TANI DA MANU

Shafi na shida

by @saratalkasum88

_*🌻TANI DA MANU 🌻*_









_(Labarin TANI DA MANU jikokin mai gari tsabiban yara masu bada nishad'i soyayya da kuma zallar dariya domin nishad'in ku masoyana)_






LABARI DA TSARAWA


_*SARAT ALK'ASUM ( Maman Nusaiba ce)*_





🔔📚

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_






بسم الله الرحمن الرحيم



1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣




Iro da yake jin tsanar TANI yace" Dan Uwarki zaku biyani ko saina muku duka daga ke har Dan ranin hankalin Yayannaki?

TANI haushi ne ya rufeta jin an zagar mata MANU tashi tayi daga jikin MANU ta warware mayafinta, burgujejan wandonta data saka take yawo a cikinsa ta tattare tana huce, mayafinta taci d'amara dashi a k'ugunta, kallonshi tayi tana watsa mishi daradaran fararen idanuwanta tace" Dan fallan farantin kifin kakan K'anan Babanka Malam Saminu mai saida taba da goro a dandali ba za'a baka ba, kai nifa akan MANU zan iya cinnawa garin nan wuta kowa ma ya mutu.


MANU dai ka zaga ko? to yau sai mun raba reni nida kai a wajan nan.

Da nayi niyar biyanka amma tinda ka zagar min MANU na ba zan biya ba kayi duk abinda kake so dan Uwar kifin naka" Ta fad'a tana huci kamar wata kumurcin maciji.


Mai Gari yaje ya janyota yace" Haba TANI na wannan zagin haka wai a ina kike koyo zagi ne?

To yanzu barshi na biyashi kud'in karya dakeki kuma karki kuma kulashi.

Kai kuma nawa ne kud'inka sai na biya?


Kada ka kuskura ko a hanya kaga TANI kace zaka daketa zan saka a zanemin kai ka gane ko.

Wai me ma ya had'aka da ita? nasan dai TANI bata shiga harkar mutum sai in yajata zata yi masa wani abu.


Kama hannun TANI yayi yace" Menene ya had'aki da wannan marar mutumcin?


TANI turo baki tayi tace" Mai Gari ba Iro bane dan ya ganmu muna wucewa nida Furera wai ya tsaida mu yace yana sona.

To shine nace mishi ni bana sonshi ka hanani kula maza.

Shine yake zagina har da kai ya zaga cewa" wai Mai Gari da babbar rigarsa kullum baya cenjawa, wai kuma yace hallau duk wanda yazo fadarka sai ka fesa masa majina.


To ni kuma shine naji haushi harda zagar min MANU shine na zuba mishi k'asa a kifin nasa" Ta fad'a tana murgud'awa Iro baki da ya saki baki yana jin yadda ta sharara masa sharri.



Yace" Mai Gari wallahi k'arya takeyi ni dai ban zageka ba ko shi MANU ban zageshi ba k'arya ne.

Itace ta zageni ma kuma yanzu ma ta kuma zagina, ni sau d'aya ya zageta.


TANI tayi caraf tace" k'arya yake Mai Gari ba wani nan ai ga Furera nan in k'arya nake mishi.

Ke Furera fad'awa Mai Gari abinda Iro ya fad'a min.


Furera ta had'e fuska tace" Eh ya zageta har cewa yake Mai garin banza har wani ya isa ya Takashi ya zauna lafiya.

Kuma yace wai idan ka isa ka ramawa TANI zagin daya mata.

Ni kuma da naga haka banyi magana ba dan kar ma yazo yayimin sharri kamar yadda yayiwa TANI.


Kuma dama kullum idan muka fita dandali sai yake cewa TANI DA MANU jikokin mai gari tsabiban yara, Mai Garin ma hatsabibine.


Tinda ya kawo kanshi gashi na fad'a sai a mishi hukunci tinda yake zagin mana Mai Gari.

Kuma wannan takalmin nashi ma satowa yayi, ranar da dare naji ana cewa ihu b'arawo.

Dana fito shine naga Iro da takalmi a hannunshi yana falla gudu.


Ni kuma nayi shuru dan karna tona mishi asiri a kamashi ya wuce, bai san na ganshi ba.

Washe gari naganshi da takalmin" Ta k'arashe maganar da cewa" Ko ba haka akayi ba TANI?


TANI tayi tsalle ta dire ta kwaso shoki ta direshi a kafad'ar Mai Gari.

Tace" kwarai kuwa anyi haka ai dama mun rufa maka asiri ne dan ba'aso a tada fitina shine mukayi shuru.

To tinda baka da mutumci yau gashi mun tona dan Mijin Uwarka.


Iro zufa ta shiga keto mishi kamar yayi hauka jin wannan kalar sharrin da akayi ta zanowa wanda baisan dasu ba.

Kallon TANI yayi yace" Ni kika yiwa sharri TANI dan nace ina sonki? To shikenan kije ba komai na tafi.


Juyawa yayi zai bar wajan Mai Gari ya janyo rigarshi yace" Kai Iro rashin kunyar taka ya wuce mutanen gari ya dawo kaina.

To zan kira Uban naka naji inshi ya daure maka gindi kake zagina.


Tsugunnawa Iro yayi yace" Dan Allah Mai Gari kayi hak'uri bazan sake ba kar a kira Babana.

Kuma zan kiyaye bari naje na gaso maka kifi.


Mai Gari yace" Ai sai ka biya tara tinda ka zagi Mai Gari.

Yanzu zan tura a kira shi kuma kullum sai ka kawo kifin miya a gidana kullum.

Idan ka sab'a maganata zansa a kaika birni wajan Y'an Sanda.


Iro yace" To zan kawo daga anjima tuba nake Mai Gari kakan TANI DA MANU.


Sakinsa Mai Gari yayi yana goge bakinsa da tsabgegen asuwakishi na maina.

Yace" To shikenan tafi ka bamu guri.


Da mugun gudu Iro yabar k'ofar Mai Gari yana yin godiya.


TANI tace" Mai Gari yunwa mukeji.

Mai Gari yace" Muje gida a siyo muku shinkafa da miya da naman kai a cen wajan Maman d'an Yarbawa.


Dad'i ne ya kamasu jin ance har da naman kai.

Gaba sukayi yana biye da su har cikin gidan.


Liman ya girgiza kai kawai yace" Ya Allah ka nuna min ranar da su TANI zasu zama mutanen kirki kamar kowa, Yara sai fitina shi kanshi Mai garin sun hana shi ya zauna lafiya.

Sauran sukace Allah ya kyauta tukun sukaci gaba da hirar su.

************************


Garin Yobe.



Wasu gidaje ne guda uku dake Unguwar J.R.A. gidajen sun tsaru iya tsaruwa, kai da gani kasan wanda suka mallaki gidan nan suna da kud'i na gani na fad'a.


Gidan duk iri daya ne komai nasu kala d'aya ne, na farkon na fara shiga domin kawo muku rahoto.


Zaune suke a rahabar gidan matasan Samari masu aji da izza da kwalisa.

Kowannensu waya yake dannawa sai murmishi suke saki lokaci zuwa lokaci.


D'aya daga cikinsu ya d'ago da kanshi masha na Furta ganin handsome Gaye hadadde, dogo ne ajin farko gashi kyakyaywa fari sol da shi har wani shud'i² yake yi kan fari.

Fuskar sa abin kallo ce mai dauke da daradaran fararen idanuwanshi masu matuk'ar daukan hankali, hancinsa d'an dai-dai, bakinsa Shiba babba ba, kuma ba karami sosai ba, masha Allah.

Kallon su yayi yace" Yaya Ibrahim wai yau bazamu d'an fita bane mu shak'ata? Nifa gaskiya na gaji da zaman nan" Ya fad'a yana turo baki gaba kamar wani yaro.


Murmishi Ibrahim yayi ya d'ago da kanshi, shima yana kyau matuk'a amma bai kai d'ayan ba, shi ba fari bane har cen.


Yace" Kai Wallahi Aminu inda kai Mace ne da naga shagwab'a, kuma fa kunfi kama da TANI Wallahi.


Naji Daddy na cewa wai in sunyi hutun school zasuzo mana visit.

Da sauri ya zaro idanunsa yace" Da gaske Yaya TANI zasu zo nan hutu?

Ibrahim yace" A to kuma sai kayi ai zaka gansu ne.


D'ayan ne ya aje wayar shi a gefe ya kwashe da dariya yace" Wallahi Yaya Aminu kana ban mamaki, wai kai me zakayi da wannan marar jin maganar?


Hade rai yayi yace" Khalifa ina wasa da Kaine, ai ni TANI tana burgeni sosai.


Tsaki Ibrahim yayi yace" Wallahi kana kwabsi dayawa ai zata zo ta isheka da shegen surutunta ga rashin ji har yanzu bata waye ba sai neman fitina.


Aminu yace" Oho dai koma meye ni tana burgeni k'anwata ce ai.


Khalifa yace" kaji dashi ni bani da lokacin wata TANI ko MANU marassa jin magana.

Wancen lokacin fa saida MANU ya targard'a min hannu ko ka manta ne.

To da suzo da karsu zo duk Uwarsu d'aya ehhe" Ya fad'a yana hura hanci.


Kyalesu yayi ya duba cikin photon wayarshi ya lalibo na TANI tana shan rake ya dauke ta, d'aya kuma tahau kan karfen dake kan matakalar benan gidan su tana lilo ya dauketa.

Murmishi yayi yace" Ku baku so a saka su a jiki ai da haka zasu dena shirme su dawo kamar mu.


Tashi Ibrahim yayi yace" To ai sai kuyi kuma.

Shima Khalifa mikewa yayi yabar Aminu zaune yana sakin murmishi.


Bayan sun tafi shima fita yayi daga gidan ya koma nasu gidan.


************************


Su Mai gari na shiga gida ya bada kud'i a siyowa su TANI abinci.


Iyatu ta kama baki tace" Hmm Allah mai iko.

Hararar ta TANI tayi tace"To me aka miki da kike wani cewa Allah me iko?

Iyatu karan dake kusan ta ta dauka zata daki TANI dashi Mai Gari yayi sauri ya tare, ai kuwa ta buga mishi a hannunshi ji kake karrr k'aran bugawa da yake karan yana da kwari.


Mai Gari ya kalli Iyatu yace" Muguwa marar mutumci, wato so kike kina dukan min jikoki ko? To bazan yarda ba.

Kalli yanzu da ita kika bugawa ai da Kin k'arya mata hannu.


Iyatu ta kalli gabas tana karkad'a k'afa tace" Mutum inya isa ya rama mana ya gani, kasan dai ba manta danbenmu da mukayi muna kamarsu nayi ba.

To yanzu saina nunawa Allah kai na sakoka da k'asa babu abinda ya shafeni.

Dama haushinka nake ji ina kallon abinda ya faru d'azu.

Nasan Iro bazai zageka ba kawai sharri ne irin na TANI.

Wallahi Mai Gari kaji tsoron Allah akan abinda kakeyi.


Cike da takaice Mai Gari yace" Ke Amina ki fita daga idona zan lafta miki rashin mutumci.

Kisan ba mutumci bane dani ko? To ki kaini bango kiga me zanyi.


Baki ta saki tana kallon Mai Gari tace" Mai Gari yau kaine ka kira sunana gatsau-gatsau haka? To yau ka tari masifa da bala'i a gidan" Ta fad'a tana mikewa tsaye.


Mai Gari babbar rigarsa ya cire yace" Ke nifa ba tsoronki nakeji ba Y'ar renin hankali ance Amina d'in, ba sunanki ba har sunan Kakarki ta lahira saina fad'a aikin banza.


Tashi Iyatu tayi zata cakumi Mai Gari TANI ta shiga gaban su.

Kallon su tayi tace" Haba Iyatu da girmanku ai na dauka yin danbe sai mu Yara ku ba K'ananan Yara bane.

Haba yanzu in muka fita sai kaji ana cewa kakarmu da kakanmu suna danbe to nidai Alkur'an in kukayi danbe saina bar muku gidan" Ta fad'a tana murgud'awa Mai Gari baki.


Iyatu ta janyo babbar rigar Mai Gari da k'arfi ji kake kiiii ta yagata, wiyar rigar ta cakumo tana fad'in" Uban daya fasa Shiba dan garin nan bane, ni zaka rena dan kaga Ina kyaleka to nagaji, ai baka manta yadda muke danbe ba lokacin muna Yara.


Mai Gari kuwa ya shak'a wai shi Iyatu zata yagawa riga lalle ta tab'o masifa da bala'i a gidan nan.

Shima dan kwalinta ya janyo ganin hakan bai mishi ba ya kama rigarta ya keta ta a biyu sai reto rigar take a jikinta.


TANI ihu tasa tace" Ladiyo kizo Iyatu zata kashe Mai Gari jama'a a kawo mana dauki za'ayi kisan kai a gidanmu.


Da gudu Ladiyo ta fito tana fad'in" Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un yau me zan gani abin kunya ace kuna fad'a oh ni Ladiyo.

K'arasowa tayi tana k'ok'arin rabasu ai kuwa Iyatu ta kawo duka ta mangare Ladiyo.

Ladiyo taji zafi sosai dan haka itama ta juyo ta shaki Iyatu ta zuba mata dundu.


Iyatu tace" Kan bukun Ubancen ni kika yiwa dundu lalle zan rama yanzu.


Fad'a dai ya kacame duk wanda ya kama d'an Uwanshi sai ya cigaba da dukanshi.


TANI ta fito a guje tana ihu wajan su Liman tazo tace" Liman kaga Mai Gari cen Iyatu da Ladiyo zasu kashe mana shi sai dukan shi suke.


Da sauri Liman ya tashi ya shiga cikin gidan.

Tararwa yayi sun danne Mai Gari sai jibgarsa suke kamar an musu wahayi.


Da sauri ya daka musu tsawa yace" Wannan wani irin hauka ne haka? Kashe Mijin naku zakuyi to kowa ta tasashi.


Da sauri duk suka tashi suna huci.


Liman ya taimakawa Mai Gari ya tashi sai surfa masifa yakeyi.


Da k'yar Liman ya samu ya sasanta su kowacce ta shige d'akinta.


TANI DA MANU suma suka nufi nasu d'akin.

Zama sukayi MANU yace" TANI wai ina kukaje haka?


Dariya tayi sosai tukun ta gyara zama ta bashi labarin komai da ya faru.

Tashi yayi ya rumgume ta yana fad'in" Wallahi kinyi TANI na yanzu ina kud'in?


Nuna mishi tayi ya amsa yace" Mu kaiwa Mai Gari ya aje dan Ubanta gobe ma ta k'ara zuwa.


Wani Yarone yayi sallama sukace ya shigo d'akin.

Langa ce babba da k'arama a hannunshi yace" Wai gashi inji Mai Gari yace ku cinye duka kada ku bawa Ladiyo da Iyatu.


Amsa suka TANI ta bashi naira biyar ya tafi yana murna.

Abincin sukaci tukun sukaci gaba da hira.

Jin ana kiran salla sai sukayo alwala MANU ya tafi masallaci daga cen zai bawa Mai Gari kud'in.

Ita kuma TANI tayi sallar ta a d'akin su.

************************


TANI ce ita da su Furera su biyar kamar kullum.

TANI tace" Kai kuzo muyi wake kafin dare yayi muje dandali kusan gobe ne wasan Samari da Y'an Mata.


Tashi sukayi a tare suka ce" Eh wallahi muyi.

Jerawa akayi Furera ta fara Waka wa.


Tace" Hajiya TANI ta Alhaji MANU jigida b'alle, dame dame kike saidawa jigida b'alle.


TANI tace" Da kan guda da kan buzuzu kawo d'ari abaki na hamsin jigida b'alle.


Komawa Furera tayi sai Bintalo ta fito ta soma Waka wa..


Tace" Hajiya Furera mai dan wake jigida b'alle, dame dame kike saidawa jigida b'alle.


Furera tace" Da kan biri da kan zakanya kawo biyar a baki na goma jigida b'alle.


Komawa Bintalo tayi tukun TANI ta fito ta sl

Soma fad'in.


Bintaloluwa Yarinya jigida b'alle, dame dame kike saidawa jigida b'alle.


Bintalo tace " kan barewa ne Yarinya kawo taro a baki na sisi jigida b'alle.


Tafi MANU da Goga sukayi MANU yace" Wannan waken yayi dad'i.


Haka sukayi ta wake saida suka gaji tukun suka dawo gida.




Idan kin karanta ki daure kiyi comments sister ko share🤝🏻






_Taku har kallum Maman Nusaiba ce_