chapter 11&12
_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_Wattpad✅_*
***
*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444
*Sirrinmu➡️*
*Yadda ake maganin ƙurajen fuska.*
Asamu garin alim da ma'ul wardi cokali biyu a haɗa arinƙa gogawa a fuska abarshi ya kai minti 15.
ko kuma a samu zuma da lemon tsami a dinga shafawa idan mutum zan ƙwanta bacci idan ya tashi ya wanke.
➡️11 & 12
…………………sosai nake sauri amman kuma suna son cimmani,ko dana fara gudu suma sai suka fara gudun ina cikin gudunne wata mota ta taho da gudun gaske.....nan da nan tayi awon gaba dani ban ƙara sanin inda kai na yake ba sai a asibiti.
a hankali na fara buɗe idona abisa silin ɗin ɗakin,kai na yayi min nauyi sosai na buɗesu tar tar da sauri na tashi zaune don na fahimci a asibiti nake,ruwan da aka sanyamin na fizgesa ina ce wa"don Allah ku faɗamin a ina nake? me ya faru dani? don Allah ku mayar danu gida wallahi ina cikin matsala babba idan ban koma gida ba".
sosai yake kallon yarinyar,yana jin wani yarrrr ajikinsa kallonta yake kamar ya taɓa ganinta awani waje amman kuma ya kasa tuna a ina ya santa?ganin abinda take yi yasa ya fita da sauri ya kira likita,tare suka shigo ya gyaramin ruwan wajen sai jini ya ke,ya ce"kiyi haƙuri ki bari ya ƙare saura kaɗan kinji,sannan idan ruwan ya gama ƙarewa sai ki koma gida ko"?.
Har lokacin kuka nake na ce"wallahi ni sai na tafi,babu fa wanda yasan inda nake kuma nasan hankula duk sun tashi".
na faɗu hakan amman a iya baki kawai don ba har zuci ba,don nasan mutum ɗaya agidan idan yaga bai ganni ba hankalinsa zai tashi shine Yaya Zubair,amman banda shi ko mijin dana ke aure ba zai wanu damu ba,ƙarshe ma sai dai zargi ne zai maye gurbin damuwar dana ke ciki.
sai alokacin na ɗaga idanuna ina kallon mutumin,shima kallona yake ya ce"to kiyi haƙuri ki bada wayarki xa a kira gidan sai a sanar musu suzo kinji".
Na ɗaga kai na kawai ba tare dana ce komi ba.
na miƙa masa wayar idanuwana suna zubar da hawaye.
kiran farko da aka ya bi ,sai da tayi ringing har ta gaji sannan aka ɗaga ina jiyo muryar Ahmad ko sallamar bai amsa masa ba ya ce"oh da ƙaton gardi ma take tare? to tunda ta zaɓe ka akaina ka faɗa mata daga yawon da taje kada ta dawo min gida".
Mtsss
ya yi tsaki tare da ajje wayar,cikin mutuwar jiki ya kalle ni ya ce"ki dubomin number mahaifiyarki in kirata don tasan halin da ake ciki".
amsa nayi hannunawa suna kakkarwa tamkar makaɗin miya,duk abinda Ahmad ya faɗa naji amman babu yadda zanyi tunda ya yanke hukunci da kansa.
Kiran farko ta ɗaga,na ce"Ammi kixo ina asibiti".sai na fashe da kuka sosai ta tsorata da jin halin da nake ciki ta ce"ok to gani nan zuwa awani asibitin ne"?.
na faɗa mata asibitin.
Alhaji Bawa ya ce"Zulaiha lafiya kuwa"?.
shiru tayi hankalinta da nutsuwarta suna kan gudan jininta tilo wato Rabiatul adawiyya.
ganin bata ce komi ba yasa ya ɗauki wayarta ya duba kiran da aka yi mata.
Kallonta yayi yana me ajje wayar ya ce"Zulaiha ki dinga ƙwantar da hankalinki fa,musamman akan Rabiatu don naga kin damu sosai akan aurenta,duk da nima na damu amman bamu da yadda za muyi sai dai haƙuri,sannan ni abinda Ahmad ya yi min ba zan iya magana akan komi ba,sannan bayan haka ma mijinta ne yana da damar hukuntata indai ba akan abinda ya zarce na hankali ba,saboda haka don Allah ki sanyawa zuciyarki salama".
Kuka ta fashe dashi ta ce"Alhaji kai da kanka kake faɗar hakan? ko de an sake kane? amman fisabilillahi kowa yasan Ahmad na cutar da Rabiatu,yaron nan fa ko biki akeyi ko suna acikin ƴan uwa baya barinta zuwa,yanzu rabona da inga Rabiatu yau wata ɗaya cur fa kenan? ina har tayi nisan da za a nemi rabani da ita? gaskiya ni ba a yimin adalci wallahi,yanzu me yasan abinda ke faruwa da ita sai Allah,tun da gashi tana asibiti ban san me ke faruwa da ita ba"?.
da sauri ya ce"subhanalillah ba tada lafiya ne ko me"?.
ta ce"ni de sai munje za mugani tunda da kanta ta kirani,kuma ta sanar dani asibitin da take".
Be yi wata wata ba ya sanya babbar alkyabbarsa irin ta manyan malaman nan sannan ya ce"bari in fito da motata sai mu wuce,ai zancan bana zama bane".
suna jalbab ɗinta kawai ta saka har da niƙab,don yana daga cikin al'adarta indai zata fita to da hijab da kuma niƙab take fita,shahararriyar malamar addini ce wacce take da lasisi a hisba,shugabar ƙaramar hukumar ce baki ɗaya, ko ba komi Ammi macece ms tsananin kyau shiyasa ko da yaushe fuskarta da niƙab.
Mama uwar gida ce ta fara ganinsu sun fito,ta kafe su da mayun idanuwanta wutar kishi na cin zuciyarta,yadda kasan ta shaƙesu haka take ji,tun ba yau ba idan ta kalli Zulaiha sai taga duk tafi dacewa da mijin na su,ita farar fata ce sol sol shi kuma baƙi ne cikakken bahaushe ita kuma cikakkiyar shuwa arab,wacce kallom farko zaka tabbatar da hakan saboda kyaun fuska da kuma na jiki,ga gashin nan yala yala tamkar ita ta dasa abinta cif cif gwanin ban sha'awa.
har suka iso gabanta bata sani ba,sai turaren Zulaiha ne ya sanar da ita sun iso gab da ita koma sun wuce,turaren na ta ba wai me masifar ƙamshi bane,a a turare ne irin na su na shuwa arab wanda ake turara kaya dashi,sai kuma taje gab da kai zakaji hakan ko kuma wanda ya santa dashi ne zai iya jiyowa.
da sauri Mama Uwar gida ta ce"a'a Alhaji ina zuwa kuma? ka manta fa yau masu kawo lefen Zahra za suzo".
bai tsaya da tafiyar da yake ba ya ce"eh inda zamuje yafi kawo lefen ne,Mamana ce babu lafiya za muje asibiti duba ta".
wani banzan kallo da harara ta bankawa Zulaiha,ita kuwa bata ma san tana yi ba don bata juyo ba,burinta kawai taje wajen ruhinta jinin jikinta wato ƴarta.
bata samu damar ƙara yin magana ba saboda ya fita daga gidan baki ɗaya.
Mama Zaliha na jinta daga falonta tana mata ƴar dariya,tare da yiwa Rabiatu fatan samun lafiya don haifar Rabiatu ne kawai bata yi ba amman itace uwar ɗakinta,don komi da ita take shawara bata taɓa ɗaukarta amatsayin ƴar kishiya ba,abinda ta ɗauka shine ƴaƴan mijinta ƴaƴanta ne don ko ba komi aure ya bata su,ko tana so ko bata so kuma daɗa da dukiya ba a musu mugunta,bakasan wanda zaiji ƙanƙa ba.
daman ranar unguwa zata fita itama,bayan ta gama shirinta ta kalli ƴammatan ɗakinta ta ce"to ni zan tafi gidab yaya Jummai,ku tabbatar kun gama girkin dare da wuri kuma sannan bana son ko nan da soro ɗayanku yaje".
Dukkansu suka amsa mata da to umma adawo lafiya.ta amsa musu ta fito tsakar gida har lokacin Mama Uwar gida na zaune tana hararar tsakar gida,ita kuwa murmushi tayi ta ce"to Yaya ni zan wuce gidan yaya jummai,saboda kinga daga gidan yayata ne za a kawo lefen nan gwara inje in zauna zuwa dare sai na dawo".
aciki ciki ta amsa mata,ita kuwa tayi wucewarta ko ƙara waigenta bata yi ba,in banda ƙaddara me zai sa ɗan yayarta ya auri ƴarta ai sai dole,har azuciyarta bata san wannan auren don yaranta duk ba suda tarbiyya,mazan ne kawai masu ɗan sauƙin kai amman suma uwarsu kawai suka sani ko wani abin arziƙinne ya samu basa bi takan kowa sai abinda ta ɗora su akai.
tafiyar da zata kai ta unguwar malali,da nisa wacce ke kaduna su kuma suna a Rigasa ne,saboda haka sanda taje har ƴan kawo lefen sun fito da aƙwatuna guda 12 reras dasu gwanin ban sha'awa.bata ji baƙin ciki ko ɗaya ba sai ma murna da tayi don a wannan lokacin ɗanka ya wuce siraɗin lefe ai ka ji daɗi.
tana shiga gidan ta samu yayarta a tafkeken falonta,da yake mijinta me kuɗi ne sosai itama kuma ta tara abin duniya babu laifi.
kana ganin fuskarta kasan tana cikin matsala sosai,ta ƙaraso kusa da yayarta ta ce"yaya Jummai lafiya kuwa? Na ganki kamar kina cikin matsala? A'i ni aganina kamata yayu kiyi murna ba wai ɓacin rai ba".
kallon ƙanwarta tayi ta ce"Zaliha wallahi sam bana son wannan auren,don anfi ƙarfina ne shiyasa nayi shiru amman wai har ni yaron nan zai dinga gaba dani don na ce kada ya auri wannan yarinyar? ni wallahi abin ma mamaki yake bani,yaron da da yake son wannan yarinyar kirkin aminiyar Rabiatu wato Salimat,amman lokaci ɗaya ya burkice wai shi sai wannan lukutar yarinyar me kama da samudawa? Allah ƴar uwa abinnan yana damuna,don kowacce uwa tana son ɗanta ko ƴarta ya samu abokin rayuwa nagari."
shiru tayi sannan ta ce"haka ne yaya,amman babu yadda zamuyi fa bamu isa mu sauya abinda Allah ya tsara ba,abinda zamuyi yanzu shi ne mu maida komi ba komi ba,mu fauwalawa Allah dukkanin lamuran mi miƙa masa komi sannan mu taya Sagir da Addu'ah Allah ya basu zaman lafiya".
yayar ta amsa da "amin Xaliha shiyasa akaf cikin ƙanne na nake jinki acikin zuciyata,don ke ɗin haske ce acikin al'umma baki ɗaya,kina da tsarkakkiyar zuciya kin san abinda ki ke yi,kuma aduk abinda za kiyi kina sanya shi ne cikin mizani bisa hukuncin ubangiji idan akabi shawararki sai aga komi ya tafi dai dai".
taguminta ta cire ta ce"wallahi yaya ni babban abinda ke damuna yanzu bai wuce matsalar da Adawiyya take ciki ba,kinga na farko shima mijin bata jin daɗinsa,sannan Faccalarta wacce itace uwa uba wajen haɗa dukkanin wani tashin hankali,sai kuma surukarta wadda ko don muna muƙwaftaka da juna ta dinga raga mata,amman wallahi idan kinji zagin da take aikowa da Zulaiha maman Adawiyya sai kinsha mamaki wallahi".
Yaya jummai ta ce"ikom Allah,au haryanzu Ramatu bata san annabi ya faku ba? bata dena muzgunawa wannan yarinyar ba? to ta barta da ƙaddarar da tasa me ta mana? kuma naga duk akan wa ƙaddarar ta faɗa mata? idan ba akan Ahmad ba? amman sun bi sun tsani yarinya sun dame ta akan mi? ni wallahi ma ahalin yanzu babu wacce nake gani da lefi sai Zulaiha,banda sakarya ce ita ta yaya za a dinga musgunawa ƴarki ki zauna ki sanya ido? yo haƙuri hauka ne? yarinya duk ta fita a hayyacinta? duk sanda kika ganta a zabure take? dalili dami duk akan abinda ya sameta wanda ya zama ƙaddara ce za a dinga hillatar yarinya?".
Zaliha ta ce"me kike son Zulaiha ta ce ya ya? kin san fa halin Alhaji? ba zai taɓa yarda ba ko? Yanzu sai kiji ya ce mata ai za a ɓata musu amintakarsu ta tun suna ƙanana? kinga kuwa ai dole abi abin da addu'ah."
haka suka yi ta hirar su ita da yayarta,sai dare ta dawo gida don yau ita ce da megidan baki ɗaya wato Alhaji Bawa.
*****
ina ganin Ammi na fashe da kuka na faɗa jikinta,sosai nake kukan tamkar bazan dena ba Ammi ma da ba tada dauriyar ganin hawaye na,ai sai ta fashe da kuka tana ce wa"luf luf luf Adawiyya,ana asif".
aduk sanda take lallashina abinda take faɗamin kenan,don da larabci muka fiya magana ni da ita.
Abbana yana tsaye yana kallonmu,sosai yake jin babu daɗi agame da abinda ke bibiyar rayuwar ƴarsa wacce yafi so aduniyarsa,bai san me yasa ba duk yawan tarin ƴaƴansa,baya jin kowa kamar yadda yake jin Adawiyya baya son ɓacin ranta ko kaɗan,yanzu ma haka dole ce yasa yake yin shiru,don da babansu Ahmad dashi aminan juna ne,don tun suna yara suke tare kuma da suka tashi aure ma rana ɗaya aka ɗaura musu,uwar gidajensu suma aminai ne wato mama uwar gida da kuma mahaifiyarsu Ahmad,kamar yadda matayen na su ke komi tare haka suma suke yi,babu me jin kansu baya son yanzu kuma aji kansu akan autayyar yaran na su.
sai da mukayi kuka me isarmu sannan Abbana ya ƙaraso ya ce"yi shiru mamana ki faɗamin abinda ke faruwa ko?".
ina ganinsa na ce"Abiey".
da sauri ya ƙaraso kusa dani,na sanya hannuwana acikin lallausan hannunsa ina kuka na ce"Abiey wai akan ƴar yaya Zubair ba tada lafiya na tafi bada jini,sannan shi kuma ya Ahmad yana barci na tafi shine dana je aka ɗibi jinin adaren na taho gida don gudun kada ya yi faɗa,to shine fa wannan ya bugeni a mota ya kawoni asibiti,to kafin inkira Ammi shi na fara kira,shi ne shi ne ya ce wai kada in dawo masa gidansa".
sai na fashe da kuka me dukan zuciyar me sauraro.
Sosai kowannensu ya girgiza da al'amarin Ammi ta rungumeni tsam ajikinta ta ce",yi haƙuri goge hawayen ki wallahi ba zaki koma gidansa ba...........Soon➡️
SHARE FISABILILLAH🙏🏻
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
MRS GREEN CE✍🏽