TANI DA MANU

Shafi na bakwai

by @saratalkasum88

_*🌻TANI DA MANU 🌻*_












_Labarin TANI DA MANU jikokin mai gari tsabiban yara masu bada nishad'i soyayya da kuma zallar dariya domin nishad'in ku masoyana)_






_LABARI DA TSARAWA_


_*SARAT ALK'ASUM (Maman Nusaiba ce)*_



🔔📚

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_



بسم الله الرحمن الرحيم


1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣



Mai Gari ne ya fito yana surfa fad'a kamar zai are baki.

Bakin kofar d'akin Iyatu yazo yana fad'in" Ke Iyatu maza fito ki tafi gidanku ,to ba mantawa nayi ba dukan da kukamin keda Ladiyo kowacce ta fito tabar min gidana.


Wato dan kun rena min hankali har tarayya kukamin kamar wani marar gata.

Yanzu ba dan su TANI ba da sai kun kasheni zaku barni.

To maza ku fito.


Fitowa sukayi a tare kowacce kanta a k'asa.

Hak'uri suka shiga bawa Mai Gari amma ya furta kwallin rashin mutumci yace bai san Hak'uri ba.



Haka suka hak'ura duk suka fito, Iyatu na zuwa saitin Mai Gari sai tajanyo rawaninsa yaja yayi baya zai fad'i.


Mai Gari yace" Ke dama baki da d'a'a ai marar mutumci , saina sakeku na huta.


Iyatu tace" ka jima baka sakemu ba aikin banza.

Fita sukayi kowacce ta nufi Gidansu ranta ba dad'i.


Mai Gari ya kulle d'akunan ya dauke makullan yasa a aljihunsa.

Fita yayi yana fad'in" Mutanen banza kuje Gidanku kuji idan zaman gidan yana da dad'i, dan kun tsufa ba shi zai hanani na sakeku baki d'aya ba.


Liman ya samu da Galadima suna zauna zaman jiranshi.

Zama yayi ko gaisuwar da suke mishi bai amsa ba.


Liman yace" Wai Mai Gari lafiya kake wannan fad'a haka? Naga su Iyatu sun fita ko baka son fitarsun ne?


Tsaki Mai Gari yayi yace" Waya fad'a maka? korarsu nayi daga gidan.

Ai yanzu suje suyi shekara guda a gidan su suji yadda ake ji, haka kawai inaji ina gani su kasheni.


Liman yayi salati ya sanarwa da Allah.

Yace" Mai Gari wannan wani irin hukunci ne haka haba d'an Allah gaskiya kayi hak'uri.

Yanzu tin kuna yara basuyi yaji ba sai yanzu da girma yazo muku kace wai su tafi gidansu?


Kayi hak'uri ka dawo da su, wannan ba dalili bane da zaka koresu.


Mai Gari yace" Kai Alkur'an bazan medosu ba sai sun zauna acen.


Liman yayi ta fama amma Mai Gari yace bai san maganar ba dole su tafi subar mishi gida, haka ya hak'uri ya kyale Mai Gari badan ranshi yaso ba.


************************


TANI DA MANU suna bacci, cikin bacci tayi mumunan mafarki akan MANU.

Wannan dogon abun ne da yake zuwa musu da dare a k'ofar gida ta gani, da kuma wasu biyun masu bak'ak'en kaya.

So suke su dauke su , shi kuma dogon ya hanasu sai fad'a suke a tsakaninsu.

Wasu biyun ne suka fito daga cikin k'asa fuskarsu ba kyaun gani.


Ihu TANI tayi tace" Waiyo MANU ka rikeni karka bari su daukemu.

Shima MANU tsoro ya kamashi ganin wannan abun tsoron.

Da sauri yace" TANI muyi karatu Mai Gari yace idan munji tsoro muyi karatu.


Da karfi suka ringa karanto ayatul kursuyu suna gamawa suka soma karanta suratul yaseen.

Ihu suka soma suna toyewa sai cewa suke.

Kuyi mana rai karku kashemu muma turo mu akayi.


TANI tace" kaji munafukai MANU mu dage da karatun.

Da k'arfi suka kuma daukar karatun.


Wani gigitaccen k'ara suka saka tukun suka kone tass kamar ba wanda ya tab'a bayyana a wajan.


MANU ya kalli dogon mutumin nan yace" Dan Allah nan a ina muke ? kuma me yasa wannan munanan suke son dauke mu?


Juyowa yayi fuskarshi a rufe fararen idanuwanshi kad'ai ake gani.

Yace" karku damu Insha Allah zan taimake ku wasu ne ke son rabaku.

Amma ina tare da ku har kuyi hankali bazaku fahimci me nake nufi ba sai kunyi hankali.

Yanzu haka bibiyar rayuwarku akeyi amma komi rintse komin wahala komin ruwa komin iska, kada ku kuskura a raba muku wajan kwana.



Idan kuwa kuka bari aka raba muku wajan kwana to makiyanku zasuyi nasara akanku, dan haka kuke Addu'a koda yaushe.

Ku Yara ne bazaku gane ma'anar zancena ba.


MANU yace" To bawan Allah ya sunanka, kuma waye yake bibiyarmu? Ni dai a iya sanina babu wanda muka takurawa da har zaike sawa ana tsorata mu.


Murmishi yayi yace" Ni sunana Muhammed ibn Abdallah, ni ba irinku bane.

Wanda suke bibiyar rayuwarku kashi biyu ne kuma duk suna nan kuna jinsu da ganin su.

Amma bazan fad'a muku ba kudai kuke Addu'a kuma karku sake a raba muku wajan kwana.


TANI ta rumgume MANU tana kuka tace" mungode Muhammed bawan Allah, yanzu ka taimaka ka fad'a mana wanda yake binmu, kaga sai mu fad'awa Mai Gari ya bamu magani.


Muhammed juya musu baya yayi yace" sai wani lokacin daga yau kun dena ganina a k'ofar gidanku dama dan na taimake ku a kan wannan ranar nake binku.

To yanzu Allah ya kubtar daku sai anjima.

Kamar kiftawa da Bismillah sukaga ya b'ace.


TANI ta saki ihu tana rumgume MANU.


Firgigit ta farka tana fad'in" Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un Addu'ar mummunan mafarki tayi, Tace" to wannan mutumin me yake nufi da ana bibiyar mu.


To Alkur'an koma waye idan na kama shi saina mishi dakan sakwarar Maman d'an Yarbawa.


Kallon MANU tayi da yake bacci ta tashesa ta fad'a masa abinda ta gani a mafarkinta.

MANU yace" To Nima haka na gani kinga sai muke Addu'a sosai kar a rabamu.

Nidai ban san me yake nufi da maganarshi ba yace wai idan mukayi hankali zamu gani.

To wai da mu bamu da hankali ne ?


Dariya TANI tayi tace" ka rabu da shi k'ila ma k'arya ce yake mana.


Da yake ba hankalin garesu ba anan suka bar maganar suka fita yawon rashin jinsu.

************************



Gari dai ya dauka cewa Mai Gari ya saki Matanshi Iyatu da Ladiyo.

Wannan abu na damun Liman ganin duk inda ya zauna sai an mishi gulmar maganar.

Yau dai ya samu Mai gari da zancen .


Gyara zamansa yayi yace" Mai Gari ina rokon wata alfarma a gareka Allah yasa zaka amince.


Mai Gari yace" To ina jinka ai kawai ka nema indai batafi k'arfina ba zanyi maka ita.


Liman yace" Inaso kayi hak'uri su Iyatu su dawo gida zaman gidan nasu ya isa haka.

Kasan yanzu kowaccensu ba Iyaye gareta a raye ba.

To yanzu suna gidan Y'an Uwansu ne, dan Allah ka maidasu dakunansu.

Yanzu haka duk inda kaje a Gari maganar ake ana maka dariya.


Mai Gari ya bud'e k'ofar hanci yana shakar iska sai goge bakinsa yake da asuwakinsa.

Kallon Mai Gari yayi yace" Liman ka rabu dasu kwanakin dana diba musu bai k'are ba.


Liman yace" A'a kayi hak'uri ka dawo da su.

Amma Mai Gari yace shifa bazai dawo da su Iyatu ba, sai hakura Liman yayi yabar maganar ba dan ranshi yana so ba.

************************


Su TANI ne suke tafiya sai shan mangwaro sukeyi suna zuba surutu.

Furera tace" Wai dama Garinmu haka yake da kaloli?


TANI tace" Kamar yaya wannan wacce irin tambaya ce?


Furera tace" naga wannan gefen ya zama koriya, gefen d'aya kuma ya zama blue cen gabanmu kuma ya zama fari da baki.


Dariya MANU yayi yace" Alkur'an Furera santine takeyi , dama fa ance duk wanda yake shan rake ko mangwaro Mai zaki to haka yake zubar magana.

Ni Allah ya soni ma har na gama sha banyi magana ba.


Goga yace" To ai wannan Furerar dama ta kusa zarewa sanine bakuyi ba, itafa idan tana shan rake ko mangwaro haka take zaro magana kamar wata mahaukaciya.


Furera data lumshe ido dad'in mangwaro na kai mata har kwakwalwarta tace" Kunga nifa abinda na gani ne nake fad'a muku, to amma tinda baku yadda ba shikenan.


Zama sukayi a wata bishiya suna hutawa ai kuwa sai ga Uwani da Ma'u sunzo wajansu.

TANI tace" Ku kuma lafiya kuka wani tsaya mana a kai kamar munci bashinku?


Uwani tayi murmishi tace" Kinga Malama ba dake nake son magana ba da masoyina nakeson magana.


Dariya TANI da Furera sukayi tace" Tsuwww aikin banza ai gaki gashi sai ki mishi maganar mugani ko zai saurareki.


Uwani da takeji kamar ta shake TANI ta mutu tace" Ke dalla cen banza karki sake magana anan wajan.


Ma'u ganin TANI ta kyale Uwani yasa taji tsoro tasan rashin mutumci irin na TANI, tace" Kinga Uwani kizo mu tafi gaskiya.


Uwani tace" Ba inda zanje sai nayi magana da MANU.

Ma'u tace" To shikenan nidai na koma gefe.


TANI tace" Malama ki fice mana anan ko yanzu nayi miki duka.

Bar ganinki k'atuwa yanzu zanyi kasa-kasa dake anan.


MANU yace" TANI rabu da ita ai ba kulata zanyi ba, ni bana son ganinta ma take wani Bina kamar rigar haihuwarta.


Shuru tayi taci gaba da carafken ta da y'ay'an aduwa.


Bata ankara ba taji Uwani ta wanke ta da mari Mai zafi.

Ai kuwa ta mike tsaye ta kalle ta da matuk'ar mamaki akan fuskarta, tace" Mai na miki kika mareni?


Uwani tace" Ki fita daga harkar MANU kar kiga kuna guri d'aya kice zaki renani.


Bakin cikine ya kama MANU ai kuwa ya mike da hanzari shima ya wankawa Uwani mari guda biyu lafiyayyu.

Yace" Ke har kin isa ki marar min TANI na a gabana na kyaleki, waye Ubanki a k'auyen nan da kike takama da shi, kinsan wacece ita kuwa?


Da yake itama mafadaciya ce ta janyo kwalar MANU zata dakeshi, ai kuwa TANI ta dauki sandarsu da suke yawon da ita ta kwad'ewa Uwani a bayanta.


Ihu Uwani tasa tana juyowa taga waye ya buga mata sanda.

Ganin TANI ce ta juyo kanta, aikuwa sukayi mata taron dangi suka mata dukan tsiya, sai da suka fasa mata baki bayanta shima sunji mata ciwo, ihu take su kuma sai zaneta suke yi.

Sai da suka mata duka son ransu takun suka barta.


TANI tace" Sa'arki ce da zaki d'aga hannu ki mareni, to gobe ma kika ganni ki mareni zakiga abinda zanyi.


Da k'yar Uwani ta tashi goshinta na zubar da jini suka tafi gida, Ma'u dai shuru tayi dan kar a had'a da ita.


Suma su TANI gidan suka dawo.

***********************



Su Iyatu dai zama ya mike a gida, Ladiyo duk ta damu kullum tana gidan su Iyatu suna tare saboda sabon da sukayi.

Ita kuwa Iyatu ko ajikin ta cewa ma tayi ya bata takardar ta ai ba Mijin aure zata rasaba idan ya saketa.


Ranar su Liman sunsha dariya yadda Mai Gari yayi tsayuwar Y'an dambe ya nad'e hannunshi da rawaninsa yacewa Iyatu su fidda reni idan ta kadashi to zai bata takardarta.


Itama ta cire mayafinta tayi zukiya dashi taja da baya tana mika hannu gaba irin dai na Y'an dambe idan za'a buga.


Liman da Galadima da sukaga tashin hankalin ba mai k'arewa bane sai sukayi sama da Mai Gari suka daukeshi daga bakin k'ofar gidan.


Iyatu tace" D'an renin hankali ni zaka renawa hankali kana wulak'antani a gaban mutane ni ba Ladiyo bace.

Idan ka takurani sai na lallasa ka kamar gayan fura a tirmi.


Yo ni har a nunamin dambe filin wasan ne kawai ban shiga ba.


Haka tayi ta masifarta ta gaji tukun ta dawo gida.

Ladiyo da taji labari tazo ta ringa yiwa Iyatu fad'a tace mata akan me zataje suyi fad'a da Mai Gari, su da sukeso a sasanta su dawo gidansu, amma sai ta bige da fad'a.


Iyatu tace" Ke nifa karr tasan karr ce nida Mai Gari dan haka dole ma ya maidamu.


Haka sukayi ta hirar su Ladiyo na lallab'a Iyatu sai wajan la'asar tukun ta dawo gida.

************************


Liman da kanshi ya dauki waya ya kiran Baban TANI ya fad'a mana komai.


Cikin damuwa Daddy yace" Kash wallahi Mai Gari da Iyatu sai Addu'a dan Allah yanzu ko kunya ma basuji ba suke dambe.


Shiyasa ai su TANI sukayo gadonsu.


Liman yace" Gaskiya dai muna ganin abubuwa, kawai yanzu gobe kazo saika maidosu nasan inkai ka fad'i magana to bazai tsallake ba.


Daddy yace" To Insha Allah Baba zanzo dama gobe zanje daukar su TANI zasuzo mana hutu, to kaga sai naje gaba d'aya tare da Ya'u zamuje.


Liman yace" Yauwa Yaron kirki Allah ya muku albarka ka gaishe min da Rahama.


Murmishi Daddy yayi yace" To Baba muna godiya da Addu'a zan fad'a mata.


Liman yace" To shikenan tukun sukayi Sallama.

************************


Yau TANI ce zatayi girki tinda la'asar ta bankawa tukunyar tuwo wuta sai murna take yau ita zatayi girki a gidansu.


MANU ne dan iza wuta ita kuma Furera Y'ar tankad'e garin masara fara, Bintalo kuma Y'ar wanke-wanke idan an b'ata kwanuka, Goga kuma dan share gida, kowa da aikinsa.


Suna aiki ana hira sai murna suke yau dai za'ayi girki ba kowa a gidan sai Mai Gari.

Mai Gari na gefe yana saka musu albarka sai cewa yake Yaran kirki yau zanci girkin ku.

TANI kam itace Uwa sai wani Iyayi take ita gata shugaba a gida.


Ruwan tuwon na tafasa TANI ta dauko d'an gari kad'an ta zuba mishi ruwa tajuya tukun ta rage ruwan tukunyar a wata k'aramar tukunyar.


Kad'an ta bari tukun ta zuba garin data zubawa ruwa.

Jijjuwa tayi tukun ta rufe ta koma gefe.


Bayan kamar minti uku haka ta dauko garin ta afka a cikin tukunyar ta saka muciya ta soma tukawa.


Bintalo ta had'a wata wutar ta daura miya.


Tuwan yayi guda-guda na gari saboda karfin TANI bai kai ta tuka tuwan nan ba.

Haka dai ta ringa tukawa inta gaji ta bawa MANU shima inya gaji ya baya Furera.


Mai Gari da yaga sun kasa k'arewa sai ya cire rigarshi babbar ya cire rawaninsa ya aje a gefe.

Amsar muciyar yayi ya soma tuk'awa yana fad'in" Haka akeyi ba waje d'aya ake juyawa ba.


Haka akayi ta kama-kama sune har wajan magariba basu gama tukun tuwon ba sai zufa sukeyi, Goga kuma na k'ara gwala wuta.


Bintalo tayi miya ta gama, jin ana kiran salla sai aka ce angama tuka tuwon.

Mai gari yaja su MANU suka tafi sallah.


Tuwon ta kwashe itama ta tafi yin salla.


Bayan sallar isha"i aka zubo abincin.

Komar farko da Mai gari ya kai ya tauna magi irin Rego d'in nan gudanshi ko narkewa baiyiba.

Zubarwa yayi ya dauko wata lomar yaji d'aci, hak'ura yayi ya had'iye yana rike wuya.


Su kam su TANI ba ruwansu cin kayansu suke tuwon sai k'aurin wuta yake, miyar sai shegen gishiri da magi , amma saboda tsoro haka suke cin kayansu saboda TANI ta tsare kowa tace sai kowa ya cinye wanda aka zuba mishi.


Haka sukeci suna zare idanu saboda gishirin rau ya kama baki.


Suna gamawa Mai Gari ya kwasa a guje ya shiga bandaki ya ringa amayar da abinda yaci, idan yace ohh amai ya tafo, sai ya saki tusa daga baya, saida ya amayar da komai tukun ya wanke bakinsa ya fito yana numfarfashi.


Suma Bayan sun gama aka wanke kwanuka,, kowa saida ya amayar da tuwon dayaci amma banda TANI DA MANU.

Suna gamawa suka tafi yawo dandali.

************************


Washe gari sai ga su Daddy sunzo sawa sukayi aka kira su Iyatu sukazo.


Daddy yace" Dan Allah Mai Gari ka dawo dasu gida mu kanmu bana jin dad'in gidan ba kowa kuma kaga Yaran nan bazasu iya abinci da kansu ba.


Mai Gari yace" Kai Alkur'an Yaron nan baka da hankali wannan mugayen zan maido.

Ai ko zasu dawo sai sunyi shekara a gidansu.


Daddy yayi murmishi yace" Haba Mai Gari hak'uri zakayi ka dawo dasu.


TANI ta fasa kuka tace" Nidai Mai Gari ka dawo mana da su Iyatu gida Bama jin dad'in zama mu kadai.


Iyatu tayi tsalle ta dire tace" Kai d'in banza harka isa ka wulak'anta mu, to ka sakemu ka gani mana ko yanzu sai mu samu Mijin aure wanda yafika komai.


Mai Gari ya taso daga zaman da yayi yace" Kut ni kika zaga yau in ban k'arya miki k'afa ba to kice ba Usman ya haifeni ba, ko kuma kice ba sunana Ibrahim ba.

Kai ku share mana waje yau saina miki filla'filla a wajan nan.


Iyatu ma ta tashi tace" Idan baka k'aryani ba bakaci sunanka Ibrahim ba aikin banza ni zan....





_*Idan kin karanta ki daure kiyi comments da sharhi sister ko share 🤝🏻*_



_Taku har kallum Maman Nusaiba ce_