chapter 7&8
_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_Wattpad✅_*
***
*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444
*Sirrinmu➡️*
ki kasance me tsaftace jikinki da kuma gidanki,yin hakan zai sa ki ƙara samun muhalli awajen me gida.
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
➡️7 & 8
…………………sosai gabana ya faɗi,don ganin Balaraba don nasan wannan zuwan na su ba zai haifarmin daɗa me ido ba,sai ma na fara jin tsoro akan abinda na yarda na aikata don sam ban so na biyo Yaya Zubar ba,amman yafi ƙarfin wannan awaje na yana iya sadaukar da farin cikinsa sabodani,duk masifar matarsa idan yaga damar abu bata isa ta hanashi basai dai gani da hange shiyasa take kirana da mayya saboda wai na lashe mata kuruwar miji.
Ban kula ba ashe tare suke da Hajiya sai da suka ƙaraso gab damu idanuwana ƙuri akansu,jikina har tsuma yake tun dama ni ina da tsoro sosai ga kuma muguwar shagwaɓar dana taso da ita awajen mahaifana duka biyu,don kaf gidanmu kowa yasan nice ta gaban goshin Abba shiyasa ma ake ce min ƴar lelen Abba ko kuma Rabin Abba.kamar daga sama naji Hajiya na ce wa"iko sai rabbani,idan baka mutu ba za kayi kallo? yanzu tsabar maita nan ɗin ma sai da kika biyo mu? yarinya ta koma kamar ƙashi duk ta dalilinki? kuruwarta kur de wallahi,duk maitarku sai da kuci kanku daga ke har uwar taki mayya masu cinye ƴaƴan mutane,shiyasa ma duk ƴaƴanta take cinye su aciki kece de da kika gado ta da maitar tsiya kika fito duniya saboda ki tayata lashe kurwar mutane".........
Kafin ta kai aya Balaraba ta karɓe da cewa"kuma wallahi ƴata tafi ƙarfinki mayya,kawai idan kina tutiya kin cinye kuruwar mijina to ni wallahi nafi ƙarfinki,kuma waye ya gayyato kixo nan wajen? tun da de babu dangin iyaa ballantana name dattin hula me kalle ƴaƴan mutane akan titi tunda uwarki ta hanashi ya cike da ta huɗu,wai ku shuwa ko? to wallahi mu baki isa ki gama damu ba,banza me bin mazan mutane karuwa".
kuka na fashe dashi kawai,zuciyata sai tafasa take tamkar xata fito waje tsabillar baƙin ciki,wai ni meye na yiwa waɗannan mutanen har haka ne? ni ba daɗin mijin nake ji ba? ballantana suce wai na gama dashi? inbanda baƙar wahalar dana ke sha uban me na tsinta agidansa? sai baƙin ciki da kuma nadamar aurensa marar misaltuwa,kullum sai nayi kuka sosai akan wannan hatsarin dana ke ciki gaba damisa baya zaki karasa inda zaka sanya ƙwaƙwalwarka kaji daɗi.
Alokacin yaya zubair ya ƙaraso ya sameni sai kuka nake idanuwana sunyi jazur,ya ƙaraso yana kallonsu hajiya ya rasa me xai ce musu ya buɗe bakinsa zaiyi magana sai ya jiyo muryar hajiya tana ce wa"to sallamamme,wai ni anya kuwa ba Zulaiha da Rabi na haifawa Zubairu ba? sai rawar ƙafa kake ka ƙaraso kana huci don ka dakemu don an daku ƴar gwal ɗinka ko?, to bari kaji wallahi tallahi idan bakayi wasa ba kan wannan yarinyar sai na sassaɓa maka."
caraɓ ta amshe da cewa"hajiya wai miyasa kike jin tsoronsa ne? ki fito ki faɗa masa mana,idan sonta yake ƙaninsa ya saka sai ya aure ta ko?, yanzu tsabad kai baƙin azzalumine shine kaje ka ɗakkota alhali ni ka kulleni aɗaki?, saboda kana sauri ku tafi hotel wajen yawon.........."
A'i bata ƙarasa ba taji wani wahalallan mari,wanda mai shi yake jin tamkar zai tsaga kumatunta saboda ya huce daga azabar raɗaɗin da ta saka azuciyar wanda ta ƙuntatawa,ta jiyo zata sake magana ya ƙara mata wani ya fara nuna ta hannunsa yana kakkarwa,hajiya tayo kansa da zagi da masifa amman bai saurare taba,sai daya gama zazzaga mata masifarsa sannan ya fara faɗa mata wasu maganganu waɗanda suka sanyata sumewa na wucin gadi ya ce"Balaraba idan kin gama faɗamin maganganun da kike so daga yau kada ki koma min gida ki tafi gidanku sai na neme ki"?.
ba ita ba hatta ni sai dana razana,ita kuwa gigicewa tayu tana ihu tana cewa"Zubairu ni kake faɗawa haka saboda wata? wannan tsinanniyar yarinyar mayya?, to wallahi zaka san kayi da ƴa don wallahi sai dai ka aikomin da takarda don wallahi ba zan cigaba da zama da kai kana wulaƙantani akan wata ba".
Hajiya ta rasa me zata ce,saboda tsabar takaicin Zubairu idan tace za tayi magana wallahi xata iya tsine masa ma,shiyasa ta kasa cewa komi saboda takaicinsa dake nuƙurƙusar zuciyarta shiyasa ta kasa cewa uffan,ita kuwa balaraba gani tayi ai hajiya tama raina mata hankali inbanda haka me ya hanata yin magana?.
saboda haka fuuu ta yi hanyar fita zata fita,sai alokacin hajiya ta dawo hayyacinta ta cs"tsaya Balaraba ai babu inda zakije indai ba wannan tsinanniyar ce zata tafi ba,indai na isa dake balaraba ki dawo zansan abinda zanyi".
ta wurga mata wani kallon banza sannan ta ce"ai alokacin da yake shirin cimin mutunci bakice ƙala ba,gaba ɗaya ma goyon baya naga kina shirin basa saboda haka sai ki zauna kici gaba da bashi goyon baya saboda haka ni na tafi gidanmu idan ya shirya sakina ma ya aikomin da takadda ta don wallahi bazan iya zama dashi ba".
tana faɗar hakan ta wuce,da sauri hajiya ta bita ta riƙe hannunta ta janyota ta dawo da ita sannan ta ce"zauna ba inda zaki idan kuma tare zai koramu sai yayi abinda yake so tunda na haifawa mayu shi".
Bai ce komi ba ya zauna yana ayyana yadda zai yi mata idan suka koma gida,don babu shakka ana sallamar khadija ghana zai koma inda yake cinikayyarsa kuma ko faɗa mata ba zaiyi ba zaiyi tafiyarsa har sai ta ganshi don idan bata bar masa gidan ba to shi zai bar mata don ya gaji da zama da ita sam ta fice masa aransa.
Haka muka zauna shiru har likita ya fito ya ce"ina mahaifin khadija"?.
ya ce"gani Allah de yasa jikin yayi sauƙi yanzu"?.
Likitan yayi murmushi ba tare daya ce komi ba ya wuce zuwa office ɗinsa.
suna shiga ya ce"an samu nasarar dawo da numashinta dai dai,kuma ansanya mata jinin yanzu saboda haka zuwa jibi ma zamu iya sallamarku,sai dai don Allah ku dinga kula da wannan yarinyar ayadda na kula sam ba a kula da ita,a matsayinta na me limoniya bai dace a barta babu kayan sanyi ba,musamman alokacin sanyi sannan sai kun haƙura da fanka ko kuma AC saboda idan ba haka ba yarinyarku baza ta samu lafiya ba,idan ma baza ku iya kula da ita ba ku samu wacce kuka san zata iya kula da ita ɗari bisa ɗari".
shiru yayi yana wani tunani ya ce"na gode likita za ayi yadda kace".
yana faɗar hakan ya fito daga office ɗin,yana ta kallon Rabiatu don yanke wata shawara akanta wacce yasan zai iya janyo mata matsala,amman zaiyi addu,ah kuma zai gwada sa'arsa.
*****
wayarsa da yake kulli yaumin cikin fare ya tsshi yi,ya tashi da ɗan sanɗa sanɗa sai jikinsa ya bashi kamar bata kusa dashi,ya juya ahankali sai kuwa yaga bata kuda dashi ɗin,da sauri ya kalli hanyar banɗaki yajo bai jiyo ƙarar ruwa ba sai hankalinsa ya ɗan tashi ya duba ko ina bai ganta ba?,ransa yayi mugun ɓaci sai ya kira number ɗinta,bugu na biyu na ɗaga ya rufeni da faɗa yana ce wa",,gidan uban wa kika je da daddaren nan?".
tsoro ya kamani sosai na ce"muna tare da yaya zubai........"
tun kafin in ƙarasa ya ce",ikon Allah yaushe hakan ta fara kasancewa banda masaniya............."?
*** *** ***
Aamiru yaja bakinsa yasa masa linzami,tun daga nan bai ƙara cewa uffan ba amman hankalinsa na kan amininsa wanda yake matuƙar tausayi ako yaushe tun akan wani shinge daya ratsa acan baya wanda ya haddasa komi.
......Autar momma tayi packing ɗin motarta daga can,hankalinta da nutsuwarta duk suna kan bro ɗinta wanda yanzu taga motarsa ta fita daga layin.
A hankali ta fito daga motar,tana takowa cikin takunta me matuƙar tafiya da mutum,samarin kuwa suka tsuro mata ido suna kallon halittar Allah kana ganinta ma ba sai an faɗa maka ba kaga kyakkyawa kuma haɗaɗɗiyar me kuɗi.
tana zuwa ta tsaya ta fara magana cikin yauƙi wanda ya kasance tamkar ɗabi'arta ta buɗe ɗan ƙaramin bakinta wanda samarin suka fi sanyawa ido.
"don Allah ƴan samari ina da tambaya"?.
da saurinsu suka ce "muna jinki ƴar kyakkyawar budurwa?".
"dama inason nasan me ya kawo wancan saurayin wajen nan,wanda suka wuce yanzu da wata farar mota"?.
samarin sukayi ƙuri suna kallonta,tamkar de suna karantar abinda ke fuskarta ne,sai da ta ƙara maimata abinda ta faɗa ɗazun sannan sukace.
"eh dama cewa yayi don Allah mu bashi address ɗin gidansu Ahmad,sai muka bashi daga nan kuma ya bamu check ɗin kuɗi ya tafi".caraf ɗaya daga cikinsu ya ce"suka bani de zaku ce ko suka bawa".
wani ƙayataccen murmushi tayi sannan ta ce"ba komi ni zan baku check ɗin yanzu kowa ya samu,amman aikin da nake son kuyi min shine duk ranar da suka ƙara dawowa ga number na ku kirani sai ku faɗamin".
Sosai matasan nan suka dinga murna,bayan ta basu check ɗin ta wuce gida cikin nishaɗi afili ta ce"uhm bro kenan daga rana me kama ta yau duk motsinka yana tafin hannuna na,don baxan yarda abinda ya faru da ya faru da kai yanxu ba,wancan ma don ba nida wayo ne shiyasa akaci galaba akanka".
tana isowa gida ta wuce sashen Momma,ta same ta da bayi zube afalo suna mata tausa taji wani iri aranta don da tana da hali da tuni ta daɗe da ƴantar da waɗan nan bayin don ba ƙaramar wahala suke sha ba,wai ahaka ma Momma ce ba tada wannan halin na wulaƙanta bayi,ba kamar Mama fulani ba wacce ta kasance uwar gida awajen me martaba,sannan sai matarsa ta biyu Fulani suraa itama ba tada mutunci,abinda de ta sani shine ta wulaƙanta talaka,duk tsabar haushinsu da take ji shiyasa bata ko zuwa ɓangarensu inde ba wani abu ne ya faru ba.
Murmushin Momma ne ya ƙaru ganin ƴarta autarta,tana son ƴaƴanta kaf ɗinsu guda huɗu da ta mallaka,Aliyu shine na farko sai Mardiyya sai kuma Zulaihat sai autarta me suna Asiya,Mardiyya da Xulaiha duk an musu aure yanzu mardiyya tana Dubai acan take aurr mijinta bature ne to acan yake da zama,sai kuma Zulaiha dake garin Kano tana auren wani mashahurin ɗan kasuwa.
"auta ina kika je haka ne?".
Ƴarfar da hannunta tayi alamun gajiya sannan ta ce"Momma na je shan iska ne".
Sallamar bayinta tayi sannan ta ce"naga kamar aƙwai magana a bakinki Auta".?
sunkuyar da kanta tayi tana son faɗawa mahaifiyarta komi amman kuma tana shayin faɗa mata ɗin,saboda bata taɓa yin wani abu ba tare da shawarar mahaifiyarta ba,duk abinda ya shafi rayuwarta ita kaɗai take saninsa don babu wani mahaluƙin daya san sirrinta kamar momma,don ita ba tada ma aminiya balle ma a shige mata kamar yadda aka yiwa yayanta aka cutar dashi bai shirya ba.
ganin momma ta tsare ta da ido sai ta ce"am dama momma wani abu nake son faɗa miki,amman ban san yadda zaki amshi batun ba"?.
riƙo hannun autarta tayi sannan ta ce"uhum ina jinki faɗamin shi auta ko menene zan ɗauka tunda na rasa iyaye".
tausayinta ne ya kama Asiya saboda haka ta ce"Momma bro fa yana son sake jefa kansa cikin masifar daya fita daga ciki wasu shekaru da suka shuɗe"
a matuƙar razane momma ta miƙe jikinta har rawa ya ke yana tsimar zabari ko kuma makaɗin miya, saboda tsabar tashin hankalin da take ciki ta fara magana cikin fushi...............Soon➡️✍🏽
ga link na facala game nema,bana son maza a grp da ƴan iska ehe😎😂.
***
DFeZycAMeQZ09jYzYRWCX0
#YARIMA
#RABIATU
#AHMAD
#BALARABA
#ZUBAIR
MRS GREEN CE.
SHARE
COMMENTS.
TALLAH TALLAH TALLAH
MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.
Abubuwan da ke cikin littafin kaloli dabam dabam na👇🏾
Haɗin Dilka
Haɗin man gyaran gashi
Haɗin sabulun gyaran jiki
Haɗin ƙugu(hips)
Haɗin gyaran (Breast)
Haɗin maganin infection
Haɗin furen zogale
Haɗin tsumin tabaje
Haɗin Kaza
Haɗin tantabara
Haɗin ƙamshin jiki
Haɗin ƙamshin baki
Ingantattun maganin mata
Bonus
Sirrin riɗi
Sirrin magarya
Sirri magaruwa
Sirrinmu(Addu'oi)
Za ku iya biyan kuɗin littafin akan farashinsa mai sauƙi #1,500 kacal amma ga garaɓasa ga
Mutum 30 da suka fara biya na farko, zasu biya 1000 kacal, ku yi hanzari ku yi payment akan lokaci don neman ƙarin bayani *** SIRRIN MOWA NA MANYAN MATA NE, MATAN SO BA MUNA MATA BA.