chapter 5-6
by @ummuaffan
_Gawurtattu uku 2024_
WANKA DA GARI...
_Ummu Affan_
*Book 1 Page 5-6*
Zuwa yanzu su Sakinaa sun kammala ƙaramar Secondary ɗin su, wato JSCE har sun shiga SS1. Ba laifi sun yi girma sun zama 'yan mata amma ba can ba, ba laifi Sakinaa kyakkyawa ce wankan tarwaɗa. Tana da ɗan jiki kaɗan, doguwa amma ba tsowo sosai ba sai dai Allah ya hore mata mazaunai sosai. Sannan tana da cikar ƙirji ga ƙoƙari a makaranta Allah ya ba ta ƙyanwa mai saurin ɗaukar karatu, domin ita ke amsar na farko a ajinsu, iyayenta suna alfahari da ita domin saboda natsuwarta da kamun kai da biyayyarta zuwa lokacin shaƙuwa mai gauraye da wani babban al'amarin da ƙarancin shekarunta ya hanata ganowa shi ke wakana tsakaninta da Hammanta Faruuƙ, shi tabbas yasan yana ƙaunar Sakinaa sai dai ita kawai ta ɗauka shaƙuwa ce a tsakaninsu.
Suna hanyarsu ta dawo daga makaranta, tafiya suke irin ta 'yan makarantar da aka ta so su ƙarfe biyun rana, ga yunwa sannan ga galabaita yadda rana ke dukansu.
Zaliha ta dubi Sakinaa ta ce, "Wai Sakinaa in tambaye ki mana, ya ku ke da Hamma Umar ne?" Sakinaa ta taɓe baki.
"Yadda na sanar miki ko baki yarda ba ne?"
"A'a kawai na gan shi kyakkyawa kuma ɗan gayu a mota fa yake zuwa duk idan zai zo gidanku."
"Ke dai baki gani ki kyale komai sai kinyi magana, kina ɗaya daga cikin sa'idinawa ana ruwa kuna irgawa."
Dariya Zaliha tayi, "Na fiki ne? Na zata duk ɗaya muke tunda sai hali yazo guda ake ƙawance."
Sakinaa tayi murmushi.
"Uhmm ke dai Zaliha ba dai iya zance ba, ni nan wallahi na ƙosa mu kai gida duk na gaji yasin." Zaliha ta ce, "Ke dai bari kawai ga shi ana rana yau sosai."
Haka suke tafe har suka kai gidajensu suka wa juna sallama.
Sakinaa na shiga ta iske Hamma Umar yazo, daman tun a waje ta ga motarsa, da murna ta ƙarasa da sallama. "Oyoyo Hamma Umar." "Oyoyo Princess kin dawo?"
"Na dawo Hammana."
Gabaɗaya su ka yi murmushi.
Ɗakinta ta wuce ta cire Uniform taja ruwa ta watsa sannan tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta fito cikin wata doguwar riga ta shadda. Umma da Hamma Umar suna zaune suna hira ta ƙaraso.
"Umma sannu da gida." Ta amsa da, "Yawwa." kitchen ta wuce don ɗauko abincinta, me zata ga ni Fate ne, ɓata rai tayi don duk a cikin abinci fate ne ba ta so
Dawowa tayi tana ƙunƙunai da cin magani. Umma ta kalle ta. "Lafiya me ya faru?" Turo baki tayi gaba. "Umma fate ne fa kika yi."
"I na sani ai, ni nayi ko?" Nan ta fara hawaye. "Amma Umma kina sa ne ban shan fate ko?"
Umma ta ce, "Hmmm shagaɓa wai tarwaɗa da kukan ƙishin ruwa, ni dai yau shi nake marmarin sha haka ma Abbanki ga Hammaki ma nan yanzu ya gama sha yana santi." Da sauri ta ce, "Faten?"
"Ƙwarai kuwa, shi Faten ba abinci ba ne?"
"Ni dai Umma ki ba ni abinda zan ci yunwa nake ji."
"Sai kuma kiyi ai, don ni ba ni da komai sai ki jira na dare."
Zubewa Sakinaa tayi tana riƙe ciki tana cewa, "Wayyo cikina yunwa nake ji Umma za ta kashe ni, ta hana ni abinci . Abbana wayyo Abbana kazo.''
Mai Hamma Faruuƙ zai yi ba dariya ba, har da tafa hannu Umma miƙewa tayi,
"Sai kiyi ta yi, fate ne idan ba za kisha ba sai kiyi ta zama da yunwarki." Nan fa taci gaba da kururuwa tana burgima.
Hamma Faruuƙ ya ce cikin dariya.
"Wai Princess mene ne hakan? Da girmanki ki ke haka?" Kallon shi tayi cikin hawaye ta ce, "Hamma Faruuƙ Umma fa na sa ne ba na sha shi ne tayi."
"To yanzun ya ki ke so ayi?"
"Kawai ni dai yunwa nake ji, kuma bazan iya kai wa har sai na dare ba."
Miƙewa tayi bari inje gurin Abbana na san zai saya mini abu naci.
Shi ma miƙewa ya yi
"A'a kar ki wahalar da Abba muje na saya miki." Da sauri ta ruga ɗaki cikin murna ta ɗauko hijab taje ta yi wa Umma sallama.
"Allah ya so ki yau Alhamis babu islamiyya da ba inda zaki je." Fita tayi kawai tana murna.
Buɗ mata motar ya yi ta shiga wani ƙamshin daɗi ya bugi hancinta sai da ta lumshe ido, shiga ya yi ya mata key suka tafi, ƙira'ar malam Ahmad Sulaiman na tashi lumshe ido tayi cikin wani sabon yanayi turaren Hamma Faruuƙ na mata daɗi sosai wanda B for B gidan ƙamshi ke haɗa masa. (Turarenta ƙarshe ne domin wallahi ni Ummu Affan na gyada yana kama jiki sosai shi ne turaren da Hamma Faruuƙ ke sakawa, mai buƙatarsa ya tambaye ni zan haɗa shi da B&B gidan ƙamshi.)
Kai tsaye gidansu ya wuce da ita, daman tun a hanya ya kira Mum ya sanar mata suna hanya, 'yar ƙauye Sakinaa ta zama lokacin da suka shiga katafaran gidan su Hamma Faruuƙ, kalle-kalle kawai take, ai hankalinta bai tashi ba sai da suka shiga Parloun gidan, gabanta ya din ga bugawa a ranta ta aiyana ko dai Hamma Faruuƙ sayar da ita yake son yi? Nan fa idanuwanta su kai rau-rau ta kalle shi.
"Hamma Faruuƙ don Allah kayi haƙuri kar ka sayar da ni ka ga ni ɗaya su Umma suka haifa kayi mini rai don Allah."
Dariya ma taba shi kallonta ya yi.
"Ko da ina sayar da mutane Sakinaa bazan taɓa iya sayar da ke ba, ki sa a ranki komi wuya Umar ba zai taɓa cutar da Sakinaa ba." Ajiyar zuciya tayi tana kallonsa, murmushi ya mata ita ma ta mayar masa.
Sama ya wuce, sai gashi suna sakkowa da Mum, nan hankalin Sakinaa ya sake kwanciya ta duƙa har ƙasa tana gaishe ta da sauri Mum ta ɗagota ta rungumeta.
"Kul Sakinaa ta so kin ji 'yata."
Cike da kunya Sakinaa ta gaisheta.
Mum ta ce, "Ya su Ummanki da Abbanki?"
"Suna lafiya ƙalau." Nan ta kira mai aikinta aka cikawa Sakinaa gabanta da abinci da nasha kala-kala, ƙasa tayi da kai cike da kunya, Mum ta ce, "Ki saki jikinki Sakinaa nan gidanku ne ki ɗauke ni tamkar Ummanki."
Ita dai Sakinaa ta kasa cewa komai don sosai take kunyar Mum, ganin haka Mum da kanta ta zubawa Sakinaa komai ta ce taci, miƙewa tayi zata wuce don Sakinaa ta samu taci wani abu Hamma Faruuƙ ya ce, "Kai Mum ni shi ke nan an man ce da ni, ko tayi ba ki yi mini ba?" Da sauri ta zauna kusa da shi. "Sorry my Son me ka ke so?" Ya ce "Abinda ki ka ba ta." Yana nuna Sakinaa da baki, nan ta haɗa masa tana ba shi a baki, ai sakin baki Sakinaa tayi tana kallonsu, a ranta take ai yana daman haka Hamma Faruuƙ ya ke. Ganin kallon da take musu yasa ya ɗaga mata gira tare da kanne mata ido ɗaya, sannan ya nuna mata gabanta, alamar tayi abinda ke gabanta, murmushi tayi ta fara cin abincin a hankali.
Ba wani sosai taci ba domin daman ba iya cin abinci da yawa tayi ba, turo ƙofar da a ka yi yasa hankalinsu ya koma can, wata budurwa ce ta shugo kyakkyawa zatayi 25 sanye take cikin riga da wando matsatstsu sun kamata sosai sai wani ƙaramin mayafi da ta ɗaura a kanta babu kallabi a kanta hakan yasa kyakkyawan gashin kanta ya bayyana, siririya ce irin sosai ɗin nan, baka iya ganin idanuwanta sakamakon ƙaton baƙin gilashin da ya kusan rufe rabin fuskarta, ta kalmin ƙafarta dogo ne sosai, hannunta mai ɗaure da ɗan siririn agwogwo da shi ta ke jan akwatinta.
Mum ta miƙe da sauri tare da kiran sunanta, "Zubaidaa!" Murmushi tayi tare da nufar Hamma Faruuƙ ta rungume shi, tureta ya yi daga jikinsa yana cewa "Haba ZubaidaA meme ne hakan?" Murmushi tayi ta ce, "Hamma Umar har yanzun ka na nan da halinka?" Taɓe baki ya yi, "To mai za a fasa mutuwar ko hisabin." Juyawa tayi ta rungumi Mum ta ce, "Nayi missing ɗinki my Mum." Murmushi tayi, "Nima nayi naki 'yata, ya ki ka baro su Hajiya Sakinar?"
"Suna lafiya ƙalau suna gaishe ku sosai."
Umar kallon Sakinaa ya yi wacce ta saki baki tana kallon ikon Allah "Princess tashi in mayar da ke gida kar Umma ta ji mu shuru." Da sauri ta miƙe.
Zubaida ko cikin ruɗu ta juyo cike da kishi jin My Hamma Umar ɗinta ya kira wata da Princess. Kallon Sakinaa tayi nan take taji ta tsaneta kai duk wata mace dake raɓar mata Umar ta tsane ta, tsana mafi muni da munana.
Sakinaa ta katse mata tunani da furta, "Mum zamu wuce na gode sosai." Murmushi Mum tayi, "Mene ne na godiya? Nan fa kema gidanku ne ina zuwa." Sama ta wuce sai gata da wata babbar leda tabawa Sakinaa, girgixa kai tayi "A'a Mum na gode." Ɓata fuska tayi "mene ne hakan Sakinaa? Kema fa 'yata ce kuma babu kyau mayar da hannun kyauta." Hamma Umar ne ya amshi ledar ya ce, "Rabu da ita Mum dole ne ta amsa." Ƙasa tayi da kai ta duka har ƙasa tana wa Mum godiya.
Ɗagota tayi ta ce, "Lalala babu godiya tsakaninmu, don uwa ta bawa 'yarta abu sai ta ce sai ta gode ki gaishe mini da Ummanki da kyau idan na sami lokaci ina nan zuwa."
"To Mum za taji na gode." Har ƙofa Mum ta raka su sannan ta juyo.
Zubaida da ta kusan sumewa a tsaye nan take ta fara hawaye.
"Mum mece ce wannan? meke shirin faruwa haka? Me ki ke so ki ce mini? Don Allah kar dai ki ce wannan Ƙwailar yarinyar budurwar My Faruuq ce? Zaunar da Zubaidaa Mum tayi Kafin ta ce "Ki kwantar da hankalinki ba budurwarsa ba ce asali ma ƙanwa ya ɗauketa. Nan ta sanar mata yadda suka haɗu.
Tuni idanuwanta suka kaɗa jawul. Ta ce, "Matsiyata ne fa, kuma talakawa fa Mum me yasa Faruuƙ ya cika kwashe-kwashe? Duk yadda aka yarinyar nan sonta yake kuma wallahi ba zai sameta ba, nice zai aura ba wata ba." Fuu! ta tashi tayi ciki.
Mum tsaki taja Zubaidaa har yanzun ba ta da hankali, wallahi bayan wasiya aka bari akan auransu, da babu dalilin da za ta yadda ɗanta ya auri wannan ballagazar yarinyar, sam ba ta da natsuwa da kamun kai, me ake da me irin halin Zubaidaa gashi shi kansa Faruuƙ baya son Zubaidaa, ita dai bata san yadda za a yi wannan cakwakiyar ba.
Bayan ya sauketa bai samu shiga ba saboda sallah da ake kira masallaci ya wuce ita kuma Sakinaa ta shiga gida, Umma alwala take don haka ita ma alwalar tayi bayan sun idar da sallar, ta nuna mata kayan da Mum ta bata, da saƙonta na gaisuwa. "Shi ne daga baki abu ki ka karɓo?"
"Wallahi sai da na ce ta bar shi taƙi shi ne Hamma Umar ya amso." Umma ba ta kuma cewa komi ba.
Bayan isha'i tare suka shugo da Abba, nan Umma ta nuna masa kayan sukayi wa Umar godiya ya ce, "Haba dai sai ka ce wani abu don Allah ku daina mini godiya mun riga fa mun zama ɗaya, jini ɗaya kuma dangin juna."
Sosai ake daru a gidansu Umar akan auransa da Zubaidaa ya ce Shi ba ya son ta, nan fa iyaye aka haɗ daman Familynsu yawa ne dasu,(Akwai tarihi a gaba kaɗan.) Yayun Dad ɗin shi suka ce wallahi bai isa ba mahaifinsu ne yabar wasiya kuma daman can su auran zuminci su ke, kowa da abinda yake cewa Dad ya dun ga rarrashinsa akan ya amince.
Ya ce, "Zan amince Dad amma sai dai idan za a ba ni Sakinaa domin ban taɓa son wata mace a duniyata ba irin Sakinaa wallahi ina ƙaunarta please Dad ka naimar mini auranta, ni dai burina a ba ni ita ko da ba yanzu za a yi auren ba."
Haka Dad yasa mi Malam Abdullahi da maganar, murmushi ya yi ya ce, "Ummaru yaron ƙyirki ne ni kaina zan so haɗa zuria da shi domin a kwai yaro mai kamala ta ko ina, ni na ba shi Sakinaa kuma na san ita ma za ta so shi duba da shaƙuwar da take tsakaninsu, amma ina so ya yi haƙuri har ta kammala Secondary sai ayi auren don haka kar ya da mu yanzu ya auri 'yar uwarsa." Nan fa Dad da Yayunsa suka yi ta godiya.
Murna da farin ciki gurin Umar kamar me, nan aka fara shirin aurensa da Zubaidaa
Yanzun su Sakinaa sun shiga ss2, kamar kullum suna haryar dawowa gida ita da Zaliha za su tsallaka titi kenan, wata mota ta rugo a guje sauran kaɗan tabi takansu saboda tsabar tsoro rungume junansu su kayi gabansu na bugawa, jin anja wani wawan burki suka dago a gigice, shi kuwa da ke cikin motar da sauri ya wani fito cikin masifa ya ce, "Ku waɗanne irin wawanyen yara ne? Wallahi da na bige ku na buge banza babu abinda za a yi, kuna tafe ba ku kallon gaban daƙiƙan yara kawai....
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakinaa