chapter 17&18
_*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}
_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚
*_Wattpad✅_*
***
*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444
*Sirrinmu➡️*
ƴan uwa mu yawaita yin sallah akan lokaci don gudun saɓawa ubangiji.
*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
***.
➡️17& 18
*…………………LABARINA*
sauri nake sosai har ina haɗawa da ɗan gudu gudu,murmushi ne ɗauke akan kyakkyawar fuskata me ɗauke da dara daran idanuwa masu kama dana turawa,daman ni tun ina ƙarama mutane da yawa ke tsokanata da ƴar bature,ba fara bace ni baƙace amman kuma ni kyakkyawa ce rawn face ce dani gashina har gaban goshi,saje kuwa har wanu nannaɗewa yake a ƙwance tamkar baƙar ba indiya.
ina da dimple me matuƙar tafiya da dukkanin ruhi da sanyaya zuciya,ni ɗaya tilo mahaifiyata ta haifa bayan ni kuma bata kuma ba har nake da shekara 13.
tun a ƙofar gidanmu na tabbatar da cewa yaya Ahmad ya dawo,nayi murmushi dimple ɗina ya lotsa ya bada wani irin sirrin kyau da tsantsar ƙuruciya, har xan shiga gida sai ga Baby ta taho da sauri tana murmushi itama,aminiyata ce tare muka taso da ita anan bayan gidanmu take,tana murmushin ta ce"yau ya Ahmad ya dawo"..
iyayi ne dani sosai,don haka cikin yauƙi da yanga ba ce"to an riga ki".
Murmushin ta sakeyi ta ce"to mu shiga a kunce tsaraba dani".
na ce"no ba zai yiwu ba,ni kaɗai nake so Ya Ahmad ya fara gani,saboda haka ki saita hanyar gidanku ato ba zaki ƙwacemin shi ba".
dariya take har tana riƙe ciki sannan ta ce"oho wallahi ni de sai na shiga".
ture ta na fara yi wai bazata shiga ba,amman sai da ta ture ni ta shige gidan na sanya kukan ƙuruciya ina ce wa"wallahi na dena kulaki banza fara kamar farin fenti".
haka tayi shigewarta gidan tana yimin dariya.
na shiga gidan ina kuka,mama uwar gida ce a babban tsakar gidan namu tana ganin na shigo ta ce"to shagwaɓaɓɓiya,uwar mi akayi miki da zaki shigo kina yiwa mutane taɓara"?.
tsayawa nayi na ce"mama wai Baby ce tace sai ta rigani ganin yaya Ahmad,ni kuma ina tsoron kada yace ya dena sona ita yake so tunda ita fara ce".
wani mugun ranƙwashi ta gasa min a kaina tana riƙe haɓa ta ce" ke kiji min shegiyar yarinya? wacce tasha ruwan karuwanci a maman uwarta idan banda haka ya za'ayi ace kamar ki shekara 13 har kinsan wata soyayya? kai gaskiya Zulaiha bata ji daɗin rayuwarta ba,ƙwaƙwar son namiji ashe ba ita kaɗai keda shi ba,ƴarta ma ta gaje ta ashe? ko da yake sanin hali yafi sanin asali zakiyi fin haka ma,don dama itama ance ba ƴar halas ba ce,kema ba don agabanmu akayi cikin ba ai sai muce can aka samo ki acab yawon sadaka yalla,wanda aka gada tun kakanni da uhm uhm".
faccalar su Ammi dake kusa da ita ta ce"gaskiya kuwa don wallahi ni tsanar da na yiwa uwarta itama ƴar ba tsira tayi ba,don bani da yadda zanyi dasu ne".
mama uwar gida ta ce"uhm ni kuwa nake da yadda zanyi dasu,ke de ki bani nan da ƙwana biyu wajen da ta fara koyon wannan decoration ɗin sai na san yadda akayi aka koreta,don naji ance ba ƙaramin kuɗi suke samu ba,don wallahi bazan so taje can tana samun kuɗi ni kuma nawa yaran suna nan jiya iyau ba".
tafa hannu sukayi suna dariya,mama safiya faccalarsu Ammi ta ce"uhm abinda harda ƙwalliya naji ance tana koya? ai ke fa idab muka zauna bamu lalata rayuwar wannan yarinyar ba,sai mu saura haka bamu ga tsuntsu ba muga tarko".
haka suka dinga dariya harda riƙe ciki,don sun gama tsara duk yadda abin zai kasance.
a bayan ɗakin Ammi na laɓe,ina jiyo duk hirar da sukeyi na goge hawayena,ina mamakin wata irin zuciya ce dasu haka? ni har mamaki suke bani,ace su kullum cikin shirya mana mugunta suke su da faccalarsu Ammi,wacce kullum rayuwarta a tsaye take,duk abinda ta samu sai nan da nan ya ƙare tamkar yabi ruwa? ina hawaye na shiga ɗakin Ammi.
na zauna afalo na ƙwanta akan doguwar kujerarta tree seater,wani kuka ya kufcemin ina cikin kukan ne Ammi ta fito daga sashen Abbanmu,sosai take kallona ta ce"ke wai wacce irin yarinya ce Adawiyya? kullum sai kuka sai kace yarinyar kenwa?".
tausayin Ammina ne ya kamani na tashi na rungumeta cikin raunin zuciya da ƙuruciya na ce"Ammina don Allah wai mi yasa su Mma uwargida da mama safiya suka tsanemu ni da ke"?.
kasa bani amsa tayi ta riƙo hannuna,ta zaunar dani cikin sanyin daya zamar mata tamkar ɗabi'a,share min hawaye ta farayi tana kallon idaniyata sannan ta ce"Adawiyya me yasa kima yimin wannan maganar"?.
na ce"Ammi yanzu ne bayan na shigo naji suna ta zaginmu ni da ke,sannan ina partyn dana ce miki za ayi a unguwar shanu? kuma nace miki mu aka ɗauka don decoration"?.
Ammi ta ce"eh na gane".
na ce"to shine naji suna maganar,ashe sunji lokacin da nake faɗa miki,wai shine suka ce zasuyi wani abu awajen,ni de Ammi ba zanje ba wallahi tsoro nake ji".
Ammi ta tsorata sosai,don a idonta na tabbatar da hakan hawaye suka ƙaru sosai na dunkuyar da kaina ina zubar da hawaye,iya karaya na karaya sosai don banason burin Ammina ya zama tarihi ya zanyi da waɗannan mutanen da suka sakoni agaba haka? tona musu asiri zanyi ko kuwa sanya musu ido zanyi? suyi ta cin galaba akanmu ni da Ammina?.
wannan shawarar danayi yasa na kamo hannun Ammina wacce ta zurfafa a kundun tunani na ce"Ammi ni de faɗawa Abba kawai zanyi".
da sauri Ammi ta riƙe hannuna,cikin tsoro ta ce"la la kada kiyi haka haɗin faɗa ne,ko ba yau ba kada ki sake kiyi irin haka,saboda zai zama tamkar ƙanwa uwar gami ne,saboda haka kada ki sake kice zakiyi haka ko babu raina".
hawayena na share sannan na ce"Ammi nima nayi tunanin haka,amman zan daurewa zuciyata ki tayani da addu'ah Allah yasa kada suyi amfani da damarsu akanmu".
murmushi tayi ta rungumeni sannan ta ce"to Adawiyya kije ɗakin Abbanku ya Ahmad ɗin yana can a'i".
da gudu na fita har ina bigewa,ina shiga na hangosa zaune cikin kayab sojoji,sai fara a yake yana sunkuyar da kansa wai shi kunyar Abba yake ki yanzu.
ina shiga kamar yaji ajikinsa ya juyo yana kallona,nima shi nake kalla cikin shashanci irin na yarinta,naje na rungumesa ina kukan yaushe rabo yau shekara ɗaya cif kenan da tafiyarsa ƙasar inyamurai don ƙaro ilimi na soja da kuma wani training.
da sauri ya cire ni a jikins a ya ce"haba adawiyya na? ya xaki ɗafeni haka? kinsan dai yanzu ke babba ce ko"?.
ɓata rai nayi na koma gefe sannan na ce"to shikkenan yaya Ahmad ni bazan ƙara zuwa wajenka ba".
Abba duk yana kallonmu yana murmushi,kuma daga ganin fuskarsa yaji daɗin abinda yaya Ahmad yayi don bai bari na rungumesa ba,saboda tun ina shekara goma na balaga kuma a tsarin addinim musulunci indai har yarinya ta balaga bai kamata ta rungume namiji baligi.
ganin na yi fushi yasa ya ce"yi haƙuri maman kowa,ba wai saboda wani anu nayi miki haka ba kinga yanzu kin girma ne".
da wayo da dabara har na saki jikina dashi,aka hau hira kamar ba nice ɗazu nake kuka ba.
*** *** ***
Gwaggwala ta kalli su autar momma ta ce"a to kun kawo magana mai kyau,dama nayi wannan shawarar saboda ma nasan iyayen naku da shegen son ƴaƴa sai naja bakina nayi shiru,na barku dasu don yanzu sai kaga ƴar shigowar da ake gaisheni aƙi zuwa,yo ni naso haka? tunda iyayenku mata na haɗani da ƴaƴana ya zanyi ne wai"?.
sai ta fashe da kuka sosai harda majina,tamkar wacce aka daka haka tayi ta kuka autar momma ta ce"yo mu kuma sai ki dinga ɗorawa iyayenmu,muma fa da kika ganmu duk muna sonsu muma bazamu rarrasheki ba kyayi kya gama".
jakadiyar gwaggwala ta tuntsire da dariya,ai kuwa gwaggwala ta ce"yimin shiru me haƙora biyu,idan da kinsan munin da wannan wangagamemen wawulon bakin naki yake idan kina dariya ai da kin dena".
Baki ɗayansu muka sanya dariya,gwaggwala ta jefa musu wani mafici irin na gidan sarauta wanda ake saƙasa da gashin ɗawisu dana jimana.
sai da sukayi raharsu sosai sai ga Galadima ya shigo,fuskarnan tamkar an baɗa masa garin kunu saboda haɗeta da yayi da sauri autar momma da bestinta Amira suka tashi tamkar sunga namijin jimina.
me kuwa gwaggwala za tayi,dariya ta dinga ɓaɓɓakawa ta ce"ƴan jar uba kawai wa yace muku barni gabas take,da kun tsaya kuna raimin wayo".
gaisheta yayi sannan ya samu waje ya zauna,yana ɗan huci yana goge gumin da ya jiƙa masa fuska,tamkar wanda yayi tsallen rastling.
suna fitowa suka fara leƙawa ta window don suji me zai faru tsakanin zaki galadima da kuma gwaggwala,musamman ma Amira da ta dinga murmushi don tasan gwaggwala dole za tayi masa maganar.
jakadiya ta kawo masa tuffa da sauran kayan marmari,don kusan mutanen dake cikin gidan sun sansa da mugun son kayan marmari.
ya ɗauki tuffa,yana yiwa jakadiya godiya da yake mutuniyarsa ce,kusan itace ma tayi rainonsa ita da gwaggwala don itaca ma ta yayesa.
yana shan tuffa ɗin zaƙinta na karaɗe sashen jikinsa da ruhinsa,ya lumshe lumtsatstsun idanuwansa masu kama dana mage,yana tuno da yaran dake gidan marayu yawancinsu abin tausayi ne su,saboda babu wani me kula dasu tunda iyayensu suka zo suka ajjesu sai suka tsintsayen ƙafafuwansu suka dena koda leƙosu,aduk sanda zaici abinci sai ya tuno da waɗanda ba suda gata,sai yaji dama duk marasa gatan duniya zai iya yaye musu dukkanin labulen talaucin daya nannaɗesu.
yana cikin tunanin muryar gwaggwala ta dawo dashi daga nannauyen tunanin daya fara yanzu.
Galla masa harara tayi sannan ta ce"ji wata masifa don Allah,?Yaro ɗanye da kai me shekara talatin dai dai,shine don tsabar ɗaurawa kai wahala ka zauna kana tunani? tukunna ma tunanin me kake har haka"?.
Kallon nan nasa yayi mata,wanda mutane da dama ba gwaggwala ba suke ganin cewa ai rainin hankali ne ,amman ku kusa ba haka bane tsabad gadon jinin sarautar da yayi ne ya kawo hakan,don tun yana yaronsa kakansa ke tsokanarsa da namijin jimina ƙoƙarin kallon ƙasa garesa.
sai kuwa gwaggwala ta zabura tana buɗo ido ta ce"inye don ƙaniyarka ni kakewa wannan kallon?yo an gaya maka nima irin ƴammatanka ne turawa daka bari acan garin daka baro? masu ɗan ɓingi ɓingin siketi? to maza ka tuna agaban gwaggwala kake".
murmushi yayi don yasan daman indai yazo wajenta sai yayi dariya.
yaɗan murmusa sannan ya ce"uhm".
daga haka bai ƙara cewa komi ba,sai kuwa ta kalleshi ta taɓe baki sannan ta ce"uhm ai ni matarka nake tausayawa wallahi,saboda ta auri miskilin namiji,kayita gana mata azaba".
yanzun ma bai ce da ita ƙala ba,sai kuwa ta ce"yauwa dama magana nakeso muyi da kai,dama da bakaxo ba zanje har fadar baban naka,magana ce akan aurenka dama".
da sauri ya wani waro ido tamkar yaga abin tsoro.............
*** *** ***
ko da Aamiru ya shigo Babbar masarauta ya kasa tsaye ya kasa xaune,ya rasa wani irin tunani ma zaiyi daya ha kamar haka bazai alfana masa komi ba sai ya wuce sashen Fulani wato mahaifiyar Galadima.....Soon➡️
***
N6TlUzv4BA
ga grp na faccala fans,ga masu son yin joining,bana son talla da tiromin iskancin banza,bana son maza a grp ɗin idan ka shiga ma zan gano ka in cire ka.
Share
comments🙏🏻
*MRS GRERN CE✅*