Chapter 3&4
_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_Wattpad✅_*
***
*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444
*Sirrinmu➡️*
manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da yiwa ƴaƴanmu zane kamar,kalangu,tattu da sauransu.domin canza halittar ubangiji.
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.
yana gyara breast sosai,masu son su ciko suyi gwanin sha'awa sai su garzaya su nemu na su.
idan kin shirya gyara ki kirawo MAMAN KHAIRYS SABAYAS🗣️🗣️🗣️🗣️.
***.
💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
➡️3 & 4
…………Jin ihu yasa Zubair ya kalli Balaraba ya ce"kamar fa ihun Rabiatu nake ji"?.
wani irin ya mutsa fuska tayi sannan ta ce"eh menene? ai ba abune wanda aka farashi yau ba,balle a daina sa yau ɗin yarinya sai shegiyar fitina,ke kullum faɗa da miji? ni wallahi banga amfanin auren mace irin Rabi ba? Ahmad baiyi dacen mace ba wallahi Allah dai ya bashi mace tagari,ni da zai ƙara aure ma ai da ya burgeni wallahi,ko ya samu farin ciki tunda ita ƴar masifar ba zata barshi ya huta ba".
Zubair ya kalli Balaraba ya ce"haba Balaraba,wai mi yasa kika tsani yarinyar nan ne? ai naga kema macece ko? ya zakiji idan akace mijinki me irin halin Ahmad ne? mijin da ba zai tashi dawowa gidansa ba sai tsakiyar dare? wallahi ni na rasa inda Ahmad ya ɗakko wannan halin".
Balaraba ta ce"au ɗakko ma halin yayi kenen? kaima halinne da kai? ga masifar son ƴammata a cikinka kamar kaine ka yankewa mamajo cibiya,kuma a haka nake haƙuri da kai ban ɗagawa kaina hankali ba,itama sanyawa kanta tayi saboda haka duk wanda ya ɗakko masifa bakinsa a'i,shiyasa Hajiyarku ta ce"yadda uwarta ke juya Babanta haka itama takeson juya mata ɗa,to shi kuma da yake ɗan halak ne sai yaƙi hakan,to shine fa abin duk ya damesu daga ita har uwarta mai taken shuwa".
Zubair bai ce mata ƙala ba ya tashi ya fita,Balaraba ta tashi da sauri tasha gabansa tana ce wa"Abban Khadija ina zaka je ne"?.
bai ce mata komi ba ya wuce ta,abin nan ya tsaya mata arai ta dai daure ta bishi don ganin inda yake son zuwa ɗin.
a hankali take binsa,ya ɗanyi murmushi don yasan Balaraba ke binsa kuma a koda yaushe haka ɗin take idan tana son yin gulma.
*** *** ***
....Ganin bakina har yana zubar da jini yasa na juyo cikin kuka na ce"Ahmad babu abinda zance a wannan lokacin,Allah yana sama yana kallo kuma shi kaɗai ne zaiyi min sakayyar duk wani abu da kake min,kai a ganinka ɓatamin ɗin da kake Allah zai barka? in sha Allah wataran sai kayi kuka akan abinda kake min na cutarwa".
wani bugun zai ƙara kaiwa bakina na gauce,na ɗanyi wata ƴar dariya wacce ake cewa tafi kuka ciwo na ce"Ahmad kenan,zaluncin bai ishe ka ba kenan"?.
a harzuƙe ya ce"wallahi kika ƙara kirana da azzalumi sai na canja miki kamanni,banza mara kunya wacce ba a bata tarbiyya agidansu ba".
Wani malolon baƙin ciki ne ya haɗu da ɓacin rai suka haifarmin da kyarmar jiki,na juyo da sauri ina hawaye na ce"Ahmad yau iyaye na kake zagi son ranka? ni ce ƴar marasa tarbiyya? ni kake jifa da irin waɗannan kalaman"?.
a matuƙar harzuƙe ya ce"da suna da tarbiyyar ne? tunda har suka kasa baki tarbiyyar da ta dace,baki san yadda zaki yiwa mijinki magana ba? kullu yaumin ke sai fitina da rigima? da kuma zargi? to ki sani ba zamanki nake ba kece kike zamana,saboda haka ki kula da duk abinda zai dinga fitowa daga wannan banzan bakin na ki".
durƙushewa nayi awajen na saki wani irin gigitacciyar ƙara,tunani kawai nake anya kuwa wannan Ahmad ne? mijina wanda ke tattalin farin ciki na? wanda baya son inyi kuka? amman yau shine yake zagina da ƙuntatamin? awasu lokutan abin ɗaure min kai yake,sai na dinga tunanin anya kuwa shine ko waninsa?.
ina cikin wannan halin ne naji ƙarar bubbuga ƙofa,na kasa tashi saboda yadda ƙafata ke kakkarwa,na fashe da wani irin kuka tamkar raina zai fita,ban taɓa jin wannan abinda nakeji yau ba,idanuwana naji suna wani irin lumshewa,sannu sannu na tashi amman kuma jiri nakeji har na buɗe ƙofar,ya yinda shi kuma ina jin tsakinsa yana shiga wanka,daman duk ranar daya dawo duk komin dare sai yayi wanka,kuma wankan daya ke ko ransuwar kaffara ba zanyi ba na wani abin ne.
ina buɗe ƙofar naga yaya Zubair,gabana ya faɗi don bana son yana jin abinda ke faruwa,don yana damuwa da halin da muke ciki sosai,saboda yaya Zubair aminin yayana ne wanda muke uba ɗaya,saboda haka ya ɗaukeni tamkar ƙanwarsa kuma nima duk damuwata bana ɓoye masa sai dai wani abin ina ɓoye masa don mata da miji sirrin juna ne.
zama nayi akan kujera ina mai sunkuyar da kaina ƙasa,wasu zafafan hawaye na ƙwaronyowa a ƙwarmin idanuwa na,na sanya hannuna ina gogewa na ce"Yaya Zubair don Allah ka dena tasowa cikin dare kana zuwa wajenmu,ko da kaji muna faɗa ka dinga haƙuri bana son matsalata ta dinga shafarka".
ɗan murmusawa yayi sannan ya ce"Rabi'atu kenan,ke yarinya ce sosai haryanzu baki san abinda zai cutar dake ba,amman irin waɗannan abubuwan da suke faruwa tun daga ƙanana har ta girmi mai girma,ma'ana idan aka bar waɗannan abubuwan suna faruwa tun daga yarintarku har ku girma kuna yi,alokacin kuna da ƴaƴa duk abinda za kuyi yaranku suna kallonku,daga nan kuma sai rigimar ta shafi yaranku azo ana abinda bai dace ba,saboda haka kika ga hankalina yana tashi sosai,amatsayina na babba bai kyautu in sanya muku ido ba,daga ke har Ahmad yara ne don haryanzu baiyi shekara talatin ba,saboda haka shima ya kamata adinga sanya shi a hanya."
muna zaune sai gashi ya fito falon,ya ɗaure fuska tamau tamkar bai taɓa dariya ba yana sanye cikin jallabiya fara sol,ya kalli yayan na sa ya ce"yaya lafiya kuwa"?.
Yaya Zubair ya ce"kai zan tambaya Ahmad lafiya kuwa? me ya haɗaka da matarka har na jiyo kukanta"?.
Ahmad ya ce azuciyarsa,oh yaya aƙwai gulma yanzu har ya ji?.
Yana cikin wannan tunanin ya jiyo muryar Yaya Zubair yana ce wa"da kai nake fa Ahmad? kayi min shiru?".
Ahmad ya ce"yaya ai ni ina ganin tunda kukanta ka jiyo ita zaka tambaya"?.
Da sauri na kalli Ahmad jin abinda ya faɗa,na ce"yanzu Yaya Zubair ɗin ma baka barshi ba"?.
Wani irin banzan kallo ya yi min sannan ya juya abinsa yana me latsa wayarsa ƙirar i phone,don na fuskanci duk maganar ma da muke yi bai ma san muna yi ba,hankalinsa da nutsuwarsa duk suna kan wayarsa.
Yaya Zubair ya ɗan gyara zamansa ya ce"Ahmad a farkon farko ina so in faɗa maka cewa kaji tsoron Allah,wannan yarinyar amana ce awajenka,saboda haka Allah da kansa ya ce dukkaninku ababen kiwo ne sannan matayenku ma ababen kiwo ne akanku,kaga kuwa matuƙar ka mutu kana me zaluntar matarka ranar gobe ƙiyama sai an tambaye ka yaya kayi kiwonka"?.
Ahmad ya ce"to macen da take zargin mijinta fa"?.
yaya zubair ya ce"ni dai da kai nake magana yanzu ba da ita nake ba,saboda haka ita mace hankalinta dana miji ba ɗaya bane,saboda haka kaji tsoron Allah kayi mata adalci a dukkanin lamuran ka,sannan in dai kace zaka tanƙwara mace ta ƙarfi to wallahi ba zata yi maka abinda kake so cikin sauƙi ba,saboda ita mace anyi tane da ƙashin haƙarƙarin namiji,to kaga idan kace zaka tanƙwarata ta ƙarfi to wannan ƙashin zai karyane,saboda haka Ahmad ka kula ka mayar da hankalinka idan ma wani abu ne yake damunka,sannan kaji tsoron Allah aduk inda kake,kada kayi zaton ita bata kallonka kaje ka aikata wani abin,idan ita bata kallonka Allah yana kallonka,in dai kaji mace tana zargin mijinta to aƙwai ɗayan biyu ne,ko dai yana raba dare bai dawo ba,ko kuma tana ji yana waya da ita ko da kuwa budurwarsa ce,wanda kuma cin mutunci ne ace kana gidanka na sunnah kana waya da wata,sannan cin mutunci ne ka wulaƙanta matarka saboda wata,saboda haka ni de ina jan hankalinka Ahmad ka nutsu ka yiwa yarinyar nan adalci,ka dena kuma dukanta don manzon Allah (S.A.W) ya ce idan matayenku suka ɓata muku rai to ko da zaku dake su ba a yarda ku dake su da bulala ko madoki ko hannu ba,kyalle ake samu aɗan dakesu kaɗan kuma cikin hikima da soyayya,ba wai cikin zalunci ba don kuwa na tabbatar muddin aka yiwa ƙanwarka haka ba zakaji daɗi ba,saboda haka kada ka yiwa ƙanwar wani".
Ahmad ya ce",yaya itama kayi mata faɗa ta dena yimin rashin kunya,ai ni mijinta ne indai tana da tarbiyya ai bazata dinga yimin tsiwa ba".
Da sauri na kallesa ina goge hawaye,wato ni ce ma mara tarbiyya? har abada ni nasan Ahmad ba zai dena xagina ko gayamin munanan kalami ba.
Yaya Xubair ya kalleni ya ce"ƙanwata aƙwai abinda kema nakeso ki sani,kuma idan da hali ji dena baki ɗaya duk matar da takewa mijinta tsiwa to ba zai taɓa ganinta da kima ba,ki dinga haƙuri kina cijewa a waɗansu abubuwan ba a komi ake magana ba,aƙwai abinda kai kasan an cutar da kai amman haƙuri da juriya shi ke kai mutum bigiren da bai taɓa tunanin zuwansa ba,saboda haka ki dena kinji ƙanwata"?.
share hawaye na nayi sannan na ce"to yaya in sha Allah na dena".
Yaya Zubair yayi murmushi sannan ya yi mana nasiha sosai dukanmu ya yi mana sallama ya fita.
Yana fita ya tashi yayi tsaki sannan ya shiga ɗaki,na bishi da kallo tamkar zan cinye shi ina masifar son Ahmad sannan ni macece mai tsananin buƙata,inason kasancewa da mijina amman hakan ya faskara,don a ƴan shekaruna waɗanda basu wuce 17 ba amma har namiji ke wulaƙantani? da ɗanyar yarintata? inason faɗawa yaya zubair wannan maganar ba,idan na faɗa tamkar na tona asirin miji na ne,tunda nasan hukuncin macen da ke tona asirin mijinta.
Anan nake jan hankalin mata,zamani ya kaimu lokacin da mace zata zauna tana sarrafa harshenta wajen tonawa mijinta asiri,baya yimin kaza baya yimin kaza ko kuma wajen shimfiɗa baya yimin komi,kiji tsoron Allah ki adana sirrinki,itafa ƙawar da kike bawa labarin a banza zata dinga ganinki,mijinki kuma idan ya fito a dinga ganinsa banza,saboda haka kiji tsoron Allah ki adana sirrinki kici gaba da addu'ah.
Balaraba tana laɓe inda take,tana jin takun sawun mijinta ta zura da sauri taku ɗaya Zubair ya yi ya kamo hannunta ya ce"ba rakiya kika yi ba? ai tunda rakiya kika yi sai ki tsaya mu tafi tare ko? ko kuwa meye na guduwa"?.
da sauri ta rintse idonta saboda kunya,yana riƙe da hannunta har suka isa ɓangarensu da yake da ƴar tafiya kafin su isa nasu ɓangaren,suna zuwa suka tarar Khadija na ta kuka tana riƙe cikinta,yarinya ce wacce ba ta wuce shekara ɗaya da rabi ba,dama ba tada lafiya ƙwana biyu.
da sauri Balaraba ta isa gare ta,tana hawaye tana ce wa"Khadija sannu kinji".
Zubair ya ce"kin gani ko Balaraba? har yaushe ne zan ja miki kunne akan gulma? yanzu ga irinta nan ai,idan ma mutuwa tayi tunda kin tafi yawon gulma ba lallai ki sani ba".
kasa magana tayi saboda kunya ta rungume Khadija.
Shi kuma ya ɗakko magungunanta aka fara bata,saboda yarinyar tana da limoniya tunda aka haifeta,fashewa da kuka Balaraba tayi ganin numfashin Khadija ya ɗauke cak.
*** *** ***
......Ranar gidan Babbar masarauta cike yake da manyan mutane,ana taya Yarima murnar dawowa shi kuwa Yarima yana maƙale kusa da Mommansa da Papansa.
Momma ta kallesa tana harararsa ta ce"gaskiya ni sai inga kamar ba aiki kaje yi ba,dubi fa yadda ka ƙara wata irin ƙiba kai dama gaka ga yadda kake".
dariya mutanen wajen suka saka,ya gimtse fuskarsa tamau ya kalli autar Momma ya ce"ke fita a falon nan".
Da sauri ta tashi zata fita Momma ta ce"ke zo nan Allah ba inda zata fita,duk kabi ka tsoratar min da Autata nan de aka sanya dariya shi kuwa sai kallon agogo yake,dama aƙwai plan ɗin daya shirya saboda haka lokaci na yi ya miƙe da sauri kamar an tsokale shi..........Soon➡️✍🏽
ga link na facala game nema,bana son maza a grp da ƴan iska ehe😎😂.
***
ZycAMeQZ09jYzYRWCX0
#YARIMA
#RABIATU
#AHMAD
#BALARABA
#ZUBAIR
MRS GREEN CE.
SHARE
COMMENTS.
TALLAH TALLAH TALLAH
MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.
Abubuwan da ke cikin littafin kaloli dabam dabam na👇🏾
Haɗin Dilka
Haɗin man gyaran gashi
Haɗin sabulun gyaran jiki
Haɗin ƙugu(hips)
Haɗin gyaran (Breast)
Haɗin maganin infection
Haɗin furen zogale
Haɗin tsumin tabaje
Haɗin Kaza
Haɗin tantabara
Haɗin ƙamshin jiki
Haɗin ƙamshin baki
Ingantattun maganin mata
Bonus
Sirrin riɗi
Sirrin magarya
Sirri magaruwa
Sirrinmu(Addu'oi)
Za ku iya biyan kuɗin littafin akan farashinsa mai sauƙi #1,500 kacal amma ga garaɓasa ga
Mutum 30 da suka fara biya na farko, zasu biya 1000 kacal, ku yi hanzari ku yi payment akan lokaci don neman ƙarin bayani *** SIRRIN MOWA NA MANYAN MATA NE, MATAN SO BA MUNA MATA BA.