chapter 1&2
_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_Wattpad✅_*
***
/user/Rabiatu333
*_𝘼rewabooks✅_* ***
com/user/rabiattu0444
*_M𝘼RUBUCIY𝘼R_*
1-Uwar gidana
2-Auren dole
3-Ruhi ɗaya
4-Farouk
5-Inayatullah
6-ƙaddarar Rayuwa ce
7-Akan aiki na
8-Jamila
9-Doctor Nawwara
10-Darasi
11-Silar fyaɗe
12-Basma
13-Abin cikin ƙwai
14-Ɗinyar makaho
15-Inda ba ƙasa
16-Zulfah
17-Asanadin abayar sallah.
18-Facala🔥.
*Doka🧧*
Ban yarda wata/wani ya canjamin labarina ta kowacce siga ba,idan mutum ya aikata shi da Allah.
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*➡️1 & 2*
………...shiri ake sosai na tarar ɗan gata autan Momma,kai ka ce wani biki akeyi agidan ko wani sashe na gidan zaka ga suna cike da nishaɗi da kuma murnar dawowar Autan Momma,har anko akayi na murnar dawowarshi gwanin sha'awa maza suna sanye cikin cort fara sol da kuma wandonta baƙi,ya yinda aka yiwa gaban rigar ƙwalliya da flower me ratsin ja an rubuta love ajiki.
mata kuma suna sanye da dogayen riganu masu santsi maroon colour wanda duk suka yi gown dashi ƴammata sune masu wannan kalar,manyan mata kuma less ne me ruwan baƙi da Red,abin dai sai wanda ya gani gwanin sha'awa.
daga can gefe wata matashiyar budurwa na hango tana shirinta ahankali tamkar dai babu inda zasu je taro babban baƙo,tana cikin saka ɗankunnenta taji ana ce wa"Autar Momma fito mana,kinsan ba bro baya son jiya kuma jirginsu ya kusa sauka".
Ɗan turo bakinta tayi kamar za tayi kuka ta ce"Allah ni don Momma tace in shirya Allah da bazan fito bama".
daga can me kiran nata ta ce"ato oya les go dai ku ki fara da dukan soja".
banza tayi mata ko ɗaura ɗan ƙwalin bata yi ba ta fito da achogen takalminta tana tafiya cikin nutsuwa.
kowa ya shiga mota aka tafi filin jirgi don tahowa da babban baƙo wato Canal Aliyu .A. Aliyu wanda aka fi sani da Triple A haka sunansa yake tun a primary har izuwa yanzu da yake a matakin Canal.
Sosai ƴammatan ke ɗokin ganin Canal,kowaccensu taci adonta na kece raini duk da ankon kala ɗaya ne amman kowacce da stile ɗin ɗinkinta mai ban sha'awa,don kowacce ba laifi tayi ba ƙarya gaskiya sai dai hasadun iza hasadan.
kowacce kuma sai bin ƴar uwarta take da harara har da ɗan tsuke fuska,alamun fa cewa kowaccensu ƴar jaraba ce jiran ƙiris take yi😂.
Ko a filin jirgin ma sai da aka ɗan raba hali,don kowaccensu tsayawa tayi jikin mota wai ita zai fara gani daya fito,Autar Momma sai kallansu take tana dariya,don tun ba yau ba tasan wanene Bro Aliyu mutum ne mai shegiyar kafiya da kuma ɗauke kai aduk abinda kasa wai don ka burgeshi sai ma gwaleka da zaiyi,don ba ma sai ya kalli fuskar taka bane zai san ka sanya wani abu? idan kuwa kaga yana hira har da ɗan murmushi,to fa kada ka tambaya ma ko dai da Momma ne ko kuma da yayansa ko kuma Abbah,wato mahaifinsu tuno da wannan yasa Autar mama ƙunshe dariyarta don tasan nan ba da daɗewa ba zasu ƙwashi kashinsu a hannu,don shi ko kallo ma bai so ballantana ma aje ga maganar so.
ƴammata fa anyi cas anyi acan acan,ana ta gyara glass da kuma tsayuwar zaman riga das a jikimsu,Momiga wato ƴar ƙanin mahaifin Canal ta kalli Autar Momma sannan ta ce"wai ke Salma me yasa kika raina mutane ne? saboda kinga munzo tarar ɗan uwanki shine kike mana wannan cin fuskar?to wallahi kiji da kanki,don ni wallahi ba raga miko zanyi ba kamarsu Fatima kina yimin zan disga ki".
Autar Momma tayi mata wani kallo,wanda ya sanya ƴaƴan hanjin cikin momiga juyawa,yarinyar aƙwaita da ƙwarjini da kuma tsare gida,kuma sam bata san raini saboda haka ma bata fiya shiga cikin muta ne ba.
bata ce mata ƙala ba amman wannan hararar ita ta wakilci maganar,tayi juyawarta ta sanya idonta sosai a filin jirgin don Allah ya sani tayi kewar ganin Bro ɗinta,shekara 12, fa ba wasa bane don tun tana ƴar shekara goma ya tafi gashi yanzu tana da shekara 22,shi kuma ayanzu yana da 29 years.
kallo ya koma kansa,don yadda ya fara sakkowa cikin kayan sojojinsa masu matuƙar kyau,sun zauna masa sosai tamkar don shi dama akayi kayan.
wai! wai!! wai!!
wannan guy ɗin yayi wa maza zarra,dogo ne samɓel farin bafulatani me ji da yarintarsa yadda kasan jini zai fito haka yake ballantana kuma daba a nan yake ba a ƙasar waje,sosai skin ɗinsa ya samu hutu har wani ɗaukar ido yake tamkar wata mace,ƴammata fa sai da suka kusa durƙushewa awajen saboda kyaun da yayi musu,gashi jikinsa a murtuke alamu dake nuna cewa ya samu hutu sosai.
nan fa aka fara rige rigen zuwan tarbarsa,sai dai kunya ce ta hana ƴammatan ƙarasawa saboda iyayensu maxa da suke wajen,cikin ladabi ya gaishesu suna yi mai sannu da zuwa.ya amsa yana murmushi yana leƙe ko zai ga Mommansa ko Papa ɗinsa,sai dai duk bai gansu ba tsabar miskilancinsa bai sa ya tambaya bama,baza kuma kayi tunanin ya damu ba ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya wuce abinsa.
masu busa fa suka fara suna yi mai kirari,Galadima ɗan sarki ya sauka Allah ya bar mana kai sarki mai jiran gado.
cikin takunsa mai matuƙar tsayawa arai yazo ya wuce ta gaban ƴammatan nan,tamkar su janyosa haka suke ji amman babu damar ko magana suyi masa,saboda haka suka ɗinke bakunansu suna mai take masa baya.
Ƙamshin turarensa ma kawai abin burgewa ne,yadda kasan turaren dayafi kowani turare ƙamshi,dukkansu suka buɗe hancinsu suna shaƙar wannan daddaɗan ƙamshin mai mantar da mutum daga damuwa.
kana shiga gidan BABBAR MASARAUTA,zaka samu kowanni babban ƙusa da kuma bayi da dogarai ta ko'ina,saman benen gidan na hango Sarki gagara badau yasha ƙwalliya cikin kayansa masu matuƙar tafiya da mutum,ado ta ko'ina sai walƙiya yake yana ɗaukar ido kuma ko ba a faɗa maka ba kasan cewa shine mahaifin Canal Aliyu Galadima.
Fara'ar dattijon ta ƙaru,kasan cewar Aliyu shine ɗansa namiji tilo daya malakka,yana masifar sonsa so mai matuƙar tsayawa azuciya,kowa kuma ya tabbatar da hakan Aliyu ɗan lele ne tako in,sai dai zuciyoyin wasu agidan Sarautan suna mai cike da shan alwashi da kuma ɗaukar fansa akan Aliyun,tun wasu shekaru da suka shuɗe wanda aka so halaka Aliyun Allah ya kare shi.
duk miskilancin Aliyu da sauri sauri ya ƙarasa wajen mahaifin na sa,ya yinda ya buɗe masa hannunsa ya ƙarasa da sauri ya rungume mahaifinsa,yana ɗan zubar da ƙwalla shi kaɗai yasan yadda yayi kewar mahaifansa musamman ma mahaifinsa wanda yake masifar so,don ya taso ne da ɗinbin soyayyar mahaifinsa aransa.
sosai mutane suka tsaya suna kallonsu,gwanin ban sha'awa wasu suna murna waɗansu kuma zuciyoyinsu kamar zasu fashe saboda tashin hankali,don dawowar wannan yaron masarauta dai dai yake da rugujewar rayuwarsu,don sun daɗe suna shuka tsiyarsu ba tare da anyi musu wani shinge ba,amman sun tabbatar zuwan wannan yaron komai ma sai ya canja.
Magajin gida ya kalli waziri ya ce"lallai aƙwai babban yaƙi a wannan masarautar,don wannan yaron me ido a tsakarka ba barinmu zaiyi ba,yanzu ma haka na tabbatar ba tsakani da Allah ya dawo ba,amman ko yana so ko baya so bai isa ya mulki ƙasar nan ba".
*** *** ***
RABIATU
..................wasu zafafan hawaye na share,na kalli agogo ƙarshe 1:30 dai dai takaici da baƙin ciki suka hanani ko da rintsawa,shekararmu ɗaya da Ahmad da aure amman zan iya ce muku rabona dashi kusan wata biyar kenan,ni ɗin dai ni ce matarsa ta halal amman nayi imani da cewar aƙwai wacce Ahmad yake raba mana ƙwana da ita,sam Ahmad ya juya min baya ƙwata ƙwata baya ganin mutuncina ko kaɗan,nayi tunani akan abinda nayi masa yasa yake wulaƙantani amman na kasa tuno da wani lefi dai dai da ƙwayar zarra,abu ɗaya na sani shima idan shi ɗinne kenan wato matsalar FACALA, wacce nake wa iƙirari da ce war tafi kishiya,don kuwa ni tawa facalar ta banbanta da kowacce irin facala,kai hatta da uwar mijina sai da ta shiga tsakaninmu,mace mai mutunci da mutunta mutane amman sai da ta shiga tsakaninmu dako gaisheta nayi,bata amsawa ko kallon inda nake ma bata yi.
Gidanmu ɗaya da Facala ta,rana ɗaya muka tare da ita don ranar da aka kawoni a matsayin amarya ranar itama ta tare agidan amatsayin amarya,don rana ɗaya akayi aurenmu sai dai muna da banbanci me girman gaske,ta fannin hali da kuma nasaba dama komai.abu na farko daya sa Facalata ke ƙuntatamin shine mijina yafi sona,don kuwa ta tabbatar da hakanne a ɗan zaman da mukayi,alokacin ina amarya hatta aiki tare mukeyi ni da Ahmad,haka zai goyani muyi ta nishaɗi kasancewar ni anyi min aure da ƙananan shekarun da basu wuce 16, ba ayanzu kuma ina da shakera 17 a duniya don dai Allah bai bani haihuwa bane,amman cikina na farko zubewa yayi tun daga nan kuma ban sake samun cikin bama.
Balaraba ta haihu wato Facalata,ayanzu haka ma tana da wani cikin gwarnai tayi don ƴatta bata fi wata biyu ba ta samu wani cikin kuma ayanzu haka gab take da haihuwa ko yau ko gobe.
Balaraba ba ƙarama bace kamar ni,don ita ayanzu tana da shekara kusan 29 ko 30 ma don mijin nata ma da kaɗan ya girme mata.
Abu na biyu daya sanya Balaraba ƙara tsanata shine kyau da ilimi,don ina da kyau sosai sai dai ni ba fara bace,ina da gashi mai kyau da kuma cika amman gashina irin me cika kai ne kuma yana da tsayi,gashi Allah subhanahu wata ala yayi min ƙira me masifar kyau,komai na jikina tamkar an tsaramin shi ne,ba ni da wani tsayi can amman baza a kira ni da gajeriya ba,kuma sannan ni ba me ƙiba mace amman ina da irin ƙirar nan da ake cewa koka kola,komai dai zan zan sannan ina da ilimin addini dana boko don kafin ayi min aure ina da haddar qur'ani cif cif akaina,sannan kuma na yi candy kafin ayimin aure,mahaifina yana masifar son yaga yaransa sun haɗa ilimi duka,don ni kaɗai ce ma ban jona da jami'a ba amman duk sauran yayyina sai sunyi degree suke aure,ni kaɗai ce awajen mahaifiyata kasancewar tunda ta haifeni bata ƙara haihuwa ba,matan Baba na uku ne ita ce kuma amaryarsu,mahaifiyata asalinta shuwa arab ce kyakkyawar gaske mai cika tamkar ni dai ƴarta ɗaya tilo.
fara ce sol ba kamar ni dana yo fatar mahaifina ba,don shi baƙine asalin hausa fulani kuma har kamanni ma wasu na mahaifina ne na ɗakko.
zumbur na miƙe ganin an turo ƙofar ɗakina,da sauri na juyo ina kallonsa shima ni yake kalla hannuna sarƙe a ƙirjina ina sanye da wata kyakkyawar rigar barci,wacce ta ƙwanta luf luf a lallausar fatar jikina,rabin cinyoyina duk awaje wai don duk a burge miji,sai dai kash ko kallona baya yi ballantana ma in sanya ran za'a yaba min,gashin kaina kuwa na tufkesa a tsakiyar kai na wanda yayi cukus yayi gwanin sha'awa kamar black america.
kallona yake sosai tamkar dai yadda ya sabayi idan yana kallona ako da yaushe.
Share hawayena nayi,don ni dai na rasa wannan masifar wallahi,muna son juna ni da Ahmad ba kaɗan ba soyayya irinta Layla majnun amman kuma yanzu duk abin ya canja lokaci ɗaya,ako da yaushe Ahmad cikin kallona yake yana masifar son kasancewa dani ayadda na fuskanta,amman kuma daya zo gare ni sai ya kasa sai dai ya koma gefe,abin yana matuƙar damuba gashi ina jin kunya na kasa faɗawa kowa,kai hatta da Innah ta mahaifiyata na kasa faɗawa,gani nake tamkar tona sirrin mijina nayi ayadda kowa yake ganin muna zaune lafiya da Ahmad,to inason aci gaba da kallonmu a haka ɗin.
Ahmad ya ƙaraso inda nake ya ce"wai me ya hanaki barci ne"?.
Tambayar tazo min a bazata,da mamaki na kallesa ina kallon agogon dake ɗaure a jikin bangon ɗakin,na ce"rashin dawowarka ne ya hanani barci habibi,kalli agogo fa ka gani ƙarfe nawa"?.
Kallon agogon kuwa yayi sannan ya ce"ƙarfe 11:30 menene"?.
Maganarsa ce ta harzuƙani na tashi cikin bala'in da ban san ina dashi ba na ce"haka ma zaka ce menene ko? kana can wajen ƴan iskan matan da kake bi shine zaka ce hak..............."
Wani irin bugu ya kaiwa ɗan ƙaramin bakina,nan da nan ya fashe har da jini na sanya hannuna ina dubawa naga jini,na firgice na fita daga hayyacina don Ahmad bai taɓa dukana ba duk da ba yau muka sabayi ba,matuƙar ya fita ya kai dare ban san lokacin da na taƙarƙare na sanya ihu iyakacin ƙarfina ba......................➡️soon🤪.
#MRS GREEN CE.
a dage da comments,da yimin share ni kuma in ta sambaɗo muku typing🥰
***
MeQZ09jYzYRWCX0
ga link ɗina ga masu son shiga grp na facala,bana son talla da turo batsa duk wanda ya turo yasin ko gidanmu ɗaya sai na cire ka ehe🤪💃.
***
CI0gOCiAvl71TTWjFS
***
gOCiAvl71TTWjFS
MATA da yawa na fuskantar matsaloli,
wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka
haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun
ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman
gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na
cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin
da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa
tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana
mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.
Abubuwan da ke ciki;
Haɗin Dilka
Haɗin man gyaran gashi
Haɗin sabulun gyaran jiki
Haɗin ƙugu(hips)
Haɗin gyaran (Breast)
Haɗin maganin infection
Haɗin furen zogale
Haɗin tsumin tabaje
Haɗin Kaza
Haɗin tantabara
Haɗin ƙamshin jiki
Haɗin ƙamshin baki
Ingantattun maganin mata
Bonus
Sirrin riɗi
Sirrin magarya
Sirri magaruwa
Sirrinmu(Addu'oi)
Za ku iya biyan kuɗin littafin
akan fara shi sauƙi #1,500 kacal
Mutum 20 da suka fara biya na farko,
zasu biya 1200, ku yi hanzari ku
shigo sannan ku yi payment akan lokaci.