Doctor Shazim season two

Episode 4

by @kainaat1515

_👨‍⚕️ DOCTOR SHAZIM 👨‍⚕_


     _*Daga alƙalamin*_

      _*kainaat... ✍*_


@Kainaat1733 Wattpad 


  _~Season two~_ 


_Ep 4_


_💋💋A heart touching love story💋💋_


................amsa mata yayi da lafiya lau, kin tsahi lafaya" 

"lafiya lau Alhmdllh " ta bashi amsa, sa'ada ce tace " noraiz ko kai ma na haɗa maka coffee ɗin ne " ɗaga mata kai yayi yana faɗin "eh" 

"to shikenan, anan zaka zauna na haɗa maka ko dinning zan kai maka" 

"A'a bari kawai na zauna " ya faɗa yana nufar ɗaya daga cikin chairs ɗin dake kusa da Aairah, zama yayi yana latsa wayar shi yana jiran sa'ada ta haɗa mashi.


bayan kamar minti uku ta kammala haɗa mashi acikin mug har gaban table ɗin da suke ta ƙara so ta ajiye mashi tana faɗin " gashinan asha lafiya, idan kayi santi ga Aairah sai tayi maka waigi karka faɗi" murmushi Aairah tayi tana sadda kai ƙasa saboda kallon da noraiz ɗin ya bita yana faɗin " ke kinyarda zanyi santin" murmushi kawai ta sakeyi ba tare da tace mashi komai ba, ajiye wayar shi yayi ya fara shan coffee ɗin, Aairah sai juya spoon ɗin da take shan coffee ɗin take a cikin cup, tunda ya zuba mata ido ta kasa cigaba da shan coffee ɗin, a ranata faɗi take

" shi wannan kallon baya mashi wuya ne, ya tasa mutun gaba da kallo har sai yaga muninshi" maganar shi ce ta dawo da ita cikin hayyacin ta

"lafiya kika daina shan naki?" 

"ai kai ka hanani" ta faɗa a zuciyar ta a zahiri kuma tace 

"bakomai"

"kodai na tashi na takura maki" girgiza mashi kai tayi tana faɗin " da gaske nake Allah ba komai " 

"indai bakomai da gaske to kicigab da sha mana " da to ta amsa tana kai spoon ɗin da ta ɗebo coffeen bakin ta, ɗauke kanshi yayi daga gareta ya maida kan wayar shi dan ya lura kallon da yake mata ne yasa duk ta takura takasa shan nata, da yagaji da latsar wayar ajiye ta yayi yana tambayar sa'ada yaushe zasu fara zuwa school 

"next week, zaka riƙa kai mu ne " hararar wasa yayi mata yana faɗin

"Allah ya sawaƙa, kawai sai na bar aikin da nake saboda ku ko"

"kai ya noor miye a ciki dan ka kai mu" Fatima ta faɗa 

"mi zai hana kuce ya shazim ya riƙa ajiye ku tunda hanyar shi ce ta zuwa hospital " tushe baki sa'ada tayi tana ɗan zaro ido tace " dan Allah ka rufa mana asiri, ina mu ina cema ya shazim ya kaimu makaranta in ba so kake ranmu ya ɓaci ba"

"ok shi da yake hanyar shi baza ku iya cewa ya ajiye ku ba saini da kuka raina ko" 

"haba ya noor wane mu da mu raina ka, tai mako dai zaka yi " 

"ilya ya riƙa kai ku, ai dai shikenan ko" ɓata fuska sa'ada tayi tana faɗin " yanzu dai bazaka kai mu ba kenan"

"zan dai iya kai su Aairah amma ku dai sai dai ilya"

"lallai ma ya noraiz, ai indai zaka kai su to ƙafar mu ƙafarka "

"Allah ya kiyaye ku sacce man tayar mota, ai nauyi zaku yi mata"

"shikenan ya tunda haka kace suma su Aairah ba su so zamuje tare duka ilyan ya kaimu" 

"taya zaki ari bakinta kici mata albasa, ki bari ta faɗi da bakin ta " ya faɗa yana kallon Aairah yace " wai da gaske baku so ke da ƴar uwar ki" ƙefta mata ido sa'ada tayi alamar tace eh, murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba 

"ka gani ko bata so in dai ba tare da mu ba " 

"ba wani nan ai ina kallon ki sa'ada ina kallon abun da kika yi mata" 

"ni ba abun da nayi mata, dan Allah ki faɗi daga bakin ki yaji" 

a hankali Aairah tace " nafiso in zaka kaimu ka kaimu tare da su" ihu sa'ada tayi tana faɗin" to kaji dai daga bakinta " 

"duk da haka banyar da ba ke kika yi mata alama da tace haka"

"wallahi ba abun da nayi mata " 

"to shikenan naji" ya faɗa, fira suka shiga yi cikin nisha ɗin, Aairah na sauraron su sai murmushi take noraiz ne ke ɗan sakata a firar tasu a haka Aaimah ta shigo ta same su ta tashi daga bacci taga ɗakin ba kowa shine ta nufo kitchen dan ta san bazai wuce suna nan ba,zama tayi itama sa'ada ta haɗa mata coffee suna sha suna fira har suka kammala girkin da suke tas suka jera dishes ɗin kan dinning sannan suka nufi ɗakin su dan yin wanka, noraiz ma part ɗin shi ya wuce bayan ya yi na shi breakfast ɗin saboda sauri yake ya tafi wurin aiki. 


wanka su kayi su duka suka shirya cikin kaya marasa nauyi, bayan sun gama shiryawa ficewa su kayi daga bedroom ɗin zuwa parlor dan yin breakfast,tun daga nesa su Aairah ke ƙare mata kallo zaune take kan dinning riga da wando ne na bacci a jikinta sun matseta sosai kamar zasu fasa fatar jikinta, suna ƙara sowa wurin Ammy na fitowa daga bedroom ɗin ta ita ma dinning ɗin ta nufo,ƙara sawa su kayi dinning ɗin su ka gashe da Ammy, fuskar ra ɗauke da fara'a ta amsa masu tana faɗin " fatana kun tashi lafiya, ya gajiyar hanya " 

"Alhmdllh " su ka amsa mata haɗi da samun wurin zama su ka zauna, tunda suka zo wurin feenah ke binsu da kallon rainin wayau,abun mamaki ya ba su a zuciyar su suna faɗin ita kuma wannan haka take, jinjina kai su kayi a hankali Aairah ta kalleta tace "antashi lafiya " Aaimah ma gaishe da ita tayi amma ko kallon arziƙi babu wacce tayi mawa a cikin su, ran fatima da sa'ada in ya kai dubu sai da ya ɓaci, tsaki sa'ada taja cikin gun gunai tace" aikin bazan dana wofi" 

" kinci gidan ku sa'ada"Ammy ta faɗa dan sarai taga sa'ada lokacin da take ma feenah tsaki da maganar da tayi, ɗan turo baki tayi tana faɗin " Ammy mi nayi?"

"ban sani ba "Ammyn ta faɗa tana kallon feenah tace " bakiji su Aairah na gaishe dake ba" duk da Ammy ta san sarai taji dan ta lura feenah batayi murna da zuwan su Aaimah gidan ba 

ɗan sosa kai tayi tace"naji Ammy"

"ok amswa ce baki iyawa " 

ba tare da ta kalle su ba tace lafiya, sannan ta kalli Ammy tace "ina kwana Ammy ba mu gaisa ba " jinjina kai Aaimah tayi a zuciyar ta tana " an zo wurin, idan taƙamar ki wulaƙanci ni zan nuna maki nafiki iya rashin mutunci mu dai je zuwa zaki san mu kika amsa ma gaisuwa a haka" 

da lafiya lau Ammy ta amsa tana faɗin" mi ya hanaki fitowa jiya yin dinner, kuma har aika sa'ada nayi kika ce gaki nan zuwa amma ban ganki ba har na shige ɗaki" hararar sa'ada tayi wacce ke neman wurin zama zata zauna,ɗaure fuska sa'ada tayi, jinjina kai feenah tayi tana faɗin 

"waya nake da momy shiyyasa ban fito ba,lokacin da nagama na fito duk kun shige ɗaki" Ammy duk ta lura da harar da feenah tayi ma sa'ada da ɗaure fuskan da sa'ada tayi, kwata kwata ta rasa gane mike damun sa'ada da feenah sai kace ƴaƴan kishiya basa jituwa kamar ba yaya da ƙanwa ba 

"to yayi, idan kin gama breakfast ki cire wannan kayan dake jikin ki" Ammy ta faɗa tana kai cup ɗin tea bakin ta, da to feenah ta amsa, tashi fatima tayi tana faɗin " Ammy zan kai ma ya dr breakfast ɗinshi "

" to shikenan sai kin dawo" da to fatima ta amsa haɗi da miƙewa ta nufi kitchen, da kallo feenah ta bita tana ya tsine fuska. 


Fitowa fatima tayi hannuta ɗauke da round tray ta nufi sama part ɗin shazim, da sallama a bakinta ta tura ƙofar parlorn, zaune yake kan sofa ya ƙurama laptop ɗinshi da yake aiki ido, ɗago da kanshi yayi yana kallonta fuskar shi ɗauke da murmushi, ɗan turo baki tayi yayin da take nufar round table ɗin dake parlorn ta ajiye trayn dake hannunta, ɗagowa tayi suka haɗa ido sake turo mashi baki tayi tana wani fari da ido, ɗan riƙe haɓa yayi yace " ni koh" ɗaga mashi kai tayi alamar eh tana faɗin" nayi sallama shine ko ka amsa man sai wani murmushi kake man "

" sorry, wa'alaikumussalam, shikenan" ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, da sauri tasa hannu ta rufe fuskar ta tana ɗaga mashi kai alamar eh, 

" to shikenan, kin tashi kafiya " 

" lafiya lau, ina kwana " 

" lafiya lau, how was za night kinyi mafarki na kuwa" ɗaga mashi kai tayi alamar eh, murmushi yayi yana faɗin to ki bani labari naji "

" ka bari sai anjima zan faɗa maka yanzu dai ka ajiye wannan akin ka zo muci abinci"

"shikenan " ya faɗa yana ture laptop ɗinshi dake gaban shi, ƙasa ya sauko kan carpet ganin haka ne yasa ta ɗauko trayn ta ajiye kan carpet ɗin kusa da shi, zama tayi suna fuskantar juna, serving ɗin su ta shiga shi kuma yana binta da ido duk wani motsin ta a kan idon shi har ta gama serving ɗin,spoon ko wannan su ya ɗauka yana bama ɗan uwan sa suna fira sama sama. 


_nace Allah dai ya bar ƙauna Autan Ammy_ 


Acan parlor kuwa suna gama breakfast kan sofa suka koma feenah kam ɗakinta ta nufa dan korata Ammy tayi akan taje ta canza kayan jikinta,suna nan zaune noraiz ya sauko da shigar shi ta zuwa aiki suits ne a jikin shi black color sai red ɗin riga daga ciki ba ƙaramin kyau kayan su ka yi mashi ba hannun shi riƙe da briefcase sai baza ƙamashi yake, sa'ada ce tace " kai ya noraiz irin wannan wanka haka kamar zaka je gasra kyau" fari yayi mata da idanu ya juya ya sake juyawa yace " to ya kika gani " 

"wow gaskiya ba ƙaramin kyau kayan nan su ka yi maka ba, dan Allah mu ɗan yi selfie mana" ta faɗa tana nufar shi da wayarta a hannu, sai da tayi masu kusan kala uku tukun su Aairah na kallon su ba ƙaramin burgesu suka yi ba 

"thanks you sister " ya faɗa yana wani fari da ido kamar mace 

"Allah ya shiryeka mai babban suna " Ammy ta faɗa, Ameen yace yana ƙara sowa wurinta yace " ina kwana Ammy nah" 

"lafiya lau, harka fito"

"eh, zan wuce " ya faɗa 

"to a dawo lafiya Allah ya bada sa'a " da ameen ya amsa yana nufar hanyar fucewa, ɗan ɗaga murya sa'ada tayi tace " adwo lafiya, kayi mana tsaraba idan zaka dawo " 

"to sannu uwar ƴan kwaɗayi" ya faɗa yana ficewa daga parlorn zuwa compound, motar shi daya sa aka wanke mashi ya shiga, key yayi mata ya nufi gate, buɗe mashi gate mai gadi yayi yana mashi a dawo lafiya, yana fita daga gidan direct gidan malam ya nufa, horn yayi a bakin gate mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga da motar, anan yaga motar da shazim ya fita da ita hakan yasa shi tunanin yayan nashi ya dawo dama yace gidan malam zai kwana idan ya dawo, parking yayi a compound ɗin gida sannan ya kashe motar ya nufi main entrance ɗin shiga part ɗin malam

da sallama a bakin shi ya shiga parlorn,malam ya gani zaune kan carpet ummi na kusa da shi tana haɗa mashi breakfast shazim kuma na zaune kan dinning shima breakfast yake jikin sa sanye da short iya gwiwa sai t_shirt mai hannun vest, breakfast yake hankalin shi kwance,ciki ya ƙarasa yana sake yi masu sallama, ɗagowa su kayi suna kallon shi, ummi ce tace " marhabun lale da zuwa,yau har nayi tunanin ka wuce "


tunda ya fara zuwa aiki kullum sai ya biyo ta gidan ya gaishe da su kafin ya wuce wurin aiki 

Zama yayi ƙasa kusa da malam yana faɗin" ina da mata kamar ke taya zan waye gari ba tare da nasa ki a idona ba"

 murmushi ummi tayi tana faɗin" to ai shine na fara cigiyar ka " 

girgiza kai malam yayi yana faɗin " nuraddeen Allah ya shirye ka, ni da matata zaka yiman ƙarfin hali ko" 

dariya yayi mai ɗan sauti yace 

"ai ka tsufa ne shiyyasa ko ummy?" ya faɗa yana kallon ummy 

"ai kuwa dai "

"to yanzu gani na zo, ina nawa kunun gyaɗar "

"yana nan na ajiye maka " 

"to a bani yau da shi zan tafi nayi breakfast kafin na zo " ya faɗa yana juyar da kan shi kan shazim yace " ya shazim ina kwana "

"lafiya lau, ya su Ammy "

"Suna lafiya, tace man ta kiraka baka ɗauka ba" 

"muna meeting ne amma munyi waya ɗazu "

"ok, ya Abdallah fa na gida shi kaɗai " 

"yanzu ai dana gama breakfast ɗin gidan zanje"

"ok" noraiz yace yana kallon ummy data ɗauko mashi kunun gyaɗar data zuba mashi a cikin stainless flask,amsa yayi yana faɗin" shukuran ummy, yau bazan wuni da yunwa ba " 

" nima saboda bana son ka wuni da yunwa ne yasa na haɗa maka shi"

"na kuwa gode ummi" 

"wai sai gode mata kake nifa kenan" malam ya faɗa yana kallon shi, ɗan murmushi yayi yace " harda kai fa malam" 

"to yanzu naji batu " 

fira su ka shiga taɓawa, noraiz ya ɗan jima a gidan har sai da shazim yace mashi "wai yau ko a nan zakayi aikin naka ne" 

"A'a yaya yanzu zan tafi " ya faɗa yana tashi yayi ma ummy da malam sallama ya fice shima shazim ɗin tashi yayi ya nufi bedroom ɗin malam anan ya kwana, daman duk randa ta buga mashi nan yake zuwa ya kwana kuma a ɗakin malam, shaf shaf ya shirya cikin kayan da yasa jiya bayan yayi wanka, bai wani jima shima yayi ma ummy da malam sallama ya nufi gida.


Horn yayi a bakin gate, mai gadi ne yazo ya buɗe mashi, ciki ya shiga da motar shi a parking lot yayi parking,fitowa yayi bayan ya kashe motar ya shiga ciki,bakin shi ɗauke da sallama wacce in ba kana kusa da shi ba zaka ji mi yace ba, tsit yake main parlor ba kowa,direct part ɗin shi ya nufa, tura ƙofar parlorn shi yayi ya shiga da sallama, Abdallah ya samu zaune kan sofa yana aiki a laptop, ɗagowa Abdallah yayi ya kalle shi haɗi da amsa mashi sallamar da yayi ɗan hararar shi yayi yana faɗin 

"sai yanzu kayi lokaci na" taɓe baki shazim yayi yana ɗaga kafaɗa 

"ok bana da arziƙin da zaka man magana kenan" 

Zama shazim ɗin yayi yana faɗin 

"kai ne da wani abu daga shigowa ta zaka fara man da ƙorafi, ko fa Ammy bata san da shigowa ta ba"

"ok haka zaka ce ko"

"eh mana, yanzu dai ba wannan ba sannunka da zuwa "

"yawwa, ya meeting ɗin"

"Alhmdllh"

"masha Allah fatan komai ya tafi daidai"

"insha Allah, ya su mom da Abie"

"lafiya lau suke suna gaishe da kai "

"ina amsawa" shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi bedroom ɗin shi yana cema Abdallah 

"bari nashiga ciki na canza kayan jikina "

"to shikenan saika fito " Abdallah ya faɗa , jinjina kai shazim ɗin yayi yana shiga ciki, Abdallah mai da kanshi yayi kan Aikin da yake. 


"Asslamu Alaikum" yaji an faɗa haɗi da turo ƙofar parlorn aka shigo Fatima ce ta shigo hannunta ɗauke da tray mug a saman shi wanda ta haɗo mashi coffee, amsa mata sallama yayi yana bainta da wani kallon mai nuna tsantsar ƙaunar ta, matsowa tayi ciki har gaban table ɗin dake kusa da shi ta ajiye trayn

"thank you" shine abun da ya faɗa, ɗan fari tayi mashi da idanu tana faɗin "you deserve it " murmushi yayi yana kai hannu ya ɗauki mug ɗin coffee ya kai bakin shi, wuri ta samu kan sofar dake kallon wacce yake zaune ta zauna, zuba mashi idanu tayi kamar ta samu tv shima yana sha yana kallon ta a wannan yanyin shazim ya fito ya same su, a bakin ƙofar bedroom ɗin shi ya tsaya hannuwan shi ya harɗe saman ƙirji yana kallon ikwan Allah, kwata kwata basu san da shi ba ko ƙarar buɗe ƙofar da yayi basu ji ba, da dai yaga dagaske suke basu ga shigowar shi ba ne yasa shi masu gyaran murya, wani mumunnan faɗi da gaban fatima yayi ko ba'a faɗa mata ba tasan shi ne mamakin ta yaushe ya shigo gidan kenan Abdallah yasan yana gidan amma shine bai faɗa mata ba,kallon Abdallah tayi tana tambayar shi da ido 

"ya shazim ne?" jinjina mata kai yayi alamar eh, da ido tayi mashi alamar "amma miyasa baka sanar dani ba"

da ido shima yayi mata alama " sai mi to idan ya dawo " 

"ɓata fuska tayi kamar zatayi kuka tana mashi alama da , wallahi ba ruwana, alama yayi mata da tayi haƙuri, girgiza kai tayi tana mashi alama da tafiya zata yi, girgiza mata kai yayi alamar kar ta fita,maƙe mashi kafaɗa tayi, shazim na tsaye yana kallon ikwan Allah, a zuciyar shi yana faɗin lallai yarinyar nan wuyanki ya isa yanka, sake masu wani gyaran muryar yayi hakan yasa ba tare da ta juya ta kalle shi ba ta miƙe simi simi ta nufi hanyar ficewa, haushi ne ya kama Abdallah ya san daga nan bazai sake ganinta ba sai yaji dama shazim ɗin bai dawo ba, hannu ta sa ta buɗe ƙofar ta fice gabanta sai dakan uku uku yake tasan Allah ne zai rabata da shazim a gidan nan, a zuciyarta kuma gungunai take tana faɗin 

"na rasa gane kan wannan ya shazim ɗin, ya hana kanshi soyayya mu ma so yake ya hana mu, haba dan Allah, Allah ya haɗa shi da wacce zai ji idan babu ita bazai iya rayuwa ba inga ta tsiya" ta faɗa tana wani turo baki da ruƙe ƙugu. 


_to Ameen fatima, amma ki fara bari idan ya kama ki tukun sai ki faɗi haka_


Ɗakin su ta nufa sai wani ɓata rai take, a zaune ta samu su sa'ada suna fira ita da Aaimah Aairah kuwa na zaune kan bed ɗin su ita da fatima abun duniya duk ya bi ya ishe ta sai trying number mus'af take amma yaƙi ya ɗauka tun tana kira tana shiga bai ɗauka harta koma kira wayar a kashe ga safwan sai kiranta yake ba ƙaƙautawa, jefar da wayar tayi kan bed kamar za tayi kuka,da sauri su sa'ada suka mai da idan su kanta sai ga fatima itama ta shigo sai ɓata rai take, sa'ada ce tace" to fa Juliet's duk mi ya ɓata maku rai daga mai jefar da waya sai zumɓure zumɓure?" ɗan tsaki fatima taja mara sauti wurin zama ta samu kusa da Aairah tana faɗin " ke dai kawai ki bari ya shazim wai ashe ya dawo ban sani ba shima ya Abdallah ya ƙi faɗa man har sai da na kwashi ƙafa naje part ɗin"

dariya sa'ada ta kwashe da ita tana "wallahi Allah ya ƙara, tun da ya Abdallah ya zo kika watsar da ni, ki godema Allah ma da bai dokekiba"

"kefa matsala dake kenan ba mutunci bane dake yanzu infaɗa maki ya dawo shine zaki man Allah ya ƙara"

"idan ban maki Allah ya ƙaraba mi kike so nayi maki, ƙiri ƙiri ji rashin kunyar da kuka so yu jiya a gaban Ammy ni wallahi da zai burge ni da fasa tafiya marantar nan kika yi yayi maki Aure kawai inya so acan wurin ya Abdallah kyayi "

"yo sai mi ni wallahi daɗi zanji" girgiza kai kawai sa'ada tayi tana faɗin "wallahi Allah ya shiryeki" 

"Ameen" fatima ta faɗa tana murguɗa mata baki, dafa Aairah dake kusa da ita tayi tana faɗin " ni dai nakasa gane mike damunki sis ko ko dai haka yanayin ki yake ban sani ba " fatima ta faɗa tana leƙa fuskar Aairah, ɗan murmushi Aairah tayi tana faɗin " mi kika gani"

"naga Aaimah ta saki jikinta amma ke duk sai a hankali"

"bana jin daɗi ne"

"Allah ya baki lafiya, Aida kin faɗi da sai na ɗauko maki magani, amma mike damun ki?"

"irin ciwan ku na masoya ne ke damunta" Aaimah ta faɗa, ɗan harararta fatima tayi tana faɗin "sai kace ke na tambaya " 

"to ai gata nan sai ki tmbaye ta ta faɗa maki" 

"to" fatima ta faɗa tana ɗan kallon Aairah tace " pls sister mike damunki dan Allah ki faɗa ko akwai abun da zan iya maki, tun jiya bana murna da ganinki haka" murmushi kawai tayi ba tare da tace mata komai ba, lallashin ta fatima ta shigayi akan ta faɗa mata mike damun ta amma tace ba komai sai da fatima ta nuna ranta ya ɓaci tukun ta sanar da ita abunda ke damunta, ce mata fatima tayi ta bari zuwa anjima ita da kanta zata kira shi da wayarta insha Allah zai ɗauka, janta da fira fatimar taita yi harta samu ta ɗan saki jikinta suna fira, sunjima a ɗaki suna fira sai da lokacin da zasu ɗaura lunch yayi tukun suka nufi kitchen............ 


_*mu haɗu gobe idan Allah ya kaimu*_


_GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM 300 NE BA YAWA_


_3169482544 MUKHTAR HADIZA FIRST BANK_


_SAI A TURA SHAIDAR BIYA TANA WANNA NUMBER *** KO ***_