14_15
by @kainaat1515
DOCTOR SHAZIM
Written ✍
By
🌹~ KAINAAT ~ 🌹
*_KING AND QUEEN WRITING CHAMBER_*
Season One
free
Episode
14_15
WASHE GARI
Tunda suka yi sallar asuba basu koma bacci ba saboda ɗokin zuwa wurin ƙunshi da gyaran kai da za suje, ko da gari yayi haske wanka kawai suka yi suka shirya sannan suka nufi ɗakin Mom, koda suka shiga basu sameta ba kitchen suka wuce anan suka same ta ita da baaba larai suna shirya breakfast gaishe dasu sukayi, Mom tace"wai ba dai har kunshirya ba"
"munshirya , tafiya ma zamuyi" suka bata amsa
Mom tace"to sai ku bari kuyi breakfast tukunnan"
Aairah tace "ba fa direct saloon din zamu wuce ba, sai fa munje gidan Aunty Safiya mutafi da Najma "
"duk da haka dai kujira kuyi breakfast sannan"mom ta faɗa, da to suka amsa mata, dole suka tsaya sai da suka yi breakfast ɗin sannan mudi ya kaisu gidan ya dawo, basu wani jima ba saboda ko da suka je Najma harta shirya su kawai take jira, basu wani bata time ba mus'af ya kaisu shagon saloon ɗin da zasuje, wurin ya haɗu babu wani nau in gyaran jiki da basa yi, kama daga wankin kai har izuwa kunshi da gyaran ƙafa......
Wannan Kenan
✨Ammy_Fatima _Noraiz ✨
Zaune suke kan dinning suna breakfast, shazim ya shigo jikin sa sanye da jogging suit white color,sai p_cap black color , wurin su Ammy ya nufo yana faɗin"ina kwana Ammy"
da lafiya lau Ammy ta amsa mashi "Ammy ai da kun bari na dawo sai muyi breakfast ɗin tare"
"kai da shigowar ka ba yanzu ba, waye zai tsaya jiranka"
"amma Ammy ba gashi nashigo da wuri ba"
"yau koh" Ammy ta faɗa
Noraiz ne ya ce "yaya da ƙarfe nawa zaka je abnoor yau"
"yau bazan jeba"
"amma yaya saboda mi"
"haka nan, zamu je wani wuri ne shiyyasa, idan kun kammala breakfast ɗin, Ammy ku shirya" Fatima tace "wannan wane bazata ne haka yaya "
Ammy ma cewa tayi "ina zaka kaimu" murmushi yayi haɗi da cewa "surprise ne, ku dai kawai ku shirya"
daɗi suka ji saboda sun san wani abun mamakin ne yake son yi masu bazata dashi, saboda shi idan ya so fa akwai wasa da dariya, in kuwa baiso ba tofa zaka same shi kadaran kada ham, duk da da man akwai kyakyawar alaƙa tsakanin sa da ahlinsa, wani lokacin in yana tare da su zaka same shi kamar bashi ba, cigaba su kayi da breakfast, shi kuma part ɗinsa ya nufa domin watsa ruwa sannan ya dawo yayi breakfast , san da ya kammala nasa breakfast din dukan su sun shirya shima ko mawa yayi part dinsa ya shirya cikin wani haɗaɗen yadi wanda yasha ɗinkin zama ni" wurin su ya dawo, Ammy ce tace "kai Masha Allah ba ƙaramin kyua kayi ba"
"nagode sosai ammy" gaba yayi yana faɗin "to ku taso mu tafi" tashi su kayi su ka bi bayan shi zuwa compound din gdn, anan suka samu motar da zasu fita da ita ilya ya gama gyara ta ya fito da ita compound , nufar motar suka yi, shi ya shiga ma zaunin driver ya yin da Noraiz ke kusa da shi Ammy da fatima kuwa baya suka shiga, reverse yayi ya nufi gate, a dawo lafiya su ilya suka shiga yi masu, driving yake , su Ammy sun zuba ido ne suga shin ina kuma zasu, wani katafaren shopping mall na ji da faɗa ya nufa dasu,sabon mall ne daga gani ba'a jima da fara aiki a cikin sa ba, parking yayi a parking lot ɗin wuri sannan yace "Ammy ku fito, mushiga ciki " to kawai Ammy tace sannan suka fito,sai da suka fito su duka sannan yace "kowa ya kalli sama " kamar yan da yace haka suka ɗaga kansu suna kallon saman shopping mall, in da aka rubuta (WHITE HOUSE SHOPPING MALL) da man yan baƙi ammy sauke kanta tayi tana kallon shazim cike da alamar tambaya, ganin kallon da ammy keyi masa yasa shi murmushi yana faɗin "surprise " cike da mamaki ammy tace "wai ni kam ina zaka kai son kuɗi ne shazim"matsowa yayi kusa da ita haɗi da dafa kafaɗar ta yace"ammy ina da ku idan ban nemi kuɗi ba mizan yi"
"haba shazim business nawa kake "
"Ammy koma nawa nake, wannan ba wani abu bane, ki sa mashi albarka "
"to Allah yasa albarka ya ba da sa'a "da ameen suka amsa su duka, shazim yace "Mu shiga ciki" ciki suka shiga ya na gaba suna binshi a baya,wani matashin saurayi ne a ƙalla zai yi kimanin shekara 27 ya nufo su, gaishe da ammy yayi da shazim,gaishe da shi noraiz da fatima su kayi, da fara'a a fuskar shi ya amsa masu, shazim yace"ya aikin hameed "
"alhmdllh, komai na tafiya dai dai"
"masha Allah,muje ina son nu na ma su ammy ko wane part "
"ok to shikenan "ciki su ka wuce, wura re ya shiga nuna masu shi da hameed , sai da ya kaisu ko ina a cikin mall ɗin sannan suka ya da zango a office ɗin shi, hameed kuma ya koma wurin ma'aikata ,office ɗin ya haɗu sosai kamar ba office ba, ammy na kan sofa su fatima na ƙasa kan carpet, shi kuma yana zaune kan swivel chair,ammy ta ce"shazim wuri yayi kyau Allah ya taimaka "
"ameen Ammy"
ammy tace "yanzu wa zai kula da nan? "
"a kwai wani ƙanin hameed shi zai kula da nan, hameed kuma noraiz sai su cigaba da kula da wan can business ɗin " "to shikenan, hakan yayi kyau"
sun jima a office ɗin sai da rana tayi sanyi suka fito,yace su shiga ciki kowa ya zabi abun da yake so,
da sauri fatima ta jawo masu cart, suka shiga jidar abun da ransu yayi masu musamman Fatima da Noraiz, Ammy kuwa shazim ke tura mata nata cart din tana daukar abun da take so, sai da kowa ya dauki abun da yake so, ma'aikanta wurin suka kwashe kayan suka zuba masu a booth, sallama suka yi ma su ammy,har parking lot hameed ya raka su,( bayan aikin asibiti shazim yana business sosai tun kafin ya fara aiki da buɗe abnoor yake business, yana sai da motoci wanda hameed ke kula da shi yana da boutique da gidan gona sai white house da ya buɗe yanzu, amma ba shi ke kula da su ba kula mashi ake da su ) mai makon ya kaisu gida wata hanyar ya kuma sake ɗauka , in da ake sai da laptop's ya nufa dasu yana parking suka fito shi da noraiz , su ka shiga ciki, noraiz ya zaɓar ma fatima laptop mai kyan gaske shima,kuɗi ya biya suka fito zuwa mota, daga nan wuren bu ɗe ido yai ta kaisu, Ammy ba ƙaramin dadi tajiba saboda rabon ta da ta shiga gari da sunan miƙe ƙafa har ta manta, sai da yamma likis sannan suka koma gida, godiya su duka suka shiga yi mashi, shi kuma yana cewa "dan Allah su bari mana,wannan ai wajibi ne a gare sa daya yi masu fiye ma da haka"
Ammy tace "duk da haka shazim, bakaji mi hausawa suka ce ba?, yaba kyauta tukwici, tunda bamu da tukwicin dazamu baka shine muke godiya"
"to shikenan " kawai ya iya cewa , ilya ne da mai bama flowers ruwa suka shigo da kayan da suka zo dasu, su kuma kowa daki ya nufa domin watsa ruwa ,Fatima na shiga ɗaki wayanta dake cikin bag ta ciro daketa ringing, ya dr ne ke kira, katsewa kiran yayi zata kira sai kuma wani kiran ya sake shigowa,picking tayi haɗi da sallama amsa mata sallamar yayi hadi da cewa"yar ƙanwata ya kike ya gida ya su Ammy? "
"lafiya lau Yaya"
"masha Allah, ina gaishe da su sosai"
"zasuji Insha Allah "
"miye labari "
"ai ni yaya fushi nake da kai, "
"to fah, kaina bisa wuya ni kuwa mi na ai kata"
"wai ace in gama secondary school, Amma yaya ko irin text dinnan na congratulations ban samu daga gareka ba kai da ya mansoor "
"Allah sarki fatima, kiyi hakuri kinji, so naima ace nazo har Lagos din, amma kuma wasu yan abu bu wa ne suka sha kaina, amma kiyi haƙuri kinji"
"shikenan yaya bakomi, dama yanzu baka wani ji dani,"
"kai , ya za ki ce haka "
"haka ne mana, yau she rabonka da zuwa Lagos, tun kuna mutunci da ya shazim sosai "
murmushi yayi mai sauti yana cewa"waya ce maki bama mutunci sosai yanzu"
"to baga shi nan ba yanzu baka son zuwa Lagos "
Fatima kenan, ya fada a zuciyar shi , a zahiri kuwa cewa yayi"fatima yana yin aiki ne kawai ba wani abu ba, amma Insha Allah ina nan zuwa Lagos very soon "
"to Allah ya kaimu ya nuna mana lokacin" da ameen ya amsa fira suka shiga yi da bisani suka yi sallama, ya mansoor ta kira shima tayi mashi ciwan baki ra shin kiranta, haƙuri ya shiga bata, sun jima suna waya,
a chan parlor kuwa Ammy ce ta fito daga ɗakin ta, Innah asabe ta samu a kitchen tana jera kayan da suka siyo, gaishe da Ammy tayi, amsa mata Ammy tayi cikin kulawa, Inna asabe tace "mi za'a dafa yau da daddare "
"A'a ba sai an dafa komai ba munyi takeaway da muka fita"
"to shikenan "kawai Inna Asabe tace, gyara kitchen din kawai suka yi.....
✨Victoria✨
"destiny wai kina ganin abun da gurutu ya bamu yana aiki kuwa, kusan fa wata daya kenan bawani chanji"
Destiny tace"karki damu na yarda da Gurutu, mukara lokaci kawai, idan ma muka ji shiru mu sake Komawa kawai"
"gaskiya abun da za'ayi kenan gara kawai mu koma"
destiny tace "to shikenan amma mu ƙara lokaci mugani "
✨Hidaya✨
Zaune take bakin gado wayar ta dake gefan ta ce ta fara ringing picking tayi hadi da manna wayar a kunne tana fadin "hello maryam ykk ya gida"on the other hand maryam tace"lafiya lau hidaya"
hidaya tace "Masha Allah"
"mi kike yine haka naji kamar muryar ki tayi ƙasa? " maryam ta tambaya, amsa hidaya ta bata da "lpy qlu, kawai dai ina kwance ne"
Maryam tace"ok to yayi, ya labari doctor kinsan kwana biyu ban shigo hospital ba, ina dai fatan kin fada masa abun da ke ranki"
sauke ajiyar zuciya hidaya tayi, sannan tace"ina fa maryam, wlh da na gansa rasa duk wani kwarin gwiwata nake, sai kawai naji na kasa fada masa"
Maryam tace"gaskiya hidaya kina da aiki, yanzu nan fada masa dinne kika kasa yi "
"uhmm maryam kenan dan dai kawai bake bace a matsayi na ba ne shiyyasa"
"ba haka bane hidaya, daurewa kawai zakiyi ki fada masa"
"to shikenan maryam zanyi kokari naga na fada masa nagode sosai"
"bakomi idan ma kin kasa sai mu nemi number shi, kota waya ne sai ki fada masa, fata na kawai shine ya amince dake amatsayin abokiyr rayuwa, in ga ta tsiyar su destiny da Victoria "
"to Allah yasa ya soni koda bai kai wanda nake masa ba" hidaya ta fada
"to ameen sister, ki cigaba da adu'a Insha Allah dr naki ne ke kadai"
"to Allah yasa"
da ameen maryam ta amsa mata sun dan jima suna wayar daga bisani suka yi sallama......
✨Aairah_Aaimah✨
Ana kammala masu saloon din da kunshi mus'af yazo ɗaukar su, mus'af ne yake cema Aairah " kai masha Allah sweetie irin wannan kyau haka kin kuwa ga yanda kunshi nnan yayi matukar yi maki kyau"
"nagode sosai" Aairah ta fada
Aaimah ce tace
"da yake ya mus'af Aairah ka dai ka sani shiyyasa kace nata yayi kyau mu ko ka kalli namu, abun yar wariyar launin fata ce"
"No Aaimah ba haka bane, na qalbie ne ya ɗauke man hankali, amma kuma naku yayi kyau sosai"cewa Aaimah tayi
"shikenan ya mus'af bakomi"
"mu tafi koh"mus'af ya faɗa nufar motar suka yi, Aairah ta shiga gaba, sai Aaimah da najma a baya,
gidan su Aairah ya nufa dasu, parking yayi a compound , su Aairah suka fita , masu decoration suka samu a compound din suna decorating, main entrance din gidan suka nufa, koda suka shiga ciki baaba larai da Mom da Aunty rabi suka samu a parlorn, suna aikin zuba souvenirs cikin jakunkuna masu dauke da sunan Aairah da Aaimah, shiga suka yi parlorn bakin su ɗauke da sallama, amsa masu sallamar su Mom suka yi, da gudu su Aairah suka nufi Aunty rabi, suna fadin "oyoyo Aunty, ashe kin zo"
Aunty rabi tace "na zo Mom ɗinku ke faɗa man kuna wurin salloon, buɗe mugani " ta faɗa tana cire ɗan kwalin Aairah
" kai masha Allah, gaskiya yayi kyau"
"na gode sosai Aunty" Aairah ta fada, Aaimah cewa tayi" to ni bari na tashi, tun da na lura Aunty baki tani ta Aairah kike"
Aunty rabi tace "sorry Aaimah, ke ma ina ta ke, mu ga naki kema" mom ce tace " to tunda abun ƴar wariyar launin fata ce ,matso kinji ƴata naga naki harda ƙunshin" ta faɗa tana miƙama najmah hannun, da sauri najmah ta ƙarasa wurin Mom, nan tashiga nuna mata
Ina wuni, suka ji mus'af yace,
Mom ce tace "wai dama mus'af tare kuke"
"eh" yaba Mom amsa, gai sawa su kayi har da su Aunty Rabi da baaba larai , mus'af bai wani jima ba yayi masu sallama ya wuce gida, shi ka ɗai ya tafi, a nan Najma zata kwana.
zama su kayi nan parlor suna taya su mom aikin da suke, har suka kammala sannan suka wuce daki, wanka ko wace cikin su tayi da sallah magrib wacce ake kira, basu fita daga daki ba sai da suka yi harda sallar isha sannan suka fice daga dakin suka nufi parlor , yanzu ma mom da Aunty Rabi suka samu a parlorn, zama suka yi sai ga abie da ya abdallah sun shigo, nan suka zauna suna fira,
✨Lagos✨
Ammy da Fatima ne zaune a parlor bayan sunyi sallar magrib da isha suka dawo parlor suna duba kayayya kin da suka yi shopping, fatima tace " wlh kayan nan sunyi kyau sosai Ammy "
Ammy ta ce"ai kuwa sunyi kyau sosai"
Fatima tace" amma Ammy yaushe yaya yace zamu tafi abuja , amma dai sai cikin wannan week ɗin ko "
"to sai dai Idan ya dawo in tambaye shi, dan gsky ni bai faɗa min yaushe zaku tafi ba, duk da munyi magana yace next week amma ban ga yana wani shiri na alamar tafiyar ba "
"ok to shikenan Ammy" nan suka shiga duba kayan suna yaba kyan su,
Noraiz ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, amsa mashi sallamar su kayi, Ammy na ce wa "ina ka baro Yayan naka"
Amsa Noraiz yaba ma Ammy da
"tare muke dashi, yana compound yana amsa waya"
Ko rufe baki noraiz bai yiba shazim ya shigo, shima wurin su Ammy ya nufo, gaishe da Ammy yayi , ya nemi wuri kusa da Ammy kan sofa ya zauna, Ammy ce tace "ga abinci, kan dinning"
"to " ya bata amsa, dinning din suka nufa, suna kammala dinner din, fatima ta gyara wurin , su kuma kan sofa suka koma, Ammy na tambayar shazim yaushe zasu tafi abuja
"gaskiya ina tunanin sai upper week,zanje jos wani hospital ne suke son ganina next week"
"amma shazim naso ku tafi next week, jiya sai da Ibrahim ya kirani shi da innah nace masu kuna nan tafe next week, yan zu idan suka kira nace kun fasa gani za su yi kamar ni ke hana ku kuzo"
shazim yace "to ammy suyi haƙuri na dawo mana kiran emergency ne, patient sun fisu buƙatar gani na " "shikenan Allah ya kaimu upper week ɗin" da ameen suka amsa su duka, fira suka dan taba sannan kowa ya nufi ɗakin sa domin bacci......
✨katsina ✨
Kwance suke kan bed
ko waccen su sanye take da pajamas ɗinta , Aaimah da najma color ɗaya white sai Aairah dake da pink color , labari kawai suke a kan yanda walimar zata ka sance
Aairah tace "wallahi harna ƙosa naga gobe tayi"
Aaimah tace "faɗi kike anaji, ni baki san yan da nake jiba, Allah dai ya nuna mana goben lpy"
da ameen suka amsa, sun jima suna tattaunawa a kan yanda walimar zata kasance , har bacci yayi awon gaba da su....
WASHE GARI
Tun da safe suka tashi, shirye shirye kawai suke na walima, har mai makeup Mom ta ɗaukko, wacce zata yi masu kwaliyya, zuwa anjima, Idan lokacin walima yayi , su Mom kuwa suma tun da suka yi sallar asuba suke cikin kitchen ita da Aunty Rabi da baaba larai, suna ida shirya abubuwan da basu gama shiryawa ba jiya.
a chan compound kuwa yasha decoration, mai kyan gaske.
wurin karfe biyu na rana gidan ya fara cika da mutane, saboda bayan la'asar za'a gabatar da walimar , har gida ya abdallah ya je ya dauko Dadi, sai Aunty safiyya wace mus'af ya kawo,yan uwan abie ba wanda baizo ba da ƴaƴen su , sai wasu daga cikin ƙawayen Mom , hakama ƙawayen su Aairah na islamiya da boko duk sun zo, sai abokan abie dake nan katsina ba laifi suma sun zo , gida dai ya ciki Alhmdllh.....
✨Ammy ✨
Zaune take kan sallaya tana adu'a,
wayar ta dake bedside drawer ce ta fara ringing, miƙa hannun ta tayi ta ɗauki wayar haɗi da yin picking bakin ta ɗauke da sallama on the other hand cikin wayar muryar wata dattijuwar mace tace wa'alaikumu salam, ammy ta ce"ina wuni innah " amsa ma ammy tayi da "lafiya " ammy tace "innah yasu alhaji ahmad da su hajiya turai" da katar da ammy matar yi da faɗin "dakata aisha bawai na kira ki bane dan kiyi taman tambayoyi, na kira ne kan maganar da muka yi da ke, naga yau kusan wata kenan amma bangan su sunzo ba" ammy ta ce "dan Allah innah kiyi haƙuri, ko jiya da daddare munyi maganar da shazim akan zowan naso,to shine yake sanar man anyi mashi kiran gaggawa jos baza su samu zuwa ba sai sati na sama " katse ammy tayi da faɗin "dallah dakata man aisha kina nufin sai abun da shazim yace kenan, ko mi kike nufi"ammy ta ce "ba haka nake nufi ba innah" on the other hand "to mi kike nu, tun yau she muke magana sai dai kice man ranar kaza zasu zo amma kuma basu zo sai anyi magana ki kawo ma mutum wani uziri" shiru ammy tayi tana sauraran ta, da kaga fuskar ammy kasan cike take da damuwa " to bari kiji in gaya maki, baku isa ba daga ke har wannan mara kunyar, zumunci ne Allah ya riga da ya haɗa kuma dole ne ayi shi, bar ganin nayi shiru na barmaki yaran a hannun ki bawai hakan na nufin bazan iya ƙwatar su ba daga hannunki bane, saboda yara basu da wasu dangi a duniya bayan mu ɗinnan dai da kika gama rainawa kikasa ƴaƴanki suke ganin kamar bamu da amfani" sosai matar ta rufe ammy da masifa ammy na bata haƙuri tana gama faɗar abun da zata faɗa ko jiran mi ammy zata ce bata yiba ta kashe wayar, shiru ammy tayi ta ƙura ma wayar ido, chan kuma ta ɗaga hannun ta sama tana adu'a wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, gefen hijabin ta ta sa ta goge tana faɗin "Allah sarki abubakar, Allah ya jiƙan ka ya haskaka kabarin ka " na ce ameen ammy, tashi tayi daga kan sallayar ta linke ta ta saka cikin wardrobe da hijabin da tayi sallah fita tayi daga ɗakin, fatima ta samu zaune kan sofa tana ta latsa sabuwar laptop ɗinta wacce shazim ya saya mata, ɗago da kanta tayi tana faɗin"barka da fitowa ammy "da yawwa ammy ta amsa mata haɗi da neman wurin zama ta zauna, fuskar ta duk a ya mutse, lura da hakan fatima tayi yasa ta cewa"lafiya dai ammy na ganki cikin da muwa " ce mata ammy tayi ba komai mikika gani "nagan ki duk wani iri ne ammy " amsa ammy ta bata da gajiya ce, "to ammy da kin kwanta kin ɗanyi bacci kafin la'asar tayi "to"shine kawai a bunda ammy ta ce mata.....
✨KATSINA✨
Sai bayan da a ka gama sallar asr ɗakin su Aairah ciki yake da ƙawa yen su na boko da islamiya , mai makeup ta fara tsara ma Aairah makeup mai kyan gaske, wayar Aairah ce ta fara ringing cema Aaimah tayi ta duba mata taga wake kira , Amsa ta bata da alaramma ne ( malamin su na Islamiyya ) haɗi da yin picking, tayi sallama, ba'a jin me na cikin wayar yake ce wa, kawai dai naji Aaimah ta ce to shikenan malam, sannan tayi rejecting tana ce ma Aairah "ya ce sun ƙara so, suna waje"
Aairah tace " to pls ki fita keda aeesha ku shigo da su, ko ki faɗa ma abie sai ayi ma su iso "
Aaimah ta ce " bari dai na faɗa ma abie ɗin kawai, dan na san babu hanyar wuce wa"
Aairah ta ce "to shikenan faɗa ma abie ɗin kawai"
dialing number abie Aaimah tayi, picking abie yayi yana cewa "lafiya Aairah , kun gama shirya wa ne"
"Aaimah ce abie "
"Ok kun gama ne"
"A'a abie dama su alaramma ne suka iso"
Abie ya ce " to bari na sa abdallah ya shigo da su, amma fa kuyi sauri bana son lokaci ya ƙure"
"to abie insha Allah mun kusa"
"to shikenan"abie ya faɗa haɗi da yin rejecting din call din
Aairah ta ce " sis ya abie ɗin ya ce "
Aaimah ta ce"gashi chan zai sa ya abdallah ya shigo da su"
Aairah ta ce "to kira su ki ce ga ya abdallah nan fi towa"
kiran su Aaimah tayi ta faɗa masu, sannan ta ajiye wayar, ana kammala ma Aairah ita ma aka yi mata, sanan najma, sai friend din su Aeesha, sosai suka yi kyau kamar ka sace su ka gudu mu samman ma su Aairah , dan ba ƙara min kyau suka yi ba, shiryawa su kayi cikin wata atamfa super ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya amshi jikin su ba ƙara min kyau atamfar tayima fatar su ba, sannan su ka ɗaura farar alkyabba saman atamfar, faɗin kyan da alkyabbar tayi masu ɓata lokaci ne, kamar wasu ɗiyan sarakai, mom ce ta shigo ɗakin jikin ta sanye da wani haɗaɗɗen lace ɗinkin doguwar riga, wuyan ta da kunnan ta da hannu sanye da gold, mom ta ce "kai masha Allah kuce kun shirya, kai amma kunyi kyau sosai, kamar zan kai ku gidan miji"
dariya friend ɗin su da ke ɗakin suka yi suna ce wa"mom ai wannan ranar sai sun fi haka bada kala" su dai su Aaimah ban da murmushi babu abun da suke, "mom ta sake cewa "to kuzo ku fita ku ka ɗai ake jira " da to suka amsa mata, fice wa mom tayi daga ɗakin, suma tashi su kayi suda friend ɗin su suka fice chan compound, suna gaba friend ɗin nasu na baya, maƙil suka iske compoud ɗin da mutane, wurin da aka tana da domin su suka nufa suka zauna, ba ɓata lokaci aka shiga gaba tar da walima, alaramma yayi wa'azi, sannan su Aaimah suka yi karatu, sosai walimar tayi kyau ta kuma ba da ma'ana, su Aairah ba ƙara min burge mutane suka yi ba, sun kuwa sumu kyauta daga islamiyyar su, haka ma abie, mom, ya abdallah , dadi, granny, papi,aunty safiya, ƙannan abie duk sun basu kyauta, sosai suka tara kyaututtu ka daga wurare daban daban, su aunty rabi da aunty safiya suka yi rabon souvenirs, sai wurin karfe 6:40 ana shirin kiran sallar magrib sannan aka tashi, kowa ya tafi yana yaba hazaƙa irin ta su Aairah da kuma ganin nagartar islamiyar su .......