashir ya ɗago da kallonsa ga Fatima ya lura da yadda tsayuwa ke son gagararta, take tausayinta ya dira a zuciyar sa duba da halin da ya ga tana ciki.
Da hannu ya mata ishara da kujerar da ke fuskantar sa "Zauna." Ya faɗa a taƙaice, ta cira ƙafafuwanta da ƙyar ta zauna a kujerar tana maida numfashi.
"Me yasa kika kashe mijinki Ahmad?"
Tambayar ta zo mata a bazata kamar sauƙar aradu "Ba ni na kashe shi ba!" Ta faɗa a ruɗe tana girgiza kanta, ya kalleta na ɗan wani lokaci.
"Idan ba ke bace wane ne?"
"Wallahi ban sani ba, amma ba ni na kashe shi ba. Me yasa zan kashe mijina uban ɗan da ke cikina?"
"Wataƙila kina son cin gadonsa ne." Ya jefa mata tambayar da ta so ɗauke jinta na wucin gadi.
"Ban taɓa damuwa da arzinƙinsa ba, ban kasance da shi saboda abin da ya mallaka ba yallaɓai." Ta yi maganar hawaye na gangarowa a kwarmin idonta.
"Ina fatan hakan, ina fatan ba kashe shi kika yi saboda ƙiyayyar da kike masa ba."
Ta ɗago ta kalle inspector Bashir ɗin kamar yadda yake kallonta.
"Hujjoji sun riga da sun zo hannunmu, yanzu za mu tura case ɗin ku zuwa kotu. Akwai manyan hujjojin da ke nuni da cewar ke kika kashe mijinki. Idan kin sauƙaƙawa kotu wajen faɗar gaskiya za ki iya samun tausayawarta wajen miki hukunci, akasin hakan kuma.." Ya girgiza kansa yana ƙwalawa Sajen kira.
Wadda ba a jima ba ta shigo "Ki maidata cell. Amma a sauya mata ɗaki mai ɗan tsafta, zan turo Dakta Asiya ta dubata saboda yanayin jikinta."
"Wallahi ba ni na kashe shi ba." Ta faɗa hawaye na gangarowa a idanuwanta, Kurtun 'yar sandar ta ja ta suka fice, wanda shima ya miƙe tsaye ya bar ofishin.
Ya fito ya tarar da hayaniya da 'yan sandar da ke tsaye da wasu mutane, suna ganinsa suka sara masa.
"Me ke faruwa anan?"
"Yallaɓai iyayen Fatima ne suka matsa akan suna son ganinta, mun ce ba zai iyu su ganta ba saboda laifinta babba ne."
Ya dafe kansa yana kallon Dattijan da suke cikin tashin hankali.
"Sajen Laure, taho da Fatima." Ya faɗa yana duba agogon da ke ɗaure a hannunsa "Ku barsu su ganta na minti biyar."
"Ok sir." Suka amsa suna sara masa daga haka ya fice a ofishin suna masa godiya.
Sajen Laure ta shigo da Fatima inda Yaya Usman yake tsaye, sai Umman Usman da mahaifin Usman sai Abba Babanta da mahaifiyarta gefe.
Wani irin kuka ne ya taso mata, ƙoƙari take ta danne amman ta kasa, jikin Ummanta ta faɗa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Rasa bakin da Umma zata rarrasheta ta yi itama ta fashe da kukan, Abba ne ya yi karfin halin "Don Allah ku daina kukan nan tun da ba abin da ya kawo mu ba kenan. Fatima!" Ya kira sunanta bayan ta saki Umma ta na duban inda mahaifinta ya ke, cikin muryar kuka ta soma magana. "Na sani Abba ku iyayena ne, kun san abin da zan aikata wallahi ba ni na kashe shi ba, ina kwance a daki bacci ya kwasheni bayan na gama girki, farkawa na yi ina zama naji amai na taso mini shine na miƙe na shiga bayi, bayan fitowa ta na ji ƙarar tv bayan nasan ni ban batta a kunne ba, shine na ƙaraso falo, ina zuwa na iske Ahmad a kwance cikin jini. A lokacin na matuƙar gigice shine na yi kansa a guje ina tattaɓa shi na ga baya motsi, sai na cire wuƙar daga jikinsa wacce na ganta an soka masa akan saitin zuciyarsa, Umma, Abba, Yaya kun sani bazan aikata ba, don Allah kada kubari a cutar da ni don Allah."
Juyawa ta yi ga Yaya Usman "Nasan ko da ace su ba za su fahimce ni ba na san kai kafi kowa sani na saboda ka san me zan yi da kuma me zan aikata a cikin rayuwata. Yaya kada kabari su hukunta ni akan abin da ban aikata ba, su Umma ba za su saka baki ba saboda suma kallan ni na aikata suke, a kan cikar muradina. Muradin da na daɗe da kashe shi ko don yaron da ke cikina."
Faɗawa jikin Usman ta yi tana sake rushewa da sabon kuka, tama ƙanƙameshi "Ban aikata ba, Yayana ka taimaka ka daukar min lauya yabi min hakkina. Sun ce kotu za su kaimu saboda sun tanadi hujjoji masu yawa."
Kuka ne ya ci ƙarfin ta ta kasa motsa labbanta sai hawaye ke bin kuncinta ta na wani irin ajiyar zuciya, fuskar ta cakuɗe da majina da hawaye.
Sassauta rugumar da tai masa ta yi, ta janye daga jikinsa, ta tsugunawa ƙasa saboda yadda ta ke jin jikinta bazata iya tsayawa ba.
Sunan Fatima Abban Usman ya kira, wacce take tsugunne a gaban su, bata iya amsawa ba sai dai ta rage sautin kukanta wanda ya rage ajiyar zuciya take saukewa akai-akai.
"Haƙiƙa Ubangiji ya na jarabtar bayinsa ta fuskokin da ba su yi tsammani ba, haka mutum bashi da tsumi bare dabara kauda kaddarar da Ubangiji ya shimfiɗa a kan duk wata hanya ta tafiyarka, dole ka bi abin da Allah ya tsaro ma a cikin rayuwarka, ba mune ke da ikon tsarawa kanmu rayuwar da muke so mu yi ba, Ubangiji shine ya ke da wannan ikon, idan muna shirya wani abu a cikin rayuwar mu tabbas shirme ne wannan, domin shirin Ubangiji shine tabbatace.