FACALA

chapter 9&10

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_Wattpad✅_*

***


*_𝘼rewabooks✅_*

 https://arewabooks.com/user/rabiattu0444


*Sirrinmu➡️*

Ƴar uwa ki kasance mai yawan yiwa mijinki da ƴaƴanki addu'ah da al'ummar musulmi baki ɗaya,don ita addu'ah makamar mumuni ce.


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️9 & 10

………………bakin Momma na rawa ta ce"wai Hafsat me kike nufi ne? bazan gane lauje acikin naɗi ba,nafi son afito min muraran afaɗamin duk abinda ke faruwa ba wai ki zauna kina ɓoye min a matsayina na mahaifiyarki ba".

 

  ta ce"Momma nasan kin gane fa? mamaki ne ya hanaki gasgata hakan,ko kuma so kike sai Bro yazo ya fuskantad dake komi,bakya buƙatar wannan a tsakaninku abinda yafi shine ki sanya masa ido sosai,sannan kuma idan da hali ki tayasa da addu'ah sosai don wallahi ɗan ƙwali yana shirin jawo hula idan ba a ɗauki mataki da wuri ba".


 Momma ta zauna tana ajiyar zuciya,wasu zafafan hawaye suka ƙwaronyo mata,ta share hawayen na ta tana ce wa"ya Allah ga bawanka nan,wanda bai san komi ba sai kyautatawa iyayensa da kuma na sama dashi,ga taimakon marayuwa da jin ƙan talakawa,ya Allah ka kyautata masa kamar yadda ya ke taimaka mana,ya Allah ka kare min shi ka kare gabansa da bayansa ".

Murmushi auta tayi sannan ta ce"oh Momma irin waɗannan addu'o'i haka? sai kace shi kaɗai ne ɗanki? gaskiya Momma duk kin fi son waccen cikulallen mutumin me zubin samudawa".

wani duka Momma ta kai mata ta ce"eh nafi son shi ɗin,kuma ai ko wani irjn zubi ne dashi a'i ya fiki kyau da komi".

dariya tayi ta ce"ato momma kin taɓa ganin inda namiji yafi mace kyau? a'i kinsan ma ba zai taɓa yiyuwa ba,kuma ma ai naga dake nake kama"?.

murmusawa kawai tayi ba tare da ta ƙara cewa komi ba,Auta ta tashi ta wuce ɗakinta don tasan wannan shirun da tayi ba ƙara magana za tayi ba,don wani miskilancin ma ita bro ɗinta ya gado ba wani ba.


  tana shiga ɗakinta ta cire dress ɗinta za ta shiga wanka,sai taga kiran wata ƙawarta wacce suke cewa Chuchu,tayi kamar kar ta ɗaga sai kuma ta daure ta ɗaga ɗin don tasan ta da shegwn surutu yanzu haka gulma zata kawo mata,ita kuma babu abinda ta tsana irin a kawo mata gulmar wani,kai baki ɗaya ma ta tsani me ɗabi'ar gulma don magulmaci wutarsa daban take.


 A'i kuwa tana ɗagawa ta ce"gimbiya wani labari nazo miki dashi da ɗumi ɗuminsa".


da sauri ta ce"kinga Chuchu ina da abin yi fa? bath zan shiga kika kirawo ni".

da sauri don kada ta katse ta ta ce"gimbiya don Allah ki saurare ni,wallahi wannan labarin da zan baki yana da kyau ki tsaya kiji saboda bana son daga baya Allah ya tambaye ni,wallahi akan bro ɗinki ne ashe ya dawo ma ni ban sani ba,ɗazu naje wajen birthday paty na abokina shine na gansa a club,nayi mamakin ganinsa wallahi don naga shi baya irin wannan rayuwar,duk dama mutum yana canjawa infact ma shi daya dawo daga turai kinga ai ba abin mamaki............."


 "dalla malama tsaya,bana son sakalci da rashin sanin abinda zaki dinga faɗa mana,ta yaya zakice wai kinga bro ɗina a club? aka gaya miki shima irinki ne me yawon bin abokai da sakalci"?.

acan ɓangaren ta ce"ok baki yarda ba kenan? ai daman nasan ba zaki yarda ba,amman na faɗa miki ne don kusan matakin da zaku ɗauka,saboda wallahi ayanayin dana gansa ya ban tausayi sosai bayan buguwar da yayi da wata yarinya na gansa fa?".


  Sosai gabanta ya faɗi ta riƙe ƙirjinta dake wani irin luguden kai kawo ta fara magana bakinta yana karkarwa "Chuchu ta yaya kike tsammanin zan yarda,ta yaya xakice yayana fasiƙi ne? me shan giya me saɓawa mahakiccinsa? no no no wallahi ƙarya kike Chuchu".


 chuchu tayi wani murmushin takaici ta ce"eh ni nasan ina da gulma amman fa duk gulmar da zanyi bana faɗar abu idan har ba dai dai bane,ina faɗarsa yadda ya faru saboda haka ki buɗe whatsapp ɗinku in turo miki hotonsa sai ki yarda".


 hannunta na rawa ta buɗe whatsapp ɗin,gabanta na faɗuwa hannayenta suna salƙewa tamkar suna taɓa wuƙa.


 Mummunan gamon da tayi ya sanya ta kusan sandarewa awajen,ta shuɗe na wucin gadi awajen tana shesheƙar kuka ta ce afili"haba bro,me ka nema ka rasa aduniyar nan? idan auren ka keso ba sai ka faɗa ayi maka ba? amman wannan wacce irin rayuwa kake so ka jefa kanka? ka kuma jefa mu? innalillahi wa inna ilaihi raji'un,la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin,wallahi sai na kawo ƙarshen wannan al'amarin a satin nan zansa aɗaura maka aure kowa ya huta".


  ajje wayar tayi ta shiga banɗaki,tasha kukanta sosai kana ganin idonta kasan tasha kuka har ta godewa Allah ta sanya doguwar rigar abaya me ɗan sauƙin nauyi,ta yana veils ɗin kayan ko mai bata shafa ba ta sanya takalminta halp shoes wanda irin na ƴan gidan sarauta,don duk mafi yawancin takalmanta irinsu ne don arayuwarta tana masifar son irin kayan sarauta.

xama tayi afalonta,tana tunanin wanda zata haɗa baki dashi a yiwa bro ɗinta aure ko a huta.

Can ta tashi da sauri ta ce"yes!.gun gwagwala zanje".


 sashen kakar tasu ta nufa,tana cike da nishaɗi don tasan halin gwaggwala da son ayi maganar aure,caraf zata karɓe tace a haɗaku da wance da wane.

tuno wata shawarar yasa ta wuce part ɗinsu Amira ƙanwar ya Aamiru.

tana zuwa ta samu mamansu a babban falo,bayinta na gefen ta suna mata tausa ta gaisheta cikin fara'a ta ce"oh Auta me mukayi ƙwana biyu ba a shigo mana"?.

auta da baby ɓoye ɓoye ta ce"faɗa mukayi da Amira".

murmushi tayi ta ce"yo ai kun saba dama in dai kune,me shiga tsakaninku ai sai yaji kunya".

ta faɗi hakan tana murmushi,ni kuma na shige ɓangaren Amira wacce ba don tana son haɗa baki da ita ba,da babu abinda zai kawo ta saboda sunyi faɗa.


  Amira ƴa ce ga ƙanin mr martaba,tun suna yara tare muka taso har makaranta duk tare sukayi,idan sukayi faɗa sai ka ɗauka ba zasu tama shiryawa ba,sai kuma daga bisani kaga sun shirya ɗin.

tun daga nesa ta hango Amira tana gaban mudubi tana cancaɗa ado,cikin riga da siket na wani cancaɗeɗen leshi,wanda ya amsa sunansa kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba kasan anyi ɓarin dukiya awajen.


 tana ganinta tayi saurin ce wa"ƴar halak,wallahi dama kina raina yanzu zanje sashenku muyi wata magana".

Autar momma ta ce"ok nima magana nazo muyi".

on serious Amira ta juyo har da zama a bakin tamfatsetsen gadonta ta ce"ina jin ki aminiya".

Autar Momma ta ce"naƙi ɗin ke ki fara faɗamin maganar sannan nima in faɗa miki".

amira ta riƙo hannuwan Autar Momma ta damƙa acikin tsakiyar hannunta ta ce"don Allah hafsy ki taimakamin,wallahi wani abu ne yake damuna amman na rasa wanda zan faɗawa,ina kuma jin kunyar su Anti khalisat ba zan iya faɗa musu ba,ke aminiyata ce Hafsa ban saba da faɗawa kowa sirri na ba sai ke,shiyasa nake yanzu ma in faɗa miki wani babban sirrin zuciyata wanda na daɗe da binnesa sai dai ba zan iya binnewa ni kaɗai ba,dole ne in samu wanda zamu to no tare".


kallon ƙasa tayi mata sannan ta ce"kinga ni fa na gaji da wannan maganganun, ni ki faɗamun meye ke going? sai musan ta inda zamu ɓullowa abin".


a hankali ta tashi tsaye ta juya mata baya sannan ta ce"GALADIMA na ke so"...............


da mugun sauri a ɗago tana kallon aminiyar ta.................






***       ***       ***

......bakina yana rawa na ce"a ,a,a, me kake nufi Ahmad? don Allah ka dinga yimin kyakkyawan zato mana? me zai shiga tsakanina da yayanka?".

sautin muryarsa taji yana ce wa"dalla malama rufemin baki,yau kika saba shagala? yau ne abin ya fara faruwa ko kuwa an daɗe ana yi? ki faɗamin gaskiya ko kuma wallahi in tona kundin sirrin da kika rufe agajimare yana yawo asama ba tare da kowa  yasan abinda ya faru ba".

 

  saurin kashe wayar nayi don bansan me zan ce masa ba,kamar yaya zubair yasan abinda ke faruwa,ya matso kusa dani ya ce"Rabiatu lafiya de ko"?.go ge ƴar ƙwalla tayi na ce"babu komi".

bai sake cewa komi ba har yaje ya siyo waɗansu magunguna ya bawa su Hajiya,waɗanda suke ta hararata tamkar idanuwansu zasu faɗo ƙasa.

ya ce"tashi in kaiki gida dare yayi sosai,nima sai in ƙwana da safe in dawo".

da sauri Hajiya ta ce"baza ka kaita ba Xubairu,wai kai wani irin mara hankali ne? kai ko kunyar kanka ma bakaji? xaka raka wannan akuyar saken daga nan aje a ƙulla maka sharrin da baka san kayi ba? to wallahi idan ba so kake raina yayi mummunan ɓaci ba ka koma ka zauna,tunda ba ƴar uwarka bace ba kuma muharramarka ba".

zai yi magana na tashi da sauri na ce"yaya ka zauna kawai bari in tafi".

babu yadda ya iya,amman fa hankalinsa da nutsuwarsa duk suna kai na har sai dana fita daga asibitin baki ɗaya sannan ya saukar da ajiyar zuciya.

  

  sautin tsakin Balaraba yaji,ta ce"wallahi aƙwai lauje acikin naɗi acikin al'amuranka da wannan tsinanniyar yarinyar,ina ganinka fa kana kallonta har tabar asibitin nan,daman ance duk inda wannan yarinyar ta zauna to sai babbar masifa ta faru,yanzu ma gashi ta faru dani don kuwa mijina yana son matar ƙaninsa".

 kanta yayo zai mari bakin maganar,don wallahi gab yake daya ji mata ciwo don shi arayuwarsa ya tsani mutum mara kunya ko kaɗan,sannan wannan kalmar da take faɗa ba fa ƙaramar kalma ce da za a barta haka ba,idan ta faɗa awani wajen anƙi yarda to tabbas awani wajen yarda za ayi.

Hajiya ta ɓalla masa wani banzan kallo ta ce"au dukanta za kayi saboda ta faɗi gaskiya? ai nima ta rigani a fili ne na rigata a ɓoye,don kuwa wannan halin naka zai kai ka inda bakayi zato ba,in banda san zuciya me Balaraba ta nema ta rasa ajikinta,yarinya ƴar duma duma ba waccan daba cinya ba sharaɓa ba,sai shegen kyau dake ruɗarku kamar ƴar aljanu".

saurin kallon Hajiyarsa yayi sannan ya ce"haba Hajiya wai mi yasa kike biyewa zancan Balaraba?duk abinda ta faɗa miki sai ki hau ki zauna? kuma idan matata tayi min mummunan zato ai ke bai kamata kiyi min ba Hajiya,ita fa uwa itace mai kare ɗanta aduk sanda wata guguwa ta faɗi masa,ba wai ita ke gayyato guguwar zuwa wajen ɗanta ba."

Hajiya ta hillatu ta kuma ƙulu ta ce"to Zubairu idan kuma kai da kanka ka gayyato guguwar fa? ai kaga ba nida hujjar kare ka ko? sai dai in faɗi gaskiyar lamari,don bazan yarda wani ɗana ya kaini wuta ba,alhali gaskiyar a bayya ne take,kuma kafi kowa sanin hukuncin me ɓoye gaskiya komi ɗacinta".


 girgiza kansa kawai yayi,don tun ba yau ba yasan wacece Hajiya,macece me mugun baki da zance idan kuma sirri kayi da ita tofa ka shiga ukunka ko kai waye sai ta faɗa,bata kunyar koma waye idan gaskiya tazo sai ta faɗe ta komi ɗacinta awajen wanda aka ɓatawa.



tafiya nake cikin sanɗa sanɗa har na iso bakin ƙaton titin,tamkar wacce ke tsoron wani abu na daɗe a titin ban samu mota ba,can sai ga wasu samari sun taho suna tafiya suna tangaɗi tamkar waɗanda ke rawa bisa iska,suyi nan suyi nan tsoro ya kamani na fara tafiya da sauri sauri,suma sai naga sun ƙarawa tangal tangal ɗinsu gudu gabana yana ta faɗuwa tuni fuskata ta fara jiƙewa da ruwan hawayen tausayin kaina....................Soo➡️✍🏽

ga link na facala game nema,bana son maza a grp da ƴan iska ehe😎😂.

***

/DFeZycAMeQZ09jYzYRWCX0


#YARIMA

#RABIATU

#AHMAD

#BALARABA

#ZUBAIR


MRS GREEN CE.


SHARE

COMMENTS.


TALLAH TALLAH TALLAH


MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.


Abubuwan da ke cikin littafin kaloli dabam dabam na👇🏾


Haɗin Dilka

Haɗin man gyaran gashi

Haɗin sabulun gyaran jiki

Haɗin ƙugu(hips)

Haɗin gyaran (Breast)

Haɗin maganin infection

Haɗin furen zogale

Haɗin tsumin tabaje

Haɗin Kaza 

Haɗin tantabara

Haɗin ƙamshin jiki

Haɗin ƙamshin baki

Ingantattun maganin mata

 

     Bonus

Sirrin riɗi

Sirrin magarya

Sirri magaruwa

Sirrinmu(Addu'oi)


Za ku iya biyan kuɗin littafin akan farashinsa mai sauƙi #1,500 kacal amma ga garaɓasa ga

Mutum 30 da suka fara biya na farko, zasu biya 1000 kacal, ku yi hanzari ku yi payment akan lokaci don neman ƙarin bayani *** SIRRIN MOWA NA MANYAN MATA NE, MATAN SO BA MUNA MATA BA.