chapter 13&14
_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_Wattpad✅_*
***
*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444
*Sirrinmu➡️*
Ya ku ƴan uwana mu yawaita addu'ar fita daga gida don neman kariya daga sharrin shaiɗanu.
Addu'ar fita daga gida.
"Bismillahi alaihi tawakkaltu alallahi wala haula wala ƙuwwata illa billahi".
addu'ar shiga gida.
"Bismillahi walajna wa bismillahi karajna wa alallahi rabina tawakkalna".
➡️13 & 14
…………………Abbana ma kasa tsaida ƙwallarsa yayi sannan ya ƙaraso inda nake,ya dafa kafaɗata sannan ya ce"Mamana inason ki faɗamin gaskiya,kin tabbatar ya cs miki haka"?.
ɗaga kaina na yi ina kuka,Ammi ta ce"tunda nake da ƴata tun tana budurwa har zuwa yanzu bata taɓa yimin ƙarya ba,to me zai sa ta yiwa Ahmad ƙarya? ni ina ganin Baban yara mu tafi da ita gida,idan yaso daga baya a yi duk maganar da za'ayi ammab idan aka komar da ita gidansa kamar ba asan darajarta bane,yarinyar nan fa ita kaɗai na mallaka arayuwata,to sabida me za a dinga son arabani da ita? duj kawai cin dana ke sai an kai ni ƙarshe"?.
Ganin ta fusata sosai yasa Abiey yin shiru,don shi a ɗabi'arsa baya biyewa mace musamman ma idan tayi fushi,kaima kayi fushi to sai arasa waye yafi wani hankali? waye mijin waye matar? sau da dama wasu mazan da kansu suke bawa matansu ƙofar da zasu raina su,in banda haka me xaisa ka biyewa mace? ko kuma tana faɗa kana faɗa sai kiga gida ya zama filin sansani yaransu kuma suna ta kallonsa,kunga kun bar musu fefe mafi ruguza rayuwa don kuwa suma idan sukayi aure abinda zai shiga kansu kenan,shine rashin sanin darajar matansu.
Duk haƙurin Abiey a wannan karon sai daya nuna fushinsa,musamman wani tabo daya gani a gefen bakina,marin da yayi min ƙwana biyu da suka wuce kenan,saboda haka tabon bai gama bajewa ba.
ina ganinsa yana son tambayata? yana kuma tunanin kada ya bada hanyar wata ɓarakar,ana neman gyara wata sai kuma a ɓaro wata daban.
Ammi kuwa ce wa tayi"momina meye a bakin ki haka"?.
Da burcewa nayi bakina na taɓa na ɗanji zafin wajen sanadiyyar taɓa wajen dana yi sai na ce"faɗuwa nayi Ammi".
Daga haka naja bakina nayi shiru,don sam bana son faɗar lefin Ahmad,ban sani ba ko don halarcin daya yimin ne abaya? ko kuma don yana amatsayin miji na ne?.
Ammi ta juya kai gefe kawai tana zubar da hawayen tausayin ƴarta,don tasan halina ko zata kashe nu ba faɗa mata zanyi ba,don yarinya ce me matuƙar zurfin ciki tun kuma tana gida ta gane hakan,don sau tari mama uwargida ko ƴaƴanta na tsokanarta,wani lokacin ma har da zaginta amman bata taɓa faɗa ba,sai dai ma ta nemi karesu ita fa duk haƙurinta sai take gani tamkar ƴarta ta fita haƙuri don ita gaskiya ba zata iya wannan haƙurin da take ba.
Ammi ta haɗamin ruwan zafi a banɗakin asibitin,wanda daga zuwanta ta cire hijabinta ta shiga bayin ta sanya masa dettol da hypo da cleanser,ta wanke shi tas ta bishi da airfreshner me daɗin ƙamshi,sannan ta riƙoni har zuwa ban ɗakin sannan ta fito,ta zauna abakin gadon dana tashi ta zauna tana me yin tagumi.
Abiey ya dawo daga sallah ya same ta anan,sosai ta bashi tausayi ya ƙarasa kusa da ita ya cire mata tagumin,sannan ya zauna abakin gadon shima ya kira sunanta cikin sigar rarrashi.
"Zulaiha kina jayayya da hukuncin ubangiji ne"?.
hawayenta ta share sannan ta ce"a'a Alhaji,amman wallahi da ina da iko da sai na datse wannan igiyar auren,ne cike da matsaloli da dama waɗanda basu san komi ba sai zaluntar ƴaƴan mutane".sai ta fashe da kuka me cin rai da zuciya da kuma gangar jiki.
a hankali ya ruƙo tattausan hannunta ya sanya acikin hannunsa,ya kalli cikin idonta sosai don damab idan yana son ya rarrasheta yasan salon daya ke binta dashi ya ce"Zulaiha kalli cikin ido na"..
ƙin kallon idon nasa tayi,don tasan so yake ya rarrasheta ita kuma bata son rarrashin saboda abubuwan da zasu biyo bayan kallon cikin idon na sa.
Murmushi yayi don yasan dama ba lallai ne ta kalla ɗin ba,amman yasan ta da masifar sauƙin kai ga saurin hawaye amnan da an rarrasheta sai asamu sauƙi.sannan komi wayon amarya sai ansha manta.saboda haka sai ya sanya hannunsa ya juyo da fuskarta sosai zuwa ilahirin zahirin fuskarsa,me cike da ƙwarjini da kuma son kasancewa da ita,sau tari Abiey zawarawa da ƴammata na yawan bugo masa waya idan ma sun samu numbar kenan,suna sonsa saboda suna ganin wa',azinsa kuma yana masifar burgesu amman sai ya basu haƙuri,don shi tunda ya auri Zulaiha yasan daɗin aure,don wallahi ba ƙarya ba Zulaiha macece ta nunawa sa'a,duk wani hali na mace tagari ta sansu uwa uba kula da miji,shimfiɗarsa,cikinsa,dukiyarsa da sauran abubuwa muhimmai acikin aure.
da sauri ta sunkuyar da kanta,wano daɗi na lulluɓe cikinta,aduk sanda ta kalli idonsa sai taji hakan bata san me hakan yake nufi ba,tasan de tana son mijinta so na haƙiƙa ƙauna mara adadi,amman kuma bata san ne yasa ba duk sanda ta kalli idonsa sai taji irin wannan abin.
Jikinta yayi sanyi sosai,kawai sai ta shiga ƙirjin gwarzon mijinta ta fara rera kuka ahankali,tana ce wa"Baban yara kai miji ne nagari,me son dauwamammen farin cikin matarsa,madalla da samun miji irinka Allah ya barmu tare har zuwa ƙarshen rayuwarmu abadan abadan!".
Murmusawa yayi yana ɗan shafa bayanta,ya ce"madalla da samun hasken zuciyata,Abin tunƙahona ke ɗaya tilo acikin mata,Allah ya ƙarawa rayuwarki Albarka Zulaiha".
OH😂dama ana soyayya haka ba yara ƙanana ba/ƴan ilov u u miss u,ƴan soyayyar ƙarya kafin aure? da anyi auren sai kaji ana zunduma miki zagi da cewa baki iya kaza ba baki iya wan ba?😂to Allah ya ƙara mana soyayya a tsakaninmu da mazajenmu Amin🙏🏻.
a tsaye na tsaya a ƙofar banɗakin don basu san ma na fito ba,ko ciwon da hannu na ke yi ban kula dashi ba,na harɗe hannuwana a ƙirjina ina kallon iyayen nawa cike da farin ciki da annushuwa,ina masifar son irin wannan soyayyar da iyayena ke gudanarwa a tsakaninsu,ko a ina ne basa jin kunyar soyayya yi idan suna tare manta kowa da komi suke su tarairayi zuciyarsu da kuma farin cikinsu,na taso da burin idan nayi aure in ƙwatantawa mijina saboda bama zai yiwu in yi kamar yadda sukeyi ba,awaje ɗaya ne suke kunya gaban matan Abba,don gaskiya yana ƙoƙarin ƙwatanta adalci,duk da awani sa'in baya iya riƙe soyayyar sai ya saki layi,ni har mamaki nake yadda Abba ke yi agaban Ammi,tamkar wani yaro ɗan shekara biyu ko ɗaya alhali shi ɗin yana da kusan shekara hamsin da biyar,Ammi kuma bata fi shekara 38 ba don dama Abbana ya girme mata ba kaɗan ba.
Abas ma kallon su yake cikin so da burin idan yayi aure ya ƙwatantawa matarsa irin wannan soyayyar.
Abas shine wanda ya kaɗe Rabiatu,yanzu ma ƴan uwansa da mahaifiyarsa ne suka zo duba ta.
Hajiyarsa ta ƙaraso cikin fara'a don itama taga komi,abin ya burgeta sosai,ta kalli Abbas tausayinsa ya ƙara ninkuwa acikin zuciyarta,yaron ta yana son yayi aure tun bayan mutuwar Bilkisu matarsa da aka ɗaura musu aure,ranar ta mutu ba tare da an kai ta gidan mijin ba,da roƙon Allah Abas ya dawo de de tun daga nan bai ƙara jin son wata ƴa mace ba,abin yana damun mahaifiyarsa sosai,don ayanzu haka yana da kusan shekara arba'in da biyar amman aure shiru haryanzu.
*** *** ***
Autar Momma ta ce"Amira kin san abinda kike faɗa kuwa? bro Aliyu fa kika ce kina so?"!.
Amira ta ƙaraso ta riƙe hannunta gam acikin na ta sannan ta ce"wallahi tallahi ban taɓa son wani ɗa namiji kamae yadda nake son bro Aliyu ba,besty na idan kika sanya hannunki a ƙirjina saitin zuciyata,za kiji adadin yawan muradinta da kuma zulamarta akan abinda take so,ki taimakamin don in samu burin zuciyata,wallahi ina sonsa da kuma ƙaunarsa".
Sai ta fashe da kuka tana me rungume ƙawarta kuma ƴar uwarta.
itama hawayen ta share don tafi kowa murnar hakan,sai dai fa tasan halin yayan na ta ba lallai ne ya amshi tayin aminiyarta ba,don shi haryanzu mace ɗaya ce aduniyarsa wacce ta kasance me shawagi da walainiya arayuwarda bata san mahaluƙin daya samu waje azuciyar yayanta ba,ita ce tauraruwar dake haska rayuwarsa kuma sannan itace wacce ta ruguza masa rayuwarsa da har yanzu ba a samu ruwan da zai kashe wutar ba.
ganin tayi ɗsn jim sai Amira ta ɗago daga rungumar da tayi mata ta cs"besty ba zaki bani goyon baya ba kenan"?.
shiru tayi sai dags bisani ta ce"Amira ko baki ce kina son yaya Aliyu ba ni zan bada goyon baya,ballantana kuma kin faɗi da kanki ai ni babu abinda zance sai dai Allah ya ƙara muku danƙon soyayya,amman sai kinyi fama sosai kinyi kuma jarumta,kin jajir ce kin janye idanuwanki daga dukkanin abinda zai je ya dawo don kinsan Bro haryanzu mikin daya suki zuciyarsa bai barshi ya samu salama ba,zanso ki zamar masa farij ciki ki maye masa gurbin wani abu daya ɓanɓare daga rayuwarsa,ki sanyashi farin ciki me tausa zuciya".
Murmushi tayi ta ce,besty duk wannan mino ne inda xan mallako bro A ba ni da matsala ta kula dashi,nayi miki alƙawarin zama dashi bisa amana da ƙaunar juna,ko da baya sona ni zan sa ya fara sona in sha Allah ba zan baki kunya wajen wannan ba."
murmushi tayi ta ce"amin de Amira".
sai kuwa ta ce,"amma besty ya kike ganin za ayi? don wallahi ina jin kunyar sanar da su Kilishi wannan maganar".
Riƙo hannunta tayi ta ce"ƙwantar da hankalinki ki sanyashi cikin snow me tartsatsin sanyi da iska,da Gwagwalo zamu haɗosu kiga aiki da cikawa don kinsan ta aƙwaita da haɗi,kuma kinsan idam tace ga yadda za'ayi sai gani sai hange".
sosai ta rungumeta ta ce"kai besty wallahi shiyasa nake sonki,Allah ya barmu tare Allah ya baki miji nagari".
Murmushi tayi ta ce"yo ai nima mijin nawa yaya Aamiru ne,kinga kuwa godiya ya kamata mu yiwa juna".
Shewa tasa ta ce"shegiya besty,yanzu dama soyayya kuke babu wanda ya sani? gaskiya kun cika munafukai".
ta ce"yo ai ashe ba mu kaɗai ne munafukan ba,tunda kema tun yaushe kike son bro me amman ai baki taɓa faɗamin ba sai da gumi tayi gumi allura ta tono garma".
Hararta tayi ta ce"to ni fa bansan raini don yanzu ni yayarki ce".
dariya auta tayi ta ce",hhh ai shiyasa nima muka ƙulla da bro Aamiru kinga don kada ki kawo min raini,kinga ina auren yayanki kema kina auren na wa,ai kinga nima yayarki ce ko"?.
Duka ta kai mata ta goce,haka suka fito har falo suna guje guje kamar yara Kilishi ta murmusa ta ce"oh waɗannan yara baƙwa girma,ina zaku je kuma"?.
Auta tayi karaf ta ce"wajen gwaggwala zamu je hira".
ta ce"oh to wallahi kada ku tsokano mana ita,don ni bana son hayaniya wallahi".
Dariya suka saka don sum san Kilishi da Gwaggwala basa shiri ko kaɗan.
suna fitowa auta ta ce"tsohuwar nan muna zuwa za kiji ta ce kai ku ɗeɓemin ƙwanukan nan,ga sha zu mamu dun zo".
Amira ta ce"hhh gaskiya kin gama fuskantar halin fitinanniyar tsohuwar nan".
Suna shigowa suka samu sashen nata da mutane fal,yawancinsu ƴan sannu ne don bata daɗe da dawowa daga masarautar kahutu.wato masarautar gidansu kenan don itama gwaggwala ƴar sarki ce a wancan zamanin don yanzu ƙaninta ke riƙe da masarautar.
Suna shigowa ta kyalla ido ta gansu ta ce"ke Saratu ɗaukemin ƙwaryad zumar nan da alkakina don ga sha zumamu sun zo".
Dariya suka sanya Auta ta ce"yo me xamuyi da wannan abin duk tsohon hannu yaƙunanne ya taɓa".
Gwaggwala ta ce",yo ai ubanki ne yasa uwarki tayo sa ta kawo min,yo kinga kuwa su ne tsoffi ba ni ba,don ni ko kallonsa ma banyi ba saboda baiyi min ba".
Dariya suka sanya suna ƙarasawa falon,jakadiyar gwaggwala wato Asabe sai dariya take.
Ai kuwa suka dirar wa wannan alkakin suka hau ci,Gwaggwala ta ce"duk zakuyi amansa ne bari in kira wanda yake de de daku".
Ai suna jin haka suka cire hannunsu suna dariya,don sun san halin Gwaggwala idan tace za tayi abu to sai ta yi,duk da kuma sun cire hannun sai da ta kira sa nan da nan idanuwansu suka kawo ruwa don ba ƙaramin tsoronsa suke ba,kallon idonsa ma kawai ke sa kayi gudawa.
da gudu suka ƙarasa kusa da ita suna bata haƙuri,sai kuwa Gwaggwala ta ce"yo an gaya muku ku kaɗai ne ƴaƴan zamani? ai nima da kuka ganni ƙwalluwa ce ina kamar ku shiyasa na ce bari in kika wanda za kuji tsoro nai".
Asabe ta sanya baki tana bata haƙuri,sannan ta ce ta haƙura amman kada su kuma shigo mata ɓangare su sanya mata ƙazaman hannunsu na tara farce,don babu abinda ta tsana irin tara farce shiyasa kullum faɗa take musu,su kuma gani suke tamkar wani gayu ne,amma ko a addinin musulunci ba abune me kyau ba ɗabi'ace ta arna.
*** *** ***
daga can nesa suka faks motarsu a dai dai ophanage ɗin,wato gidan marayu Aamiru ya ƙosz ya ce"man wai ni lafiya mukazo wannan gidan"?.
Kamar yadda ya tsammata bai ce masa komi ba,ya cigaba da takunsa cikin ƙwarewa awajen tafiya sai da yaga ya yi masa nisa sannan ya biyosa abaya don ya ƙosa yaga me za suyi agidan marayu?.
Suna shigowa gidan ya kira wani awaya,nan da nan sai ga su sun fito da wani yaro a hannu sosai Aamiru ya waro manyan idanuwansa yana kallon mamaki da firgici tamkar wanda yaga zaki ko kuma namijin miciji........Soon➡️
***
***
ga link bana son talla da turo batsa,iya mata kawai.
Atayani share ƴan uwa,ni kuma in ta sanbaɗo muku wnn littafin me cike da wa'azin rayuwa.
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
*MRS GREEN CE*