AZAAD JUNAID

003

by @jeeddah3256

*AZAAD JUNAID*

(The Young Billionaire)

SECOND EDITION.

Na

JEEDDAH ALIYU

     

  003. 


Amrah na fita bata zarce a ko'ina ba sai wani ƙaramin super market, kamar za tayi siyayya sai da taga hankali mutane baya kanta. Ta dinga tsintar biscuits da Madara na sachet tana cusawa cikin zaninta ta fice da mugun sauri batare da ta bari mai shagon ya ganta ba. Gudun kada a ganota da fitarta ta kwasa da gudun bala'in ta nufi gida, cikin sa'a babu kowa a tsakar gida tai wuff! Ta shige ɗakinsu kamar wacce aka jefo. Daga Aslamiyya har Amal sai da suka firgita domin a zatonsu ko Dadda ce.

Kallo ɗaya za ka yiwa Amrah ka gane bata da gaskiya sai wuƙi-wuƙi take da idanuwa kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin ɗakin. Ta cire hijab ɗin jikinta tare da kayan da ta sato ta ajiye ta ɗauki wani tsohon kofin silver wanda tun na aure mahaifiyarsu ne bata ce dasu uffan ba ta fita gindin famfo ta taro ruwa rabin kofi. Koda ta dawo ɗakin Aslamiyya tana jujjuya biscuits ɗin da madara.

"Ga ruwa ki kaɗawa Amal madara ta haɗa da biscuit ko da na koma wajen mai koko ya ƙare shine na siyo mana madara da biscuits sai dai na manta ban siyo sugar ba. Sai da na iso ƙofar gida na tuno.

Tana magana manyan idanuwan Aslamiyya suna kanta sai da ta sauke ɓoyayyen numfashi kafin tace

"Ina kika sami kuɗi Amrah?" Iya sanina naira hamsi muke dashi kin Kuma ri ga da kin siyo koko ya zube"

"Ke ɗai miyya kidinga kyautata minzato Abban Saleem ne ya bani kuɗin wankau da nayi musu na kwanaki, da basu biya ni ba. To shine Ina dawowa daga siye koko na haɗu shi a ƙofar gidansa ya bani"

"Amrah!"

"Miyya!"

Amrah ta kira sunanta kaman yadda Aslamiyya ta kira ta, har tana haɗawa da turo baki.

"Amrah idanuwanki sun nuna min akawai rashin gaskiya da kika yi faɗamin me kika aikata?"

"En! Na tuna da zan shigo na haɗu da Baffa Sani ƙofar gida  nai kaman ban gannshi ba  shine yaso ya dake ni dalili da yasa na shigo da gudu kenan baya ga wannan ban yi komi ba.

"Ya yi miki kyau Amrah duk abunda na hane ki ba za ki hanu ba ko?".

"I'm sorry mommana!

Cewar Amrah tana kama kunneta da hannunta ɗaya yayin da ɗayan ke riƙe da cup. Miyya ta yarda da ƙarya da Amrah ta shara mata dalili kuwa tasan tana bin bashin kuɗin wankau gidan Maman Saleem. Sai kawai ta miƙa hannunta ta karɓi cup ɗin ta haɗa musu madara, Amal ta fara ba wa tasha ta ƙoshi saboda iya ruwan madara take iya sha.

**********************

Sosai Azaad Junaid yake kyakyalar dariya Abdul-hakeem ya riƙe baki yana kallonsa, saboda shi bai ga abin dariya ba, da kyar ya yi controlling dariyar tasa, kana ya nufi water dispenser ya tsiyaya ruwa masu sanyi a handle cup ya sha fiye da rabin cup.

"You're insane Abdul in banda kana mahaukaci ko zan yi aure sai na rasa wacce zan aura sai ƙaramar yarinya?"

Murmushi Abdul-hakeem ya yi kafin ya nufi kujera da ya tashi akai ya sake zaunawa, ya dubi Azaad Junaid da girar ido a ɗage "gata nake so nai maka Aj ka samu ka more garar da muka daɗe muna kwasa"

"Na yafe idan kana so mai nonuwan a tsaye ka nemi abarka, ni kuma nai maka alƙawari zan biya ma sadaki"

"Wai gatsali kake min?"

"Miye abin gatsali naga kaman ka fi ni buƙata"

Ya ƙarasa magana yana gintse baki.

"Shikenan Aj tun da ba ka so yanzu amma nasan komai dare daɗewa sai ka nemi ni da wannan buƙatar.

"Allah ya tsare ni da abin kunya"

"Ƙara sunnah ma'aiki shine abin kunya?"

"Ba haka nake nufi ba auren ƙaramar yarinya ne ba zan iya ba.

"Are you sure?"

Abdul-hakeem ya faɗa yana murmushi.

Sai da Azaad ya nemi ɗaya daga cikin cushion ɗin da ke cikin office ɗin ya zauna, kafin ya furta.

"Hundred percent sure!

Har Abdul-hakeem ya yi yunƙuri sake furta wata magana yai sauri katse shi ta hanyar faɗin

"Please Hakeem mu ajiye zance mai nonuwa a tsaye mu yi aiki da ke gabanmu"

Daga haka suka shiga tattaunawa akan contract ɗin da suke, aiki akai. Sai yamma lis suka rabu Azaad Junaid ya nufo gidansa a downstairs parlor ya tarar da Nanny Lacey tare da Ahlam dake wasa da toys ɗinta. Airah  tana Assignment princess Aneesa kuma tana ɗakinta, tana chat da friends ɗinta.

  Nanny Lacey ta gaida shi ya amsa ta hanya ɗaga mata hannu, Airah ta ɗago tare da furta.

"Welcome Daddy!

Ita ma hannu ya ɗaga mata kamar yadda ya yi wa Nanny Lacey, kai tsaye ya wuce bedroom ɗinsa dake upstairs. Wanka ya yi ya shirya cikin dark blue ɗin jallabiya ya wuce masallaci sai da ya yi sallar isha sannan ya dawo gida ya shiga ɓangaren Jadda mai aikinta Mero ya tarar a falo, Jadda tana bedroom ɗinta. Direct ɗakin nata ya shiga tana zaune akan sallaya da casbi a hannunta, ya nemi gefen gadonta ya zauna. Cikin natsatsiyar muryarsa ya gaidata ta amsa masa cikin kulawa.

Kana suka zarce da fira sai ga Mero ta shigo da tray mai ɗauke da tsadaddun warmers ta dire a gabansa, tasake fita ta dauko mishi lemo da ruwa. Jadda da kanta tai masa serving tuwon semovita da miyar agusi taji tantakwashi da tsokar busasshe kifi. Sosai ya ci tuwon saboda shi mutum ne mai matuƙar son abincin mu na gargajiya sai dai kashh! Allah bai haɗa shi da wacce ta iya ba. Madam Salima ko ruwan zafi na shan tea bata da lokaci dafawa. Duk wata kulawa da ya dace ta ba wa mijinta housemaids ke yi mishi ga Azaad Junaid da shegen kyakyami. Kuma gaba ɗaya 'yan aikinta Christan ne ba Musulma ko ɗaya, shiyasa Azaad ya ƙauracewa abincin 6angarensa sai dai ya zo na Jadda ya cika cikinshi.

Bayan ya kammala cin tuwonshi hadda su taune ƙashi Jadda ta tsare shi da kallon tausayi, har sai yaushe Azaad zai zama cikakken mutum?"

Domin ita ganinta bai cika mutum ba rabin mutum ne, sai ya share watanni uku cur! Ba tare da Salima ba, tayi iya kokarinta akan ya ƙaro aure abin yaci tura dole tana ji tana gani ta zuba masa ido, ba don ganinsa haka yana mata daɗi ba. Sosai al'amarin iyalinsa ke ci mata tuwo a kwarya kullum cikin masa addu'a take Allah ya kawo masa sauya na alkhairi.

"Anya kuwa Dattiya wannan rayuwa da ka zaɓawa kanka za ta fishe ka kuwa?"

"Jadda in-sha-Allah nesa ta zo kusa domin na sanar da Salima ta ajiye aikinta....

"Dallah..! Rufe min baki sakaran banza nusari wofi kullum cikin faɗar haka kake har yau ka sa aiwatar da komi. Saboda haka na ba ka nan da wata uku ko ta ajiye aikinta ta zama cikakkiyar matar aure ta amshi ragamar kula da gidanta hannun arna. Ko kuma ni na nemo maka wacce za ta kula min kai da yaranka"

"Ki yi haƙuri Jadda in-sha-Allahu ba ma zai kai mu da haka ba .

"Sai ta kai mu domin ba ajiye aikinta za ta yi ba ni kuma idan har ba mutuwa tai min sauri ba sai na auro ma 'yar mutunci mai nagartattaciya tarbiyya.

"Ni dai ina ƙara ba ki haƙuri Jadda"

"Haƙurinka na banza da wofi, ka dai ji na faɗa ma wata uku na ba ka, idan ba haka ba wannan ƙarin aure ba ka so ya zame ma dole. Ba kuma shawartarka nake ba ko jin ra'ayinka dole ka bi abinda nake so.

"Jadda rigima Ke ɗai sam bakyaso a zaman lafiya mu ajiye wannan zance ki sha maganinki"

Ya ƙarasa magana tare da dauko mata ledar maganinta da ke cikin bedside drawer, bayan tasha magani ya shafa mata na ciwon ƙafa sannan ya koma ɓangareshi. Har zuwa lokaci madam Salima bata dawo gida ba, kuma  tun fitar ta da safe.

Dama haka take yi in tafita sai baba ta gani take dawowa dabi'unta sam ba su yi kama dana musu aure ba, tafi Kama da masu zaman kansu.

Ɗakin yara ya wuce ya tarar da Airah tana game a laptop ɗinta, princess Aneesa, tana aikin nata na chat ganinshi yasa ko wacce ta dakatar da abin da take yi.


#Azaad Junaid

#Abdulhakeem

#Jadda

#Airah

#Aneesa

#Team Azaad Junaid.