FACALA

chapter 15&16

by @rabiattu0444

_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_

    {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}




       _BY_

_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚


*_Wattpad✅_*

***


*_𝘼rewabooks✅_*

 https://arewabooks.com/user/rabiattu0444


*Sirrinmu➡️*

ƴan uwa mu yawaita yin istigfari,Allah ya yafe mana baki ɗaya.


*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*

ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.

***.


➡️15& 16

…………………da sauri ya ce"bro wannan yaron da kake kama dashi haka fa? ban taɓa gani ko sanin kana da ƙani namiji ba? amman yau sai ga me irin kamanninka"?.


 ayanzu ma bai amsa masa ba,ya sanya lallausan hannunsa ya ɗauki yaron yana murmushinsa me mugun tsada,don sai kuyi shekara dashi baka taɓa ko da ganin haƙoransa waje ba.

binsa kawai ya ke amman bakinsa cike ya ke da muradin son sanin ayar tambayar da take akan yaron,don wannan yaron inde ba ƙaninsa ba to wallahi baya raba ɗayan biyu ɗansa ne,to idan ɗansa ne ayaushe ɗin yayi aure? shi de yasan yayansa bai taɓa aure ba? to a ina ne zai samo yaro me kama dashi haka?.

Sosai yake wasa da yaron,tun yana fara'ah har ya fara ɓaɓɓaka dariya,shi kuwa Aamiru kallonsa kawai ya ke yana mamaki,anya kuwa ba aƙwai wata aƙasa ba? anya kuwa ba wata Galadima ya yiwa ciki ba? tun yana wannan tunanin sai yazo ya dena yi don gani yake kamar hakan ba zata taɓa faruwa ba,don yasan yadda galadima ya tsani zina,barshi dai da wasu halayensa wanda ba kowa ne yasan dasu ba,ko iyayensa basu san da wannan harƙallar da yake yi ba shiyasa yake tunanin babu abinda zai canja Galadima zuwa wannan baƙar rayuwa me cike da tafki me zakuna da kunamu.


ƙuri ya ƙurawa yaron kallo,kai hatta bakinsa da idonsa duk na Galadima ne babu abinda baiyi irin na ubansa ba.

ya ɗago ya kalli Aamiru yaga ya ƙurawa yaron ido,tamkar wanda yake rubutu ajikin allo sai da suka daɗe ahaka sannan ya ce"Aamiru bana son sa ido arayuwata,duk abinda mutum ya gani yana da kyau ya ɓoye abinsa aransa,dom shi ciki ba don komi akayi sa ba,don rufe sirri aka yisa saboda haka bana buƙatar kowa yasan munzo nan,kai amintar dake tsakaninmu ce ta sanya ni zuwa da kai nan,kasan dai inuwar sharri sai fitilar sharri ko?idan ka sake bakinka ya furta wani abu kan wannan zuwan,uhm".


 yana faɗar hakan ya juya ya cigaba da yiwa yaron wasa,suna ta ɓaɓɓaka dariyarsu gwanin sha'awa kan Aamiru ya kulle sosai ya rasa ta inda zai ɓullowa wannan babban hamshaƙin lamari,wanda ya girmami ƙwaƙwalwa balle ayi maganar ajje tunani,kamar yadda ya faɗa masa inuwar sharri sai da fitilar sharri shi ne,yasan halin amininsa aƙwaisa da mugun riƙo muddin ya yarda da kai kaci amanarsa to ko kai waye sai ya rama ta salama,ya biyo maka ta bayam fage ta yadda babu ta inda za ka iya gane komi,shiyasa ayanzu ma yake shawara da zuciyarsa Allah yasa kada ta ruɗesa ya faɗi wannan ƙabli da ba'adin,ta inda aka hau ta nan ake sauka saboda haka daya gama shawara da zuciyarsa sai ya juya ga amininsa ya ce.



  "Aliyu"!.


A hankali ya juyo ya kallesa tare da amsa masa,don yadda ya faɗi sunansa full sai hakan ya bashi mamaki sosai don rabon da yaji ya faɗi sunansa tun suna yarinta,shima idan sunyi faɗa ne yasa yake faɗin sunansa,abinda yafi faɗa idan zai ambaci sunansa shi ne,Raba gardama ko kuma Galadima ko kuma soja sa maza gudu,amman ya yi mamaki sosai daya ji ya faɗi sunan na sa.


  Ganin mamaki a fuskar aminin na sa yasa ya ce"mamaki ka ke dana faɗi sunan ka ko?to ba abin mamaki bane saboda wallahi kai na ne a kulle,da xaka sanyawa zuciya da ruhi salama da ka aminta dani ka faɗamin gaskiyar komi,wala alla asamu bakin zaren".


wasa ya cigaba dayi da yaron sannan ya ce"uhm an samu bakin zaren a'i".


 Aamiru ya kasa magana,ji yake kamar ya tamfatsamai maruka waɗanda zasu sanya ya dawo daga tafkin zaren ƙulalliyar da yake son afkawa ciki,ya cije leɓensa har sai da yasanya shi jin zafi ya tashi tsaye amatuƙar zuciye ya ce"Aliyu ni zan tafi,idan ka gama ƙulalliyar saƙar da kayi ka kasa warware ta sai ka taho,idan kuma kana zaman jiran wani ya warware maka saƙar ne sai ka zauna,dabara dai ta ragewa me shiga rijiya".


  gaba yayi abinsa bai jira cewar sa,don yasan ko kashesa zai yi ba zai faɗa masa ba,don ya rasa wani irin mutunne galadima tamkar zuciyar mace haka zuciyarsa take,sai ya iya barin abu shekara aru aru ba tare da wani mahaluƙi yasan komi ba,ko shi da yake amininsa wani abun sai ankai ruwa rana sannan yake sanin komi.


  Bai kuwa tsayar dashi ɗin ba,ya barshi ya tafi abinsa yana ta yi wa yaron wasa ya ɓata awanni da dama sannan ya yiwa yaron wasu irin hot kisses kamar ba yarima ba,sannan ya tashi ya kaishi wajen masu kula dashi ya yi musu sallama yana jin wani irin nauyi tamkar an sanya masa wani jiminin dutse aransa,rayuwa kenan sai ka ganka da kuɗi da komi amman kuma sai ka rasa farin cikin rayuwa da sukuni kullum sai dai ka kasance cikin wani hali,yana addu'ar Allah ya kawo masa ranar da zaiyi farin ciki arayuwarsa.






***       ***       ***

"Hajiya ni fa zan fita ne,tunda na ga Khadija ta fara samun lafiya".

caraf tayi da ce wa"wajen malamin nan zakije ko? don Allah idan kinje ki faɗa masa halin da Khadija take ciki tunda wannan mayyar ta kama ta sai maganin asibiti kawai muke bama na malamai".

wani kallo ta yiwa Hajiya sannan ta ce"ni na gaya miki ga inda za ni,Hjy bana son shisshigi a dukkanin lamurana ki dinga sanyamin ido aduk abinda zanyi? anami? ke kike aure na ko mi"?.

Hjy ta ce"yi haƙuri ƴa ta,dama tuna miki na yi ayi aikin da baki ɗaya ma wannan tafiyar da tayi gida kada ma ta dawo,don wallahi na tsani yarinyar nan tamkar me".

Balaraba de ta turo ɗaurin ɗanƙwalinta gaba,sannan ta ce"ok na gane amman idan waccan gantafalallan ɗan naki ya dawo ki faɗa masa ke kika aikeni,kada yazo ya sanyani agaba da tambaya don tunda ya fara sanya hannu ajikina nasan zai iya aikata komi".

adawo lafiya tayi mata da samun abinda taje nema.




uhm oh ni😳😥rayuwa,wai suruka ce ke ƙara tunzura matar ɗanta taje wajen boka? ko malamin tsibbu? wanda ko da matar ɗanka na yi za kaji duk ka tsaneta saboda bin bokaye? Amma madadin taji haushi da kuma kishin ɗanta sai ma ƙara tunzurata da take yi? ya Allah ka tsarkaka mana zuciyoyinmu.

anan nake janyo hankalin mata masu asiri,don cikar wani burinsu na duniya su kiyayi ranar tsayawarsu agaban jalla sarki Allah,suji tsoron Allah su dena kafin ranar tsayuwa.




****


Malamin ya juyo da sauri ya ce"caɓɓijan,aƙwai matsala fa Balaraba idan baki tashi tsaye ba".

Sosai ta waro ido ta ce"na shiga uku malam,wacce irin matsala kuma?".

Bushewa yayi da dariya sannan ya ce"ai ina faɗa miki idan baki yi abinda muka sanya ki ba zaki iya shiga cikin mummunan tashin hankali,saboda haka ku bada kai bori ya hau kawai".

shiru tayi tana tunani sannan ta ce"amma boka babu wanda yasan fa da wannan matsalar,ina tunanin kada Zubairu ya gane komi don wallahi inasonsa ba zan iya rabuwa dashi ba,asan dai yadda za ayi kawai komi ya zama tarihi".

dariya yake ta ƙeta sannan ya ce"Balaraba ina jiye miki faɗawa halaka mafi muni arayuwa,sabida haka ki yarda kawai da abinda zan faɗa miki" .



wani irin kallon banza tayi masa,a fakaice tana ɗan toshe hancinta ta saba mu'amala da manya manyan malamai waɗanda suka amsa sunansu,don kuwa ko ƙamshin turarensu ma na musamman ne,amman shi wannan sai ɗan karen wari tamkar ma baya wanka,amman ahaka yake son ta kasance dashi saboda biyan buƙatarta? anya kuwa za ta iya? ita dai ta sani arayuwarta macece me masifar son turare duk da itama ba tsaftar ce da  ita ba amman kuma tana son turare,kuma mijinta ma mutum ne me masifar son turare,abinda ma ta lura dashi shi ne duk ƴaƴan hajiyar suna da son ƙamshi,shiyasa itama zama da maɗaukin kanwa yasa take son ƙamshin.



maganarsa ce ta dawo da ita daga hayyacinta,don irin gardawan nanne masu masifar ƙatuwar murya,ba don aikinsa yana da kyau ba da tuni tabar masa wannan shegiyar tabarmar tasa me cike da dauɗa da wari.


  "nasan kina tunanin wannan warin dana ke yi ko? to kada kiyi mamaki don kuwa sai inyi wata biyar banyi wanka ba,shiyasa aikinku yake ci sosai son haka mukayi alƙawari da aljanun birnin maƙasudi,kinga kuwa ai bana karya musu alƙawari ba,amma kada ki damu idan za muyi sai inyi abinda ba zakiji warin ba".…


kallon ƙasan ido tayi masa sannan ta ce"kai gaskiyar magana inason cikar burina,amman kaɗan shafa turare mana".

kallon ƙasa shima yayi mata sannan ya ce"uwa riyonki yarinya,ni zaki yiwa wayo ki karyamin sihiri ko kina so ko bakiso dole sai nayi abinda nake so saboda nima ai ina miki abinda kike so".

ba yadda za tayi don tun ba yau ba tasan halinsa,kuma matar da ta yi mata hanyarsa ta faɗa mata dattijon aƙwai maita,idan kuma ya sanar miki muddin bakiyi ta daɗi ba,to tabbas za ki haɗu da masifu kala kala da ke da kanki zaki kawo kanki wajensa.

gudun kada ta samu matsala yasa ta bada kai bori ya hau.



***       ***       ***

ranar da aka sallameni kuwa gida nayi,don Ammina ta kasa ta tsare tace babu inda zanje,sabida haka ma yasa ban wani damu sosai ba don tun inason Ahmad yanzu naji ya fice min araina baki ɗaya.

Umma ce tazo dubani amatan Babana,amma Umma uwargida ce wa tayi babu inda za taje,kuma ko kunyar Ammi bata jiba tace ita fa baza ta zo ba.

Umma ta kalle ni ta ce"yanzu Adawiyya haka Ahmad ɗin ya ce miki"?.

ɗaga kai na nayi cike da kunyarta,don ma nafi buɗe mata cikina akan Ammina duk na faɗa komi,alokacin Ammi ta fita waje siyo min ayaba dana ce ina so.

Umma ta ce"Adawiyya har ga Allah yanzu bana son zamanki da Ahmad,sannan ni ayanzu ma na fara zargin aƙwai wata maƙarƙashiya,zaman gidan auren ne ba a son kiyi sannan ni a ƴan ƙwanakin nan ina mafarkai da dama akanki don Allah kada ki koma don ni dai sam zuciyata taƙi jinin gidan da kike ciki".

  kama hannunta nayi ina kuka na ce"Umma ya zanyi ne wai? duk sanda na kawowa su Ammi ƙararsa kafin ma in ƙarasa sai suce wai inyi shiru,damuwa tana yimin yawa Umma wallahi na tsani Ahmad yanzu,saboda shi bai san damuwar kowa ba sai tashi,sannan uwa uba mahaifiyarsa da facala ta Allah sun tsaneni Umma,da za a basu damat harbeni da tuni sunyi yadda suke so dani,Umma yaya xanyi yanzu don nasan halin Abba zai iya cemin in koma daga baya".

Rungumeni tayi a ƙirjinta,hawayena yana ɗiga a kafaɗarta tana rarrashina har Ammi ta dawo.


tare suka shigo da Abbas,ya ƙuramin ido tamkar tsohon maye ni kuwa haushinsa ma ya sanya ni juyawa kawai ba tare dana ce komi ba,wasu hawaye masu xafi suna sakkomin alokacin dana tuno da rayuwa ta tabaya wanda magogi ba zai taɓa goge mummunan tabon dana adana azuciyata ba,wanda kuma ya fito fili bai kai wanda na adana ba...........soon➡️


a tayani share masoya🥰



#ZUBAIR

#ALIYU

#RABIATU

#BALARABA

#AHMAD.


MRS GREEN CE.


MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.


Abubuwan da ke cikin littafin kaloli dabam dabam na👇🏾


Haɗin Dilka

Haɗin man gyaran gashi

Haɗin sabulun gyaran jiki

Haɗin ƙugu(hips)

Haɗin gyaran (Breast)

Haɗin maganin infection

Haɗin furen zogale

Haɗin tsumin tabaje

Haɗin Kaza 

Haɗin tantabara

Haɗin ƙamshin jiki

Haɗin ƙamshin baki

Ingantattun maganin mata

 

     Bonus

Sirrin riɗi

Sirrin magarya

Sirri magaruwa

Sirrinmu(Addu'oi)


Za ku iya biyan kuɗin littafin akan farashinsa mai sauƙi #1,500 kacal amma ga garaɓasa ga

Mutum 30 da suka fara biya na farko, zasu biya 1000 kacal, ku yi hanzari ku yi payment akan lokaci don neman ƙarin bayani *** SIRRIN MOWA NA MANYAN MATA NE, MATAN SO BA MUNA MATA BA.