chapter 7-8
by @ummuaffan
_Gawurtattu uku 2014_
WANKA DA GARI...
©UmmuAffan
*Book 1 Page 7-8*
Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba! Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT ***
Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka *** Tana Bauchi tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.
*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa ko wanne da farashinsa. Na gode.
...Cikin tsananin fusata Sakinaa ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido kuwa, da tsiwa ta ce, "Aikin banza taka wuƙar zakara kawai, kai da ka ke tuƙin kai baka kallon masu tsallakawa ne, ko kai makaho ne? Ko kuwa titin naka ne? Wallahi da ka bige mu ba ka bige banza sai an ɗaukar mana mataki, da har zaka fito kana wata fafarka ta banza."
Ido kawai ya zuba mata zuciyarsa na harbawa, lokaci ɗaya yaji yarinyar ta tafi da imaninsa, ganin taja hannun Zaliha za su wuce ya sa shi yin saurin shan gabansu.
Idanuwansa akan Sakinaa ya ce, "Kuyi haƙuri ban san ku ɗin na musamman ba ne. Tabbas na gane laifina ne amma hakan ba zai kuma faruwa ba."
Wata muguwar harara ta ban ka masa, Kafin a matsagaitan mintoci ta ƙare ma sa kallo, fari ne yana da tsayi kaɗan ba za a kira shi dogo ba amma shi ba gajere ba ne tsaka tsakiya, yana da baƙar suma a kan sa ya yi askin nan irin na samari 'yan kwallo an aske gefe sannan an bar wata cinkum a tsakiya, ba laifi shima yana da kyau daidai misali, sai dai leɓensa sun yi duhu alamar yana shan sigari. Shadda ce a jikinsa ɗinkin da samari ke yayi, cikin mintuna biyu Sakinaa ta ƙare ma sa wannan kallon
Taɓe baki tayi domin ko kwatar Hamma Umar ɗinta bai kai ba, sannan ita fa a rayuwarta bata wani ƙaunar farin namiji sosai, duk da take da duhu tafi son baƙin namiji ko wankan tarwaɗa, sake magana ya yi a karo na biyu.
"Please ku zo na rage muku hanya na ga ranar nan kamar tana damunku." Sakinaa tayi saurin cewa.
"Muka sanar maka? Ka ga malam don Allah ja ƙafarka ka ba mu guri, ba ma gayyar soɗi." Ta ƙarasasa maganar tare da murguɗa ma sa ƙaramin bakinta, bin bakin ya yi da kallo cike da sha'awa don shi yana son mace me tsiwa haka nan daga kallo ɗaya da ya yi wa Sakinaa yaji duk duniyar nan baya da abin so sama da ita, wata irin kaunarta ke fuzgarsa.
Yadda yake kallon Sakinaa haka Zaliha ke kallonsa, domin kallo ɗaya ta ma sa taji ya tafi da duka zuciyarta, ba ta taɓa soyayya ba, hasalima dukansu biyun ba su da samari, tana kallon gayen nan taji ya mata kuma zata iya aurensa.
Sakinaa taja hannunta, "Kin ga Zaliha zo mu wuce wannan ba shi da aikin yi." Riƙe hannunta Zaliha tayi gam alamar ta tsaya, kallonta tayi cike da mamaki ta ce, "Haba Sakinaa ya gane kuskuransa ya ba mu haƙuri don Allah mu hakura mana kin ga rana ta ishe mu tunda ya ce zai rage mana hanya don Allah kizo mu shiga, tunda babu ƙyau mayar da hannun ƙyauta.'' Da sauri ya ce, "Yawwa ƙanwata na gode gaskiya kina da saukin kai kin burge ni." Murmushi tayi tare da far da ido, cikon iyayi ta ce "Nima na gode."
Ba domin Sakinaa taso ba haka suka shiga motar. Zaliha ce gidan gaba Sakinaa daman baya ta shige, ba haka ya so ba amma ba shi da yadda zai yi. Sun fara tafiya ya kalli Zaliha tare da kallon Sakinaa ta madubi da ke kallon hanya, murmushi ya yi yarinyar na burgesa.
"Sunana Mubarak Sani Gata. Kuma yana da kyau naji sunanku."
Zaliha tayi fari da ido ta ce, "Wow nice name."
"Na gode ƙanwata.''
"Ni suna na Zaliha Shehu ƙawata sunanta Sakinaa Abdullahi."
"Da kyau, manyan sunaye masu daraja." "Mun gode." Zaliha ta furta. Tambayar da ya yi unguwarsu ta sanar ma sa suka kama hanya.
Daidai ƙofar gidansu Sakinaa ya yi parking yana tsayawa ta fice da sauri ta shige gida Zaliha da Mubarak suka fito ta ce, "Am kayi haƙuri wallahi ƙawar tawa ni kaɗai nasan kanta." Murmushi ya yi.
"Kar ki da mu ai ƙawar taki mai tsada ce." Baban Zaliha ya buga addu'a take kar Allah yasa Mubarak ya ce Sakinaa yake so sai ita amma sai ji tayi yana cewa "Wallahi Zulaihat kallo ɗaya nayi wa ƙawarki naji duk duniya ba wacce nake so sama da ita, don Allah ki taya ni neman soyayyar ƙawarki."
Ƙirjin Zaliha babu abinda yake sai bugawa, yana ba da wani irin sauti mai ƙara, murmushin yaƙe tayi, "Kar ka da mu Mubarak, sai dai Sakinaar ce a kwai tsiwa, amma zan taya ka in sha Allahu."
"Yawwa ƙawarmu na gode sosai. Nan ne gidanku duka?"
"A'a nan gidansu Sakinaa ne." Da hannu ta nuna ma sa nasu gidany.
"Ok na gode sosai Zulaihat."
"Babu komai." Kuɗi ya bata taƙi amsa, ganin ya dage ta amsa sannan suka yi sallama ya wuce, bin motarsa tayi da kallo, daga bisa ni ta wuce gidansu jikinta a matuƙar sanyaye.
Suna zaune take sanar da Sakinaa duk abinda ya faru, tsaki taja ta ce, "Yana son wa? Wai ni?" Gyaɗa kai Zaliha tayi alamar
"I."
"Hmmm idan ma ni ce gara ya yi haƙuri domin ni ba aure ba ne a gabana, hasalima karatu zan yi yanzun nake ss2 ban kammala Secondary ba balle naje jami'a. Don haka ya je ya nemi wata, kin ga Abbana ma ya mini faɗan kar na kula kowa haka Hamma Umar ya ce kar na kula kowa nasa karatuna a gaba don haka sai ki ba shiaɗ haƙuri, ke nifa ma mutumin nan bai mini ba wallahi tunda na kallesa na san baya cikin tsarina, fuska kamar jan ƙosai, kin san fararen maza ba sa cikin jadawalina." Ota dai Zaliha ba ta ce komai ba sai bin ta da ido take.
Yana parking a babban harabar gidan ya fito da sauri A Parlour ya iske Hajiyarsa da ƙannansa, jikin Hajiyar ya faɗa yana sauke a jiyar zuciya. Sannu kawai take ma sa tana shafa kansa, Ƙannansa suka ma sa sannu.
Hajiya ta ce, "Mubarak lafiya yau na gan ka wani iri haka?" Sumar kan sa ya shafa tare da fesar da huci mai ɗumi ya ce, "Hajiya yau na samar miki surika." Shewa ta zuba haka sauran ƙannansa Safah da Marwah sai Laurah.
Tuni suka dawo jikinsa Hajiya ta ce,
"Wannan wacce mai sa'ar ce ta sami santalelan yarona ɗan zamani son kowa ƙin wanda ya rasa, sannan ɗan Hajiya?" Yaƙe ya yi ya ce, "Uhmm Hajiya yarinyar fa na lura ba ta sona ni ne kawai ke haukana, kuma wallahi idan na rasata daidai yake da rasa numfashina." A harzuƙe ta ce, "Wace ce wannan? Wane ne ubanta a garin nan? Da har za ta ce ba ta sonka?
Uban waye ubanta a ƙasar nan da har zata ce ɗana son kowa ga kuma kwalisa dukiya mulki ga uwa uba kyawu." Larah ta ce, "Kai Hajiyarmu duk irin wannan washi haka, shi so fa ba ruwansa da kyawu ko kuɗi da sauransu." Harara Hajiya ta zuba mata ta ce, "Matan zamanin nan me suke so idan ba kyakkyawan saurayi mai 'ya'yan banki bugun Abuja ba?"
Mubarak ya ce, "Duk ba wannan maganar ba, ni dai Hajiya a nemo mini soyayyar Sakinaa kawai nake buƙata, kuma ko ta halin ƙaƙa ne."
"Ta ya?" Larah ta tambaya.
Hajiya ta ce, "Larah ko ta halin ƙaƙa ne ina ruwanki wai? Tashi ki bar gurin nan domin duk a yarana ke ce ki ka banbanta da sauran, sai ka ce ba ni ce uwarki ba. Ni Hajiya Amina naci dubu sai ceto."
Miƙewa ta yi, "Shi ke nan bari in ba ku guri, amma ina son ku sani shi so na gaskiya ba ruwansa da kuɗi ko ilmin, mutum da kyawunsa Allah yana da sa so ne a duk zuciyar wanda ya yi niyya." Tana gama wa tayi wucewarta suka bita da tsaki Hajiya kallon ɗan nata tayi mafi soyuwa a zuciyarta wato Mubarak ta ce, "Yarona faɗa mini sunan ubanta a faɗin ƙasar nan ko 'yar wace ce dole ta so ka, kai ko da shugaban gasa ne ubanta kuwa."
Kallon Hajiyar tasa ya yi wacce a saninsa ta tsani talaka kowa ye, bata hurɗa da ƙananun mutane ya ce, "Hajiyata Sakinaa ba kowa ba ne ubanta, hasalima yarinya ce ƙarama bata wace 16years ba, ba kowa ba ne ubanta sai matalauci, sai dai ina son ki san wani abu guda, idan ban same ta ba wallahi mutuwa zan yi."
Kallon ɗan nata tayi cikin so da kauna, wannan wacce irin jarabawa ce ɗan ta zai kamu da son 'yar matsiyata? Amma ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta ce, "tashi muje gidan." haka ta tasa shi a gaba har ƙofar gidan a tsiya ce ta kalli gidan ita unguwarma sam bata mata ba,
"Yanzu Mubarak ka rasa gidan da zaka ɗauko aure sai a unguwar matsiyata, don Allah kabar wannan maganar 'yar wannan akurkin gidan za ka ce kana so? Gabaɗaya yankin nan bai mini ba."
Ya ce"Hajiya kina so ki ra sani ko? To ina son ki sani 'yar wannan akulkin gidan ce farincikin ɗan ki, tunda dai wanka da gari ba shi maganin yunwa sai an sha." Numfashi taja cike da ƙyanƙamin layin.
Fita tayi ta nufi cikin gidan, Umma na zaune kan kujera 'yar tsugunnau tana firfita wutar itace a mirhu. Sakinaa kuwa ta fito kenan cikin shirin islamiyya Abba yana gareji.
Ko sallama Hajiya ba ta yi ba, sosai suka tsorata. Umma har da salati, kallonta Hajiyar tayi cike da kyama ta ce, "Gurin Sakinaa nazo." Daga Sakinaar har Umma ido suka zuba mata cike da mamaki, duk a zatonsu ba musulma ba ce jin ba tayi sallama ba, kuma ko hijabi ko gyale babu a jikinta kuma sai su kaji tayi hausa.
Cike da takaici Umma ta ce, "Malama lafiya gidan musulmai fa ki ka shugo." Harara Hajiya ta ban ka mata ta ce, "Ai ina sane sallamar ce bata da ce da na muku ba, domin baku isa ba shi ya sa."
Kallonta suka ci gaba da yi ta sake cewa tambayar Sakinaaa tazo nema. Ganin kallon da Umma take aika wa yarinyar da ke tsaye a gurin yasa Hajiya ta ga ne ita ce Sakinaa, kama hannuwanta Hajiya tayi suka fita waje, Umma kuwa saboda mamaki kasa cewa uffan tayi sai raka su da ido.
Hajiya ba ta tsaya da Sakinaa ko ina ba sai bakin mota. Mubarak na ganinsu ya fito yana washe baki, tana ganinsa gabanta ya buga da ƙarfi har lokacin Hajiya bata saki hannun Sakinaa ba. Mubarak zubawa Sakinaa ido ya yi ita ma ta zuba ma sa ido.
Yayin da Hajiya ke ta wasu 'yan surkullenta da hannun Sakinaa lokaci guda, Sakinaa taji kan ta ya mata wani nauyi lunshe idanuwanta ta fara zuwa wani lokaci tayi luuuw zata faɗi da sauri Mubarak ya ruƙota jikinsa. Hajiya ta ce, "Aiki ya yi kyau shi ya sa nace maka ko ɗiyar shugaban ƙasa ka ke so zaka samu in dai ni ce uwarka." Murmushin farin ciki ya yi ya ce, "Shi ya sa nake ƙaunarki Hajiyata, tsafinki yana aiki kobme nake so kina mini gaskiya naji daɗon gadon nan da kika yi na mahaifinki." Murmushi kawai tayi ta dafa saitin zuciyar Sakinaa wajen minti biyu sannan ta dafa saitin zuciyar Mubarak. Dariya su ka yi gabaɗaya sannan ta bubbuga jikin Sakinaa nan take ta farko zata kurma ihu Mubarak ya yi saurin ɗaura hannunsa saman leɓenta, nan take tayi shuru sai ta zuba musu ido.
Hajiya ta ce, "Sakinaa ina son ki shiga cikin zuriata hakan ba zai samu ba sai kin amince da auren ɗana Mubarak ko me ki ke so za muyi miki abinda ma yafi wanda iyayenki ke miki."
Shuru tayi tana kallonsu gabanta ya tsananta bugawa. Mubarak ya ce"Ina ƙaunarki Sakinaa kema kina so na?" A hankali ta buɗe baki za tayi magana sai suka jiyo muryar Zaliha na kiran Sakinaa.
Daidai ƙarasowar Zaliha Sakinaa ta buɗe baki ta ce.
Ta ce, "Ina sonka nima kuma zan aure ka." Hajiya da Mubarak suka kalli juna su kai murmushi. Zaliha kuwa dafe ƙirji tayi tana kallon Sakinaa kafin ta ce "Sakinaa lafiyarki kuwa?"
Kallonta Hajiya tayi ta ce, "Wace ce ke?" Cikin rawar murya ta ce "Ni ƙawarta ce." Hajiya zatayi maganantu sai ga Abba shi da Hamma Umar gurin, suka ƙara so har da Umma, wacce jin Sakinaa shuru ta fito domin ta ga ko lafiya.
Abba ya ce, "Sakinaa Zaliha me ku ke a nan?" Shuru dukansu su ka yi suna kallon-kallo, a nan Umma ta sanar masa abinda ya faru, cike da mamaki ya kalli Hajiya kafin ya kalli Sakinaa ya ce, "Zo ki wuce." Kasa ɗaga ƙafarta tayi tana son bin umarnin Abbanta amma ta kasa.
Murmushi Hajiya tayi ta ce, "Kai malam ka ke kowa, to bari kaji ɗana ne gashi nan Sunansa Mubarak, ta nuna sa taci gaba da cewa "shi ne ke son 'yar ka bayan ma ya nace me za mu yi da 'yarka yana sonta kuma cikin satin nan nake son a ɗaura musu aure."
Cike da tashin hankali suka bita da kallo Abba zai yi magana Hamma Umar ya ce, "Wannan wanne irin hauka kike, ke kuwa matar nan kina da cikakken hankali da tunani? A wanne garin mahaukatan ake haka?" Abba ya ce, "Gaskiya da dai sauƙi Ummaru, to ina son ki sani bazan ba ɗanki 'yata ba domin daga ke har ɗan naki ban ga kuna da alamun tarbiyya ba, ke barama kiji me kankat nawa 'yata miji lokaci kawai nake jira a ɗaura mata aure."
Sakinaa ce ta kalli mahaifinta a rikice ta ce, "Ka ba da ni kuma Abba? Ni dai ban so wannan nake so." Ta nuna Mubarak daga Abba Umma Hamma Umar Zaliha ido suka kyalalo suna kallonta.
Hajiya da Mubarak kuwa murmushi suka yi, Hajiya ba ta ce komai ba ta kama hannun Mubarak suka koma mota, bayan sun shiga Mubarak ya ce, "Hajiya ya na ga haka?" ta ce "kai dai ja mota mu tafi Sakinaa da kan ta zata nemeka."
"Amma ban sanar da ita inda nake ba."
"Kai dai muje gobe zaka dawo....
***
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina