Shafi na tara
_*🌻TANI DA MANU 🌻*_
_(Labarin TANI DA MANU jikokin mai gari hatsabiban yara masu bada nishad'i soyayya da kuma zallar dariya domin nishad'in ku masoyana)_
LABARI DA TSARAWA
_*SARAT ALK'ASUM ( MAMAN NUSAIBA CE)*_
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
بسم الله الرحمن الرحيم
1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣
Su TANI a hanya sai surutu sukeyi duk suncika motar da ihun maganarsu.
TANI tace" Daddy idan mukaje zaka hana su Yaya Ibrahim su dakemu ko?
Murmishi Daddy yayi yace" Insha Allah zan fad'a musu bazasu dakeku ba ko sau d'aya, ai Mai Gari zai zanesu idan suka tab'a ku.
Kuma nima zan zanesu karku kulasu idan kukaje tinda basa son ganinku.
TANI tace" To Daddy ina sonka dayawa.
Kanta ya shafa yace" Nima ina sonki Amaryar Mai Gari.
Dariya sukayi gabaki dayansu.
MANU yace" kambun Iyatu mai furfura a kai.
Yo Daddy taya ma ta zama Amaryar Mai Gari?
Shi Mai garin ai yace mana idan muka zama manya narka-narka kamar su Yaya Ibrahim zai mana gidanmu nida TANI.
Kuma yace wai zai siya mana kujeru irin na Umman birni ko TANI" Ya fad'a yana kallan TANI data had'a rai.
Jin Daddy yace mata Amaryar Mai Gari.
Turo baki gaba tayi tana mitsitsika ido tace" Uhmm Daddy nidai yassen bazan auri Mai Gari.
Yanzu ka tab'a ganin inda D'iya ta auri Ubanta?
To nidai Alkur'an da sake ato inba haka ba zan kama MANU mu koma gida" Ta fad'a tana k'ok'arin bud'e motar.
Da sauri Baba ya saka key ganin da gaske fa TANI budewa zatayi su fad'o suji ciwo.
Su shiga uku a wajan Mai Gari.
Daddy yayi saurin fad'in haba TANI wasa fa nake miki, ai ke ta MANU ce shima nakine.
Yi hak'uri karki sakamu a tsaka mai wuya.
Dawowa tayi ta zauna tana hura hanci sama tace" To nidai banaso kai yanzu in na cemaka Angon Umma zakaji dad'i ne?
Ai kaga kaima ita ta haifeka mu kuma Iyatu da Mai gari suka haifemu.
Kuma Daddy shekararka nawa da fitowa daga cikin Umma?
Kaima Baba ai mommy ce ta haifaka ko? Ta fad'a da iya gaskiyarta.
Ita a tunaninta su Umma suka haifesu.
Baba dariya yake harda buga sitiyarin motar.
Yace" Kai yaran nan wallahi idan mutum yana da hawan jini to kune maganin warakarsa.
Daddy ya tsayar da dariyarsa da k'yar yace" Wallahi Ya'u yaran nan sai Addu'a kaji fa k'arfi da yaji sun kwace mana Iyaye.
TANI tace" To Daddy waye yake da hawan jinin a cikinku?
Naji Mai Gari yace wai idan mutum yana da hawan jini to yake jik'a tsamiya da sugar yana sha.
Kuma da dare yake yin turare da ganyan maina.
Kasan hawan jini mayu suke sawa mutum idan suka shigesa.
To mudai mayu basu kama mu ba muna nan rass da mu tass muke kwass damu d'ass wallahi in gaya maka Daddy.
Amma Daddy kaima kayi abinda Mai Gari yace kaga saika samu lafiya.
Saboda kar Ummanka tarasa k'atoto kamar kai da Baba.
Daddy daya rike ciki yace" To TANI dan Allah kiyi shuru zaki saka muyi accident wallahi.
MANU yayi caraf ya amshe zancen da cewa.
Tab lalle ma Daddy to saboda me zamuyi shuru haka kawai.
TANI tace" Rass muke ba ciwo kai ba bana k'afa ba.
Haka kawai ace baza muyi magana ba.
Allah ya yaga mana baki a hanamu yin magana, to Alkur'an da sake ato" Ta fad'a tana daura k'afafuwanta a kan MANU, shi kuma yana matsa mata.
Baba shuru yayi cen k'asa da murya yayi yace" Dan Allah Yaya Sa'id muyi shuru Yaran nan bazasu kyale ba shiyasa nakeson zama dasu.
Yanzu tinda kaji suna magana a hankali k'ila ita mai bakin aku d'in bacci zatayi.
Daddy yace" Gaskiya dan na lura Yaran nan kila aljannu garesu masu sakasu zaro magana.
Kuma maganar ma bakai ba k'afa.
TANI DA MANU sai hira suke k'asa k'asa.
Cen sai bacci yayi gaba da ita.
Shima MANU yana yiwa su Daddy surutu yayi bacci.
Ajiyar zuciya Baba ya sauke yace" Kut har motar tayi dad'i.
Yaran nan ai bazaka je wajan taro dasu ba sai su baka kunya.
Daddy yace" Ina ai harkarsu sai Addu'a kawai.
************************
Aminu ne ya k'araso gidan su Umma a harabar gidan ya zauna yana jiran zuwa su TANI.
Khadija itama ta zauna tanaso yau taga MANU, saboda ita duk a Y'an Uwanta tafi sonshi fiye da sauran.
Su Ibrahim ne suka fito waje ganin Aminu sai wani shan k'amshi yakeyi sai suka tsaya.
Khalifa yace" To harda su kaza acin dank'o.
Su Khadija yau kece a gidan mu Lalle ma.
Murmishi tayi tana dariya tace" Eh nice ai munzo tarbar su Yaya MANU ne.
Dariya Khalifa yayi yace" Eh ba shakka ga kuma Oga a gefe kai wannan abu yayi kyau.
Aminu yace" Ke rabu da su suma suna son zuwansu kawai iskanci ne yasa suke basarwa.
Khadija zata sake magana suka ji hon na mota.
Da sauri Aminu ya mike yace" Gasu Takwara sunzo.
Murna Khadija take tace" Waiyo ga Yaya MANU sunzo yau muna da manyan baki.
Bude musu Get d'in akayi suka shigo.
Daddy ya juya yace" TANI ku tashi munzo ga Yan Uwanku nan na jiranku.
Da sauri TANI ta tashi daga jikin MANU ta zaro.
Tace" La Daddy munzo ashe, MANU tashi budemin jakarmu na dauko kayan kwalliyata.
Daddy ya rike baki yace" Kayan kwalliya kuma TANI me zakiyi dasu yanzu kuma.
TANI ta yage baki zasa kuka tace" To nidai yaseen sai nayi kwalli haka kawai dan su Khadija su renani.
Baba yayi saurin fad'in" To yi shuru maza kiyi abinki Y'ar kirki.
Bud'e jikar tayi ta dauko madubi da kwalli da janbaki bak'i.
Jagira tayi ta saka kwalli a ido.
Janbakinta ta yab'a a baki yayi bak'i, tukun ta goga fauda a fuskar.
Duk da kwalliyar ta shirme ce amma saida tayi kyau sosai.
Kallon Daddy tayi tace" To Daddy nayi kyau?
Daddy yace" Na bugawa a jarida ma kuwa maida su mu fita.
To tace tana k'ok'arin maida kayanta.
Shi dai Aminu ya k'agu yaga su TANI sun fito.
Khalifa yace" Kaga har wani mazari yake kamar zaiga sarauniyar kyau ta duniya.
Aminu yace" Ba ruwanka malam ka kyaleni ka gane.
Fitowa Daddy yayi Baba shima ya fito.
Bude musu k'ofar sukayi suma suka fito.
Murmishi TANI tayiwa Aminu dake binta da kallo mai wuyar fasaarawa.
Kama hannun MANU tayi shi kuma ya dauko ghana masgo d'in su suka nufosu.
Khalifa yace" A'a Oyoyo ga jikokin mai gari.
Iyee lalle kun girma masha Allah.
Dariya TANI tayi bata ce komai ba taji dad'i da Khalifa ya taresu.
Ibrahim ma Murmishi ya sakarwa K'annan nashi yace" Welcome to home my sister and brother.
B'ata fuska TANI tayi tace" To Alkur'an karka kuskura ka zagemu dan munsan turanci ehhe" Ta fad'a tana watsa mishi daradaran fararen idanuwanta.
Murmishi yayi yace" Allah ya baku Hak'uri ke TANI dama kinfi MANU masifa.
Kyaleshi tayi bata kulashi ba.
Aminu shi kam kamar ya dauke TANI yakeji ganin yadda ta kara girma kyanta na kara bayyana.
Hannu ya bude musu yace" Oya come here.
Y'ar dariya sukayi TANI ta kwasa a guje tace" saina riga MANU zuwa wajan Yaya Aminu.
Shima MANU da gudu ya bita a baya , saboda Aminu yana dan nesa dasu ne.
Tana zuwa ta shege jikinshi tana dariya da murna.
Shima MANU na zuwa Shima ya shige jikinshi.
Rumgume su yayi yana dariya suma sunayi yace" Oyoyo Yan Uwana.
Kusan tin d'azun nake jiran zuwanku.
Ya su Iyatu ina Mai Gari da su Ladiyo su Bintalo?.
MANU yace" Ai suna nan lafiya lau Yaya bakaga yadda Mai Gari yake kuka ba da zamu tafo.
Dariya Aminu yayi gace" Eh Lalle Mai Gari bayaso ya rabu daku.
TANI tace" Yaya inasonka sosai kai kake sonmu nida MANU na" Ta fad'a tana hararar Ibrahim.
Kiss ya mata a goshi yace" Nima ina sonku Yan K'annanna muje ciki.
Tsayawa TANI tayi tace" Yaya Aminu zaka kaimu wajan wasa ko?
Dariya yayi yace" Sosai ma ai dole na kaiku gobe daga kun tashi zamuje, in Allah ya kaimu.
Tsalle TANI tayi ta d'ane bayan Aminu tace" Aiyiriri Amarya tazo gida ita da Angonta.
MANU yace" A fito Amarya ta sauka lafiya ina iyayen Ango suke ga amana na kawo muku.
Ibrahim duk da shi miskili ne amma saida ya ringa dariya.
Yace" Daddy gaskiya Yaran nan har yanzu basuyi hankali ba.
Kalli fa yadda ta Haye bayan Aminu wai Amarya ta sauka lafiya.
Girgiza kai Daddy yayi yace" Ai Yaran kawai kamar renon aljannu.
Baba yayiwa Daddy sallama ya tafi gida su kuma suka shiga ciki baki d'aya.
************************
Tin kafin su k'araso ihunsu ya isarwa da Umma zuwansu.
Tace" Tofa Manya manya maganin K'anana K'anana an shigo Gari.
Da sallama suka shigo su Aminu suka fara shigowa ciki.
Tsayawa yayi yace" To sauko munzo ga Umma a zaune.
Sakkowa tayi tana dariya tace" Yaya Aminu bayanka akwai dad'in goyo.
Murmishi yayi yace" To shikenan zanke goyonki ai.
MANU yace" Nima zanke goyon TANI, kaga Yaya Aminu ni Babbane ko bazaka iya goyona ba saidai ka goyi TANI.
Aminu yace" Haka ne K'anina kai babbane.
Umma tace" To shikenan kuje kuyi wanka ko.
Mai aikinsu ta kira tazo.
Kallonta tayi tace" Ki kaisu dad'insu da suka saba sauka.
Ki zuba musu ruwan wanka suyi.
Cikin girmamawa tace" To shikenan Hajiya.
Hannun TANI ta kama tace" Zo muje Y'ar gidan Mai Gari, saboda tasan TANI dan ta jima a gidan.
Hannun MANU ta kama tace" muje muyi wanka.
Binta yayi suka tafi.
Har sun kusa baki k'ofa TANI ta dawo da gudu wajan Umma.
Umma tace" Ya dai kika dawo?
TANI tace" Umma bakiga kwalliyata bane, banji kince nayi kyau ba.
Murmishi Umma tayi tace" Kinyi kyau sosai TANI d'in MANU, wannan kwalliya haka ai saimu kasa ganeki dan kyau.
Murna sosai tayi jin an yabeta sai ta koma .
*********************
Umma ta kalli daddy tace" Daddynsu dariyar me kakeyi haka?
Daddy yace" Ai yau munsha nishad'i tin daga k'auye har kusan garin nan muna ta kwansar dariya.
Aminu yace" kai dai bari daddy kana gani fa yanzu ta Haye bayana wai Amarya ta sauka lafiya.
Umma tace" Ai wannan da labari a bakinsu bari dai suyi wanka aci abinci tukun musha labari.
Daddy ya basu labarin abinda suka ringa yi a mota.
Khalifa yace" Wato Daddy nifa Yaran nan inaga basa rasa junnu a jikinsu.
Yara sai kace renon aljannu.
Daddy yace" Babu abinda ya samesu kawai dai yarinta ce, idan sun girma zasu dena.
Hira sukaci gaba da yi.
************************
Su TANI ana kaisu d'aki, Y'ar aikin tace" Yauwa ga kayan da zaku canja.
Kuma na had'a muku ruwan wanka sai kuyi wanka.
MANU yace" Mungode Inna bari muje muyi.
Murmishi ta sakar musu jin sunce mata Inna.
MANU ya fara shiga dan yin wankan.
Saida yayi ta shirme a toilet d'in ya shafa jikin bangon ya kalle kanshi a madubi.
Da yazo wanka ya tara ruwan kumfa ya ringa wasa da shi.
Saida yayi me isarshi tukun ya shiga ciki yayi wankan.
Yana fitowa TANI tace" Amma dai baka wanku ba.
MANU ya b'ata fuska yace" Na wanku mana kije kiyi wankan kema.
To ta fad'a tukun ta dauki zananta a cikin kayansu ta daura ta shiga.
Itama kamar wata sabuwar ganin irin wannan toilet d'in tayi ta yawo yana kallan kanta a madubi.
Tana gama wanka ta fito ta samu MANU zaune bai saka wani kayan ba.
Tace" To kasa kayanka mana.
MANU ya hade fuska yace" Ankonmu zamu saka kinga nan birni ne kar a renamu.
Zama tayi tace" Eh haka ne bari na fiddo mana kawai.
Dinkinsu ta fiddo na shidda da atamfa.
Ita TANI sket din atamfa rigar shadda.
Shi kuma MANU wandon shidda rigar atamfa.
Suna sakawa ta dauko musu cap guda biyu iri daya ita da shi.
Sakawa sukayi.
TANI ta juya gaban cap d'in baya ta maido bayar gaba.
Gashinta ta dauri da zaren data saba daurewa.
Safarta baka tasa har gwiwa tukun ta dauko k'afa cikin takalminta tasa.
Shima MANU cap d'insa a dai-dai ya Sakata.
Shima takalmin ya saka tuka jera suka fito zuwa babban falon,inda ake jiransu.
************************
Tin daga nesa Khalifa ya fara ganinsu, aikuwa ya ringa dariya yana nuna su da hannu.
Umma tace" Kai lafiya kake dariya kamar ka zare?
Daddy ma ya gansu shi kuma ya sadda kanshi kasa yana dariya.
Umma ta juya dan ganin su waye sukewa dariya.
Ganin su TANI itama sai ta kama dariyar.
Su TANI kuwa da sukazo bakin k'ofar falon sai MANU yace suyi tafiyar Yan birni.
Jerawa sukayi idan suka mika k'afa a tare sai su kalli gefe tukun su kuma yin taku d'aya Shima su dan yi sakanni tukun suyi gaba.
TANI idan sukayi taku sai tayi farr da ido wai ita gata Y'ar gayu, shine Khalifa ya gansu.
K'arasowa sukayi falon.
TANI ta d'ane hannu tace" Heyy guys how far.
MANU yace" Fine fine to you my grandfather you are welcome to gidan Maman Daddy, how to day my life, you are single a problem Umman su Daddy.
Ya kuma cewa" Yaya Aminu welcome to gidan Umman su Daddy, this is a beautiful girl friend.
Juyawa yayi wajan TANI da take tsallen murna sun iya turanci.
Tace" Yes yes yes yes my name Sweetie and zuwa gidan Umman su Daddy.
My home my sister my phone number a little problem.
Tafawa sukayi a tare tukun suka rumgume juna.
Khadija birgima take tana dariya sai cewa take.
Waiyo Allah cikina Daddy dan Allah kace turancin nasu ya isa haka.
Umma kuwa baya tayi zata fad'i tana dariya tace" Oh ni Rahama yaran nan sun karo wulak'anci.
Aminu kuwa rumgume juna suka su uku suna dariya harda hawaye.
TANI tace" Umman su Daddy I love you too and market.
Umma ta daure tace" To muna godiya da wannan batu ku zauna muci abinci.
MANU yace" where is Hassana a Usaina I kewarsu nake ji so much.
Daddy ya tashi yace" Wannan lamari yafi karfina.
Hannun TANI ya kama yace" Kuzo muci abinci kunga an kusa salla.
Bin daddy sukayi suma su Aminu suka nufi kan dinning d'in.
Suna zama aka zuba musu abinci daddy yace" Bismillah .
Har TANI zata kai baki MANU ya rike hannunta yace" D'an waken langar Iyatu mai furfira a ka.
Ajewa tayi tace" Mai Gari mai rigar Yan gayu ya face majina ba tisho ya saki tusa gari ba manya.
Babbar rigar mai gari nabi takanta na yaga.
Soyayyan dankalin Ladiyo nayi arangama na take.
Tafiyar Iyatu nayi gudu na dauka.
Rawanin Mai gari na dauka na wanke.
Iyatu gidan masifa na mata daurin goro irin Malam Saminu mai saida taba da goro a dandali.
MANU na goyaka a bayana muntafi tamkin k'auna.
Furzar da abincin da daddy ya kai bakinsa yayi yana tari yace" Rahama ki kaimin abincin nan d'aki.
Wallahi yaran nan kasheni zasuyi da dariya.
Umma da suke dariya ta mike da k'yar tace" To zan kai maka.
TANI tace" Bismillah zamu fara alwalar mak'oshi.
MANU yace" Ashe tuwo ashe tuwo sarki ne, miya Galadimace mak'agaro makwarari tinbi k'ofar fad'a.
*Idan kin karanta ki daure kiyi comments da sharhi sister ko share🤝🏻*
*Nima na tafi naci abinci na🏃🏼♀️🏃🏼♀️😂😂😂*
_Taku har kallum Maman Nusaiba ce