KOWA DA ƘADDARARSA

04

by @faddabanan

Lokacin da agogo ya nuna minti arba'in da tahowar ta sai ga wayar shi yana tuhumar ina ta maƙale haka, shi ya gaji ita kaɗai ya ke son gani. Shewa kawai muke yi kafin ta juya ta tafi in da ta baro su ɗazun.

Chan muka hango Surayya tana tahowa, tsabar ɗokin mu ji me ya faru yasa muka ga ba sauri ma take yi ba kuma sai dariya take yi. Ko da ta qaraso ma cewa tayi a jira Zara'u ta dawo, yanda ba sai ta bayar da labarin sau biyu ba.

Ko minti goma ba'a yi ba sai ga Zara'u ta dawo fuskanta ɗauke da fara'a tace "Surayya ke kuwa ina kissar taki? Kin san me Umar yace? Wai ba ya son ina hulɗa da ke, kaman idonki ya buɗe da yawa. Nayi-nayi ya faɗa mun abin da kika masa da har ya ga hakan, amma ya kafe ba komai kawai dai ba ya son mu tare."

Surayya ta amsa " Ai yanda kika san bulo haka Umar ɗin ki yake. Masifa! Kin san tun da kika bar mu bana jin yayi mun cikakken zancen da ya kai takwas. Bari dai na kunna maku ku ji."

Kaf tsayin lokacin Surayya ce kawai take ƙoƙarin jan sa da hira, sai yayi kaman zai saki jiki su yi magana sai ya yanke maganar, ƙarshe sai ya koma amsa wa da 'ummm', 'uhm-uhm' ko 'hmmm'. Daga baya ma cewa yayi "Wai ke bakin ki ba ya gajiya da surutu ne?". Matuƙa abun ya ba mu dariya, har Surayya na faɗin kawai dai don ya gan ta tare a Zara'u ne, amma da a wani waje ne sai dai a ji sabon labari. Daga bisani muka yanke shawarar Zara'u ta sanar da shi gaskiyar zance, kar yake ganin baƙin Surayya.


*******************************

Ina komawa gida na iske motar mai littafi yana shirin barin ƙofar gidanmu, yana gani na ya dakata yana faɗin "Allah ya taimake Ni ba sai na ƙara dawowa ba, barkan ki da zuwa Ummul."

Mamakin ganinsa nake yi, ashe har sunana ya sami kenan. Na amsa "Yauwa mai-littafi, shine rannan ka yi tafiyar ka ba ka jira na ɗauko maka littafin ka ba ko? Don ma ka sani Ni ba yanzu zan bayar ba."

Ya amsa cikin murmushi "Ni dama ba littafi ya kawo Ni ba, ke kawai na zo gani. Sannan Gadanga ƙusar yaƙi nake ba mai-littafi ba."

"Aliyu?" Na tambaya

"Na'am"

Haka yayi ta ja na da hira har aka yi kiran Sallah sannan ya yi mun sallama ya tafi.


Tun daga ranar kusan kowanne ƙarshen sati yana gidanmu har ba zan ce ga lokacin da muka fara soyayya ba. Bai jima da fara aiki ba tun bayan kammala karatun shi a jami'ar Bayeron.

Shaƙuwar mu ta san ya san duka 'yan gidanmu don suna haɗuwa idan sun zo hutu, amma sun fi sabawa da Yaya Naziru (barin ma yanzu da ya dawo Kano gabaɗaya don ƙarasa bautar ƙasar). Faɗar cewa sun saba da clique ɗina na makaranta ma ɓata lokaci ne, ko bana kusa shi da su Fatima kan zauna su sha hirar su kamar shi suka sani ba Ni ba.


Ranar wata Laraba muna zaune kafin mu shiga lecture ta gaba, sai ga Umar ya zo, har da kawo mana take away ganin rana ta take kuma yau har shida za mu kai. Nan tare da mu ya zauna ana hira gabaɗaya, Surayya ce kaɗai ba ta nan. Kamar haɗin baki sai ga Aliyu shi ma tafe da na shi take away ɗin har Fatima na tsokanar su da cewa so suke mu yi ƙiba dai da alama.

Surayya ita ma ta iso daidai lokacin ta yi sallama. Tana ganin Umar ta kwashe da dariya tana faɗar "An gaida Saraki na Saraki" shi ma dariyar yayi yace da Aliyu "Kasan me yaran nan suka yi mun kuwa?"

Aliyu yana murmushi bayan sauraron Umar yace "Amma fa sun solaka,amma da yake mata ne afuwa za'a yi masu, su a zaton su kyau ne ke ruɗarmu...." 

Umar ya katse shi da cewa " Allah yayi maka albarka ɗan uwana! Abin da nake so su fahimta kenan. Babu ƙarya in an ce kyau ya ɗau hankalin mu, mu mutane ne ai kuma masu jini a jika, amma so ai daban ne."

*****************

A haka lokaci yake ta tafiya har muka gama jarabawar ƙarshen zangon karatu na farko, muka tafi hutun sati Uku kacal. Ranar da na kammala jarabawa ina zaune a falo bayan na yi sallar Isha ina kallo, don tun kafin na fara jarabawar na watsar da komai shine yanzu nake son rama abin da ya wuce mun. Ko nisa ban yi ba sai ga Hussain ya zo kirana wai Aliyu ya zo. Cikin ɗoki na tafi wurinsa don rabona da shi tun kafin na fara jarabawa kasancewar Ni na hana shi zuwa don na samu sararin karatu sosai.

Yana gani na ya tsare Ni da ido yace "Wai duk wannan dogon wuyan na menene? Examz ɗin farko kika yi fa akwai wasu a tafe, bai kamata ki dinga ɗaga hankalin ki ba ga shi tubarkallah kina da ƙwaƙwalwa." Ni kam ban saurari ƙorafin da yake mun ba, dariyar daɗin ganinsa kawai nake yi.


Amma fa abin da ya kawo Aliyu yau wurina yana cike da rikitarwa a gare ni, domin abin da ban zata ba ne ya zo mun da shi. Yana buƙatar na amince da shi ya turo magabatansa gidanmu domin tambaya, idan da sarari ma a taho har da kuɗin gaisuwa. Ban amsa masa nan take ba, domin ban taɓa zaton zai ce zai turo yanzu ba, na fi zaton nan da lokacin da na shiga aji uku yanda kafin a kammala komai na gama makaranta gabaɗaya ko ina gab da gamawa.

Abu ɗaya na sani, son da nake yi wa Aliyu zazzafa ne, zan iya haƙura da buƙata ta don na zauna da shi har ƙarshen rayuwata. Mun bar maganar akan cewa zan faɗa wa Mama buƙatar shi, ko me a ciki zan sanar da shi.

Ko da na shigo gidan kai tsaye wurin Yaya Naziru na wuce don na faɗa masa abinda Aliyu ya zo da shi. Shiru yayi kamar yana nazari sai kuma yace "Ummu za ki iya haɗa karatu da sabgogin da ke cikin aure? Da yake tsakanin mu babu boye-boye sai nace "Ni fa ban sani ba, kawai dai nasan ina son Aliyu da yawa da har zan iya yin abubuwa domin faranta masa. In dai bai ce zai hana Ni karatun gabaɗaya ba, i think I can manage."

A daren Yaya Naziru ya samu Baba da maganar, abin da Baba ya fara tambaya shine"Ita Ummun tana son shi?" Shi kuma ya amsa da cewa "Ai ita ce ma ta kawo zancen tace na sanar da ku, duk abin da kuka yanke sai a faɗa masa."

Baba yayi shiru ɗan jim haka sannan yace "Je ka Naziru, babu komai. Bari na sanar da mahaifiyar ku, ba zai yiyu mu yanke shawara mai mahimmanci irin wannan ba ba tare da ta sani ko ba da gudunmawa ba. Zan sake neman ka."

A kuma ranar aka yanke shawarar ba shi damar fitowa kaman yanda ya buƙata ganin cewa ina son shi Ni ma. Har na kwanta bayan na kora Hassana ɗakinsu na jiyo Mama tana kira na daga falo. Tare da Baba na iske su. Tambayoyi Baba ya dinga mun game da Aliyu da kuma neman tabbacin ko ina son shi ko a'a, daga ƙarshe yace na tura nasa Aliyu yana son ya gana da shi.

Washegari da marece sai ga Aliyu yazo, ni da na gan shi da farko ma na ɗauka ba shi da lafiya don har idonsa sun faɗa yayi zuru-zuru. Shi yasa ma na kasa zama na shiga tambayar shi me ke damun shi. Murmushi mai kama da yaƙe yayi bai amsa ba, sai damuwa da ta ƙaru akan fuskarsa. Gaba na yayi mummunan faɗuwa da wani irin hanzarin na buɗe ƙofar mota ta ɓangaren shi na tsuguna, ƙwalla ta cika mun idanu.... Ganin hawaye a idona ya sanya shi razana, cikin hanzari ya sa hannu yana goge hawayen da ya fara gangarowa daga fuska ta yace "Haba Ummul haba mana, don Allah ki bar kukan nan, ki daina zan faɗa maki abinda ke faruwa, yi shiru, kin ji?"

Hannunsa na sauke daga fuskanta tare da jan hancina, na miƙe tsaye tare da rungume hannayena na jingina jikin motar shi ina kallon ƙasa da nuna alamar sauraro. Ya ɗan yi jim yana kallo a kafin shi ma ya fito daga motar ya tsaya daf da Ni har ina jiyo saukar numfashin sa sannan a hankali ya fara magana "Ki yi haƙuri Ummul fargaban abinda za ki faɗa mun ne ya tarwatsa mun ciki (gudawa) kuma na kasa cin komai. Ban san iyakar soyayyar da wannan zuciyar take maki ba, nasan na so kaina saboda nasan yanda kike son karatu sosai, tsorona ɗaya kar ki ce sai kin gama makaranta tukunna don Allah ma ya sani ba zan iya jira wasu shekaru...." Ya tsaida maganar yana sauke ajiyar zuciya.

Tausayin kan mu ya kama ni, a hankali na juyo na fuskance shi nace "Haba Aliyu! I fall for you before you even knew of my existence, ni kaina ban sani ba sai daga baya. Yanzu haka bana tunanin son da kake mun ya wuce nawa. Na riga na sanar da su, Baba yace dama idan ka zo na faɗa maka yana son ganin ka tukunna kafin ka turo....." Juyowar da yayi da sauri ne ya sanya na yi shiru, sai kawai ya fara hamdala "Idan Baba na ciki ki faɗa masa gani na zo." Ina dariya na amsa "Sun fita da Yaya Naziru kuma ban san lokacin da za su dawo ba."

Muna tare har aka yi magriba amma quaker oats na samu na dama masa, yana ta mita bakinsa ba daɗi ba zai sha ba, haka na dinga lallaɓa shi har ya sha da dan yawa. Ya yi baya da kujerar motar ya jingina sosai, ba yanda ban yi da shi ya je gida ya kwanta ba amma ya ƙi wai ganina ma magani ne, idan ina son ya warke na bar shi yayi ta kallona ko da ba za mu yi hira ba.

Mun yi sallama kenan yana shirin tafiya sai gasu Baba sun dawo. Ai kuwa ya maƙale ya ƙi tafiya, tare suka yi Sallah a masallacin layin mu kafin ya samu damar tattaunawa da Baba. Ko da ya gama bai nemi Ni ba sai tashin motar sa naji kawai kuma ya figeta kamar me tashi zuwa sama.


Yaya Naziru ne ya faɗa mun yanda Baba suka yi da Aliyu. Kawai tambayoyi ne da suka danganci aikinsa, danginsa da sauran tambayoyi dai da suka dangancesu. Ina kitchen ma na jiyo Baba yana faɗawa Mama ya yaba da hankalin yaron, Allah ya sa kuma ba pretending yake yi ba. Mama tayi dariya tare da faɗin "In shaa Allah babu damuwa, Allah kuma ya haɗa kansu." Farin ciki ya lulluɓeni ganin ya samu karɓuwa.

Washegari wurin ƙarfe goma na safe sai ga Yaya Zainabu ta bugo waya, mamaki kawai take yi domin ta san alwashin da na ci akan karatu tare da faɗin sai na gama zan yi aure. Na amsa da cewa "So ne Yaya Zainabu, Allah wani banzan abu ne da yake rushe dukkanin wani ƙuduri, just wish us well kawai."

Dariya tayi tace "Yau na ga ta kaina Ni Zainabu, wai Ni Ummu ke yi wa lecture akan so." Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya tare da katse kiran.

Kwana biyu bayan nan 'yan gidansu Aliyu suka zo tambaya da kuma kawo kuɗin gaisuwa sannan sun ce a kusa za su dawo sa rana.

Tun bayan nan kusan kullum da marece ko dare Aliyu na gidanmu, shaƙuwa tsakanin mu sai ƙara yawa take yi. Ranar wata Litinin yana tasowa daga aiki kai tsaye ya taho gida wurina, kallo ɗaya za ka yi masa kasan a gajiye yake hakan ya sa na koma gida na ɗauko masa abinci da lemo. Zan koma ɗauko darduma ya hana ni wai zai ci a mota kawai.

Ya fara cin abincin muna hirar mu, garin dariya sai wanda ya ɗebo a cokali ya ɗan zuba gefen rigar shi, da saurina na sa hannu na fara goge masa wurin amma sai ya sa hannun shi ya riƙe nawa hannun tare da maido su jikina sannan ya mayar da nashi bisa ƙafarsa. Shiru ya biyo baya kowa da abinda yake zagayawa a cikin ransa.

Ni kam kaina a ƙasa yake, kunyar duniya ta rufeni sai tambayar kaina nake me yasa nayi hakan ma tun farko? Shikenan mutuncina ya girgiza kenan, yanzu haka ma ɗauka zai yi na saba yin hakan da wasu, wayyo Ni, ƙasa tsage kawai na shige...

Tunanina ya katse saboda maganar da ya yi cikin murya mai matuƙar sanyi "Ummu ki yi haƙuri, i can guess me kike tunani probably ma kin ɗauka wulaƙanci ne ya sa na sauke hannunki haka amma ko kusa ba haka ba ne, i did it for your own good and safety. Bari na faɗa maki wani sirri da ba ki sani game da Ni ba." Ya juya tare da ajiye farantin abincin a bayan mota sannan ya juyo da nufin kama hannuna amma sai yayi sauri ya mayar da su kan ƙafarshi. Ya cigaba da magana "Allah ya yi ni mai matuƙar ƙarfin sha'awa amma ke Ummul tsananin so nake maki shi yasa kika ga ko attempting na riƙe ki bana gwadawa, domin ji nake kaman kina passing electric current yana ratsa dukkanin jikina. Ranar da nazo ba Ni da lafiya har na goge maki hawaye a wahale na kwana, ciwon ciki kaman ba zan kai safiya ba kuma idan kin tuna za ki ga sai da kwana biyu bayan nan ban zo ba ai ko? Bana son ɓata pure alaƙarmu, besides ma shine ƙarfin ɗago maganar auren mu a wannan lokacin. Na roƙe ki ki yi mun afuwa, amma na fi kowa son na kasance tare da ke. Ummul Pleaseeeeeeee?! Ya ƙura mun ido yana jiran amsa.

Ni kuma yanda ya ja kalmar Pleaseeeeeeee ɗin nan ta saukar mun da wani yanayi a jiki na da ba zan iya kwatanta wa ba, ga kunya kamar na ɓace daga wurin kawai, da kyar na iya cewa "it's okay" na juyar da kaina ɗayan ɓangaren, wannan wane irin katoɓara ne a bakin Aliyu saboda Allah?

Tun daga ranar ban ƙara yarda na yi kusa da shi sosai ba bare na kai ga taɓa shi, shi ma ya lura amma ba shi da bakin magana.