Shafi na biyar
_*🌻TANI DA MANU 🌻*_
_(Labarin TANI DA MANU jikokin mai gari tsabiban yara masu bada nishad'i soyayya da kuma zallar dariya domin nishad'in ku masoyana)_
_LABARI DA TSARAWA_
_*SARAT ALK'ASUM (Maman Nusaiba ce)*_
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
_*Wannan shafin na sadaukar gareki my Sweetie Addaty na🥰kiji dad'in ki*_
بسم الله الرحمن الرحيم
9️⃣⏩🔟
Cike da tsoro Uwani tace" Kai Kuturu wannan abubuwa ranki ya dad'e a ina zan samo su?
TANI ta kuma mak'ale murya tace" zakije dajin k'are kukan ka ne acen zaki samu nonan birinya, sai kije dajin macizai anan zaki samo kitsen maciji, sauran kuma sai ki tafi dajin duhu acen zaki samo su, idan kin samo to zan miki aiki" Ta fad'a tana yin dariya kamar bokanyar gaske.
Uwani ji tayi cikin ta ya bada kululululu bata san lokacin data saki zawo ba sai zare ido take, zufa ta shiga keto mata tako ina baki na rawa tace" Ranki ya dad'e yanzu babu wanda za'a tura su kawo wannan abu sai ni zanje da kaina?
TANI tace" Ina ai babu wanda zaije sai ke sai kuma in zaki bada kud'i sai na saka aljani mai k'ahon yan gayu ya kawo miki, amma fa sai kin bada kud'i da yawa.
Jiki na rawa Uwani ta ciro kud'i dubu biyar ta bada tace" Nidai a taimakeni ace shi aljani mai k'ahon yan gayun yaje yau gobe zan dawo, idan ma kud'in bai cika ba to zan k'aro wani.
TANI tace" Hahaha ba matsala tashi maza kuje gida karku kuskura kuyi waiwaye idan kuna tafiya a hanya, idan kuka kurkura kuka waiwaya to duk abinda kuka gani karki dawo min nan, Aljani d'an baiwa zai muku rakiya gashi nan a tare da ku" Ta fad'a tana nuna musu Furera.
Furera sai ta dauki sanda ta ringa dogarawa tana mak'ale hannu da baki tayo wajan su Uwani.
Dunk'ulewa sukayi a waje guda suna k'yarma dan tsoro ganin yadda Furera ke zaro musu ido tana girgiza wani gashi a hannun ta irin wanda Yarbawa ke rikewa a hannun su.
Dariya tayi tace" Muje a muku rakiya bak'in mu wanda suka dauke kayansu daga gaban rahamar Allah, maza muje kar wanda ya waiwayo.
Da sauri sukayi gaba Furera na binsu a baya har gudu suke ita kuma tana binsu, sai da ta d'anyi nisa tace" To kuje gida kar wadda ta waiwayo kunji dai abinda shugaba tace dai ko?
Kamar wasu kad'angaru suka gyad'a kai suna fad'in" Eh hakane.
Tace" To kuje ina kuma jin duk abinda zaku fad'a.
Ai a 360 suka bar wajan kamar anyi walk'iya.
Dariya Furera tayi tace" Kai TANI muguwa ce itama ko da yake ai gara da tayi haka kar a rabata da masoyinta.
Dawowa tayi inda tabar TANI, dariya sukayi TANI tace" Ban mu kashe K'awata.
Hannu ta bata suka tafa har da shewa.
TANI tace" Y'ar bantan uba ita mai son MANU to zanga ta yadda zaki soshi, wai tana so MANU na ya tsaneni saina kuma miki b'alle-b'alle a d'uwawukan ki Y'ar banza mai hali irin na Uwar ta.
Furera tace" rabu da ita muje gida kinga mun baro MANU yana bacci kar ya tashi yaga baki nan.
Kamayya sukayi suka nufi kogi dan su wanke fuskar su.
************************
A b'an garan MANU kuwa juyawa yayi dan ya tab'a TANI saboda ya saba suyi bacci a rumgume da juna.
Ji yayi ba kowa idon shi a rufe ya kuma lalibawa yaji ba kowa , yace" TANI wai ina kike kar dai ki koma bayana na danne miki hannu, shuru yaji ba'a amsa mishi ba.
Bud'e idon shi yayi yaga wayam ba kowa a wajan abun sai ya bashi mamaki, tunawa yayi k'ila tana bandaki ne.
Zama yayi yana jiran ta fito.
Sai da yafi minti goma zaune ya tashi ya nufi bandakin shiga yayi yaji ba kowa, ai kuwa nan da nan ya shiga tashin hankali.
Da sauri ya fito yana fad'in" Ta..ta..TANI ina kika shiga ne?
Ganin dai ba mai bashi amsa sai ya fito tsakar gidan yana kwala mata kira.
Iyatu ce ta fito tace" Kai wannan masifa da yawa take, yanzu da ranar nan kake mana ihu a gida anya kana da hankali kuwa MANU? To ka fice nana a tsakar gida" Ta fad'a tana had'e fuska.
MANU yace" Iyatu TANI ce ban ganta ba yanzu fa muka kwanta amma na farka bata nan, naje bandaki naga ba kowa kuma kice wai naje to ina take?
Iyatu tayi tsaki tace" Shashasha kawai to k'ila ba suna tare da su Bintalo ba, ko kuma sun tafi gidan Matar d'an Yarbawa, kasan tace zata je taga jaririrya.
MANU kuka yasa yana yawo a tsakar gidan yana fad'in" Nidai ki fito min da TANI d'ita ko na fad'awa Mai Gari.
Iyatu ta rike baki tace" To ai sai ka kira shi koya zaneni saina nemo maka ita, kai ba dama ta fita ita kad'ai dole sai da kai.
Fita yayi yana kuka kamar wani d'an shek'ara biyar abin dariya.
Wajan Mai Gari ya k'araso yana fad'in" Mai Gari ina TANI take?
Ta sauri mai Gari ya tareshi yana cewa' Subhanallahi meya faru MANU?
MANU yace" TANI ce ban gani ba kuma na tambayi Iyatu tace min wai itama bata sani ba , wai ko kila taje gidan d'an Yarbawa.
Mai Gari ya tashi yana tattare babbar malin-malin d'in sa ya rike a hannu yace" To ina ta tsaya ne haka zauna zan sa Yaro yaje cen gidan d'an Yarbawa a dubo min ita.
Kuka MANU ya kuma sawa ya kwanta a k'asa yana birgima yana cewa" Waiyo Allah nidai a nemo min TANI, idan ba'a nemota ba saina fad'a rijiyar gidan Liman kowa ma ya dena ganin mu waiyo TANI na nidai Mai Gari kaje da kanka ka nemo min ita" Haka ya ringa birgima kamar wani yaro dan shekara biyu ko uku yana fad'in a nemo mishi TANI.
Mai Gari duk hankalin shi ya tashi ganin yadda MANU yake kuka sai yaji duk ya damu, sai da ya face majina tukun ya juya kan MANU.
Su kuwa su Malam Liman suna kallon ikon Allah wannan abu yana damunsu, sai dai baza su iya magana saboda me gari zai musu tass ya koresu.
Mai Gari ya ya d'ago MANU yace" To kayi shuru muje cen mu gani ko taje.
Dena kukan yayi ya goge hawayen shi ya saka takalmin sa suka bar k'ofar Mai Gari.
Galadima yace" Kai Wallahi Mai Gari daga shi har jikokin nashi sai an musu Addu'a ina dalili, Yaran nan sun addabi mutane a Gari, shi kanshi Mai garin basu barshi ya huta ba, ni ina mamakin wannan abu Wallahi anya kuwa yaran nan ba bak'in Uwa ba garesu nin...
Bai k'arasa ba Liman ya daka mishi tsawa yace" Kai Galadima ai ko mutuwa tana tsoro ido jikokin namu ne masu bakin Uwa? To ka shiga hankalin ka ko ka manta Matar Sa'id Nina haifeta ita kuma ta haifi TANI iyee? To bana son na kara jin ka aibata mana jikoki wannan ai cin fuska ne Kai ko kunyata baka ji ba a gabana kake ce musu masu bakin Uwa, to zan fad'awa Mai Gari yana dawowa.
Galadima da sauri ya rufe bakin shi yace" Tuba nake ranka ya dad'e dan Allah karka hadani da mai gari, Wallahi korata zaiyi in har yaji wannan maganar dana fad'a.
Liman yace" Shikenan amma ka kiyaye dan duk lalacewar naka to naka ne ba yanda zakayi da shi, suma kuma yarinta ce suke ji da zarar sunyi hankali zasu dena.
Shi dai Galadima Hak'uri yayi ta badawa yana dana sanin furucinsa.
***********************
Su TANI bakin kogi suka nufa nan suka samu Yara suna wanka.
TANI tace" Yauwa Furera muyi wanka sai mu tafi.
H
Furera Tace" A'a kizo dai muje cen d'in kinga ba nan da maza, kuma MANU yana cen yana bacci.
Sai yanzu TANI ta tuna da MANU da sauri ta juya tace" Zo mutafi gida kar MANU ya tashi yaga bana gidan.
Da sauri suka wanke fuskar su tukun suka tafi, sai sauri suke zubawa, kasancewar tani akwai sauri yasa Furera ke binta da gudu, ita kuma TANI na mata dariyar mugunta tana k'ara sauki.
Sai da taga ta gajiyar ta Furera sai da k'yar take tafiya tukun ta tsaya tana dariya.
Furera na huci tace" Wannan ai mugunta ce Wallahi baki da kirki wani lokacin, haba dan Allah.
Kama hannun ta tayi suka ringa tafiya a hankali.
************************
Su Mai gari suna zuwa gidan d'an Yarbawa yace ana sallama da d'an Yarbawa.
Da sauri d'an Yarbawa ya fito yana washe baki yace" Allah caski mi gari kece a gida namu yanju, to muna meraba da juwanki.
Mai Gari yace" eh nine d'an Yarbawa TANI nake nema bata zo nan ba?
D'an Yarbawa yace" A'a gaskiya TANI baizo gidan nan ba.
Mai Gari yace" To shikenan ba damuwa sai an jima ya kama hannun MANU da yake ta sharar kuka, saboda baiga TANI ba.
Suna dawowa gida MANU ya koma bak'in k'ofar gida ya zauna yana ta rera kukan shi, Mai Gari yayi ta rarrashin duniyar nan amma yaki yayi shuru sai Hak'ura yayi yasa mishi ido.
***********************
TANI suna tafiya suna hira suka had'u da Iro a hanya yana cewa a sayi kifi a sayi kifi, ganin su TANI sai ya tsaya yana fad'in a'a TANI kune haka da ranar nan ina zuwa haka?
Furera ce tayi murmishi tace" Eh mune daga kogi muke ai.
Ita kuwa TANI sai hararar shi take saboda ta tsani ya mata magana.
Sauke kifin yayi yace" TANI nifa tinda aka kawoki daga birni nake k'aunar ki, ke kuma kin kasa tsayawa ki fahimceni, ina sonki sosai idan kika k'ara girma sai muyi aure.
Zaro ido Furera tayi zatayi magana TANI ta dakatar ta.
Kallon shi tayi tace" Lalle baka da hankali ni zaka Kalla kace wai kana sona to nafi karfin ka kaje cen ka samu wanda kake so amma ba TANI ba ka gane, me zanyi da kai sai warin kifi kake ,na aureka kake cika min daki da warin kifi bare ma ba sonka nake ba, to ka fita harka ta bana son renin hankali" Ta fad'a tana girgiza jiki.
Haushi Iro yaji jin tana mishi wulak'anci yace" Aikin banza ke dan nace ina sonki shine kike fad'a min magana son ranki? Banza dake ma marar tarbiya kangararriya kawai, dan zan taimake ki na aureki shine kike min borin hauka.
Iya k'uluwa yau TANI ta shak'a sosai har wuya.
Zagaya shi tayi tace" Ni kake cewa ina borin hauka? To yanzu kuwa zaka ga hauka mai rawani ganin idonka.
Kallon Furera tayi tace" muje kici gaba.
Tafiya tayi ita kuma ta sunkuya kasa kamar ta taka k'aya, kasa ta ciko hannun ta biyu da su ya juya mata baya, tace" Iro ka can.
Sama ya kalla yaga abinda take nuna mishi amma bai ga komai ba.
Ita kuwa TANI yana d'aga kanshi Sama ta bad'e mishi kifin nashi tass da k'asa, ta kuma ciko hannun ta ta k'ara ta falla a guje.
Iro juyowa yayi dan ya tambayi TANI me ta gani a Sama, amma sai yaga wayam ba kowa , farantin kifindhi ya kalla yaga ta zuba mishi k'asa.
Dubawa yayi ya hango ta cen nesa tana gudu, kamar zaiyi kuka yace" Ni kika zubawa k'asa a cikin kifina, Yarinya sai na kaiwa Mai Gari ya biyani" Kayan ya dauka ya bita a baya.
***********************
TANI na isko Furera ta bata labarin abinda tayiwa Iro ai kuwa suka ringa dariya.
Tin daga nesa ta hango MANU zaune yayo tagumi yana gyangyad'i.
Da gudu ta k'araso inda yake tace" MANU, MANU ka tashi na dawo.
Firgigit ya bud'e idon shi ganin TANI a gaban shi da sauri ya rumgume ta yace" Ina kika je ina ta nemanki?
Murmishi tayi ta goge me hawaye tace" To naje rafi ne tashi muje na baka labari yau na samo mana kud'i.
Mai Gari ya k'araso inda suke yana washe baki yace" TANI ina kika je muke ta neman ki?
TANI tace" cen kogi muka je da Furera naga yana bacci ne shiyasa ban tashe shi ba.
Inuwa suka koma zasu tashi sai ga Iro da babban ice yana huci yace" Ina kike dan Uwarki maza kizo ki biyani kud'in kifina ko kuma yau na kakkarya ki kowa ma ya huta da fitinarki.
TANI ta makale a jikin MANU tana b'oye kanta ganin Iro kamar mahaukaci.
Idan kin karanta ki daure kiyi comments sister 🤝🏻
_Taku har kallum Maman Nusaiba ce_