TANI DA MANU

Babi na ɗaya

by @saratalkasum88

_*🌻TANI DA MANU 🌻*_







_Labarin TANI DA MANU jikokin mai gari Hatsabiban yara masu bada nishad'i soyayya da kuma zallar dariya domin nishad'in ku masoyana_




LABARI DA TSARAWA



_*Sarat Alk'asum ( Maman Nusaiba ce)*_




🔔📚

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_




Marubuciyar



_*AMEER DA AMEERA*_


_*ALJANAR JARUMAI*_


_*HAFSAT*_


_*K'ADDARA CE*_


_Yau ma gani dauke da daddad'an labarin mai suna TANI DA MANU masoyan asali_



_*Ya Allah yadda na fara rubuta littafin nam lafiya Allah kasa na gama shi lafiya, ameen, ya Allah ka rabamu da sharrin mak'iya da mahassada ka kuma karemu da yiwa wani hassada ko kushe, Allah ka rabamu da munafiki koda yana tare da mu ka kuma ramu da yiwa wani munafurci, ya Allah ka rabamu da maciya amana ka kuma hanemu cin amana wani, ya Allah ka rabamu da bakin duniya, Allah ka bamu zaman lafiya da kowa ka shiga tsakanin mu da masu fuska biyu ameen yaAllah rabamu da fitina komin k'ank'antar ta , ya Allah ka daukaka alkalamin mu, ya Allah ya iya mana da iyawarka*_






بسم الله الرحمن الرحيم


_Da sunan Allah mai rahama mai rahama Mai jin k'ai_


1️⃣➡️2️⃣



Jahar Yobe k'aramar hukumar fika cikin garin goge, mai garin garin yana da Mata biyu Amina amma ana kiran ta da Iyatu, sai Salaha itama ana kiran ta da Ladiyo, da kuma Yara biyar.


Sa'id da Muktar da Ya'u.

Sai mata Hansatu da Hadiza.

Iyatu tana da yara uku maza biyu mace d'aya,

Sa'id shine Babban d'an su a gidan sai Hadiza ita ke biya mishi sai Muktar.


Ladiyo na da Yara biyu, Ya'u da Hansatu.

Tinda suka taso Yaran kansu a hade yake saboda Mai Gari baya bari koda sa'insa suyi a tsakanin su ,idan kazo gidan bazaka gane wannan d'an waye ba sai in har su suka fad'a maka, Sa'id ya taso da son karantu kuma dake shine Babba a gidan duk ya saka su a boko da Islamiya, hakan yayi wa Mai Gari dad'i matuk'a, suna gama karantun su a k'auyen Sa'id yace shifa zai koma birni da karatu, Mai Gari badan yaso ba yayi magana daga gwamnati aka dauke shi zuwa garin Yobe, anan yaci gaba da karatu da Muktar shima ya gama nashi Sa'id yazo ya dauke shi ya maida shi cen birni, haka shima Ya'u daya gama karantunsa ya dawo wajan su Sa'id.


Haka sukaci gaba da rayuwa da anyi hutu suke dawowa gida idan kuma lokacin damuna ne su dawo suyi noma, duk da Mai Gari yana ce musu ba sai sunzo ba amma da anyi hutu sai sunzo sun taimakawa Mahaifin nasu.

Sa'id yaga Y'ar Gidan Liman yace yana so babu muso aka saka musu biki ranar Iyatu kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha.

Mai Gari yace to su Muktar suma su kawo wadda suke so ko a musu auren zuminci.

Ya'u yace shifa ba zai yarda a mishi auren gida ba yana da Budurwa a birni, shima Muktar yace haka, Mai Gari ya bugawa Abokin sa na cen yace yaje ya nemawa d'iyan sa aure a gidan Y'an Matan da suke so.

Haka kuwa akayi Abokin Mai Gari yaje ya nema musu auren babu wata matsala, sai aka saka bikin nasu duka lokaci guda.

Lokacin biki na yi aka sha biki aka kai Amare gidajen su.

Haka sukaci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya gidan su d'aya kowa da part d'in sa.


Matar Sa'id ta fara samun ciki ai kuwa sunsha murna nan da nan aka shiga bata kulawa, lokacin haihuwa nayi ta haifo d'an ta Namiji ranar suna Yaro yaci sunan Mai Gari Ibrahim, lokacin da Ibrahim ya isa yaye Iyatu taso a basu Ibrahim amma sai Uwar Yaron tace su bari inta haifi wani zata basu, hakan yasa suka hak'ura da Ibrahim.

Bayan wasu shekaru ko waccen su ta haihu Matar Sa'id Mai Suna Rahama tana da yara uku maza biyu mace d'aya Ibrahim da Khalifa sai autar su Amina saboda sunan Iyatu gare ta ai kuwa tace sai an bata ita, ba muso Rahama ta bawa Iyatu Amina nan take kiran ta da TANI .


Matar Muktar Mai Suna Dausiya ita kuma Yaran ta biyu mace guda Namiji guda, Usman da kuma K'auseer. Tinda aka haifi Usman Mai gari yace tinda sunan Baban shi ne a basu, ba dan taso ba ta basu Usman, tinda aka kaishi k'auye suke kiran shi da MANU.


Matar Ya'u Mai suna Ikilima itama yaran ta hud'u, Aminu da Khadija da Hassana da Usaina.


Haka suke rayuwar su cike da farin ciki, TANI DA MANU kuwa sun zama ciwon ido a k'auyen baki d'aya basa jin magana kamar d'iyan Allah bani haihuwa, kuma Mai Gari ne ya daure musu gindi bana son lefin su, MANU shekarar shi 16 ita kuma TANI shekarar ta 11.


_*WANNAN KENAN*_

************************


Mai Gari ne ya fito daga d'akin shi bakin shi da wani zabgegen asuwaki yana ta goge bakin sa ,wannan rawani shima anyi shi a gaban goshi ga kujejiyar rigar shi da take jan k'asa idan yana tafiya sai yayi ta share hanya da ita.

Hanyar fita ya nufa saida yazo bakin k'ofar gida yace" Iyatu wannan d'umaman yaji daddawa da magi, kuma kiyi sauri a kawo min shi nan bakin k'ofar gida nida su Liman, wai Iyatu baki jina ne? To na dai fit...


Bai k'arasa ba yaji an bangaje shi kafin ya d'ago aka bi ta kan bayan shi ji kake kass ihu Mai Gari ya saki , bai kuma dawowa ba aka bi ta kan k'afar shi, juyowa yayi yaga TANI tayo sufa tana zuwa wajan shi ta tuje mishi rawanin shi tayi gaba a guje ta shige inda du MANU suka shiga.


Mai Gari yayi rashe-rashe sai nishi yake saboda bayan shi na mishi ciwo face majina yayi ya janyo rawanin sa ya goge hancin shi yace" Wato Yaran nan baku da mutumci wallahi yanzu ni kuka yiwa wulak'anci haka? To ba komai bari dai na tashi kar su kuma dawowa.


Zama yayi yana wash k'afa ta bayana, jin k'arar gudu ana Y'ar rige-rigen fitowa daga d'aki Mai Gari ya kwalalo ido waje, ganin zasu dawo kanshi bai san lokacin daya yi sufa ba ya mike a guje ya fad'a d'akin shi.


MANU ya shiga gaba TANI a gefen shi Bintalo a baya ita da Furera da goga.

MANU yace" Kun shirya?

Suka ce eh mun shirya muje zuwa.

MANU yace" D'aya biyu uku,nan suka fita a guje suna ta falfala guda duk wanda suka gamu da shi a hanya to bangaje shi zasuyi suyi gaba babu ruwan su da su tsaya.


Liman ne ya shayo kwanar zuwa gidan Mai Gari, Su TANI da suka tafo kamar wasu dawaki in suna tseran gudu suna haduwa da Liman suka ingiza shi yayi baya suka bi ta kanshi suka wuce.


Da k'yar Liman ya tashi yana fad'in" Wannan Yara kun ishi mutanen garin nan, ba dama mutum yayi magana Mai Gari ya rufeka da masifa baya son lefin ku.

Kamar dan kaciya Liman ya ringa tafiya har ya k'araso k'ofar Mai Gari.

Mamaki ne ya kama shi ganin Mai Gari bai fito ba, sallama yayi gidan Iyatu ce ta fito tana fad'in " waye yake sallama?

Liman daya rike k'ugunshi saboda zafin da yake ji yace" Nine Iyatu nine Mai Gari fa?

Iyatu tayi dariya ta rangad'a gud'a tace" Ai in gaya maka Man Liman Mai Gari futsararrun Yaran nan suka yi Y'ar tsere a kanshi, ni wallahi ko a jikina tinda shi ya daure musu gindi suke abinda sukeso a garin nan.

Jinjina kai Liman yayi yace" Kai Iyatu kema fa baki da mutumci wallahi to meye na yin gud'ar kuma?

Iyatu ta turo dan kwalin ta gaban goshi ta harari Liman tace" Ai indai akan Wannan Yaran ne duk abinda suka yiwa Mai Gari sai dai na mishi dariya, tinda shi yake daure musu gindi kaga kuwa babu abinda ya shafeni, ke Ladiyo zo kiji wani renin wayo.


Fitowa Ladiyo tayi tana fad'in" Yaya Iyatu lafiya kike kwada min kira haka?

Iyatu tace" Wai kinji Liman dan nayi dariya yace bani da mutumci ai duk abinda su MANU suka yiwa Mai Gari shi ya saya da kud'in sa.

Ladiyo tace" Kwarai da gaske ai ina jinsa nak'i fitowa dan haka nama koma ciki na huta kar su dawo su mana wani muguntar.


Mai Gari ne ya fito yana gyara babbar rigar shi rike bayan shi yayi yace " Munafukai marassa mutumci wato dama kuna jina ba wanda yazo ganin me ya sameni, to shikenan to Alkur'an yau baza kuci tsiran D'an Lami ba, kuma babu ruwan ku da Yaran nan mugaye kawai, ke kuma Iyatu kije ki dafa min tuwon nan Malam Liman muje waje.

Dariya Iyatu tayi tace" Aikin banza kaji da shi d'umame yanzu zan maka,kuma tsire dole muci a gidan nan, to ina ruwan mu da wasu Yara.


Fita Mai Gari yayi yana surfa fad'a wai sun takurawa TANI DA MANU jikokin shi Yaran albarka.

************************


Su MANU ba su tsaya ko ina ba sai a jikin wata babbar bishiya ta mangwaro , Bintalo tace" Kai ku kalla nayi kyau kuwa?

Kallon ta sukayi tasa rigar atamfa kala daban zanin ta kuma na Aisha Buhari dan kwali kuma irin mai sulb'in nan, wannan fuskar tasha kwalliya bakin nan yasha janbaki ja ga wata Gira data zabga kamar kura.


Dariya MANU yayi yace" Alkur'an kin had'u Bintalo ai yau idan muka je makaranta sai kinyi saurayi.

Wani farrr Bintalo tayi da ido jin ance tayi kyau.


TANI ta kalli MANU kamar zatayi kuka tace" MANU na nima nayi kyau ko?

MANU yace" To TANI bari na duba na gani.

Kallon ta ya soma yi daga k'asa har sama tasha kwalliya tayi girar ta har ta had'e daga gaba, a kumatunta tayi d'igo-d'igo ko wani kunci yafi goma, dan k'aramin bakin ta yasha bakin kwalli sai maik'o yake, ta saka kwalli a idon ta har bakin idonta bak'in kwallin.

Jikin ta kuma riga kala da ban ta atamfa Sket ne shima na atamfa kala da ban, takalmin ta k'afa ciki ta saka wata doguwar safa har gwiwa, sosai kwalliyar ta yiwa farar fatar ta kyau, tayi tsukiya da bayafin ta a k'ugun ta, kasancewar ta doguwar fara sai tayi mugun kyau sosai.


MANU yace" Hahaha sai kinyi TANI na ai kinfi kowa kyau bari muga Furera ma.


Tsalle TANI tayi tace" Yeee sai ni TANI ta MANU, rawa ta taka tana karkad'a k'ugu.


Furera ya soma k'arewa da kallo, itama kamar su TANI yadda sukayi ado itama haka tayi fuskar ta sai walk'iya take saboda man data shafa, da kayanta dana Bintalo iri d'aya ne, ita Bintalo tasa riga Furera tasa zane, tukun kalar daya ita Furera tasa riga Bintalo ta saka zane, abun dariya inka gansu kamar wani yan Lela.


Goga yace" Wannan wanka yayi Abokai ku tashi muje kar Malamin mu yazo kunsan wannan Bayeraben ba mutumci bane da shi.


MANU yace" To ya muma wankan namu yayi bana so a rena mu fa.

Shima da hular shi zanna sai rigar shi ta atamfa iri d'aya da sket d'in TANI, wandon kuma irin yadin fulani Mai zanen nan rakatau, takalmin shi irin na TANI k'afa ciki shima da safar k'afa har gwiwa.



Shi kam Goga yasha doguwar hular nan kamar marok'i da rigar shi babba tayi a saka biyun shi amma haka yasa yake ta yawo a cikin ta, takalmin shi irin na sojojin nan wanda yake har gwiwa, wiyan shi kuma ya saka wata sark'a fara idan yana tafiya sai take bada sauti kakacau-kakacau, abin dai sai wanda ya gani.


Kamaiya sukayi dukkan su suka nufi Makarantar dake cen gaba da su kad'an.

A hanya suka ga wasu sun koma gefe suna futsari, MANU ya dawo baya yace" Kuzo muga d'uwawu bak'ak'e kamar gawayi.

Dariya Bintalo tayi tace" Kut wannan mutane ka gansu wasu sunk'uma-sunk'uma to yassen sunyi ukun mu.

TANI tace" Hmm wannan mutane kamar fa irin samudawan nan da Iyatu ke bamu labarin su kin tuna, ganin sunyi gaba yasa ta bisu da gudu.


Mutanen suna futsari sukaji ana fad'in' Yeee munga d'uwawuka bak'ak'e yeee kuzo kowa ya kalla.

Da sauri suka tashi shi d'ayan ma a jikin shi ya k'arasa futsarin.

MANU ya tsare su yace" Uban waye ya baku izinin yi mana futsari a gona? Ko kunsan gonar waye nan da kuka shiga.


Kallon su suka yi d'ayan yace" Oh dama ai munji labarin ku hatsabiban yara kawai, to munyi.

TANI ta yage baki ta soma kuka k'arya tana fad'in" MANU kana gani suke zagin mu ko bazaka rama mana ba , nidai wallahi yau in muka je dandali ba zamuyi rawa da kai ba.


Da sauri MANU yace" Tab ai yanzu zan rama miki kinji" Yana fad'in haka suka ringa watsa musu k'asa suna musu ihu marayi.

A guje suka bar wajan sai karo suke suna fad'uwa amma saboda mugun ta irin ta su basu kyale su ba saida suka raka su har bakin fanfon garin tukun suka dawo.


Suna zuwa Makarantar basu kula kowa ba , shi kanshi Malamin tsoron su TANI yake dan ya lura basu da mutumci shiyasa ko sunyi lat baya kula su, idan kuwa yace zaiyi magana to fa sai sun mishi wani muguntar.

************************

Da dare suka shirya zuwa dandali duk sunyi kwalliya ansha damara a k'ugu, sun gama shiryawa suka je wajan Mai Gari suka ce ya basu hamsin zasu tafi dandali.

Mai Gari yana washe baki yace" A'a wannan kyau haka bari na duba sai da ya face majina ji kake fiii ya fesawa Bintalo, ai kuwa suka kama mata dariya, hade rai tayi tace ai zata rama itama.


Hamsin d'in ya basu kowa N 10 TANI ce mai N 20 haka yake musu dama kullum.

Fita sukayi suna murna sun samu kud'in shan rake.


Suna zuwa dandali ya cika taf sai su ake jira makid'in ganga ne yazo shine aka zagaye shi yan mata nata cashewa Samari suna musu liki.

Da sauri suka k'araso cikin filin, marokin yace" Hee a dakata ga tawagar TANI DA MANU sun k'araso dama su kad'ai ne basu taka rawa ba.

Su TANI kuwa sai wani hura hanci take jin ana wasasu ita da K'awayen nata.


MANU ya shigo yana k'ara maido hular shi gaban goshi yayi doro ya soma taku d'ai-d'ai yana zagaye Mai gangan, Yan Matan suka kwashi ihu suna fad'in ,sai MANU na TANI sai kayi.


Mai ganga ya gyara zaman d'an hela yace" Hee a dakata da magana yanzu TANI DA MANU zasu zo suyi mana rawa anan muna so wannan tawagar su bada kala a nan.

Wajan ne ya dauki tafi ram-ram.


Kid'an aka soma yi TANI ce ta fara shigowa, mai Kid'an ya soma kad'a mata.

Ga TANI ga MANU jikokin mai gari, wannan kid'an naku da bane ga TANI ga MANU.

Idan Mai kidan yace" Ga TANI Sai TANI ta rike k'ugu da hannu d'aya d'ayan hannun ta kama kwankwason ta sai tayi takun rawa ta bada kas-kas har sai ta kusa zuwa k'asa tukun ta mike tayi gaba taci gaba da rawar ta.

MANU yazo yana mata like yan biyar- biyar wajan ne ya kwashi ihu ana k'ara zuga su...




Share fisabilillahi masoya🙏🏻




_Taku har kallum Maman Nusaiba ce alƙalami yafi takobi⚔️_